Sashe 162
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sosai Fillo ke jin daÉ—in yanda Mum da Maama ke tarairayarta, musamman a wajen Hajiya Madina, don rainon cikin take yi cikin kulawa ta musamman daga wurin Kakarsa Hajiya Madina.
macen da kullum cikin siyan kayan jarirai take yi, hatta gadon Baby tana zuwa saudiyya ta taho da shi, motsin Fillo kaÉ—an ta tambayeta me take so.
Rayuwa ta cigaba da tafiya, a yayinda wasu abubuwan rayuwar kan sauya, lokaci yana tafiya a kullum kuma a ko da yaushe. wani lokacin cikin farin ciki wani lokacin baƙin ciki.
A duk lokacin da agogo zai motsa, lokaci ne yake wucewa, lakacin da baza a sake maimaita irinsa ba, lokacin da ba zai taɓa dawowa ba.
Sau da yawa ɗan Adam ya kan ƙagauta akan lokaci ya zo masa, musamman idan ya ƙosa akan cin burin wani abu da ya saka a ransa, sai ya gaza fahimtar irin saurin da lokacin yake yi, har sanda zai ankare da zuwan wannan abin da ya saka a ransa, anan ne zai ga tamkar ansa igiya ne ana janyo wannan lokacin.
hakan take a ɓangaren Fillo, tun daga ranar da likita ya ƙayyade musu watanni biyar a matsayin watannin da zata ɗiba kafin ta haife abinda ke cikinta, daga wannan ranar ta ƙosa da zuwan lokacin, zuwan ranar, sai ta koma ko da yaushe cikin kallon kaɗawar agogo take, cikin lissafa kwanakin kalanda, cikin haddar kwanakin da muke shiga muna maimaita su, cikin lissafi da hasashen irin soyayya, kulawa, ilimi tare tarbiyar da zata bawa abin da ta haifa.
sau tari mu kan yiwa kanmu lissafin tanadin abubuwa, sai dai abubuwa sukan zan zo mana ne a yacca ubangiji ya tsara mana ba yacca muka tsarawa kanmu ba.
wani lokacin ɗan Adam kan iya ƙirga sautin fitar numfashinsa, ba tare da ya san lokacin da numfashin nasa zai daina fita ba, fitar da ba zai ƙara samun damar ƙirga shi ba.
buri wani abu ne da kowanne É—an Adam ke cin sa, sai dai ba duka burin É—an Adam ne ke cika ba, kuma sau tari cin buri na katsewa É—an Adam ne a lokacin da numfashinsa ya daina fita.
Rayuwa babbar nasiha ce ga kowanne É—an Adam, akan ya gane cewa ba komai ba ne yake da tabbas ba a rayuwa, idan aka cire lokaci, lokaci ne kawai yake da tabbas, sai dai É—an Adam ba shi da tabbas É—in zai kai kowanne lokaci na bugawar agogo, ko tabbas É—in lokacin da yake ta lissafawa rayuwarsa.
ubangiji ya riga ya ƙayyadewa kowanne bawa iyakacin lokacin da zai ɗiba a duniya, numfashin wani zai daina fita ne a bugawar sakan, yayin da numfashin wani zai daina fita ne a bugawar minti, kowanne bawa na tafiya ne kawai akan lokacin rayuwarsa.
a rayuwa ba ko da yaushe ne É—an Adam yake yin murmushi ko dariya ba, ba kowa ne yake samun damar rayuwa tare da wanda yake so ba, ba kowa ne yake samun rayuwa a irin yacca yake so ba, babu wani bawa da ke samun É—orewar farin ciki a rayuwarsa, fa ce wataran sai yayi kuka.
*MUTUWA*, ita ce tabbatacciya, kuma ita ce abar dake kan kowanne rai, wacca bata da wani banbanci a tsakanin me kuÉ—i da talaka, babba ko yaro, me mulki ko mara mulki, ita ce wacca bata barin wani don wani yaji daÉ—i.
sau tari ɗan Adam kan zauna yay ta tunanin yaushe ne zai mutu?, kuma ai na?, taya zai mutu ɗin?, mene zai iya zama ajalin nasa?, sai dai waɗannan tambayoyi babu wani mahaluƙi da yake da amsar su, mutuwar ce kawai take zuwa da kanta, walau ɗan Adam ya shirya mata walau bai shirya ba, ko ana so ko ba'a so, da zarar ta zo tafiya kawai ake yi, ta datse wannan numfashin da bawa yake fitar da shi, acikin jin daɗi wa ko akasin hakan.
mutuwa ita ce kaɗai abar da ke iya yanke ƙaunar da ke tsakanin uwa da ɗanta, ko miji da matarsa, ko masoyi da masoyiyarsa, ko aboki da abokinsa.
ta kan zo ne bagatatan ba tare da ta sanar ba, sau tari mu kan kasance tare da mutum, kuma a yayin da aka sami giftawar wani lokaci bayan rabuwar mu sai muji ance wane ya rasu, ko kuma wane ya mutu, a lokacin ne zamu yi tunanin me ya sami mutum?, taya za'ai ace ya mutu bayan muna tare a É—a zu muna hira cikin wasa da dariya?, to ita mutuwa haka take, ta kan É—auki bawa ne da lafiya ko ba lafiya, kuma a lokacin da wani ke kan hanyarsa ta zuwa duniya, a lokacin mutuwa ke É—aukar wani ta raba shi da wannan duniyar duk son da yake yi mata kuwa, hakana duk son da ake yi masa.
in ace mutuwa zata bar wani don wani yaji daÉ—i, da tabbas bata raba É—a da mahaifiyarsa ba a lokacin da yake zuwa duniya ba, wata uwar kan samun damar ganin yaronta kafin mutuwar ta É—auketa, yayin da wata yaron na fito ita kuma zata yi sallama da duniyar.
a lokacin da aka ce mutuwa ta raba mu da wani mutum da yake sashi na jikin mu, ruɗewa da tsananin shiga tashin hankali tare da fitar hayyaci kansa mu gaza yarda da cewar an mutu ɗin, anyi tafiyar da babu dawowa, har ta kai ga ba ma gama yarda da cewar tabbas mun rasa wannan da muke jinsa wani ɓangare na jikin mu, har sai lokacin da aka ɗauki gawarsa acikin makara, aka tafi da ita zuwa maƙabarta, aka kama gangar jikin aka zura acikin ramin ƙabari, har a jera tukwane akan gawar, da ƙasar da za'a zuba akan tukwanen, sannan a shafe hasken farin likkafanin dake lulluɓe da gawar.
a sannan ne zamu yarda da tabbas an tafi, an yi tafiyar da ba za'a sake dawowa ba, tafiyar da ba zaka ƙara ganin mutum ba sai a lahira, har ko da yaushe fatan guda ɗaya ne, mu mutu muna masu aikata alkhairi, mu zama masu cikawa da imani, mu zamto mun mutu ana yabon mu.
a lokacin da kumburarrun ƙafafuwanta ke sakkowa daga matattakalar benen a hankali, a lokacin take jin wani baƙon yanayi yana ziyartarta, a lokacin take jin wani abu da bata saba jinsa ba, wani irin yanayi ne take jinta a ciki, wanda ya ke zarcewa har can ƙasan zuciyarta, ya motsa zuciyar tare da abin da ke cikinta.
sai a lokacin da ta isa parking lot, tasa key ta buÉ—e motar, sannan ne ta fahimci kamar kewa ce take kamata, kamar dai zata yi kewar wani abu me muhimmanci a rayuwarta.
sai dai abu guda ɗaya take so ta sani, menene dalilin da yasa take jin jikinta yayi sanyi sosai?, irin wannan sanyi da bai taɓa ji ba.
wayar da ke riƙe a hannunta tayi ringing, duk irin farin cikin da take shiga a sanda taci karo da kira daga gare shi, yau sai taji wani mix feeling ya kamata, taji kamar tana tausayin shi me kiran ba ita kanta ba da take zama da ƙyar tashi da ƙyar.
ta ɗaga kiran ta kara a kunne cikin jin sanyin jikin da ya ƙaru a gareta.
"uwar ƴaƴana ina kewar ki, kullum idan bana tare da ke sai in ji ina kewarki kamar zan mutu, na kasa yin aiki yau gaba ɗaya, tun da na shigo office na zauna nayi jugum, sai nake jin kamar ban taɓa kewar ki ba sai yanzu ne zan fara, gabana yana faɗuwa, zuciyata ta kasa samun nutsuwa, yau jina nake tamkar maraya, kuka zan yi Fulani Nah, ina jin kamar zan yi kuka irin wanda ƙanan yara ke yi, Fulani Nah in taho gare ki yanzu?, in zo in kwanta akan ƙijinki in dinga jiyo sautin bugawar zuciyarki a yayinda kike lallashina?, jikinki kawai nake buƙata ayanzu Fulani Nah, ina ji daga yau ba zan ƙara matsawa daga kusa da ke ba, zan daina fita aiki saboda ke, kina lafiya Fulanin Turaki?".
maganganun da suka fito daga bakinsa kenan, kuma maganganun da suka haddasa wata muguwar faɗuwar gaba a ƙirjin Fillo.
bata san lokacin data shiga motar ta zauna ba.
"ki shirya yanzu kije wurin Maama, yanzu zan taho, ba zan iya zaman office É—in ba, ina so yau mu yini tare, hira nake so muyi sosai, É—a zu ta kira ni tace min faten tsaki take sha'awar ta sha".
Fillo ta dafe goshinta,"Laaa ƙwara da Allah yasa ka yi wannan zancen, kamar na sani na dafa mata shi tun ɗa zu, kuma kaga har na fito zan tafi na kai mata ashe na barsa ban ɗauko ba".
"ki bata ta ci da yawa Fulani Nah, duk yawansa kisa ta ta cinye shi kin ji, tana sonsa, shi ne favorite É—inta, ta ce me kifi take son ci, in few minutes zan iso gare ku, ki kula min da kan ku, zan siyo miki mangoro, Maama kuma zan siyo mata gwanda".
"tom Jannaty sai ka dawo, nima yau kewarka da nake yi ta banbanta da ta ko yaushe".
"Fulani Nah saura 20days mu zama Mum and Dad ko?".
"insha'Allahu Jannaty".
"Allah yasa ki haihu da ranki da lafiyarki".
bayan gama wayar ta su Fillo to koma ciki, tana shiga kitchen É—in ta kira lambar Hajiya Madina.
daga ɓangaren Hajiya Madina ta ce,"Daughter yanzu nake shirin kiranki, ina ta jin kewarki na damu na, idan babu abin da kike yi ki taho yanzu, in Me Babban suna ya dawo sai ku tafi tare".
Fillo ta ce,"Maama faten tsakin me nama nayi, kina so ko nayi miki me kifin?".
fuskar Hajiya Madina ta washe da murmushin jin daÉ—i, duk duniya tana bala'in son souls É—in nan guda biyu, Turaki da Fillo.
"kar ki wahalar da kanki, ba sai kin ƙara ɗora wani ba, zanci wanda jikana ya ci".
"to Maama idan na zo ba zan dawo ba, yau ba'a ɓangarena yake ba".
"to shikenan. ki hanzarta ki zo Daughter, ina so zan yi wasa da jikana, ina so yau nayi ta kallon fuskar ki".