← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 176

Sashe 16

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"saboda nace kici ƙazantarki shine za ki buɗe ba ki kice min Hajiya ce ta girka, what do yo mean by saying that?".

ta ƙanƙame jikinta saboda ganin kamar zai saka ma ta hannu, ya hankaɗa kujerar baya ya fito yay tsaye gabanta, tana jin yanda hucin isakar hancinsa ke sauka a jikinta. kallonsa ta ke ta ƙasan ido, zata iya rantsewa wannan mutumin ko me jinnu ko kuma me ƙarancin lafiyar ƙwaƙwalwa.

yana shirin kai hannu ya shaƙi wuyanta don ta fassara masa abinda ta ke nufi da maganarta, sai ga Zaytuna ta shigo parlon, tun daga bakin door da ta hangesa tayi saurin ƙarasowa ta riƙe hannunsa tana dubansa a rikice.

"matsa baya". tace da Fillo wadda ke duƙe har lokacin, kuma jin hakan yasa tayi saurin matsawa da baya ta raɓe daga bango tana sauke numfashin kamar wacca tayi tseren gudu, zuciyarta cike fal da tsoronsa.

Zaytuna ta juya ta ƙara kallonta sannan ta ƙara maido da kallonta kansa. "please Hamma nah sorry".

idan da zata zauna zaman lissafi zata iya lissafa wucewar kusan rabin shakara rabon da taga ya shiga cikin wannan mood É—in, mai sauya shi ya fita daga Turakinsa ya koma wata halittar ta daban. zata faÉ—a ko aina ne he is very simple Man, abu biyu ne kawai a duniya masu rikiÉ—ar da shi, su saka ya fusata har ya aikata wani mummunan abun ba'a cikin hayyacinsa ba.

sai dai mamakin da ta ke ta ya Fillo ta fama masa ciwon da ke zuciyarsa, ko kuma garin ya ta taɓa abunda zai iya aikata kisan kai akansa?.

tana kallon Fillo tace,"me kika yi masa?".

tana girgiza kanta tace,"ni ban masa komai ba. abinci yace sai na cinye kuma ni na ƙoshi".

"an kira shi a waya ne?".
"ni ban sa ni ba".

Zaytuna tayi shiru, dole cikin biyun abunda ke haddasa masa ƙunci zuci ya faru. tasan ko menene baida alaƙa da mahaifiyarsu tunda Fillo bata san komai ba akai, amma duk yanda akai bisa kuskure ta taɓa Maama, shi kuma ɓangaren da baya ɗauka kenan.

idon Fillo na kan Turaki, tsab zata iya lissafa adadin jijiyoyin da suka fito raɗau ajikinsa, tun daga kansa har hannayensa da wuyansa. fahimtar da tayi masa mutum ne shi da ba'a sanya mahaifiyarsa a cikin kowanne lamari saboda muhimmancinta. kuma ita sai a yanzu take ganin rashin kyautarwarta, bai kamata dan yace taci ƙazantarta ba ta buɗi baki tace ai Hajiyarsa ce ta dafa, kenan jagwalgwalon ba nata bane na uwarsa ne, matsayinsa na wanda tasan ya bata shekaru da yawa bai kamaci irin wannan maganar daga gareta ba.

ko babu wannan ma yaci ace ta darajarta shi duk da jin kai da ta fahimci yana da shi, tunda ita da Kakarta a ƙarƙashinsu suke rayuwa sama da shekaru biyar, ba'a taɓa haɗasu da mara kyau sunci ba matsayin su na ƴan aiki, haka kuma ba'a basu makwanci mara kyau ba. idan ba zata manta ba me gidan da kansa na shiga ɓangarensu ya gaida tsofaffi, Hajiya Madina ce ma bata taɓa gani amma ta taɓa ji ance ta shiga sau ɗaya.

kawai sai tayi ƙasa da idonta tana jan yatsun hannunta, maganar Kaka na dawowa cikin kunnenta na wani lokaci can baya da ta taɓa faɗa mata.

"Halima dan Allah ki rage jin kai domin ke ba ɗiyar kowa bace, ki rage zafin zuciya, ki zama me haƙuri, ki zama mai sadda kai ga wanda duk kika san ya shiga ɓacin rai ta sanadiyarki, karki ce ba za ki bada haƙuri ba domin tsugunawa wada ba gajiyawa bane, ka zama me haƙuri ma da iya bada haƙuri wani babban arziƙi ne gare ka...bada haƙuri babu abinda zai rageki da shi sai dai ma ya ƙareki da abubuwa da dama...zai iya sawa aga mutumcinki, zai iya zama silar ɗaga darajarki".

Fillo ta rufe ido ta haɗiye wani busashshen yawu, a hankali ta shiga sauke gwiwoyinta har ta kai su ƙasan tiles ɗin. muryarta ta fito da amon rashin jin daɗi tace,"dan Allah kayi haƙuri".

hannunsa na cikin na Zaytuna ya damƙe da kyau, ya waigo yana mata wani irin kallo kamin yace,"cinye abincin nan shine zai wanke ki".

itama sai ta ɗago ido ta kalle shi,"to idan na cinye zaka haƙura?".

"kurma ce ke da ba kiji me nace ba".

faɗin hakan yasa ta miƙe ta zauna kan kujerar, har yanzu hannunta bai bar rawa ba ta ɗauki spoon ta fara tura abincin bisa dole. kuma har lokacin su na tsaye shida Zaytuna idanunsu duk akanta, daga yanda ta ke ci yasan cin dole kawai takeyi, sai dai shi babu ruwansa ko zata amayar sai ta cinye.

sai da tacinye tass tukunna ta É—ago da kanta ta kalle shi idonta na zubar da hawaye, yay saurin rumtse idonsa yana kauda kai gefe, idan da abinda ba ya son gani a rayuwarsa shine hawayen mace.

yana jin zata miƙe ba tare da ya kalleta ba yace,"wa zai shanye miki tea ɗin?".

jin hakan yasa tasa hannu ta ƙara goge wani hawayen, sannan ta kalli Zaytuna tace,"Anty na ƙoshi idan na kuma cin wani abu amai zanyi".

Zaytuna tace da shi,"Hammah ai mata afuwa".

ya wurgawa Zaytuna wani kallo sannan yace da Fillo,"kin zuba kinsha ko sai na barki da Allah akan zagar min Uwata da kika yi".

tayi saurin girgiza masa kai.
yace,"to zuba rabin kofi ki shanye".

tana zuba tea ɗin tana hawaye haka ma har ta shanye bata bar kuka ba. sai a sannan yay ƙasa da murya yace,"aikin da aka kawoki shi kawai za ki dinga yi, duk ranar da kika ƙara gigin saka hannu a abinda zanci sai kin cinye shi ta hanci".

yana faɗar hakan ya bar wurin, yana fiddo waya daga aljihunsa yay picking call ɗin Bello Ƙaraye. a bakin ƙofar parlo ya tsaya yana cewa,"bana part ɗina ina part ɗin Maama".

da faÉ—in hakan ya katse wayar ya maida aljihu sannan ya nufi kujera ya zauna.

Zaytuna ta wuce upstairs bayan tace da Fillo idan baƙo ya shigo ta kai masa ruwa da lemu. ta amsa da tou, sannan ta miƙe ta kwashe kwanukan abincin da aka tursasa mata ci ta kai su kitchen, ta dawo ta gyara wurin ta goge ya zama fess sai ƙyalli glass ɗin yake.

a kitchen ma kusan duk wani abu da ake cin abinci a cikinsa sai da ta fito da shi ta wanke, wannan koyarwa Kaka ce gareta, kwanukansu kullum sai sun wanke su ba iyaka wanda suka ci abinci ba kaÉ—ai.

a hankali ta ke yin komai gudun kar ta fasa wani abun tunda komai tangaran ne. bayan ta gama gyara kitchen É—in ta fito ta hau upstairs ta tambayi Zaytuna aina zata É—auki lemun.

Zaytuna tace,"ki buÉ—e friedge za ki gansu aciki, amma karki manta ki haÉ—a da cup".

ta amsa da,"to Anty". sannann ta sakko ta koma kitchen ɗin, sai da ƙyar ta iya buɗe friedge ɗin saboda bata san yanda ake buɗe shi ba.

drinks ne kala-kala aciki da ruwa na jarka, ta san dai ruwan amma lemun idan aka cire fanta bata taɓa ganin duk sauran ba musamman five alive na kwali. kawai sai ta ɗauka ƙaramin tray ta saka kowanne guda ɗaya tare da faro guda biyu.

lokacin da ta iso wurinsu Turaki ya sauke hannun rigarsa na dama yana nunawa Bello yanda ciwon wurin yayi, babu wanda yasan da zuwanta wurin balle tsayuwar da tayi tana bin ciwon nasa da kallo ganin yacca yay rami, ita bata taɓa ganin ma irin ciwon da yay haka ba.

cikin kaɗuwar ganin ciwon ta sauke idonta ƙasa kawai tayi tsaye a wurin, tafi ƙarfin minti uku kamin Bello ya ankare da ita yace,"bismillah mana". ya faɗa yana kallonta.

ta ƙaraso ta aje tray ɗin saman table ɗin da ke tsakiya, sannan ta tsuguna ta gaida Bello cike da ladabi shima kuma ya amsa mata da fara'a.
tana durƙushe Zaytuna ta iso itama hannunta ɗauke da bowls guda biyu, duka snacks ne aciki.l ta aje kusa da tray ɗin.

idonta na kallon Bello tace,"Hammah Bello ina kwana".

shima nasa na kanta yace,"lafiya lau Zaytun, ya kike ya hutu kuma?".

ta amsa mishi da,"lafiya lau wallahi, ya office?".

ya amsa da,"office babu daÉ—i, aminina ya gudu ya barni ni É—aya".

Turaki yace da shi,"sai ka jira Maaman ta dawo tunda ƙorafi ya kawo ka gidan".

Bello yay murmushi bai ce da shi komai ba suka shiga taɓa hira shi da Zaytuna. idon Turaki ya kai kan Fillo da ke durƙushe a wurin har yanzu, wani haushi ya kama shi, tunda ake ƴan aiki a gidan nan ba'a taɓa bagidajiyar yarinya irin wannan ba, shi bai san ba ma ko hankali ne bata da shi kwata-kwata.

"ke sai ance ki tashi ki tafi sannan za ki gurgura ƙafafunki ki tafi, ko kuwa kin zauna jin hirar da ba taki ba?".

kanta a ƙasa yake, kuma hankalinta ba'a garesu yake ba dan hirar da suke ma bata ji, banda yanzu da maganar tasa ta shigeta, tasan da ita yake, ba tare da ta ɗago ba tace,"ina jira a bani umarnin tafiya ne".

rai ɓace yace,"kiyi ta zama har a busa ƙaho".

ile kuwa yaga ko motsawa bata yi ba, wani sabon haushi ya turnuƙe shi, duk yanda akai ko aji bata taɓa shiga ba.

Fillo dai cikin ranta faɗi ta ke yi akan me zaisa ta tashi ba'ace taje ba salon ace tayi ba dai-dai ba, bata manta da wani lokaci ba lokacin da suka zauna a masarauta, Fulani ta bada aike a kaiwa Yarima Mansur, ita Kaka ta bawa ta kai, ta sameshi a wanjen shaƙatawa shi da abokinsa, data ajiye musu zata tafi ai cikin tsawa ya maido da ita da cewar uban wa ya bata izinin tafiya, akan haka har kusan horar da ita akayi, to dan dai Kaka na da matsayi ne a wurin Fulani.

to ita kuwa yanzu me zai sa ta kuma maimaitawa, ai jini ba wasa bane, shi da Yarima Mansur duk abu guda ne, balle shi wannan É—in da ta ke ganin yana da girman izza.
Chapter 16 · 0% Book details