← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 176

Sashe 145

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*53*
*Azima Tahir Lukman.*
ashekarun baya masu yawa da suka shuɗe, Azima Tahir Lukman wata matashiyar budurwa ce, wacce ke matuƙar ji da kanta a ɓangaren kyau, ilimi da kuma dukiya ta mahaifiyarta wadda ta kasance ƴar siyasa.
kyau irin na Azima ke tasirantuwa a zuciyoyin maza da dama, daga masu kuÉ—in har talakawa, a inda ta ware manyan masu kuÉ—i da masu mulki waÉ—anda su ne take ganin su kaÉ—ai ne suka isa su mallaketa.
kuma a kaf mazan da tayi mu'amala da su babu guda É—aya aciki da zuciyarta ke jin tana so ko kuma zata iya aurensa, no; zata mu'amalanceka ne kawai domin kuÉ—in da suke aljihunka, da zarar ta gama da kai shikenan, saboda ta mallaki kuÉ—i a wurin irin alahazawan da ke zuwa wurinta ta kashe rai ba É—aya ba, ba biyu ba.

zuciyar Azima ta so mutum guda tallin tal ne a rayuwarta, wato Alƙali Habib Dikko, shi kaɗai zuciyarta ta so tsakani da Allah, wanda har take jin she can go to the extend akan taga ta mallake shi, alhalin kuma yana matsayin saurayi ne na aminiyarta da ta san cewa an saka musu rana.
Ramla Muhammad Turaki itace babbar aminiyarta da suka yi university tare anan london, duk wanda yasan Azima ya san Ramla, haka duk wanda ya san Ramla yasan Azima, su kwana tare su tashi tare, su ci abinci tare su yi yawo tare, haka zalika ba sa taɓa aiwatar da abu sai da shawarar juna.

Azima ta samu Ramla ne tare da Dikko, tare ta gansu, wanda shi ma kuma ya aminta da ita sosai, musamman da yaga Ramla ta É—auki duk wata yarda da amana ta bawa Azima.
sai dai daga lokacin da Dikko ya fara shirin kai lefen Ramla, a lokacin Azima ta fara kunno wutar gobarar da zata lalata lamarin auren, ta fara ɓata Ramla a wurinsa, abubuwa iri iri da zai sa yaji ya tsani Ramla babu wanda ba ta faɗa masa ba, tun baya yarda har ya zo ya fara yarda da ita, saboda sauyin da yake gani a tare da Ramla a lokacin da bata ba shi attension ɗinta, sakamakon final exams da za su fara.

hatta vedion tsiraici na lesbian Azima ta ɗauka ta bayar anyi editing ɗinsa da fuskar Ramla ta bawa Dikko, daga wannan lokacin kuma yaji ya tsani Ramla kwatakwata, ita kuwa Ramla a lokacin bata kawo komai a ranta ba dangane da watsi da lamarinta da Dikko yay, ta ta'allaƙa hakan ne da space ya bata saboda ta samu tayi karatun exams sosai.

sai dai kuma a lokacin da Azima take tunanin tayi nasara, a lokacin Allah ya toni asirinta a ranar wata laraba, inda wanda yay ma ta editing vedion tsiraicin Ramla yaje ya sami Dikko ya faɗa masa gaskiyar komai, a lokacin soyayya ta riga tayi nisa tsakanin Dikko da Azima, dan saura ƙiris su shigar da iyaye cikin maganar, dan Azima ta gama tsara yacca zata shimfiɗar rayuwar aurenta da shi.
kuma duk wannan lamari da ke faruwa Ramla bata da labarin komai, yacca Azima ba ta bari ta fahimci wani abu ta ɓangarenta ba, haka shi ma Dikko bai taɓa tunkarar Ramla da irin abubuwan da Azima tayi akanta ba har kawo iyau da take matarsa, uwar gidansa, kuma uwar ƴaƴansa, wucewar shekaru sama da 20.

lissafi ɗaya Azima tayi a bayan da Dikko ya juya ma ta bayansa, shi ne ba zata taɓa yin nisa daga gare shi ba, zata bi wata hanyar da zata kusance shi har ta wanke laifinta, kuma har ya yafe ma ta yace zai aureta kamar dai yanda taci burin hakan.
dalilin da yasa ta shiga rayuwar Mai Martaba Hashim Latif kenan, saboda ta lissafa cewa ta wannan hanyar kaɗai zata iya samun damar kusantar Dikko, ta hakan ne ba zasu yi nisa da junansu ba, ta hakanne zata samu damar wanke laifinta gare shi, in ya so a sanda yace ya yafe mata sai tayi duk iyakar ƙoƙarin da zata yi ta raba aurenta da Mai Martaba domin ta mallaki Dikko, amma sai dai me!, lissafin da hasashenta duk sai ya tarwatse ya bi iskar da ta kaɗa tun a ranar da ta sanya ƙafafunta acikin gidan mai martaba.

kuma daga lokacin da ta fahimci cewa ba zata taɓa samun Dikko ba, daga lokacin ta ɗauki alwashin ƙuntata rayuwar duk macen da ke rayuwa tare da Dikko hatta kuwa da ƴaƴan da zai haifa ba tare da ita ba.

shigowarta cikin rayuwar Mai Martaba ta gane asalin menene mulki da kuma daɗin da yake cikinsa, wannan yasa ta dasa cin burika da yawa a rayuwarta, lokacin shaiɗan ya fara buga ma ta sabuwar ganga acikin kanta, akan aikata mugwayen abubuwan da ba zasu ɓulle ma ta ba, ya dinƙa rinjayar zuciyarta da cewa tayi duk fafutukar da zata yi wajen ganin ta mallaki kaso 70 cikin tarin dukiyar Mai Martaba kafin ta barshi.

shiyasa daga lokacin da ta haifi Ilham, sai tabi duk wata hanya da zai sa Mai Martaba ya koma ganin ƴarta kawai a matsayin ita kaɗai ce ƴar da ya mallaka, wannan dalilin yasa ta kama fufutukar bin bokaye  kenan, wanda ya zama mafi muhimmanci a wajenta.
kuma tayi nasara akan hakan, domin kuwa cikin Æ´aÆ´a goma da Mai Martaba ya mallaka Ilham kaÉ—ai idanuwansa ke iya gani a matsayin wacca ya haifa da cikinsa, wanda hakan ya janyo rabuwar kawuna a tsakanin sauran Æ´aÆ´an da ita Ilham É—in, domin ya mayar da ita tamkar É—a namiji, duk wani abu nasa da ya mallaka yana rubuta shi da nata sunan, har ya kan yawan buÉ—ar baki yace _na so ace Ilham Namiji ce, da ta gaji wannan kujerar tawa tun ina raye._

sai dai babu wanda ya taɓa gane Azima na ɗauke da wani mummunan ƙudiri, kasantuwarta mace mai dabara, macen da ta ke lulluɓe da mayafai guda biyu, ciki baƙi waje fari, sai dai ba ta taɓa barin wani mahaluƙi ya ganta da wannan baƙin lulluɓin sai dai farin da ta yafa daga waye.

_"har yanzu mun kasa gano taƙaimemen ciwon da ke tare da ita. duk wasu injina da ya kamata muyi amfani da su sun gaza yin aiki wajen gano cutar da ke tare da ita"._
maganar da ɗaya daga cikin likitocin ke yi kenan acikin ofishinsa, acikin asibitin masarautar kaltungo, Mai Martaba ya miƙe cikin mutuwar jiki suka fito tare da Dr ɗin.

a sanda suka fito ya tsaya daga can nesa yana kallon matar tasa ta silin hanyar da ta buɗe ta ƙofar ɗakin da take kwace.
kallo ɗaya zaka yi mata tun daga nesa kaji zuciyarka ta motsa saboda tausayin mawuyacin halin da take ciki a yanzu, ka kuma ƙara jin tsoron ruɗin duniya, a yayin da zuciyarka za ta tuna ubangiji da dukkan irin ikon da yake zartarwa akan rayuwar kowanne bawa.

kwance take an ɗaureta ajikin gadon ɗakin asibitin da ke cikin masarautar saboda yawan girgiza da take yi yanzu, idanunta a tsaye suke sun ƙafe akan windon ɗakin da ta nan ne kowa ke iya samun damar ganinta, har kuwa da ƴarta guda ɗaya da ayanzu ita ma bata iya zama tare da ita saboda bala'in ɗoyin da take yi wanda kowa ke cutuwa da shi, hatta kashi idan tayi sai ta jima cikin su kafin azo a kula da ita.

gaba ɗaya ta gama lalacewa, ta koma ita da ƙwarangwal babu maraba, a halin da ake ciki yanzu, dukkan wani ɓangare na zuciyarta ya riga ya gama dagargajewa a ƙirjinta, tana jin ƙirjinta ne kamar Allah bai taɓa halittar komai a cikinsa ba, zuwa yanzu duniya gaba ɗaya ta gama yi mata zafi, babu abin da take fata sama da mutuwa, sai yanzu ta gane ka zalunci mutum Allah ya baka damar neman yafiyarsa, ko ka saɓawa Allah ka nemi gafararsa tun kafin ya damƙe ka, wata rahama ce babba daga ubangiji, atleast ka iya samun sassauci na daga bala'in da zaka shiga.

halin da take ciki a yanzu ta tabbata babu wani abu na awo a duniyar nan da za'a auna ya fitar da kalmar da zata fassara shi, a yanzu ta afka ne cikin wani rami na nadama, nadamar da ta ke kira da mara amfani.
ta kuma sa ni har ta mutu Allah ba zai bata damar yin magana ba, balle ta samu ta fayyace mugun abubuwan da ta aikata, balle har ta nemi yafiyar waÉ—anda ta cuta. ta sa ni wannan kaÉ—anne daga cikin hukucin da Allah zai yi mata.

_(Ya Allah ka kiyashe mu daga sharrin zuciya, ka rabamu da aikata aikin danasani.)_

Hajiya Ramla ta zo tayi tsaye a bakin windon É—akin Fulani Azima, kallon junansu suke yi, idon Fulani Azima sai hawaye yake zubarwa kamar an kunna famfo, tana ta girgiza kan gadon da take, da alama so take yi ta sauko, kuma so take yi tai magana da Hajiya Ramla, so take yi a bata aron dama ko da guda É—aya ce, ko da ta minti É—aya ce.

in har Hajiya Ramla tace bata ji tausayinta ba tayi ƙarya, abu ɗaya ne kawai ta san da shi, shi ne ko akwai sama da abin da yafi tausayi ba zata taɓa yafewa Azima ba ko da ace zata shiga halin da yafi wannan muni.
ta sauke numfashi tana ƙara kallon Fulani Azima wacca har yanzu idonta ke maƙale akanta tana jijjiga gadon.
Chapter 145 · 0% Book details