Sashe 71
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Turaki ya dubesa da mamaki “Bauchi fah kace your Highness..!”
“Bazaka iya zuwa bane..?!” Ya tambaya yana duban wani b’angaren..
Turaki yace “A’a ni ban isa nace haka ba Rankaidad’e, Ina Jos ina Bauchi ai ko Borno kace zamu tafi yanzu babu b’ata lokaci balle nan Bauchi..!” Ya k’arashe yana mai janyo jakan kayan Muhibbah...
Ta d’ago tana duban Mahmood kaman zatai magana, kafin tai maganar sai cewa yai cikin dakewar murya “Tashi muje...!” Babu musu ta mik’e tabi bayansa jiki a sanyaye...
SameenaAleeyou📚
[8/15, 9:48 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*46*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Har suka shige Mota Turaki bai daina mamakin Wai da gaske Mahmood yake barin gari zasuyi tsakar safiyar nan, Wai ma Toh wacece wannan yarinyar, ga dukkan alamu sunsan juna itada Prince, kuma ko a wasa bai tab’a kawo masa labarinta... Turaki ya murmusa a hankali yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa saidai ba Mahmood d’in ba, abinda zai baiwa mutane mamaki shi ba komai bane wajensa...
Back seat Ta shige Turaki na driving Mahmood na mazaunin mai zaman banza, yanda ta tak’ure cikin motar zai tabbatar maka har lokacin tsoron abinda ya faru da ita bai fice daga jikinta ba... Ta side mirror yake dubanta zuciyarsa naci gaba da k’una, ya k’udiri niyyan bazai k’yale Yazeed ba da abinda yayi mata, tabbas sai ya koya masa darasi ta yanda nan gaba idan yaga mace ko wata irice zai koyi girmamata, a duniyarsa yak’i jinin yaga ana wulak’anta mace a cewarsa duk namijin da zaici zarafin mace shi d’in ba namiji bane, hasalima bai cancanci a kirasa namiji ba.. Kuma Wai a haka Yazeed yake ikirarin zama Sarki da wannan disgusting halin nasa...! Ya k’arashe tinanin yana mai ci gaba da murza zobban dake hannunsa har lokacin fuskarsa a matak’ar murtuk’e... Lokaci zuwa lokaci Turaki Ke satan duban b’angaren Mahmood d’in amma Ko gizau fuskar nan nasa babu alamun walwala sam.. Sanin halin abokin nasa za’a iya tafiya duk nisan duniyar da za’a tafi baice uffan ba yasa Turaki danna radio d’in motar, ya kamo tashan labarun wasanni dan yafi zaman hakan....
**
Tinda Jamal yaji cewa Umaima na asibitin hankalinsa ya gaza kwanciya, baya fatan ta gansa a halinda yake ciki dama da yakeda cikakkiyar lafiyarsa bata so shi balle yanzu da ya riga ya zama nakasasshe... Ya rintse idanunsa a hankali hawaye na kwaranyo masa... Zahra jiki a mace ta matsa jikin gadon nasa tace “Uncle please ka k’yale Anty Umaima ta shigo ta ganka wllhi ta damu dakai sosai...!”
Jamal ya dubi Zahra da idanunsa masu zuban hawaye, lokaci guda yake girgiza mata kai alamun a’a “No Zahra... Umaima can’t see me like this, dan Allah kice mata ta tafi kawai na gode da gaisuwa...!” Ya k’arashe wasu hawayen na kuma zubo masa...
Zahra ta fuzar da fuci a hankali kana ta kaikaito tana duban Zuhra wacce itama juyin duniyar tayi kan Jamal ya k’yale Umaima ta shigo ta gaishesa amma yak’i amincewa... A hankali Zuhra ta tako gaban gadon nasa, sukai shiru gaba d’aya suna sauraren yanda Jamal Ke kuka mai tsuma zuciya, lokaci guda yake ci gaba da fad’in “Labarin soyayya na ya k’are tun kafin ya fara... Bayan abinda na zama yanzu na tabbata Umaima bazata tab’a sona ba, shikenan burina bazai tab’a cika ba... Mace d’aya k’wal da nake so bazan tab’a kasancewa tareda ita ba... Bazata tab’a yarda ta auri mai nakasa irina ba Zuhra...Shikenan na rasa farin cikina har abada..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya...
Zuhra tasa ‘yar yatsanta ta goge hawayen da ya mak’ale mata cikin ido, ta girgiza kai a hankali tace “Jamal don’t talk like that... Nakasa ba kasawa bace, kuma dukkanmu nan da kake gani babu wanda ya isa yace hakittarsa ya kammala har sai ranan da Allah ya kiramu zuwa gareshi... Jamal, a kowace rana na rayuwarmu sabon shafin rayuwace take bud’ewa kuma Ko wacce tana zuwa ne tareda k’alubalenta da jarabawar data k’unsa... Kowa da kake gani a nan yanada nasa damuwar babu wanda zaice maka rayuwarsa gaba d’aya jin dad’i ne duk dukiyarsa duk lafiyarsa duk mulkinsa... In one way or the other yanada nasa matsalan da yake dealing... Jamal this is the reality now, you just have to accept it, and stop making things harder on you... Ina fata Allah ya baka lafiya ya kuma baka ikon cinye wannan jarabawa da ya jarabceka dashi..!”
Daga Jamal har Zahra shiru sukai suna saurarenta, dagajin yanda take magana zaka fahimci wani damuwa dake kwance cikin zuciyarta take son amowa.... Basu ankare ba sai hango Umaima sukai tana shigowa hawaye na gangarowa saman k’uncinta....
Jamal yana hangota yai saurin kauda fuskarsa hawaye naci gaba da siraro masa lokaci guda yake k’ok’arin janyo bedcover yana kuma rufe gundulumin k’afarsa....
Zuhra na ganin haka ta janyo hannun Zahra suka fice suka basu waje...
D’akin ya rage saura su biyu... Fuskarsa naga wani b’angare yake furta “What are you doing here...Maiyasa kika shigo...? Dan Allah ki fice bana san ganinki, just get out please..!” Ya k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka...
Bata fice d’inba saima kuma matsowa kusansa da tai...Ta lumshe idanunta a hankali hawaye suka ziraro mata, lokaci guda take furta “You can’t avoid me forever Yaya... Maiyasa zaka gujeni bayan kaid’in masoyina ne... Maiyasa bazaka karb’i k’addarar ka ba bayan ansan musulmi mai imani da yarda da k’addara kyakkyawa koko akasinta... Ya Jamal dan Allah kada canjin dake jikinka a halin yanzu yasa ka gujeni kaji... Promise me bazaka gujeni ba..!” Tai maganar cikin rawar murya su duka biyun hawaye na gangaro masu...
Girgiza mata kai take a hankali yana mai furta “You deserve someone better than me Umaima... Tambayar da na miki kwanakin baya bata buk’atan amsa, halinda na tsinci kaina ciki yanzu itace amsar..!”
Ta girgiza kanta da sauri tana mai kuma share hawayen fuskarta take fad’in “Don’t talk like that please... Muyi fatan Allah ya baka lafiya ni kuma na maka alk’awarin bazan tab’a guje maka ba...!”
Yai mata K’uri tsananin soyayyarta na kuma ratsa duk wata k’ofa na zuciyarsa...
Shigowar Dr ne ya sanyasu k’ok’arin saita kansu, Umaima ta fice ta barsu da Dr Jamal sai binta da kallo yake har ta b’acewa ganinsa... Likitan ma saida ya fahimci haka d’in ya kuwa samu abin zolayar Prince Jamal..
**
Tafiyar awanni biyu jal sukai suka shigo garin Bauchi, idanunta naga window abubuwa da dama cikin zuciyarta harma batasan sun kusa shige unguwarsu dake daga farkon shigowa gari ba... Turaki ya d’an waigo kad’an ya dubeta yace “Destination..?”
Tai k’ok’arin saita kanta kana tace “Tambari housing estates..!”
Sai lokacin Mahmood ya kaikaito yana dubanta, Shiko Turaki idanunsa naga kwalta yake fad’in “Aiko mun shige Tambari dan gashi har mun iso Zaranda...!”
Cikin ‘yar daburcewa tace “Laa dan Allah kuyi hak’uri, ban kula bane...!”
Turaki ya murmusa yace “A’a Rankidad’e karki damu ba wani abu bane ai sai muyi U turn, Keda kike tafe da rakiyar Mai Martaba da kansa...!” Kallon da Mahmood ya jefa masa ya hanasa k’arasa zancen nasa...
Ya d’anyi gyaran murya kad’an ya dubi Mahmood d’in yace “Rankaidad’e sannu da hanya..!” Yanda yai maganar dole ya baka dariya amma Mahmood Ko gizau bai dariyar ba, idan da Sabo ya saba da halin Turaki, abokinsa ne amininsa ne kusan tare suka taso,Kakansa Tukari shine Turakin Jos mai rasuwa.. Asalin sunansa kuwa Yusuf ne Yusuf Turaki, tun daga makaranta Turaki yabi bakin mutane dashike family name d’insu ne hakan yasa gaba d’aya sunan nasa ya koma Turaki..
Itada Turaki ne suketa maganarsu yanda take masa kwatancen street d’in nasu har suka iso, shiko mai sarautar tamkar kurma haka ya koma cikin motar, baya um baya umum... Suna isowa Turaki ya bud’e motar, ya fito ya bud’e booth ya ciro jakan kayanta... Fuska d’aukeda murmushi ta gyara zaman mayafinta, ta risina tanaima Turaki godiya...
Turaki ya murmusa yace “A’a Rankidad’e ai ba wani zakiyi godiya ba... Wa Rankaidad’e zakiyi godiya...”
Ta d’ago idanu tana duban Mahmood dake zaune gaban mota shid’inma ita yake duba... Haka kurum taji gabanta yayi mugun fad’uwa, Ji take kaman ya fahimceta ita d’in itace silar tashin hankalin dake tsakaninsa da d’iyarsa.. Gaba d’aya sai taji kaman duk Duniyar kallon mai laifi ake mata...
Kanta a k’asa tace “Na gode Rankaidad’e... Na gode sosai da taimakonku gareni...!”
Ta d’an kuma duban Turaki tace “Bazaku shigo ku sha ruwa ba..!”
Turaki yace “Wai ai sai abinda Rankaidad’e yace, idan yace mu shiga musha ruwa bazamuk’i tayin Sarauniya ba...!” Mahmood ya jefo masa wata kallo da tabbas yasan ma’anar kallon...
Girgiza mata kai Turaki yai yace “Mun gode da tayi Rankidad’e, amma yanzu zamu d’auki hanyar Jos, Kinsan yanayin da muka baro Masarautar ciki..!”
Ta jinjina kanta a hankali tace “Haka ne... Allah Ubangiji ya tsare maku hanya ya kaiku lafiya.. Na gode sosai...!”
Turaki ya amsa mata da Ameen sai kuma yace “Rankidad’e na shigar miki da jakan ciki mana..”
Yanda yai maganar yaso bata dariya,ta d’an murmusa kad’an tace “A’a karka damu zan iya na gode sosai ..!”
Turaki ma ya murmusa yace “Tunda kince haka shikenan Kinsan ba’a jayayya da mutanen Fada..” ya k’arashe yana mai bud’e mota ya shige... Turaki na k’ok’arin jan mota Mahmood ya dakatar dashi, kallo yabi bayanta dashi har saida yaga gidan data shige... Tana shigewa kuwa yace suje... Turaki yaja mota yana shirya kalolin tambayoyin da yai zaiwa abokin nasa kan wannan yarinyar da Ko shakka babu yana jin akwai wani alak’a mai girma tsakaninta da Mahmood d’in dukda kuwa yasan bazai samu amsoshinsa yanda yake so ba sanin ko wanene abokin nasa...
Tindaga nesa da ya hango mota k’irar BMW new brand Ta fito daga ciki yaketa alla alla ya iso dan idanunsa ya gane masa kaman itace ta fito daga motar... Aiko tana k’ok’arin tura gate motarsa ya k’araso, duba d’aya yai mata yaji gabansa yayi mugun tsinkewa musamman da ya ganta da kaya ga kuma yanayin da take ciki wanda zaice bai tab’a ganinta ciki ba...
Ta kaikaito a hankali tana dubansa, murmushin da yafi kama da yak’e ta sakar masa... Yana k’ok’arin fitowa tace “Yi zamanka Dr bara na bud’e maka gate d’in...!”