Sashe 113
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
idanuwan Turaki suka kawo ruwa calmly yace da ita,"kin tabbatar kina son Abba?".
tayi saurin ɗaga masa kai, yace,"to indai kina sonsa ki nuna masa hakan ta hanyar yi masa adu'a ko da yaushe, itace abar da yafi buƙata daga gareki ba kuka ba, kuma ta hakan zai yarda da cewar kina sonsa, sai yay ta saka miki albarka daga can".
ya ɗago haɓarta yana kallon cikin idonta yace,"Fulani nah wanda ya mutu ba ya dawowa, Abba ya tafi tafiyar da ba zai ƙara dawowa garemu ba sai dai muje mu same shi a aljannah a yayinda muma muka zama tarihi, dan haka ki daina kuka kinji Fulani nah, idan Abba ya tafi kina da ni, ni zan maye miki gurbin Abbanki, zan ba ki wannan gatan da kike buƙata, zan ba ki kwatankwacin irin wannan kulawar da kike biɗa, uba dabanne ba zance zan ba ki soyayya irin tasa ba, amma zan ba ki soyayya irin wacca ba za ki yi maraici ba".
Fillo ta janye hannunsa daga haɓarta ta faɗa jikinsa ta kewaye shi da duka hannayenta, tayi ta kukanta a hankali a hankali yana jin hawayenta na sauka a bayansa masu ɗumi, hawayen da yake jin zafinsu kamar garwashi, bai hanata ba har sai da tayi me isarta tukunna ya janyeta yana tambayarta me take son ci.
kanta na ƙasa tace,"bakina babu daɗi".
"daurewa za kiyi, kinga cikinki babu komai, idan ba ki ci abinci ba Ummi zata shiga damuwa".
ya sauka akan gadon yaje ya buÉ—e duka coolers na abincin kusan guda goma yace,"look here".
ta É—ago ido tana kallon coolers É—in abincin da mamaki, kamar abincin da sarki ya biÉ—i a kawo masa, kowanne kuma babu na yarwa, yaga idonta ya manne akan cooler É—in ferfesun kayan ciki, sai yabi duk ya rufe sauran sannan ya É—auko plate ya zuba kayan cikin da yaji ganyen zogala aciki, yazo ya ajiye akan table ya rufe.
ya dawo bakin gadon ya kamo hannayenta yace,"muje ki wanke baki".
tana kallon babban yatsanta tace,"ya akayi naji wancan ciwon?".
ya É—an rufe idonsa yaja numfashi sannan yace,"kin manta?".
ta É—aga masa kai, yace,"ok to zo muje mu dawo sai in tuna miki".
yay helping ɗinta ta sauko akan gadon suka wuce toilet, shi ya shiga ciki ya tatsa macline ajikin sabon tooth brush sannan ya fito ita kuma ta shiga, after 4minutes ta fito tana yamutsa fuska saboda jikinta da take jin duk gaɓɓanta na mata ciwo, yana kallon fuskarta ya san alwala tayi, ganin ƙafar ma janta take yi yace,"ko in ɗauke ki?".
tayi saurin girgiza masa kai alaman a'a,dan haka ya kama hannunta suka tafi a hankali har kan gadon, babu yanda bata yi ba akan ya barta taci ferfesun da kanta san yaƙi, shi ya dinƙa bata har sai da ta cinye shi akan dagewar da yay tukunna ya aje plate ɗin.
kusan duk abin da aka ajiye a wurin nan sai da ya dinƙa ɗiba yana bata ko da 1 spoon tayi sai ya haƙura, ya ɓalle murfin hollandia shima ya zuba a cup, ta dinƙa sha da kaɗan kaɗan. yana cikin bata ne wayarsa ta shiga ringing, ƙwayar idon Fillo ta sauka akan sunan me kiran, ta ɗago ta kallesa sau ɗaya, ta kauda fuska daga cup ɗin da yake kawowa bakinta, bata san me yasa ba ta tsinci zuciyarta na yi mata wani irin zafi, kawai sai ta koma ta kwanta ta juya masa ba ya tana zura duka yatsunta a baki tare da rumtse idonta.
ya aje cup ɗin hankalinsa tashe ya shiga tambayarta menene, ya kai hannu zai shafa fuskarta ta ma-ke hannun tana janyo top ɗin rigarsa da ke aje a gefen gadon ta rufe fuskarta, ya dinƙa kallonta a ruɗe yana jin kamar bai san yanda zai yi ya lallasheta ba.
a karo na uku wayarsa ta kuma yin ringing, yaja gajeran tsaki ya É—aga wayan ransa babu daÉ—i, yay shiru ba tare da yace komai ba, sallamar ma a ciki ya amsa.
daga ɓangaren Ilham tace da shi,"Hammah mun dawo".
tayi maganar da sauti me bala'in ban tausayi. jin yay shiru ta sake cewa,"Hammah".
sai da ya taushi zuciyarsa sannan yace,"kun dawo lafiya?".
tace,"lafiya lau".
yace,"ya me jikin?".
ta fashe da kuka tace,"ba sauƙi, har gwanda ma Mami ta mutu akan halin da take ciki".
yace,"Allah bada lafiya, ina abu ne yanzu".
yana faɗar hakan ya katse kiran ya mayar da hankalinsa kan Fillo, duk yabi ya rikice da sheƙar kukanta da yake ji na fita a hankali, yay ƙoƙarin ɗagota taƙi bari sai da ya shiga roƙonta kamar ƙaramin yaro sannan ta yarda ta miƙe zaune.
yaga uban hawaye duk sun wanke mata fuska, ya zare yatsun nata daga bakinta, daidai da kukan da ta ɓoye ya samu ƴancin fitowa, hankalinsa ya kai ƙololuwar tashi ya rungumeta yana cewa,"da kin san irin azabar da nake ji da zubar hawayenki, da kin tausaya min kin ƙara taimakona a karo na biyu, na roƙe ki dan Allah dan Annabi ki daina kar hakan yaywa zuciyarki da ke cikin ƙirjina illa".
ta janye a jikinsa ta kallesa tace,"dan Allah".
yace,"dan Allah what?, me kike so nayi miki? faÉ—i duk abunda kike so Fulani nah am ready to do it".
tayi ƙoƙarin dakatar da kukan tace,"ka sakeni dan Allah".
sai ya ƙame ƙam kamar wanda aka dannawa remote, ya zareta daga jikinsa, kallonta kawai yake da wani irin yanayi da shi ɗaya ya san me yake ji, in har da tasan wannan kalmar ta saki abin da take haifar masa da ba zata dinƙa faɗarta ba, to amma bai san ta yanda zai yi ya fahimtar da ita hakan ba, kuma yanzu lallaɓata yake ita da lafiyarta shiyasa ba zai yi amfani da fushinsa wurin nuna mata cewar ba ya so ba.
ta ƙara cewa,"in kana ƙaunar Allah da Annabi ka sakeni, ni ba zan iya zama da kai ba". ta faɗa tana kuka sosai.
ya sauke doguwar ajiyar zuciya yana furzar da iska daga baki sannan yace,"idan ban sake ki ba za ki mutu?".
ta É—ago kumburarrun idanuwanta tace,"ni ban sani ba amma dai zan cutu".
idanuwansa cikin nata kamar yanda nata ke cikin nasa ya kama hannunta ya ɗora a saitin zuciyarsa yace,"to ni muddin na sake ki wallahi mutuwa zanyi, so please kar ki ƙara faɗin haka i beg you".
ta dinƙa masa kuka Turaki ya rasa inda zai tsoma ransa, ƙiris shima yake jira yasa kukan, ga kiran wayar Boɗejo sai shigowa yake yi, yay banza da kiran yaƙi ɗagawa.
sai da kiran Baffa ya shigo sannan yay picking, kuma yana ɗagawa abinda Baffa yace da shi yasa shi damƙar hannun Fillo ba shiri.
Baffa ya kashe wayarsa ransa a ɓace, Boɗejo na tsaye akansa sai zazzaga bala'i take yi.
Turaki yay calling lambar Maama, ko da ta ɗaga daga muryarsa ta shaida ɓacin ran danke danƙare a xuciyarsa, tace,"lafiya me babban suna?, ba damuwa naji a muryarka ba illa zallar ɓacin rai, mene ya faru?, kai da wa?".
ya rumtse ido yace,"Maama Baffa ne ya kirani".
"yace maka me?".
kamar zai yi kuka yace,"wai na koma yanzu Ilham ta dawo, Maama...".
bai ƙarasa ba tace da shi,"baka ce masa mahaifin matarka ne ya rasu ba?".
yace,"Maama to ba ya sani ba, ina jiyo muryar BoÉ—ejo nata hayagaga".
tayi tsakin takaici tace,"kayi haƙuri me babban suna, kashe wayar ga shi yana kirana, i will call you letter".
Turaki ya kashe wayar yana kallon Fillo da ke ta kokawa da shi tun É—azu tana so ta sauka daga kan gadon shi kuma ya hanata.
"da me kike so naji wai?".
ta kifa kanta a ƙirjinsa tana ƙara faɗin,"dan Allah ka sakeni ni bana sonka".
yace,"naji, yanzu dai ki yi shirun zan yi abin da kike so".
tayi shirun tana É—agowa ta kallesa tace,"yanzu ai nake so, ni ka sakeni yanzu sai kayi tafiyarka can É—in".
yace,"ehh zanyi amma idan kin yarda kin bini munje gida tare, zan miki abin da kike so a daren yau, gobe da safe sai na dawo da ke".
yana faɗar hakan tasa hannunta da iya ɗan ƙarfinta ta ture shi ta fita daga ɗakin, a ƙofar ɗakin ta sami Kaka zaune akan kujera ta faɗa jikinta tana fashewa da sabon kuka.
*Vote, Comment and Share.*
[9/4, 13:21] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
*44*
duk ta yanda aka so a lallashi Fillo tayi shiru akan kukan da takeyi taƙi ta daina, ta ƙara bawa kowa matuƙar tausayi, kukan nata ya dinƙa taɓa zuciyoyi, Adda Asma ta kwantar da ita jikinta anata ƙara bata haƙuri.
lokacin Hamid ya shiga office ɗin Dr ya karɓo takardar sallama, dama a daren za'a sallamesu su wuce da safe to kuma ganin jikin nata yayi sauƙi sai suka ga is better su wuce kawai, bai fi 10minutes ba a office ɗin Dr ba suka fito tare da Bobbo da ya shiga office ɗin daga baya.
Hadimai suka dinƙa fito da kaya daga room ɗin da akayi addmiting nata suna kaiwa motar Bobbo, sai a yanzu da suka zo tafiya Fillo ta sami damar ganin sabbin fuskokin da bata taɓa saninsu ba a rayuwata, but tana kallon Gaji da Adda Hassana gabanta ya faɗi, saboda kamannin da suke yi sosai da Abbanta, shi kawai ya fisu haske ne dan kamar Umminta yake, in ba sani kayi ba za kai tsammanin larabawa ne ba fulani ba, su Adda Asma kuma duk kana kallonsu ka san jininsa ne, abinda ya bata mamaki kowa sai nan da nan yake da ita kamar wata gwal.
Turaki dai na tsaye yana ta kallonta ya kasa ɗauke idonsa akanta, zuwa lokacin yayi recieving kiran Baffa yafi sau biyar duk akan ya taho, kowanne kira kuma ya ɗaga sai yaji Boɗejo na zazzaga masifa da bala'i, banda ma dai Baffa ɗin ke kira da babu abinda zaisa ya ɗaga, daga ƙarshe ma sai ya fara ignoring call ɗin.
Adda Samira ce ta fahimci yana so ya keɓe da matarsa hakan yasa taja su Adda Juwaira da su Kaka suka bar wajen, kamar ƙiris yake jira kuwa suna barin wajen yana saurin isa gaban Fillo da hazari ganin tana ƙoƙarin tashi ta bar wajen.