Sashe 99
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Samha tai picking call ɗin Maama da ya shigo wayarta, daga ɓangaren Hajiya Madina tace da ita,"ina kika tafi kuma?".
fuskar Samha na bayyana wani irin farin ciki da jin daɗin da bata taɓa jinta ba a ciki tace,"Maama yanzu zan dawo, naje siyo special gift ɗin da zan bawa Mum ne".
ta jiyo fitar sautin murmushi a tare da Hajiya Madina wacce tace,"good, but ki dawo da wuri". tace,"tom Maama". sai kuma tace,"muna tare da Fillo ma yanzu haka, na ganta hanya zata wuce school na É—auketa".
da sauri Maama tace,"bani ita". Samha ta miƙawa Fillo wayar, daga ɓangaren Hajiya Madina tace,"Fillo ƴata, Allah yayi miki albarka kinji, ubangiji yasa ki gama da duniya lafiya yarinyar nan, wallahi shigowarki rayuwarmu alkhairi ne. Fillo nayi amfani da shawarar da kika bani akan su Samha kuma naga nasara, domin kuwa Samha da kanta ma tazo tana faɗa min duk abinda suka aikata ita da Sameer, Allah yay miki albarka Fillo yanzu hankalina ya kwanta banda damuwar komai, ƴaƴana sun shiryu".
Fillo dai murmushi take bata ce komai ba, daidai sanda suka zo gate na makarantar tasu, tace. "Maama mun kawo makaranta zan sauka".
Hajiya Madina tace,"to shikenan, sai kin dawo Allah ya bada ilimi me albarka. a dage sosai kinji, gobe da safe ki shigo ina son ganinki, ko da yake ma zan aiko driver yazo ya É—aukar min ke".
daga haka sukai sallama, Fillo ta fita a motar, har ta bar wajen Samha ta kirata ta bata wani biro me kyau. ta karɓa tayi mata godiya sannan ta wuce, ta tafi tana me jin tausayin Samha a ranta, lallai rashin nunawa ɗa soyayya daga wurin uwa ba ƙaramin ƙalubale bane a rayuwarsa. banda hakan dama me zai kai su Samha ƙudurtar cewa sai sun kashe ɗan uwansu alhalin su babansu ba wata kujerar mulki garesa ba.
ta tuna sanda ta zauna ta bawa Umminta labarin duk abinda ya faru ga me da taimakon da Hajiya Madina tace zata yi mata akan ta shiga jikin Samha ta dinga yawan bibiyar al'amuranta dan ta dinƙa jiyo mata plans ɗinsu akan Turaki. wannan dalilin yasa tace ta dage ta iya turanci saboda Samha bata fiya magana da hausa ba ko fulatanci sai dai english.
kuma ba tare da dogon nazari ba kai tsaye abinda Ummi tace mata shine,"duk abinda yaranta suka aikata laifinta ne, domin babbar illar da zaka yiwa kanka shine ka nuna banbanci a tsakanin ƴaƴanka, ka nuna soyayyar wancan tafi ta wannan a gareka, ka kasa ɓoye musu yanda kake jin matsayin kowannensu a zuciyarka, tabbas idan zuciyar wani ta ɗauka ta wani ba zata ɗauka ba, nuna banbanci tsakanin ƴaƴa kan haifar da matsala sosai, domin zuciyar wasu zata yi ƙoƙarin ganin yanda za ai su kauda wanda ake so ko kuma su illata shi".
Ummin tace mata,"dan haka yanzu shawara ɗaya da zaki bata tunda suma Allah yasa mahaifiyarsu ta dawo, to ta maida hankalinta kan waɗannan yaran masu raunin zuciya, karta ce zata fasa yiwa su Turakin abinda take musu dan hakan zai iya kawo gurɓataccen tunani a zuciyar mutane, ta mayar da kulawar yaranta equal to yanda take son su Turakin, shine kawai samun kwanciyar hankalinta".
*Vote, Comment, and share.*
[8/31, 01:25] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
*39*
*08:30am.*
acikin bedroom ɗin na Baffa, Hajiya Ramla ce tsaye gaban mirror ita da shi, sanye take da shadda golden colour tasha azababben aiki ajiki, anyi mata ɗinki bubun sai ƙyallin stones take yi, tayi masifar kyau kamar balarabiyar usuli, ita da Baffan iri ɗaya sak.
daren jiya tailor ya kawo musu ɗinkin su uku iri ɗaya, ita take taimakawa Baffa wajen shirin da yake yi, tana shirya shi ɗin suna hira cikin annashuwa da jin daɗi tare da alfaharin ƙara kasancewa da junansu.
turare ta ɗauka ta fesshe shi da shi tuni kuwa ɗakin ya ɗauka da wani daddaɗan ƙamshi, Baffa ya rungumeta jikinsa yana faɗa mata irin son da yake mata da kuma kewarta da yay a sanda bata tare da su, albarka kawai yake zunduma mata kamar yawun bakinsa zai ƙare.
wayarsa tayi ƙara ta zame daga jikinsa tai saurin isa kan gado ta ɗauko wayar, sai da tayi picking tukunna ta kara masa a kunne.
daga can ɓangaren Boɗejo tayi sallama suka gaisa da Baffa, tana kuka ta-ke shaida masa halin da Fulani Azima ke ciki, shi kansa Baffa da ya dawo a jiya jikinsa yayi matuƙar sanyi ya kuma tsorata ainun da yanda ya sami Fulani Azima, ya ƙara jin tsoron Allah da kuma tsoron sharrin duniya, saboda yanda ta dawo kamar ƙwarangwal halittarta dai babu kyan gani a yanzu, har ƙwalla sai da yay musamman da ya fahimci tana so tayi magana da shi, to amma shi har ga Allah ba zai iya bata wannan damar ba saboda ba zai iya zaman kusa da ita ba dalilin mugun ɗoyin da take yi, mijinta kansa sai ta window yake ganinta balle kuma shi, yana ji ma ana batun dawo da ita gida saboda su kansu asibitin sunce ba zasu iya da ita ba.
cikin sigar kwantar da hankali Baffa yace da Boɗejo,"kiyi haƙuri, adu'a zamu cigaba da mata Allah ya bata lafiya".
ta ƙara sautin kukanta tana faɗin,"Dikko ni ƴarta nake tausayi, a jiya yarinyar nan Ilham tayi suma yafi biyar, ko abinci bata iya ci Dikko, aljanun da bamu santa da su ba sai tashi suke, yau baka ga yanda suka farfasa mata jiki ba". ta faɗa tana kuka sosai.
Hajiya Ramla dake jiyo komai ta sauke numfashi tana jinjina al'amarin sakayya, ita dama tun can bata da niyyar tonawa Fulani Azima asiri akan abinda tayi mata, abunda zuciyarta ta yanke mata kawai shine zata barta da Allah sai kuma sun haɗu acan lahira, amma anan dai ba zata taɓa faɗar cewa ga wacca tai silar barinta gida ba, duk da cewar tunda ta dawo ta bada labari kowa ke cewa aikin asiri ne, to amma ko kusa bata yarda ta bar hakan a zuciyar mutane ba, duk da Hajiya Madina taso ta ɓaro komai ɗin dan har sunan Fulani Azima sai da ta ambata tana cewa wallahi sai taci ubanta zata kawo ƙarshen makircin matar, to da ƙyar dai ta tausheta ta bar maganar.
BoÉ—ejo na kukan sosai tace,"Dikko ka bawa Ramla wayar ina so nayi magana da ita".
"tom shikenan, amma ki daina kukan hakan dan Allah".
tace,"Dikko ina ni ina daina kuka kuwa yanzu, ai ni da barin hawaye har sai Azima ta mutu, amma indai zanke ganinta a wannan halin hankalina ba zai kwanta ba kamar yanda hawayena ba zasu tsaya ba, wallahi ma ni daka ganni na yafe mata duk wani kalar rashin kyautawa da tayi min".
Baffa ya miƙawa Hajiya Ramla wayar, suka gaisa da Boɗejo, tai ƙasa da murya tana cewa.
"kiyi haƙuri Ramla ƙarar ɗanki na kawo miki, wallahi yaron nan azzalumi ne baya tsoron Allah kwata-kwata, kinga dai ko maƙiyin Azima yana zuwa ya dubata amma shi tunda ya kawo matar tasa ya yasar anan bai ƙara waigowa ba, tace min ko kiranta a waya ma baya yi, idan ita kuma ta kira shi suna gaisawa ɗan banzan yaron nan zai kashe wayar baya ko tambayar lafiyarta balle ta uwar dake cikin wani hali, to dan Allah ki faɗa min wannan mijin aure ne, kuma wallahi ƙarya yake yi yace baya son Ilham, dan dai kin ɓata ne lokacin yarintarsa amma da ko ke sai kin aura masa Ilham, to ni dai yanzu abinda nake so daga gareki tunda kin isa da shi kisa yazo wajen matarsa ko da ba zai zo duba Azima ba dan wataƙila sharrin da tayi masa ne bai manta da shi ba, ba haka ake ba sam wallahi, ya kamata yazo ya kasance da ita ya kwantar mata da hankali da irin salon ma'aurata, to da yake dai shi ɗin baida addini shisa, kuma rashin hankali da tunani ke damunsa, duk da nasan Madina ce take zuga shi wallahi, kuma zan dawo ne zata gamu da fushina da bata taɓa gani ba".
Hajiya Ramla ta tari numfashinta da cewa,"a'a BoÉ—ejo Maamansa ai ba zata hanasa zuwa ba, ita kanta ina mai tabbatar miki da bata san da wannan rashin tunanin nasa ba da tuni ta tsawatar masa, amma zan faÉ—a mata insha'Allahu".
Boɗejo tace,"to ai dama Madina ta gama hanadameki ke da ƴaƴan, sai yanda tayi da ku. ke yanzu Ramla baki da ikon sawa da hanawa ga ƴaƴanki dake kanki sai dai Madina?, ni ko a tarihi ina na taɓa jin wannan yardar dake tsakanin kiahiyoyi, ai tun a auren nan na san Madina ba haka ta bar mutane ba, to ni dai wallahi tallahi zan baɗawa idona toka, in mance da cewar Turaki jikana ne in maka shi a kotu, Allah sai nayi ƙararsa akan zaluntar Ilham da yake dan ubansa, ina na taɓa jin kalar wannan auren me cike tsantsar zalunci da rashin adalci, wato yana nufin ma bai damu da ita ba ya huta da ƙaya kenanan tunda yanzu bata kusa da shi".
Hajiya Ramla ta kwantar da murya tace,"kiyi haƙuri Boɗejo zai zo insha'Allahu".
"ke ni rufe min baki sokuwar uwa kawai wacce wata ta fita iko da abinda ta haifa".
tai maganar a fusace tana kashe wayar cikin ɓacin rai, daga can ɓangarenta sai masifa take yi a asibitin muryarta ta karaɗe ko'ina, faɗawa me martaba take cewar yazo ya kaita kotu na ƙasar nan wallahi sai ta kai ƙarar Turaki akan wofuntar da matarsa da yay, sai taga ubansa Alƙali d ya tsaya masa.