← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 162

Sashe 82

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ubandoma ya jinjina kai yace “Shiyasa Giwa Ta janyo ni jiki take amfani dani... Kinsan ance da d’an gari akanci gari... Mahaifina shine Hadimi mafi kusanci ga mahaifin Sarki AbdulJabbar Wato Sarki Mahmuda, Mahaifina yasan tarihin Masarautar nan sosai wanda shima wasu daga nasa Mahaifin ya gada ya sani, nima nawa mahaifin ya sanar dani wasu abubuwa gameda Masarautar har kawo lokacinda aka had’a baki dasu tsautsayi ya auka masa yaci amanar masarauta aka kawosu wannan fursunan da kikaga na San da ita... Giwa Tasan inada masaniya sosai gameda Masarautar nan shiyasa batai wasa da tarayyarmu ba... Babu wanda ya kaini sanin cikin Masarautar nan wannan dalili yasa idan Mahaukaciya Izzatu ta b’ace cikin Masarauta ta shiga wani sak’on babu mai iya zak’ulota sai ni...!”
Ubandoma yaci gaba da fad’in “Kar na shiga miki wani labari daban kinji dalilin...!”

Muhibbah ta kuma jinjina kai a daidai sanda suka shige wata k’ofa wanda itama ba lallai ka fahimci k’ofa bace idan ba kanada masaniya ba.... Haka sukaita ture gidan gizo gizo suna kutsawa alamun an jima ba’a non wannan hanyar....

Tafiya mai d’an tsawo sukai kana suka fita daga cikin Masarautar...
Ubandoma yace “Alhamdulillah mun fita daga cikin Masarauta... Shin zaki iya gane hanyar komawa..?!”

Muhibbah tai shiru tamkar mai nazari sai kuma tace “Idan ban gane ba sai na bi ta Sabon titi na shiga ta babban k’ofa wanda kowa ya San da ita...!”

Ya jinjina kai yace “Hakan yayi dan kar wani ma ya zargeki, nasan watak’ila Giwa ta soma nemanmu cikin Masarautar....!”

“Toh yanzu Baba wa zai kaiku tashar mota...?!” Ta tambaya tana dubansa...

Ubandoma yai shiru yana dubanta cikeda kulawa, wasu abubuwa suna zuwa kwanyarsa... “Amma yarinya kafin mu d’auki hanya ina son sanin wacece Ke...?!” Tambayar da yai mata kenan yana mai tsareta da idanu...

Ta d’ago idanunta masu cikeda rauni wannan karon jin irin tambayar da yai mata... Kafin ta kaikaga basa amsa ya d’ago ‘yar yatsarsa guda yana nunata... Lokaci guda yake furta “Tabbas kece... Kece SAUDATU... Yarinyar da matsafan Giwa suka bata tabbacin cewa K’addarar wannan masarauta na tafe da tata k’addarar... Tabbas kece yarinyar da Gimbiya Turai take nema... Kece silan aje Mahaukaciya Izzatu da Turai tayi... Bansan labarinki ba yarinya amma Rayuwarki na cikin had’ari Babba a wannan masarauta, mai ya dawo dake yarinya..?!”

Muhibbah ta share hawayen da suka gangaro mata kana tace “Kaman yanda kace Baba, da izinin Allah ni ce nan zan kawo k’arshen mulkin zalunci da Turai ta d’aura Masarautar nan bisa wannan kad’ai ya isa dalilin da zaisa na dawo... Karka damu Baba, Allah bazai bata nasara ba wannan karon... In sha Allahu bazata kuma cutar da wani wanda baiji ba bai gani ba...!”

Ubandoma ya jinjina kai yace “Tinda kikace Allah kin gama magana... Wanda duk yakeda Allah shi yake da babban makami da kariya a tattare da shi... Allah Ubangiji ya tsareki ya kareki ya kuma dafa miki...!”

Ta amsa da “Ameen Baba, kuma kuyi sauri ku d’auki hanya kafin wani abin ya faru...!”

Ta maidoda dubantaga Izzatu wacce ta kasa janye idanunta daga barin dubanta, ta tako har gabanta a hankali kana Ta kamo hannayenta ta rik’e cikin nata, saida ta sakar mata murmushi mai kyau kana tace “Kin tsira da izinin Allah... Babu wanda zai kuma azabtar dake...Ku tafi cikin aminci da kariyar Ubangiji..!”

Mahaukaciyar ta sakar mata murmushi itama kana tasa hannu ta shafi Fuskar Muhibbah, tai wani magana da bazaka iya fahimta ba sabida rashin wadataccen harshe cikin bakinta....

Ubandoma ya dubi Izzatu yai mata alama da hannu kan cewa su tafi kada a cimmasu.... Ta kuma duban Muhibbah kana ta k’araso ta rungumeta sosai cikin jikinta... Hawaye suka gangaro wa Muhibbah da k’yar suka raba jikinsu itada Izzatu ko damunta daud’an jikin matar baiyi ba...

Bata bar wajensa saida ta tabbata sunyi nesa da Masarautar kana Ta juyo tana k’arewa Masarautar kallo daga nan yanda take tsaye....
Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana tasa kai ta soma tafiya ta bayan Fada dan bazata iya komawa Ta hanyar da Ubandoma yabi dasu ba...

Ta k’ofar bayi ta b’ulla hakan yasa kawai tabi wannan k’ofar ta shige cikin Masarautar Allah yasa dama tun shigowarta Kuyanga guda ta amshi jakan kayanta ta kai mata masauk’i...

Kai tsaye sashen Giwa ta nufa b’angaren su Umaima da Zahra...

Nan ta tadda Zahra na sharb’an kuka Umaima na bata baki..Tsaye tayi tana sauraren abinda Zharan Ke fad’i “Wllhi Anty Umaima na tsane matar nan na tsaneta Ta ya Paa zaice zai aureta... Of all mata ya rasa wacce zai d’auko sai wannan matar... Wllhi ban sonta kuma bazan tab’a sonta ba....!”

Umaima ta dafata tace “Zahra Raheema batada matsala kece dai baki sonta, Aminiyar Aunty Zuhra ce fah kuma kiga yanda kowa yake yabon kirkin Aunty Zuhra cikin Masarauta nan... Ki kwantar da hankalinki kiyi addu’an Allah yasa haka shine mana alkhairi gaba d’aya..!”

Galala Zahra Ke dubanta kana ta kuma goge hawayenta tace “Ni nasan yanzu Paa bai sona bai damu da abinda nake so da wanda bana so ba, yanayin haka ne kawai dan ya k’untata min sabida ya daina sona, He’s changed now, and he’s becoming more violent har marina yayi abinda bai tab’ayi ba a baya, he really is hiding something from me...But if not for that maiyasa zaice zai auri matar nan all of the sudden..!”

Umaima ta nusa tace “Zahra neman izinin auren suka tafi ba auren ba, watak’ila ya sauya ra’ayi idan har baki sonsa da ita...!”

Ji tai bakinta ya bud’e tana furta “Rankaidad’e ne ya tafi neman izinin aure..?!”

A tare suka juyo suna dubanta, Zahra ta tafi da gudu ta rungumeta “Tiaaa..! I’m glad you’re finally back, you’ve no idea how badly I need you right now... You’re the only one who understands me after all..!” Tai maganan tana mai tab’e baki har lokacin bata saki Muhibbah ba...

Muhibbah ta k’ak’aro murmushi tace “I’m here now... Tell me meke faruwa... Naji kuna maganan saka Rana....!” Tai maganar cikin yanayi na yak’e...

Zhara baki ture tace “Can you believe my Pa, ya tafi neman auren wannan witch d’in... Wai aurenta zai very soon..!”

Umaima ta katseta da fad’in “Ba da wannan zamu fara ba, da gaisuwa ya kamata mu fara kafin komai ya biyo baya...” Ta dubi Muhibbah tace”Sorry Zahra ta tareki da zance babu ko gaisuwa balle sannu da zuwa..”

Murmushin da yafi kama yak’e ta kumayi kana tace “No is alright, after all ni na tambaya...Ya kuke...? How are things here...?!”

Tai maganar tana mai janyo hannun Zahra suka zauna saman couch...

Zahra tace “Um ba wani abu mai dad’i da ya auku a nan tinda kika tafi... Koda yake akwai abu mai dad’i guda d’aya... An sallami Uncle Jamal daga asibiti... And guess what..!” Ta k’arashe tana duban Umaima cikeda zolaya taci gaba da fad’in “Anty Umaima said yes to him... They’re getting married anytime soon... At least auren da mukeso ba irin na Paa da wancan witch d’in ba..!” Ta k’arashe tana kashewa Umaima idanu, itakaw Umaimar sai k’ok’arin toshe bakin Zhara take su duka biyun suna dariya...

Gaban Muhibbah ya kuma yankewa dan tasan sam Umaima bata dace da Jamal ba, ita d’in mutumiyar kirkice shi kuwa akasin haka, kaman yanda Mahmood bai dace da Raheema ba, shid’in mutumin kirki ne itakaw akasin haka....

Zahra taci gaba da zolayan Umaima, Umaimar na kuma janyota tana toshe bakinta tana fad’in zata had’ata da Uncle d’inta... Sai dariya suke cikeda nishadi yayinda Muhibbah tai nisa duniyar tunani... Ta yaya zata hana yuwar wad’annan auratayya...? Kaman daga sama ta sinkayo Umaima na fad’in “Hibbah sorry bamu tambayi jikin Mommy ba, kuma tinda kika tafi baki had’amu a waya ba, shi Dr kam ma ban samun layinsa...”

Jiki a sanyaye Muhibbah ta murmusa tace “Jikinta da sauk’i sosai shisa na dawo....!”

Sukai mata addu’a gaba d’aya Muhibbar tana amsawa da Ameen cikin tsananin sanyin jiki...

Gajeren hira sukai Muhibbah tace zata masauk’i ta d’an huta gajjiya...

Zahra tace zata shigo anjima kafin la’asar... Da kai kurum ta amsa mata amma ta kasa aminta da abinda taji...Wai Rankaidad’e zai auri wannan Trap d’in wacce Ta gama watsewarta da wancan watsattsen k’anin nasa... Inaa no she can’t allow him to fall into her trap, but ta ya zatayi haka... Ta yaya zata bud’e idon Rankaidad’e ya gane wanan matar ba k’aunarsa take ba..? In fact su biyu d’’in duniyarsu Ta banbanta....! Amsar data kasa nemowa... Alolan sallan la’asar tai kana Ta d’an kishingid’a saman gado idanunta na kallon sama, sai faman sak’e sak’e take cikin zuciyarta... Allah ya gani ta k’agu taga ya dawo Masarautar yace ya fasa auran Raheemah ko hankalinta zai kwanta...
Tana nan a haka bacci yayi gaba da ita....

**

Wane irin k’aik’ayi ne na bala’i ya addabeta lokaci guda, ga b’arin kanta yanda sumar suka k’one sunayi ga kuma hannunta k’onanne da shima ya addabeta da k’aik’ayin.... K’aik’ayi ne mai fidda hayak’i wanda ba kowa Ke iya ganin hayak’in ba face ita da abin Ke jikinta.... Tun tana Susa a cikin kallabi hardai Ta cire kallabin tayi wurgi dashi.... A baya susa ba girmanta bane a matsayinta na mai jida mulki da izza sai gashi yanzu Susa na nema ya zama babban d’abi’arta.... Ko dan sabida yawan k’aik’ayi dake addabanta bata fita fadarta cikin mutane.... Yau d’inma a d’aki suke itada Jakadiya taketa faman soshe soshen, k’arshe ta umarci Jakadiya ta sosa mata kanta ita taji da hannunta....
Abin yayiwa Jakadiya banbarak’wai Giwa da susa babuji babu gani....

Jakadiya tace “Allah shi taimakeki Susa ba girmanki bane.... Anya wannan k’aik’ayi naki ba ture bane... Kodai asibiti za’a tafi....!”
Chapter 82 · 0% Book details