Sashe 164
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta karɓi ledojin da ke hannunsa tana ƙara faɗin,"Allah lafiyarta lau, amma idan kana ganin a tasheta ɗin to".
"a ƙyaleta?".
ya gyaÉ—a kansa kawai, sannan a hankali ya tafi zuwa gadon, da tafukan hannunsa guda biyu ya kama kan Maama ya gyara mata kwanciyar.
ya zauna akan bedside drower yana kallon fuskarta, kamar tayi haske?, kamar kuma ta ƙara yin kyau?, sai yasa hannunsa a saman goshinta ya goge guntun gumin da yake ganin kamar idanuwansa na haska masa.
wucewar minti É—aya!, biyu, uku har zuwa biyar, zuciyarsa ta kasa samun natsuwa da baccinta, saboda haka sai ya kai hannunsa gefen filon, ya shiga dukan filon a hankali yana faÉ—in,"Maama, Maama, Maama".
ya kira sunan sama da sau goma amma shiru bata buÉ—a idanunta ba.
a yanda ya sani, duk tsananin baccin da Maamansa ke yi kiran suna ɗaya ne ya farkar da ita, balle ma ita bata da irin nauyin baccin nan, hasalima ko baccin take aka murɗa ƙofa aka shigo sai ta farka, ko kuma idan taji motsi.
dan haka zai iya cewa bai san lokacin da ya miƙe daga kan drower ɗin ba.
kuma maimakon zama a bakin gadon kamar yanda yayi niyya sai ya tsinci gwiwoyinsa da zubewa a ƙasa, kafin yaji wani nauyi ya ziyarci hannunsa, irin nauyin da sai da ƙyar ya iya ɗaga shi ya taɓata.
"Maama".
hannunsa ya sauka akan jikinta da yay sanyi, a yanzu da ya taɓata bai ga ta farka ba, haka bai ji ta motsa ba, sai yaji adadin faɗuwar gabansa ya ninku da kusan kaso tamanin da biyar.
sai kawai ya tsinci kansa da shiga tashinta kamar ƙaramin yaro, babu abinda yake da buƙata a yanzu irin ta tashi, ta buɗe idonta, ta kalli cikin ƙwayar idonsa kamar yanda zai kalli tata, ta faɗa masa wannan maganar da tace zasu yi idan ya dawo, bai taɓa jin ya damu da baccinta ba irin yau, bai taɓa jin baccin wani ya tsorata shi ba irin yau, bai yarda da wannan baccin ba, bai yarda da shi ba sam.
girgiza ƙafafunta kawai yake yi yana kiran,"Maama, Maama, Maama ki tashi na dawo, kin ce Papaya ta ƙare na taho miki da ita ga shi na siyo, ga takardar scaning ɗin jikokin naki ma na karɓo, su biyu ne kamar yanda kika gansu a mafarki. kuma mun yi magana da Baffan yace za'a buɗe makarantar islamiyar, idan ya so sai a haɗeta da boko, kuɗin da kika ce na kai gidan marayun na kai ga receipt ɗin, amma sun ce na faɗa miki akwai yara guda goma sha biyar da aka kwantar a asibiti, to sai naje asibitin na biya bill ɗin da ake buƙata, waɗan nan yaran ma da aka kai su sudan, sun kira ɗazu sun ce na faɗa miki result ɗinsu yayi kyau, gobe za su sauka a ƙasar nan, sun ce na faɗa miki suna sauka wurin ki za su fara zuwa, suna ta cewa ayi miki godiya su da iyayen su. gwandar a markaɗa ko yanka miki za'a yi?".
gaba É—aya a wani ruÉ—e yake maganar, kamar dai wanda ya susuce, ya juyo ya kalli Fullo da Nihal waÉ—anda ke tsaye a bayansa.
"Nihal ɗauko wuƙa ki yanka mata gwandar".
sai kuma yace da Fillo,"Halima taci faten?". a karo na farko da ya taɓa ambatar ainihin sunan Fillo.
"a'a naga tana bacci shiyasa ban tasheta ba".
"sauri ki zubo mata Halima, yanzu zan tasheta".
kusan a tare Fullo da Nihal suka juya jiki duk a sanyaye, hannayen Fillo na karkarwa ta buɗe flask ɗinta zuba faten tsakin da yawa, kafin ta yunƙura ta miƙe daga duƙen da take Turaki yazo ya karɓa, karɓar tasa tayi daidai da shigowar Nihal daga ɗauko wuƙar, ta ɓara ƙwallon gwadar ta yi masa wata iriyar rabawa, cikin sauri ta isa ta ajiye plate ɗin akan table ɗin da Turaki ya ɗauko ya ajiye a gaban gadon.
har yanzu baya jin mazaunansa za su iya zama akan wani abu, don haka ko a yanzu ma gwiwoyinsa ƙara zubewa suka a gabanta, kafin yasa hannu ya juyo da kwanciyartata saitinsa, ya kalli fuskarta, ya kalli murfin idonta da yake a rufe, sannan ya kai ɗaya hannunsa ya kamo tsintsiyar hannunta guda ɗaya ya riƙe, tare da kai ɗaya hannun nasa ƙasan hancinta.
jijiya bata motsi!, haka ma numfashin baya fita!, sai ya ƙara maida hannunsa wuyanta, nan ma beat ɗin dake wurin ba ya harbawa. ya san akwai suma kuma ya san akwai mutuwa, kamar yanda ya san banbancin kowanne, sai dai ba ya jin zai iya ɗaukar abin da yake ganin gaskiya ya ɗora Maama a wannan matakin, ba zai iya ba, ba kuma ya jin zai iya.
don haka sai ƙafafunsa duka biyun suka tankwashe, yayinda da dukkan hannayensa ke riƙe da nata, a sanda kuma ƙwayar idonsa ta kasa ƙiftawa akan fuskarta.
"ba ki taɓa yin bacci me nauyi ba irin na yau Maama, ba ki taɓa ba. tun ina ƙarami ba kya iya baccin rana kawai saboda mu, balle ma har ki sami damar yin me nauyi, amma yau zan bar ki ki huta, ki yi baccinki yanda ya kamata, na san kin gaji ne, zan zauna tare da ke har sai kin farka".
a lokacin da yay shiru da maganar, a lokacin yaji tarin ruwan hawaye sun cika ƙwayar idonsa, zubowa suke so suyi ya sani, amma ba zai ba su damar hakan ba har sai abun da yake gudu akan farin cikinsa ya tabbata.
shigowar Hajiya Ramla ɗakin yasa shi juyawa ya dubeta, sai ya ganta gaba ɗaya a rikice, cikin irin rikicewar nan da bai taɓa ganinta aciki ba.
"Madam, Maaman yara, kar muyi haka da ke, kar kiyi mana irin wannan baccin, tashi haka don haka don Allah Madam".
zantukan da Hajiya Ramla ke yi kenan a sanda ta sami zama a gefen Hajiya Madina, sai ta É—agota zuwa jikinta, sai taji gaba É—aya jikinta ya saki, jikin Hajiya Madina ya zame daga nata ya koma makwancinsa.
ƙafafun Fillo suka tsuguna a kusa da Turaki, ta dafa kafaɗunsa hannuwanta na rawa, sai taji ɗan cikinta ya motsa a lokacin da ya riƙo nata hannun, ya juyo ya kalleta, suka haɗa ido tana ganin abun da bata taɓa gani ba acikin idonsa, ruwan hawaye!, ruwan hawayen da su ka sanya zuciyarta bugawa.
lokacin da Hajiya Ramla ta tabbatar da baccin Hajiya Madina ba na farkawa ba ne, lokacin tayi ƙarfin hali da dakiyar kallon Nihal, wacce ke tsaye ta kasa ƙwaƙwƙwaran motsi, idanuwanta duk biyu a waje.
"Mum Maama bacci take yi ko me?, suma tayi?, zata farka?, ana ta tashinta taƙi ta tashi".
"idan baka saba aiki ba kayi to duk jikinka sai ya mutu, ina tunanin gajiya ce tasata wannan baccin me nauyi, ba sai mun tasheta bamu barta ta huta sosai".
sai ta juya ta kalli Turaki, ta ƙara juyowa ta kalli Nihal ta ce,"ina wayata?".
"Mum gata nan a hannun ki ai".
tsabar ruÉ—ewa ta manta ma da wayar na hannunta, ta shiga contact ta danna kiran lambar Family Doctor É—in su.
yana É—aga tace da shi,"don Allah ka iso gida yanzu".
bayan ta ajiye wayar Nihal ta ce da ita,"Mum wa kika kira?".
"Dr Ibrahim ne".
sai a sannan Turaki ya ɗago ya kalli Mum, mene na buƙatar likita kuma a wannan lokacin?, idan ya zo me zai yi?.
su ka haɗa ido da Mum ɗin, tace da shi,"da yake tace min tana ciwon kai ɗazu, gwara ya zo ya dubata wataƙila BP ɗin ne ya hau ba mu sani ba".
ta fita a riki ce, tana sauka ƙasa taci karo da Sameer da Khaleel, sai suka tsaya kallon juna.
"da ma ba ku fita ba?".
Khaleel yace,"dawowa muka yi, lafiya Mum muka ganki a haka?".
"a'a babu komai, ko zaku koma kuga idan Baffa ya dawo?".
Sameer ya ce,"yanzu ya kira mu, yace ya kira wayoyin kowa bai samu ba".
"to ku tsaya anan ku kira min shi a waya".
ta faÉ—a tana juyawa ta koma saman, Khaleel ya bi bayanta da kallo zuciyarsa cike da nazari da zurfin tunani.
a san da Dr Khamis ya ƙaraso, idanuwan kowa na kansa a lokacin da yake wasu dube-dube a fuskar Hajiya Madina, da kuma gwaje-gwajen da yake yi.
ban da Turaki da idonsa ke kan Maama kawai, yana jin wani bala'in ruÉ—ani na shigarsa.
cikin ƴan mintuna kaɗan Dr Khamis ya gama bincikensa, a sannan ne kuma idanuwan Turaki su ka koma kan likitan, yana kallonsa ya matsa kusa da Mum da Khaleel, wanda yake tsaye cikin ƙarfin hali. ya san dai likitan bayani yake yiwa su Mum, domin yaga bakinsa na motsawa, laɓɓansa na motsawa da harufan da riga ya san ma'anar su.
kuma cikin sakanni uku sai ga Hajiya Ramla ta dawo kusa da Hajiya Madina, ta kamo hannayenta ta riƙe acikin nata, kafin a hankali laɓɓanta su tale da furta kalmar,"innalillahi ra'inna ilaihi raji'un, gare shi mu ke kuma gare shi zamu koma".
furucin da ya haddasa motsawar zuciyar Turaki sannan ƙarfin bugunta ya ƙaru a lokaci ɗaya.
idanuwansa suna kallo Mum ta ɗauki zani ta rufe Hajiya Madina da shi, ta rufeta har fuskarta, ta lulluɓeta da wannan zanin da ta ɗauko a jiya tace musu ta siyo shi ne saboda goyon jikanta.
ba zai manta da wannan lulluɓin ba, ba zai manta da shi ba har a bada.
sai kawai ya kifa fuskarsa akan ƙirjin gawar, hannunsa na dama kuma ya shige cikin sanyayyan nata hannun na dama.
"Maama, Maama, don Allah ba yanzu ba Maama".
yay maganar da wata karyayyar murya, a san da yay wannan furucin, a sannan ne hawayen da suka taru acikin idonsa suka sami nasarar gangarowa saman kumatunsa. idanuwansa suka runtse, hoton rayuwarsu na tsawon shekaru 27 na haska masa daki-daki, a lokaci ɗaya kuma duk wani sauti na muryarta na amsakuwa acikin kunnensa da cikin kansa, sautin muryar da ya tabbatar ba zai ƙara jinsa ba.