Sashe 130
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fillo ba ta iya ba ta amsa ba, haka ba ta iya kallonta ba, Hajiya Madina ta riƙeta suka yo waje tana cewa da Nihal,"ko ma ki tayar da mota". sannan ta ƙara cewa da Fillo,"ina me babban sunan?". sai a sannan ta iya buɗe baki tace,"ya fita".
san da motar Maama ta fita da ga gidan Baba me gadi ya girgiza kansa cike da tausayin Fillo, yarinya ƙarama ana neman a ɗora ma ta hawan jini, tun ranar da aka kawota ya fuskanci ba auren soyayya akayi ba, dan shi dai bai taɓa ganin Turakin ya shiga part ɗin ba sai ɗazu da ya fito a fusace kamar macijin da aka dannewa kai.
direct asibiti mafi kusa suka wuce, tun tahowarsu Maama da Nihal ke jera ma ta sannu, su na zuwa cikin gaggawa Dr yay ma ta treatment ɗin wajen, ya cicciro pieces na glass yafi biyar a tafin hannunta, aikuwa tasha azaba dan jini kamar ana tatsarsa hannun duk ya caɓe, akai ma ta allurai, Nihal taje pharmacy ta karɓo maganunguna, lokacin da ta dawo an naɗe hannun Fillon da uban bandage.
daga fitowarsu zuwa yanzu kuwa Maama ta kira wayar Turaki yafi sau bakwai duk ba ta shiga, kuma duka lines É—in nasa, hankalinta duk a tashe yake da ciwon Fillon, ta kira wayar Mum ta tambaya ko Turaki ya zo gida ta ce ma ta a'a, Bello ma yace ba sa tare.
kan hanyarsu ta dawowa Maama ta matsa mata da tambaya akan yacca akayi taji ciwon, ta kasa haɗa ƙaryar da zata faɗawa Maama ɗin, tai shiru ita dai sai rera kuka takeyi a hankali, har sai da taji ɓacin rai a muryar Maama tukunna ta ce,"wayarsa na fasa masa ban sani ba".
Maama na kallonta ido buÉ—e ta ce,"fasa waya kuma sai kiji ciwo haka?".
tayi shiru tana daɗa yin ƙasa da kanta, Maama ta dinƙa kallonta tana so ta nazarci yanayinta, uwar ramar kaɗai da yarinyar tayi ya isa ya shaida maka hankalinta ba'a kwance yake ba sam, dole akwai wata matsalar a ƙasa, dole da akwai abin da yake faruwa wanda basu san da shi ba, tun da me gadi yace ma ta Turaki ya fita babu jimawa ta san akwai matsalar da ke faruwa musamman da taga Fillo a wannan yanayin, babu tantama saɓani suka samu duba da yanda duk Fillon take a tsorace.
_me ce matsalar?._ tambayar da ta yiwa kanta kenan, sai dai babu amsarta. hakan ya sa ta kamo hannun Fillo tana kallonta ta ce,"ɗago ki kalle ni a matsayin Umminki wacce ba za ki taɓa iya ɓoyewa damuwarki ba".
idanuwanta suka kawo sabon ruwa sanda ƙwayar idonta ke shiga cikin ta Maaman, tausayin Maaman shi ya fara kamata ganin duk ta damu, kafin girma da kwarjinin Maaman su mamayeta gaba ɗaya, ba zata iya yi ma ta ƙarya ba sam saboda ta kare kanta ko kuma ta kare shi, ta sauke kanta ƙasa muryarya a hankali ta ce,"da wayar ta fashe ne shi ne ransa ya ɓaci yace sai na kwashe glass ɗin da hannuna".
da tsananin mamaki Maama ta ce,"me babban sunan da kansa?, ya ce ki kwashe glass da hannunki?, cikin hankalinsa yake kuwa?".
wannan furucin kaɗai ya shaidawa Fillo ran Maama ya ɓaci sosai. Maaman tai shiru ba ta ƙara magana ba sai faman jijjiga kai da takeyi, idanunta na kan waya tana ƙara trying lamar Turaki, cikin sa'a kuwa yanzu ta shiga sai dai har ta gama ringing bai ɗaga ba, ta ƙara kira nan ma bai ɗaga ba, sai da ta kira har sau uku sannan ta haƙura ta jefa wayar a jaka, cikin zuciyarta sai jinjina abin da Turaki ya aikata takeyi, ko da yake da ma ba'a sanin wani mugun halin namijin sai bayan ya yi aure.
Fillo dai idonta na kan hanya, tunaninta É—aya ta yanda zata faÉ—awa Hajiya Madina a sauketa a hanya, ta ga motar ta tsaya bakin wani islamic chemist, Maama ta buÉ—e ta fita ba tare da tace da su komai ba, ta bi ta da kallo ta glass har ta shiga kantin.
a lokacin ta buÉ—i baki ta cewa da Nihal,"Adda don Allah ina ne hanyar tashar barin gari?".
Nihal ta waigo tana kallonta ta ce,"me za kiyi acan?".
tai shiru ba ta ce komai ba, lokacin Maama ta buɗe motar ta shigo, sanda ta rufo ƙofa Nihal ta ce ma ta,"Maama wai tambayar tashar da za'a bar gari take yi".
Maama ta waiga taita kallon Fillo, wacce idonta ke kan hannun ciwon nata, tana nufin gidan su zata tafi kenan?, ta san ba komai bane ke damunta fa ce yarinta, bata ce komai ba tayi ƙwafa me ƙarfin gaske tana ɓallo maganin da ta siyo a islamic chemist ta bawa Fillo.
Nihal ta kashe sautin waƙar da ke tashi, saboda ta san idan ran Maama ya ɓaci ba ta son jin komai na shiga cikin kunnenta.
bayan doguwar tafiya Fillo taji motar ta tsaya, ta É—ago kanta tana kallon gate É—in gidan, gabanta taji ya faÉ—i hakan yasa babu shiri ta juya tana kallon gefen da Maama take tace,"Maama yace na bar masa gida".
"ki bar masa gida?".
ta É—aga kanta tabbacin hakan.
"saboda kawai kin fasa masa shegiya waya ya buÉ—i baki ya ce ki bar masa gida?".
sai kuma ta bar kallon Fillo ta koma kan Nihal ta ce,"shiga ciki ki gano min ko ya dawo".
a tsure Fillo ta ce,"Maama ai...".
kuka ya kubce ma ta ta kasa cewa komai.
Maama na kallonta ta ce,"ai me?".
ta buÉ—e baki tana jin kamar yawun bakinta yayi kaÉ—an su yi maganar da zata yi, tace,"he divorce me".
da wani mugun shock Maama ta ce,"what?, divorce!, ƙalu innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ya sake ki fa kika ce?".
tayi maganar tana jin kanta na mugun sara ma ta, tai saurin dafe shi tana rumtse ido ta jinginar da kanta jikin kujera.
Fillo ta fashe da kuka, Nihal ta shigo motar tana cewa,"bai dawo ba Maam...".
maganartata ta tsinke jiyo numfashin Maama na fita da ƙyar, a ruɗe ta ce,"innalillahi, Maama".
ta faÉ—a tana fitowa ta zagayo ta buÉ—e side É—in da take, "Maama". ta faÉ—a tana kamota.
Hajiya Madina na dafe da ƙirjinta da ƙyar ta iya cewa,"mu je gida da sauri".
tun kamin su ƙarasa gidan Nihal ta kira Mum a waya ta sanar ma ta cewa BP ɗin Maama ya tashi, kafin su ƙaraso tana tsaye a compoud hankalinta a tashe sai safa da marwa takeyi.
ko parking Nihal ba ta ƙarasa ba Mum ta buɗe, ita ta kama Hajiya Madina suka wuce, ko lura da Fillo ma bata yi ba, sai bayan ta kai Hajiya Madina bedroom ne ma taji tana ce mata,"ina amanar da mu ka karɓa?"
Mum ta ce,"wacce amana?".
Maama na magana da ƙyar ta ce,"Fullo". sai kuma muryarta ta karye tana cewa,"your excellency me babban suna ya cuce mu, sati ɗaya da aure ya saki yarinyar mutane".
Mum ta zabga wani salati tana waro ido waje ta kalli Nihal da Fillo da ke shigowa ɗakin. sannan kuma ta juya tana ƙara kallon Maama wacca taga kamar ba'a hayyacinta tayi maganar ba, ta ce,"wai saki kamar ya ya dai Madam?, saki na aure? ko wanne kalar saki ban gane ba?".
cikin ƙarfin hali na irin zafin da Maama ke ji a ƙirjinta ta ce,"divorce dai da kika sa ni, kawai saboda ta fasa masa waya bata sani ba, ki duba hannunta ma ki gani ciwon da yaji mata".
farat ɗaya ran Mum ya kai ƙololuwar ɓacin da bai taɓa yi ba, ta ce,"ba shi da hankali ko kuwa shaye-shaye ya fara bamu sani ba?".
ta kalli Nihal tace,"kirawo min shi dan ubansa".
sannan ta kalli Fullo tace,"laifin me kika yi masa da har zai sake ki?".
ta zube gwiwoyinta a ƙasa tace,"ai dama tuntuni na ya sake ni".
Maama ba ta san lokacin da ta miƙe zaune ba tayi warkewar lokaci ɗaya, Mum ta nemi wuri ta zauna, a tare suka jefa mata tambayar,"wacce tuntunin Fullo?".
"tun before na tare, na kasa faɗawa kowa ne...". kuka yaci ƙarfinta tayi shiru tana rumtse ido.
Maama ta saki baki kamar yanda Mum tayi duk suka kasa cewa komai, wucewar daƙiƙu muryar Nihal ta kutsa cikin shirun na su da cewa,"Mum bai ɗaga ba".
ba tare da tace ma ta komai ba ta miƙa ma ta hannu Nihal ta ɗora ma ta wayar, ta lalubo lambar Bello ta kira, bugu uku ya ɗaga, a fusace tace da shi,"da kai da shi kunci kutumar ubanku, kuna ina?". tayi tambayar a tsawace.
zagin da tsawar suka daki kan Bello yayi zillo akan kujerar da yake, ya haɗiye yawu da ƙyar ya ce,"Mum". tai saurin katse shi,"zanci ubanka idan ka ƙara kiran sunana, na ce kuna ina?".
cikin ƙinƙina Bello yace,"ni ina office shi kuma ban san inda yake ba".
"ƙarya kake yi munafiki".
yace,"wallahi Mum rabona da shi tun last week, ko haÉ—uwa bama yi a office".
tayi shiru kafin tace,"to ka kira kirasa ka faÉ—a masa minti ashirin na ba shi yazo ya sameni".
ta katse wayar, Nihal tayi saurin karɓa ganin tana ƙoƙarin jefar da ita a ƙasa.
bayan minti biyu kiran Bello ya shigo, ganin Mum bata da niyyar É—agawa Nihal ta É—aga yace ma ta,"ki faÉ—awa Mum wallahi ina ta kiransa bai yi picking ba for morethan 4times, kuma ni ban san inda yake ba".
Nihal ta faÉ—awa Mum, sai tace ta kira ma ta Khalil, yana É—agawa Mum ta ce da shi,"ka kira min É—an banzan Hamma'nku ka faÉ—a masa tun banyi masa baki ba ya sameni a gida cikin gaggawa".
ba tare da jiran cewarsa ba ta kashe wayar.
ɗaki dai yay shiru tamkar babu wata halitta acikinsa, ran kowa a cunkushe, zuciyoyin kowa da abunda take saƙawa.
minti goma minti ashirin suka wuce, rabin awa ma haka, aka cika awa guda ma, duk su na zazzaune jungum jugum, Hajiya Madina ma ta kasa shan magungunan da aka ajiye mata.