← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 162

Sashe 2

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin taku irinta wanda jinin mulki da k’asaita ke Yawo a jini da b’argon jikinsa yake k’arasowaga ‘yan uwan nasa, lokaci guda ya saki hannun budurwar dake rik’eda ita, duban masarautar nasu yake da wane irin idanu, Masarautar da ya rasa matarsa farin cikinsa a acikinta, Masarautar da yai alk’awarin k’aurece mata tsawon rayuwarsa... Toh amma yau ganin ‘yan uwansa haka ya sanya zuciyarsa karaya, shakka babu yayi kewar gida, d’aya daga cikin samarukan ne ya tako har gabansa, su duka biyu suna duban juna cikeda shauk’in sake ganin junansu, matashin bai iya furta komai ba sai rungumesa da yayi siririyar hawaye na d’igo masa murmushi bai bar saman fuskarsa ba, sosai suka rungume juna, kana matashin ya soma furta “Yaya... Yaya Barka da dawowa gida....Nayi murnan ganinka, na gode da ka amsa kiran Maami Welcome home...!” Ya k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa, mutumin da ya kirada Yaya ya d’an buga kafad’arsa kad’an kana ya furta “Na gode _(Príncipe Fu’ad, Estoy feliz de verte_,)naji dad’in ganinka...” Daidai lokacin d’aya saurayin ma ya k’araso had’ida kai masa runguma, suka rungume juna cikeda Farin ciki kana matashin ya furta “Sannu da zuwa Yaya... Barka da sauk’a...!”

Murmushi ya kumayi da gefen bakinsa kana yace “An gaida Veterinarian... Na gode k’warai Prince Jamal... Gracias...!”

Saurayin da ya kirada Jamal ya murmusa kad’an kana ya matsa gefe daidai lokacin da Yarima Mahmood ya d’ago yana duban d’aya d’an uwan nasu wanda da gani ya girmema wad’ancen samari biyun, su duka biyu Sun kafe juna da idanu kaman babu mai motsawa Daga matsayarsu, lokaci guda d’aya matashin ya d’an saki murmushi wanda da gani kasan cike take da ma’anoni kana ya soma takowa cikin tsananin mulki, tak’ama, sarauta da kuma isa... Hannayensa duka biyu a hard’e yake takowa, ko ba’a ce kasan wann bawan Allah mulki da sarauta Sun gama ratsasa Sun kuma jik’asa...

Har ya k’araso gaban Yayan nasu bai furta koda kalma ba sai wannan shu’umin murmushin dake bisa fuskarsa... “Yazeed...!” Yarima Mahmood ya furta cikeda kulawa....

Yazeed ya kuma sakin murmushi mai bayyana hak’wara wannan karon kana ya k’araso ya rungume d’an uwan masa yana mai furta (“Bienvenido a casa hermano) Barka da dawowa gida Yaya....!” Yai masa gaisuwar cikin harshen Spanish...

Murmushi ya saki a hankali saidai kafin ya sami zarafin amsasa ya sinkayo muryar Yazeed cikin sigan rad’a daidai lokacin da suke rugumeda juna, saitin kunnensa yake rad’a masa “Karka rud’i kanka da kalaman da wad’ann dogarai Ke maka kirari dasu... Till now ba’a tantance wanene Magajin Kujerar masarautar nan ba... Sannan Jarumi masanin al’adun cikin gida shi ya cancanci rik’on kujerar ba wanda ya shafe shekaru a k’asar turai ba....!” Yai maganar fuskarsa fal murmushi...
Yana k’ok’arin janye jikinsa, Mahmood ya damk’o damtsensa kad’an, saitin kunnensa shima yake rad’a masa “Hausawa na cewa Ba’a sanin maci tuwo sai miya ya k’are... You might be right, I might not be familiar with all you’ve listed, but let me remind you this,(Hermanito) K’aramin k’anina... As they say D’an na gada yafi D’an na koya, so as long as jinin sarauta yana yawo a jijiyoyin jikina, Mulkin Masarautar nan ka iya fad’owa hannuna... Saidai duk bama wannan ba... Ka sani bashi ya dawo dani ba... Inada babban dalilin da yasa na dawo wannan masarauta wanda yafi yak’in neman mulki da sarauta...Mantén esto en mente (Ka aje hakan a zuciyarka) k’aramin k’anina....!” Ya k’arashe yana mai gyarawa Yazeed rigar kuftarsa had’ida d’an buga kafad’arsa guda.... Yarima Mahmood ya d’aurada “Na gode da tarban da ka min... Prince Yazeed...!” Ya k’arashe kyakkyawan murmushi saman kyakkyawan fuskarsa....

K’uri Yazeed yai masa har saida yasa kai ya shige yayinda sauran ‘yan uwan masa suka rufa masa baya...

Suna dosowa mashigar parlorn kuwa bayi suka soma zubewa suna gaidasu....

Parlor ne da ya amsa sunansa wajen tsari da had’uwa, dik yanda royal parlor yakai to wannan parlor yakai, iyaka tsayewa ya gama tsaruwa, parlor ne da za’a iya kiransa da Aljannan duniya...

Daga cen center kana iya hango wata kyakkyawar mace fara tas mai d’an jiki da tsawo zaune saman Hamshak’iyar kujerar, k’afarta d’aure suke saman babban pillow da akai mata kwalliya da asalin fatar damisa, kayan dake jikin matar kad’ai zai tabbatar maka dik yanda mulki da sarauta ta duniya take wannan mata ka iya taka wajen.... A haka bazakai zaton takai shekarun da take ba sabida jin dad’i da kuma kwalliya da gayu, sai ka k’araso sosai ka fahimci girma ya sauk’o mata, Dattijuwa ce ‘yar kimanin shekaru 65 a duniya....
Saida wata mata da ko ba’a fad’i ba zaka fahimci Jakadiya ce ta shigo cikeda risinawa ta sanar da isowar Yarima Mahmood kana tai masu izinin shigowa....

Fu’ad ne gaba sai Jamal Ke biyedashi sannan Mahmood Ke take masu baya... Matar Ta fad’ad’a murmushinta idanunta tab k’walla... Babban D’anta mafi soyuwa a gareta take hangowa tsakiyar ‘yan uwansa, ji tai tamkar Ta mik’e Ta rungumesa, Ta kasa b’oye tsananin Farin cikint dikda cewa a b’angaren Mahmood d’in ba hakan ne Ta kasance ba, sam babu d’igon annuri a fuskarsa saima kallon k’urilla da yake wa mahaifiyar tasa.... Wasu irin hawaye masu tsananin d’umi ne yaji suna zuwa cikin idanunsa, yayi saurin sadda idanunsa k’asa
A hankali matar ta mik’e tana k’ok’arin kamo hannayensa, hannayenta duka biyu tasa had’ida tallafo fuskarsa, yai saurin kauda fuskarsa gefe saidai tuni matar ta rungumesa tana matsan k’walla...
Take akai dismissing dik wani wanda ba ahalinsu ba cikin parlorn...

Cikin tsananin rawar murya take furta “Sadauki, ashe zaka dawo... Barka da dawowa Magajin Babanshi... Naji dad’i da baka watsa min k’asa a idanuna ba, ka amsa kiran da nai maka, ka dawo mahaifar ka...!”

Kaman wanda ya tina wani abu, ya saki murmushi wa mahaifiyar tasa for the first time tin bayan shigowarsa parlorn...
Hannayenta cikin nasa yake furta “Maami kin wuce haka a wajena, kiyi hak’uri da na sab’awa umarninki a baya... Por favor perdoname Maami na...!” (Ki yafe min Maami na)

Ta saki murmushi cikeda jin dad’i had’ida mamakin canzawar da Sadauki yai, kodashike tinda ya amince zai dawo Masarautar tasan tabbas tasan ya canza, lokaci guda ta janyo hannunsa suka zauna saman kujerar alfarmar dake parlorn, wani irin shauk’i da k’aunar d’an nata ke ratsa dik wata k’ofa Ta zuciyarta, murmushi mai gauraye da Hawaye a fuskarta take furta “Har kullum albarka ta ce a tattaredaku gaba d’ayanku....” Ta d’ago tana duban Jamal da Fu’ad kana tace “Ina Yazeed...?”

Duban juna sukai kaman bazasu ce komai ba sai Mahmood ya tari zancen da fad’in “Ya tarbeni Maami... Duka ‘yan uwana sunmin tarba mai kyau da naji dad’insa... Madallah da ahalin marigayi Babana Sarki AbdulJabbar... Madallah da ahalinki Giwar Sarki....!!” Ya k’arashe yana mai kod’a mahaifiyar tasa...
Ta kuma sakin murmushi cikeda shauk’i, Mahmood yai mata k’uri yana jira yaji Ta tambayi d’iyarsa Zahra, saidai sam Maami bata tambaya ba, ko dashike yasan hakan ka iya faruwa Dan haka baiyi mamaki ba....
Tuni Maami Ta mik’e taci gaba da bada order na shagalin da ake shirin had’aka da dare a fadar dan sanar da dawowar Babban d’anta...
Shiko Mahmood Fu’ad ya tambaya ko Ina Zahra take... Nan Fu’ad ke sanar dashi tana cen sashen Yazeed...
Jinjina kansa kurum yai kana ‘yan uwan Jamal da Fu’ad sukai directing nasa zuwa nasa b’angaren yanda aka gyara masa, babban abinda ya dad’a baiwa Yazeed takaici shine cikin sashen Marigayi Mahaifinsu aka baiwa Mahmood masauk’i, da gaske da k’arfi so ake a mallaka masa sarautar gidan, bayan dik tsawon shekarun da ya d’iba yana jiran wannan mulki ta fad’o hannunsa, dik wani taron sarakuna na mahaifinsu idan bazai sami halarta ba shi yake wakiltawa, komai na mahaifinsu shine akai, sai yau rana tsaka Mahmood da bai sha wahalan komai ma masarautar ba ace shi zai gaji mahaifinsu, idan akai haka tabbas ba’ai masa adalci ba, da yawan mutane suna masa lak’abi da Wakilin Sarki wasu kaw Magajin Sarki suke kiransa, yau rana tsaka ace D’an uwansa ne zai gaji sarautar da ya jima yana buri bashi ba, tabbas hakan ba mai yuwa bane, bazai tab’a barin hakan Ta kasance ba...
Da wannan tunanin ya k’arasa sashensa cikin huci tamkar zai kifa k’asa...

***

Zuhrah matar Yazeed ne da yaranta guda biyu Najimi mai kimanin shekaru 6 saiko mace mai kimanin shekaru 4 zaune a hamshak’in Parlorn nasu sai zuba surutu suke had’ida murnan ganin ‘yar uwarsu Zahra wacce sauk’arta a k’asar kenan... A haka Yazid ya shigo tamkar zai kifa k’asa, D’iyarsa Noor Ta tafi a guje tana k’ok’arin d’alewa jikinsa take fad’in “Daddy guess who’s here....” Saidai Yazeed bai ko bari ta k’arashe ba ya tureta daga jikinsa cikeda tsawa... A matuk’ar razane yarinyar ta kauce kaman zata kurma ihu... Ta juyo a guje zuwaga mahaifiyarta.... Kuyangin dake kaikomo tsakanin sashen tuni suka soma k’amewa suna kuma zubewa k’asa sanin k’asaita da mulki da Ubangidan nasu kedashi, hanyar da Yazeed yabi bawa bai isa takawa ba.... Daidaida matar tasa da yaran nasa basu ishesa kallo ba ya nufi sama kaman zai kifa da k’asa sabida tsananin huci da yake...

Noor ta dubi mahaifiyar tace “Mummy what’s wrong with Daddy....?”
Kafin Zuhra Ta bata amsa namijin mai suna AbdulJabbar suna kiransa Sultan yace “Maiyasa yake fad’a...?”

Dafa yaran kad’an Zuhrah tai kana tace “Ku zauna da Addarku Zahra, I’ll go check on your Dad...”
Gaba d’aya yaran suka jinjina mata kai harda namijin....

A parlorn sama Ta samesa ya kwab’e rigar sarautar dake jikinsa sai singlet, goran ruwan sanyi hannunsa sai faman kwankwad’a yake lokaci guda yana fidda wane irin fuci....Ta jima tsaye wajen tana karantar mijin nata kafin ta nufi gefensa ta d’an zauna a d’arare...

Cikin kwantar da murya Ta soma fad’in “My Prince Wai meke faruwa ne....Why are you like this...? You scared the kids...!” Ta k’arashe cikeda kulawa....
Chapter 2 · 0% Book details