← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 162

Sashe 143

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan yafi ko wanne bata wahalan fahimta dan bayan sunan d’aki data sani batasan wani kalma ba kuma dake cikin takardan sannan d’akuna da dama a wajen batasan wanne yake nufi ba... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana kuma nanatawa, zuciyarta tace kawai ta bud’e duk wanda ya kwanta mata... Ta shiga bin k’ofofin d’akin da kallo tana tinanin wanne zata bud’e tinda idan ta bud’e ba wanda yake nufi ba k’ila ta fad’i jarabawarta..

Kalmar k’arshe ne ya fad’o mata dan haka ta nufi k’ofa na k’arshe har bata tura taga d’akin dake gefe gefe da wannan key d’in jiki yana d’an kad’awa a hankali alamun ba’a jima da bud’ewa ba.. Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana mai furta Allah yasa daidai tayi.. Da Bismillah ta tura k’ofar d’akin...

Tai tsaye tana mai k’arewa d’akin kallo... A hankali Ta soma takowa cikin d’akin tamkar mai gudun kar aji motsinta, taita yaba kyaun d’akin da tsarinsa... Can saman gado ta hango wani kwali ajiye... Ta k’arasa a hankali tana duba kwalin... Jikin kwalin taga an rubuta open... Ta saka hannunta a hankali tana d’aga marfin k’aton kwalin... Cikin tsanaki take zaro abindake linke cikin kwalin wanda rigace ta bacci ‘yar yaloluwa mai siririyar hannu... Ta zaro idanunta waje tana kuma juya rigar mai kalar ja...

Cikin girgiza kai tana mai kuma juya rigar take furta “No.. I’m not wearing this... I’m done playing your games Rankaidad’e..! bazanci gaba ba kuma.” Ta k’arashe tana mai jifa da rigar saman gado... But idan bata k’arasa jarabawarta ba shikenan Rankaidad’e zai ajeta gidan tsaffin matan sarakuna... She can’t afford to fail the exam..Bata da wani zab’i da ya wuce taci jarabawar nan komin wahalarta... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana ta janyo rigar ta nufi wani hanya dake daga can gefe cikin d’akin wanda tayi zaton closet ne... Canza kayan jikin nata tai tana mai duban yanda rigar ta zauna jikinta wanda ita kanta kunyar kanta taji...A gefen mirror taga an rubuta da hausa wannan karon “D’aki na k’arshe...”

Ta furta cikin rarrabewar kalma...Duban kanta Ta kumayi jikin dressing mirror kana ta janyo Alkyabba ta rufa ta tukukuye jikinta cikin Alkyabbar, Allah ya gani bazata iya tunk’arar Rankaidad’e da ‘yar wannan rigar ba, ta fito ta nufi d’akin k’arshe.. Zuciyarta sai tsinkewa yake... Tafi minti uku masu kyau tana tsaye bakin k’ofa tana zullumin shiga cikin d’akin.. Sai tazo kaman zata shige sai ta fasa... Daga k’arshe dai tai ta maza ta murd’a handle d’in sallama saman bakint kanta a k’asa... Ta ida shigowa tana mai ayyana kyau da tsari na d’akin.. Tai tsaye tana faman waige waige dan bataga kowa ba... Saitin kunnenta ta sinkayo muryarsa yana furta “I don’t remember asking you to wear this Alkyabba your Highness..” Yai maganar cikin wane irin salo

Ta rintse idanunta a hankali tanajin tururin numfashinsa cikin kunnenta,.. Murya na rawa take furta “But Rankaidad’e..!”
“Shiiiii” ya d’aura yatsarsa guda saman labb’anta, har lokacin tsaye yake Ta bayanta “No buts.. Remember the rules.... Take it off..!” Ya fad’i cikin tsarewa..

Ta Ware idanunta a d’an zabure... Kaman mai shirin kuka take furta “Rankaidad’e ni dai dan Allah wllhi kunyar nake..!”

Taso basa dariya yanda tayi maganar amma ya gimtse yace “Do you want to fail the exam..?”

Idanunta a rufe take girgiza kai alamun bataso ta fad’I jarabawar...
“Then take it off..!” Ya kuma fad’i babu wani walwala...

Rintse idanunta kurum tai tanajin sanda alkyabbar Ke k’ok’arin isa k’asa... Zuciyarta taci gaba da harbawa hawayen na k’ok’arin ciko idonta... Tai k’ok’arin kai hannunta zata rik’e alkyabbar taji ya kamo hannun nata cikin nasa...har lokacin idanunta a rintse suke ta kasa bud’esu... Tana jin hucin numfashinsa saitin kunnenta yana rad’a mata “You’re more beautiful like this..!” Ta ware idanunta da sauri tana jin abin wani irin bambarak’wai Wai Rankaidad’e Ke furta wad’Annan kalman... Ganin yana k’ok’arin kaikaito da jikinta su dubi juna ya kuma sanyata saurin rintse idanunta...Sosai taso basa dariya yanda ta tamke idanun nata da k’arfin gaske... Ya murmusa da gefen baki yana mai duban fuskar nata wanda har lokacin light make up d’inta na nan, d’an bakin nata shi yafi komai tafiya dashi kafin ya soma sauk’o da idanunsa yana duban yanda ‘yar rigar ta zauna cas a jikinta...
“Open your eyes..!”

Kasa bud’ewa tai saima dad’a tamke idanun da tai... Ya d’auki lokaci sosai yana k’are mata kallo kafin ya bud’e murya yace “Kinsan idan baki bud’e idanun nan ba zamu koma daga farko komai ya rushe..?”

Zumbur ta bud’e idanunta had’ida waresu tar saman fuskarsa... Kallon kallo suke ma juna zuciyarta naci gaba da tsinkewa... Tamkar wacce aka zabura cikin rawar murya take furta “I think I’m hungry your Highness.. Can I please go get something downstairs..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...

Saida dak’ik’ai suka gifta ya bud’e murya yace “So bakici that spicy food da kika bani ba...?!”
Ta d’an dubesa a razane, shi d’inma ita yake duba fuska a tsare, lokaci guda yaci gaba da furta “Does the Queen know that har yanzu ina jin yajin a bakina.. I can’t get rid of the taste..” Ya k’arashe yana mai kuma tsareta da idanunsa masu matuk’ar firgitata..

Ta d’an kauda kanta gefe tana dariyar mugunta a hankali, ashedai abincin yaji yayi shiyasa Rankaidad’e ya kasa had’iyewa at first.. Yayi just one spoon ya ajiye.. Ahtoh mai yake expecting an tara mata girkin gayya... Ya gode Allah ma da ba gishiri bane.. Itakam saidai ma tace Allah k’ara alhakinta ne ya kamasa..

Ya tallafo fuskarta yana furta “Dariya kike...?”

Ta girgiza kai kad’an had’ida sadda kan nata k’asa har lokacin bata daina murmushi ba sai kuma tace “Wai gani nayi Sarki bai kamata yaji zafin yaji ba..”

Ya saka hannunsa guda a kunkuminta ya d’an janyota zuwa jikinsa da hannun nasa “Why..? Is he not human..?” Ya fad’i yana kasheta da wane irin duba wannan karon..

Dukda tsananin tak’ura da tai hakan bai hanata furta “Sabida shi Sarki ne.. Baijin zafin komai... Baka tab’a jin tarihin Sarkin da aka kulle yatsarsa a mota ba bai magana ba har saida suka isa yanda zasuje aka bud’e yatsar nasa.. Da kuma Sarkin da kunama ya cijesa ya take kunamar ba tareda yaji zafin cizon ba...”

Tinda Ta soma magana yake duban yanda bakin nata Ke motsawa a hankali, baisan ta iya zuba surutu haka ba... Ta cika masa kunne da surutu bata ankara ba taji ya manne bakunansu waje guda... Tanzaro idanu waje tanajin bak’on Al’amarin da Rankaidad’e keyi... Saida suka jima cikin yanayin kafin ya cire bakinsa a hankali yana jin yanda ta kwantar da kanta cikin k’irjinsa sabida tsananin kunya da ya dabaibayeta... Cikin sigan rad’a yake furta “You talk too much...!”

Lokaci guda tsakala yatsunsa cikin nata ya soma janyotaya suka nufi tapkeken gadon nasa ta alfarma... Binsa kurum Muhibbah take tamkar rak’umi da akala... Tana gani ya nufi wani d’an madaidaicin fridge ya d’auko farm fresh ya mik’a mata “Drink this..!”

Ta mak’e kafad’a tace “I’m not hungry anymore... I just want to sleep, na gaji sosai, please ka k’yaleni na tafi..!” Ta k’arashe cikeda shagwab’a...
Hab’arta ya tallafo yana mai k’ura mata idanu lokaci guda yake furta “Yau daren jarabawarki ne Rankidad’e, babu bacci...!”

Idanunta da sukai rau rau take dubansa dasu, bata kuma fahimtar abinda Ke wakana tsakaninsu ba cikin wane irin salo da ya jefata shakkun anya da Rankaidad’e take tare kokuwa dai an canzasa ne... Illahirin jikinta ya d’auki rawa, yanayi ne da ya jefata cikin tunanin abinda ya faru da ita shekaru gomasha hud’u ba... Hawaye suka shiga gangaro mata, ta soma shid’an numfashi tana tuno sanda suka keta mata tufafi sukaci zarafinta... Wane irin k’ara ta saki tana mai janye jikinta had’ida tak’urewa waje guda hawaye na kuma ambaliya a fuskarta.. Cikin sauri Mahmood ya rungumota cikin jikinsa yana k’ok’arin calming d’inta “Is ok.. Kiyi shiru kinji... Ya isa bazan miki komai ba..!” Ya d’anyi fasali yana mai kuma shafa bayanta a hankali yanajin yanda take shan zuciya alamun tsoro da tashin hankali... Yaci gaba da lallashinta yana furta “Until you’re ready..!” Ya kwantar da ita a hankali had’ida rik’eta sosai cikin jikinsa bai daina lallashin nata ba.. Yanajin yanda tai lak’was a jikinsa zuciyarta naci gaba da bugawa, A haka ya janyo masu bargo ya rufa yanajin yanda zuciyarta Ke tsananin bugawa kusan tare tare na nasa bugun zuciyar...Idan yace zai tab’a yafe masu kan abinda suka aikata wa Muhibbah Tabbas yayi k’arya... Yana jin wane irin zogi da rad’ad’i cikin zuciyarsa wanda bazai iya misaltuwa ba... Gaba d’aya sun cancanci duk wani misfortunes da suke fuskanta... Ya lumshe idanunsa a hankali yana mai shak’an k’amshin sumarta...

A haka bacci b’arawo yayi gaba da su...
**

Safiyar Washe gari koda Ta farka bata gansa a gefenta ba, saidai taga takarda aje gefe yanda ya kwanta da red rose saman takardan, Tai saurin janyo takardan tana warwarewa...

_Buenos dias su alteza_ (Barkada safiya Rankidad’e) Ina tayaki murnan cin jarabawarki zagayi na farko...

Murmushi saman fuskrta ta ida karantawa Wanda ita kanta batasan daga yanda murmushin ke zuwa ba, a hankali ta shafe fuskarta tana tuno abubuwan da suka faru daren jiyan... Kaman dai ba Rankaidad’e ba... Ta sauk’e fuci a hankali tana tuna sauranta kwanaki biyu...
Tana nan zaune tana sakin murmushi a hankali Ta hango saitin kaya aje daga gefe.. Ta mik’e ta nufi yanda kayan yake tana duba, shima takarda ne aje saman kayan an rubuta
_De rey a su reina_ (Daga Sarki zuwaga Sarauniyarsa) Tabbas Ta fahimci kalmar Sarki da Sarauniya a wajen.. Ta kuma sakin murmushi tana duban tufafin wanda Sarkin nata ya ajiye mata domin tai masa kwalliya cikinsa...

A hankali take furta “Yau naga wane irin jarabawa ni Muhibbah wanda ake maka da yarenda baka iya ba..!”

SameenaAleeyou📚
[10/2, 12:37 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*82*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Chapter 143 · 0% Book details