Sashe 123
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bello ya ƙyalƙyale da dariya bai ce komai ba, for few seconds sannan ya ce,"yanzu ma ai na san akwai abin da ka ke so ka faɗa min tun ranar nan amma ka kasa, kuma na tabbatar ba dai-dai ka aikata ba shiyasa ka ke shakkar faɗa min, yanzu dai ina jinka me ka ƙara zuwa ka aikata da babu shawara balle zurfin tunani, dan na lura da kai tun da masu jeren kayan nan suka zo ka bi ka rikice kamar mara gaskiya".
Turaki ya dafe kansa, sai da ƙyar ya iya faɗawa Bello abin da yake ransa, furucin farko Bello ya ce da shi,"totally MT baka da hankaliii, what are you telling me?, kai wai mistake ɗin farko ba ya zamar maka izina sai ka aikata da yawa?, har yanzu fa baka fita da ga matsalar da kake ciki ba shi ne zaka ƙara saka kanka a wata?, ko kuma ɓacin ran iyayen ne ba ya damunka?".
ya daki dining table ɗin da hannunsa yana nuna shi da yatsa ya ce,"sam sam babu hankali a tare da kai, abubuwan da kake aikatawa masu lafiyar ƙwaƙwalwa basa yinsa".
Turaki ya ture yatsan nasa yana cewa,"karka ƙara nuna ni kuma karka ƙara ce min banda hankali, damuwata nake faɗa maka matsayinka na aminina, mafita na ce ka tayani nema ba wai ka tsaya faɗa min baƙaƙen maganganu ba".
ran Bello a ɓace ya miƙe tsaye,"an faɗa baka da hankalin, ka yi abun da za'ai maka kallon me hankalin ne?, har yaushe ka zauna ka zartar da wannan hukuncin akan yarinyar da gaba ɗaya ba ta cancanci haka da ga gareka ba?, kai da ba zaka zauna ka yi shawara da mutum ba sai bayan ka aikata abun da zai zame maka damuwa, kai ko da wani ma ya ce ka saketa ma ai sai ka zazzage shi, amma saboda toshewar basira irin taka yarinyar da banda taimakon Allah da kuma taimakonta da yanzu ka zama tarihi ko kuma da yanzu kana nan acikin lalurar da aka kasa maganceta, asiri fa!, asiri fa ta dinga ɗaukewa akanka MT, akwai wanda zai iya sa kansa a haɗari ne just becouse to save some'ones life irinta, sunanka fa kawai ta sa ni ba kai ba kuma tayi helping ɗinka har kake raye zuwa yanzu kuma cikin ƙoshin lafiya".
takaici yasa Bello yin shiru yana rasa ma a wanne sahu zai saka Turaki, sai ya ƙyasta yatsunsa biyu ya ce da shi,"to bari kaji na faɗa maka, fushin Baffa akanka ba komai ba ne akan fushin Mum da zaka gamu da shi, sarai dai ka san da cewa tana son yarinyar nan. kuma in ƙara faɗa maka abu ɗaya, ba zan waiwayeka ba a sanda ka faɗa cikin cakwakiya ta biyu, ban san ka aikata ba kuma ba kai shawara da ni ba a sanda zaka aikata ba, dan haka karka kuskura ka neme ni".
yana gama faɗar hakan ya fice, Turaki ya bi bayansa da kallo kafin ya tashi ya wuce ɗakinsa. babu abin da yake so yanzu irin yaje gidan su, amma Baffa ya ajiye ƙaton soja a bakin gate ya ce duk ranar da yaga wata fuska ko da mai kama da tasa ne a kama shi a ɗaure.
washegari da safe yana kwance a ɗaki aka murɗa handle ɗin ƙofar ɗakinsa, motsin ƙofar yasa shi buɗe ido yana kai dubansa ga me shigowar, ganin Maama yasa shi miƙewa zaune da sauri, ta iso wajensa tana jin tausayinsa na ratsata, ta zauna a kusa da shi ta dafa shoulders ɗinsa ta ce,"ya ƙarfin jikin naka".
ya ce,"da sauƙi sosai".
ta bi shi da kallo sosai tana lura da yanayin jikin nasa, babu kumburin ko kaÉ—an duk ya sace, ramar ce dai kawai da tayi masa yawa.
ta sauke numfashi ta ce,"Bello ya ce min ba ya gari shiyasa na taho, ina drugs É—in naka?".
yana kallonta ya ce,"ƙarya yake yi, fushi yake da ni shi ne ya tafi".
Maama ta girgiza kai tana murmushi ta ce,"Allah dai ya kyauta muku, anjima ne za ku shirya ai".
ta miƙe tana isa table ɗin da yake tsakiya ta ɗauko magungunansa ta dawo ta zauna, ta ɓallo ta zuba masa a baki.
"ka sha ka ƙara jin ƙwarin jikinka, anjima akwai dinner. su ma suna kan hanya sun taho kawo Fillo, amma ba nan ɗin zasu kawota ba direct, za su sauka a wurinmu after an dawo da ga dinner sai mu kawo maka ita, hakan ai ya yi ko? baka da lafiya ban zauna nayi shawara da kai ba me babban suna".
shi dai bai iya cewa komai ba, Samha ta shigo ta dire basket na kayan abinci, ta zuba a plate kamar yanda Maama ta umarceta.
kamar wani ƙaramin yaro haka Maama ta dinƙa feeding nasa, bayan ya gama ci ta cika masa bathtube da ruwan zafi ya shiga yay wanka, sanda ya fito ba ta ɗakin, bayan ya gama shiryawa zai fita sai gata ta dawo.
"ai ba fita zakayi ba, koma ka kwanta ka huta. alfarma ɗaya nake so a wurinka me babban suna, ka cire damuwa don Allah, ka ɗauko rigar walwala da farin ciki ka saka, yau babbar rana ce a wurinka, ranar da ta ke zaɓinka".
ya ce,"Maama Baffa...".
ta dakatar shi tana faɗin,"sau nawa zan faɗa maka in dai batun Baffanku ne ka ajiye shi a gefe, kai fa kujera ne a wurinsa kana zaune zai neme ka, duk wannan hawa saman da ya yi na ɗan lokaci ne, tsohuwarsa na hucewa zai huce, space kawai yake buƙata, kai ma kuma da ma kana buƙatar space ɗinsu, mu kanmu da ka gani ba ya kula mu, jiya ma ya bar mana gidan ya kaɗa inda bamu sa ni ba".
Turaki ya ja ajiyar zuciyar zai yi magana ta ƙara katse shi,"Bello zai zo maka da kayan da zaka saka anjima, Khalil zai riga ku zuwa can wajen dinner ɗin".
ya gyaÉ—a kansa kawai kamar yaro bai ce komai ba har ta fi ce.
*Taraba*
tun safe da Fullo ta tashi tana yin sallar asuba ta shiga toilet ta rufe kanta, a ƙasan tiles ta zauna tana ta kuka ta damƙe takardar sakinta a hannunta, so take ta yi musu bayani amma ta rasa ta inda zata fara.
Sai da Ummi ta shigo sannan da ƙyar ta buɗe toilet ɗin ta shiga ta fito da ita, ta bi su Maijidda da duk suke kwance kan gado suna ta baccin gajiya, dan ba su tashi a event ba sai 11 na dare, kuma suka dawo gida suka ƙara ɗorawa da wani ba su suka kwanta ba sai 3, shiyasa sallar asuba ma duk da ƙyar suka yi.
Ummi ta zaunar da ita akan darduma ta ɗauko Alqur'ani ta bata ta ce,"kiyi ta karantawa za ki ji sauƙin koma me ke damunki. tun da dai ni da nake mahaifiyarki ma ban isa ki faɗa min matsalar da ke damunkin ba, to ga maganin kowacce kalar damuwa nan ki ta karatu, ƙarfe sha ɗaya naji Dada na batun jirginku zai tashi".
Fullo dai kallonta kawai take yi, har Ummi zata fita sai kuma ta ƙara cewa da ita,"in ma kina tsoron faruwar wani abu ne a auren naku ki yi ta ambaton innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, Allah zai sanya komai ya zamo mafi alkhairi a gare ki, ni dai har zuciyata bana jin komai a game da tarewar nan taki ba, kullum adu'a nake ina faɗawa ubangiji, kuma na gamsu da son da yaron nan yace yana yi miki".
Ummi ta fita ta barta, ita kuma ta buÉ—e suratul Yusuf ta shiga karantawa, kamar almara sai ta fara jin duk wata damuwa da fargaba da komai yana tafiya yana barinta.
ƙarfe takwas Ummi ta dawo ɗakin, hannunta riƙe da tray wanda ke ɗauke da kayan breakfast, ta ajiye a gaban Fillo, ita kuma ta aje alqur'anin hannunta ta miƙe ta shiga toilet ta wanko bakinta ta dawo, tare suka yi breakfast ɗin ita da Ummi, su na ci Ummi na yi ma ta ƴan nasihohi akan sabuwar rayuwar da zata tsinci kanta, da maganganu tausasa da duk suka sanya sauran damuwar da ke tare da ita barinta.
ƙarfe tara Ammi ta shigo ɗakin nasu tare da me makeup, ta tarar su Maijidda da Amatullah sun sa Fillo a gaba sai tsokanarta su ke, saboda ta daina kukan da ta ke yi sai su ke cewa ashe dama so take yi akaita gidan miji shiyasa ta ishe su da kuka, yau kuwa ga idonta nan ƙyam sai ƙyallin farin ciki da yake yi, ita dai tana zaune babu wanda ta tankawa.
Me makeup É—in ma sai da ta tsokaneta, Ammi na kallonsu duka ta ce,"to bara ta bar muku É—akin sai inga wa zaku takurawa".
ta kamo hannun Fillo suka bar É—akin suka wuce sashin LamiÉ—o É—akin matarsa Diyam, anan aka zaunar da Fillo don shiryata, simple makeup aka yi ma ta amma tayi masifar kyau, gyaran jikin da akayi ma ta na 4days sai ka rantse an É—auki watanni ana yi, sai faman shining take yi kamar fatar kifi, fatarta ta zama kamar madara tsabar kyau.
riga da skirt na material me tsada cikin lefen da akayi ma ta na gida, sai aka É—ora ma ta alkyabba me mugun kyau red colour.
Dadda ta shigo ɗakin, ta shigo tana faɗin,"kaiii Diyam ɓangarenki ai gaba ɗaya ya karaɗe da ƙamshin amarya".
ta ƙarasa tana buɗe fuskar Fillo ta ce,"Masha Allah, Tubarkallah. Lallai Muhammad Turaki ya yi da ce da kyakykyawar ƴar mu, ai danasani na ƙayyade masa sabon sadaki".
zuciyar Fillo ta buga, tasa hannu ta dafe takardar sakin da ke maƙale acikin brezier ɗinta.
Dadda ta ce da ita,"ungo sha wannan".
Fillo tasa hannu ta karɓa tana yatsine fuska, zata yi gardamar da ta saba Dadda ta ce,"ke wannan ba magani ba ne ruwan tofi ne Dottijo ya bayar a kawo miki, ma za yi bismillah ki kafa baki ki sha".
tayi bismillah a fili ta kafa baki, ba ta sauke ba sai da ta shanye tass da ma tana jin ƙishirwa.