← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 162

Sashe 43

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta kuma murmusawa kad’an kana tace “Gida na sarauta Rankashi dad’e sai anayi ana taka tsantsan kasan abin magana baya kad’an a gida irin naku, ni kuma bazanso naga abinda zai b’ata maka suna da martabarka ba dukda cewa ba abu maras kyau mukeyi ba...but nasan da yawa bazasu fahimcemu ba only few can understand...!” Ta k’arashe cikeda k’issa...

Fu’ad ya jinjina kai yana mai amintada kalamanta yake fad’in “K’warai kuwa kinyi gaskiya Gimbiyata... Abun magana baya kad’an a wannan gida namu... Ni d’in shaida ne, kuma bazanso na zamto silan da zaisa ki bar Masarautar nan ba...Zanyi hak’uri naci gaba da ganinki a makaranta har zuwa lokacinda zaki amince mu bayyana soyayarmu ga kowa a cikin Masarautar nan....!”

Rausayar da idanu tai cikeda k’osawa Dan Allah na gani kan sole take waya da Fu’ad, jin muryarsa da kalamansa take tamkar garwashin wuta cikin kunnuwarta... Lokaci guda ta saki murmushin dole da k’yar kana tace “So Ya kuka sami mai jiki....?”

Fu’ad yace “Toh gashi nan dai bazamuce babu sauk’iba.. An godewa Allah... But yanda mukaga jikin Baba Wambai da alama ya d’aga hankalin Yaya Dan koda muka dawo tuni ya nufi sashensa, dik yanda yake k’ok’arin b’oye tashin hankalinsa hakan taci tura saida fuskarsa ya nuna... Tinda naji yayi kiran Jakadiya nasan hankalinsa a matuk’ar tashe yake... Yayana ya fuskanci rashi da dama a rayuwarsa ga mahaifinmu ga kuma matarsa shisa yakega kaman zai kuma rasa Baba Wambai ne...!” Ya k’arashe cikeda kulawa...

Muhibbah Ta mik’e daga zaunen da take cikin sauri Dan tinda taji Fu’ad yace Mahmood yayi kiran Jakadiya jikinta ya bata wani abin Ke faruwa, ya zama dole tasan yanda zatai ta shiga sashen Mahmood danjin abinda zai tattauna da Jakadiya....
Suna ida waya da Fu’ad ta mik’e tai shirinta tsaf kana ta nufi sashen Mahmood a sace...

Tana mak’ale jikin gini ta hango Jakadiya ta nufi sashen Yarima Mahmood Gimbiya Raheema na biye bayanta...

Muhibbah ta murmusa a hankali tana mai ayyanawa dama jikinta ya bata sauyawan Mahmood da Fu’ad yace nada babban dalili... Suna shigewa ta sad’ad’o a hankali, daidai lokacinda Jakadiya ke magana da Dogarai masu tsaron k’ofa hakan ya bata daman shigewa cikin sand’a ba tareda sunyi noticing d’inta ba...

SameenaAleeyou*MUHIBBAH*

*029*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Tsaye ta hangosa yana fuskantar window ya baiwa parlorn baya, k’irjin Raheema yaci gaba da dukan tara tara... Harga Allah batasan mai zatace ba, batasan da wata kalma zata soma kare kanta gaban Yarima Mahmood ba, ganin har Ta ida shigowa cikin parlorn tai tsaye bai juyo ba bai kuma tankata ba abin ya kuma tada mata hankali... Ta soma k’ok’arin had’o kalamai saman harshenta da nufin gaidashi.. Har lokacin baice da ita komai ba bai kuma juyo ba...

Itadai Muhibbah na rakub’e daga gefe tana kallon ikon Allah... Saida suka kwashe dak’ik’ai a haka kana Mahmood ya juyo har lokacin hannayensa hard’e ta baya... Ba Raheema dake tsaye cikin parlorn ba harta Muhibbah saida yanayin fuskar Mahmood ya bata tsoro... Zatace bata tab’a ganin tsananin b’acin rai kwance saman fuskarsa kaman yanda Ta gani yau ba....

Raheema kaw rawa jikinta ya d’auka gaba d’aya sai ta tsure gani take tamkar yasan alak’ar dake tsakaninta da d’an uwansa Yazeed ne... Ta had’iyi miyau d’in da ya tsaya mata a mak’ogoro da k’yar...

Kujera yai mata nuni murya a dake ya furta “Zauna...!”

Jiki a matuk’ar sanyaye ta isa ta zauna kaman yanda yace.. Lokaci guda shima ya tako ya zauna a kujera guda...

Dak’ik’ai suka kuma shud’ewa a haka kaman babu mai cewa komai cikinsu har saida Raheema Ta d’an d’ago ta saci kallonsa, tai saurin maida kanta k’asa zuciyarta naci gaba da tsinkewa... Hardai Muhibbah ta sadakar Bawan Allahn nan bazaice komai ba sai kuma ta sinkayo muryarsa mai amo kama daga sama yana furta “Maiyasa kika aikat..Why..?!!” Yai tambayar yana mai tsare Raheema da idanu...

Raheema taci gaba da k’ok’arin had’o kalamai saman harshenta “Your Highness... Wllhi Allah ni dama kawai I wanted to help ne...Allah wllhi ni taimakonka nake son y.....!”

Katseta yai da fad’in “Na tab’a neman taimakonki..?!”
Tai saurin girgiza kai alamun a’a...
“Na tambayeki ki taimaka min...?!”
Nanma girgiza kai tai alamun a’a...
“Namiki kamada mabuk’acin taimako daga wajenki..?!”
Izuwa lokacin Hawaye sun soma wanke fuskar Raheema tai saurin girgiza masa kai tana mai furta “Dan Allah Your Highness kai hak’uri... Na sani na shiga hurumin da ba nawa ba but in sha Allah bazan sake ba... Dan Allah kai hak’uri ka yafe min...!”

Mahmood yai mata K’uri yana karantarta kana ya kumayin gyaran murya kad’an yace “Kinsan hukuncin abinda kika aikata a dokan Masarautar nan...?!”

Tai saurin d’agowa a zabure tana dubanta zuciyarta naci gaba da tsinkewa....Lokaci guda taci gaba da girgiza kai had’ida had’a hannayenta biyu waje guda “Rankaidad’e dan Allah kai hak’uri... Dan Allah kada ka sallameni daga Masarautar nan... Dan Allah kada ka bari a maidani Masarautar mu... Wllhi ina matuk’ar k’aunarka Yarima... Bazan rayuwa babu kai ba....!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin sabon kuka....

Yai mata k’uri yana dubanta cikin yanayin zamansa irinta masu mulki ba tareda ya furta mata komai ba... Har saida kukan ya tsagaita dan kansa kana yace “Banikeda alhakin sallamarki daga Masarautar nan ba dan har yanzu ni ba sarki bane... Ita kuma wacce kikasa ai bincike akanta fah...?”

Gaban Muhibbah ya yanke ya fad’i, wacece Raheema tasa abincika mata...? Bata ida tinanin ba ta sinkayo muryar Raheemar tana fad’in “Your Highness wllhi sharrin Juwariyya ne ni ban umarceta tai wani binciken k’wak’waf kan Muhibbah ba... Yarima dan Allah ka yarda dani... Why would I have her investigated... What for..? Wllhi sharri ne kawai irin ta mutanen Fada...!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya mai raunin gaske...

Daidai nan Ubandoma ya shigo parlorn yana mai zubewa k’asa yake fad’in “Ina mai neman afuwan Babban Yariman Masarautar nan da shigowa da nai Kai tsaye...Tuba nake Allah shi baka yawan rai...!”

Mahmood yace “Ina saurarenka Ubandoma meke tafeda kai....?!”

Ubandoma yaci gaba da fad’in “Dama su Galadima Danmadami da Talba da kuma D’anisa harmada Madaki ne sukace ai masu iso wajenka... Gaba d’aya suna haraba suna jiranka Allah shi baka yawan rai...!”

Jinjina kai Mahmood yai kana yace “Ubandoma..!”
Ubandoma ya amsa cikeda ladabi kana Mahmood ya k’arada “A bud’e masu Galadima Babban gwani su shiga ciki Ina nan tafe..!”

Ubandoma ya kuma rusinawa yana mai amsawa had’ida mik’a gaisuwarsa ga Raheema tareda mata kirari kana ya mik’e da azama dan isarda sak’on ubangidansa...

Ubandoma na ficewa Raheema ta kuma kifa kanta tamkar wata mumina tana mai ci gaba da shesshek’an kuka dan kawai Mahmood yaji tausayinta... Tsaye ya mik’e yana mai fuskantar center hannayensa hard’e Ta baya irin tsayuwar da masu mulki suka faye yinta... Lokaci guda ya karkato da fiskarsa yana dubanta kaman zai magana sai kuma yasa kai yai shigewarsa cikin tafiya da tafi kama da sassarfa...
Yana ficewa Raheema Ta d’ago kanta had’ida sakin makirin murmushi, a fili take furta “Sannu a hankali zaka shigo hannuna..!” Ta kuma sakin murmushi kana ta waiga gefe da gefe... Lokaci guda tai azamar mik’ewa tsaye yayinda Muhibbah ta kuma mak’alewa bayan staircase tana hangota sosai...

Cikin azama Raheema ta shiga d’aga alkyabbarta, tai saurin zak’ulo wani garin magani dake d’aure cikin leda bak’a... Ta kwance d’aurin cikin sauri kana ta isa saman kujerar da Mahmood ya faye zama.. Nan ta saki murmushi sannan Ta soma barbad’a garin maganin, haka tabi sauran kujerunma duk ta barbad’a sannan ta yayyafa a bakin k’ofar fita... Tana ida barbad’e barbad’enta ta cusa ledar maganin cikin alkyabbarta kana ta bubbuge hannayenta ta gyara zaman alkyabbarta sosai sannan Ta fice daga sashen zuciyarta nai mata sanyi... Tasan yau dole Aunty Zeenat tai alfahari da ita... Yau dai kam ta cika aiki tasan babu yanda za’ai Mahmood tsallake tarkonsu yau tinda hardai zai shiga sashen dole ya bi ta saman shirinsu sannan hardai zai zauna a parlorn toh fa sai ya zauna akan shirinsu... Daga rana mai kaman ta yau Mahmood ya zamto sai yanda tai dashi a Masarautar....

Raheema na ficewa Muhibbah ta sad’ad’o ta fito tana mamakin abubuwan da taga Raheema ta barbad’a... Ta K’araso cikin parlorn sosai tana ware idanunta ko zataga alamun garin magani amma to her surprise babu ko alamun gari... Bazaka tab’a cewa an zuba wani abu mai kaman gari wajen ba... Tsaye tai tana tinanin abinyi kafin wani ya shigo ya ganta a sashen.. Amma kam tabbas sai tayi yanda tasan ta kawar da abinda idanunta sukaga Raheema ta barbad’a koda ace bata iya ganin abin a zahiri... Waige waige ta soma cikin parlorn nan ta hangi goran ruwa saman dining table, tai saurin k’arasawa Ta d’auko goran ruwan, cikin azama ta warware d’aurin d’ankwalinta ta zuba ruwan ta jik’a d’ankwalinta dashi kana tabi gaba d’aya kujerun Ta gogesu da d’ankwalinta mai damshin ruwa... Haka dik yanda taga Raheema tayi barbad’an a parlorn saida tabi Ta goge tsaf... Harta da bakin k’ofan parlorn saida shima ta goge shi tass... Tana idawa ta Sauk’e huci a hankali kana tai k’ok’arin sad’ad’awa Ta fice daga sashen....
Chapter 43 · 0% Book details