Sashe 4
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kaka minanata bana mi nyaman kodume". (Kaka kawai bana jin daÉ—in bakina ne).
"To ko ananata beldum 6anduma?, nde an nyauma heftata'ke sae to guwallinima wakkati gotel.". (to ko ba kya jin daÉ—in jikinki?, Tunda ke ciwonki ba gane masa ake ba sai in ya kwantar da ke lokaci guda).
"mi jamo Kaka. nane Amir waddiniyam mangoroje, daga mi nastai min njaride be Maijidda.". (ƙalau na ke Kaka, ɗazu Amir ya kawo min mangoro, tun kamin na shigo muka shanye da Maijidda).
Kaka ta jinjina kai tace,"ni ai na iya fita a ban abin duniya na hana duk wanda ya gani na kawo maki saboda ina ƙaunarki".
Fullo ta ƙyalƙyale da dariya bata ce komai ba.
Kaka ta nemi wuri ta zauna tana gyaran man shanu, sallamar Maijidda ta ratsa cikin kunnuwansu san da take shigowa hannunta ɗauke da kwanukan abinci. Kaka da Fullo suka haɗa baki wurin amsa mata, ta ƙaraso kusa da Kaka ta aje kwanukan abincin.
"a'a me muka samu haka?". Kaka ke tambaya tana buÉ—e murfin tasar abincin.
"masa'Allah tuwon dawa har haka. Aina Yami ta samo si?".
Maijidda tace,"tace na faɗa miki Jakadiya babba ce tace a kawo miki. Wai kici ki ƙara ƙarfi da ƙiba".
Kaka tayi dariya tana faÉ—in,"to sikenan, godiya nake sosai. Dama kinga duk mun kasa cin shinkafar É—azu".
Rufe bakin Kaka kenan tambayar da Fullo tayi mata tayi wani wawan duka a cikin kanta, inda har sai da ta zabura taja da baya.
"Kaka idan mutum ya tone asiri ko ya ƙone shi, wani abu yana samunsa ne?".
"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yanzu wannan tambayar daga ina?, Fullo kullum faɗa miki nake bakinki ya dinga faɗar alkhairi ko yay shiru, yanzu tsakani da Allah kamarki ina ke ina magana akan asiri?, yanzu inda baƙuwan fuska wajen ba sai ya tsammaci wani abun daban ba. Dan shi ba zai dubi rashin hankalinki ba".
"kai jama'a Kaka, ina batun rashin hankali anan, tambaya ne fa mabuÉ—in ilimi...amma shikenan tun ba ki amsa min zan tambayi Amir".
"aikuwa tambayarki gare shi dai-dai yake da rabuwa da ke. Dan tsammani zai yi shi za ki asirce ko kuma kin yiwa wani ne. Kinga ni dai ki rabani da batun asiri, dama ya ya lafiyar kura? Ban gama fita daga tashin hankalin ɗazu ba za ki ƙara jefa ni cikin wani".
Maijidda tace,"Kaka tashin hankali kuma?, me ya faru?".
Kamin Kaka tayi magana Fillo ta amshe. "bafa wani abu bane. Akan wutar da ta tashi ɗazu ne wai shi ne take ta tsoro kar binciken da aka saka na gano musababbin tashin wutar ace ɓangaren masu aiki ne".
Ta miƙe tana ɗaura ɗan kwalinta tana cigaba da cewa,"kuma na faɗa mata tunda dai tasan ba ita ta saka ba mene zai sa ta damu kanta".
Maijidda tace,"to taya ma za'ace ɓangarenmu ne mu da ba zuwa wajen muke ba". Ta faɗa cikin dakiya, dan tunda akai zancen wutar jikinta ya fara ɓari, saboda ɗazu tana ji Yami na faɗin wai wutar sai da ta shiga har cikin lambu, ta kusa cinye rabin shuke-shuken ƴaƴan itatuwan da ke ciki.
"to ma ace ma ɓangaren namu ne, dama ni na gaji da zaman gidan nan...kinga idan aka koremu ma koma rugarmu mu hankali kwance".
Kaka ta ɗauko murfi zata ƙwala mata tayi saurin matsawa daga wurin tayi bakin ƙofa tana dariya. "Kaka bara muje gaida Hajjah Gana, kwana biyu ban leƙa ba kar ta shigo tana miki ciwon baki".
"kar ki yi dare". Shi ne abinda tace da ita, sannan suka sa kai ita da Maijidda suka fita.
Tun da suka fito Maijidda ke ta surutunta, Fullo dai bata ce mata komai ba. Har sai lokacin da Maijiddan ta ankare da inda suke nufa sannan tayi saurin dakatawa da tafiyan ta dubi Fillo tace.
"wai ina zamu je?".
"ina kika ga mun nufa?".
"cikin gida".
"to muci gaba da tafiya".
Maijidda tayi shiru tana kallonta kamin tace,"idan kina wani abun kamar ba ke ba. Wanne ɗan aiki ne kika taɓa ganin yaje ɓangaren masu gida idan ba Hajiya ce ta buƙaci zuwansa ba...ko kuma kin bawa wani ajiya ne?".
"babu wanda ya taɓa zuwa dan ko Kakata ma sau uku ta taɓa shiga. Ni kuma yau ina son shiga kuma tare da ke zamu je, dan ke ɗaya ce hanyar da nake da ita tiryan tiryan da zata kaini ɗakin Turaki".
Ai shirunta sai ya haÉ—e da sauke hannunta da Maijidda tayi daga saman kafaÉ—arta. Tayi saurin juyawa a tsorace zata koma inda suka fito. Da azama kuwa Fillo tasha gabanta.
"ke ban faɗa miki ba. ɗazu fa wutar da na haɗa asiri na ƙona". Ai kamin ta ƙifta ido ta buɗe Maijidda ta kwasa da gudu ta barta a wajen, dan ita har ga Allah ta fara tsorata da lamarin ƙawartata.
_Please don't skip any page without commenting, react and vote. Becoz thats the only way you will show your love and appreciation towards me. It encourage me to do more🥰._
Don Allah share to other groups fisabilillahðŸ™
Youtube Channel-Nishadi Multimedia
[8/6, 19:29] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
*©ï¸Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
*4*
*E9611, Ibb Way. Maitama Phase 1 Abuja.*
ÆŠil 1,2,3,4,5, Adadin seconds É—in da suka buga kenan ajikin agogon da ke manne a bangon É—akin, tagogin windon É—akin a buÉ—e suke, iska ta busa inda ta shigo ta cikin windon ta É—aga labulen tagar zuwa sama.
hasken rana ya ratso ta tsakanin labulen ya haska idon Turaki da ke tsaye a gaban madubi yana saka agogo a tsintsiyar hannunsa. Wannan hasken yasa shi kanne ido tare da ɗagowa ya kalla tagogin da iskar ke ta busowa zuwa ciki, na tsawon seconds ɗaya sannan ya maida kansa ƙasa yaci gaba da ɗaura agogon.
haka kawai daren jiya da zai kwanta yaji ba ya buƙatar iskar bature, ko ta fanka ko ta Ac, dalilin da ya sa shi buɗe window kenan, kuma ko da ya tashi sai ya manta bai rufe ba har ya kunna Ac, wanda sai a yanzu ya fahimci dalilin da yasa Ac ɗin taƙi yin sanyi yanda ya kamata.
ya gama taje sumar kansa ya miƙa hannu bakin gadon da hularsa ke ajiye zai ɗauka, yana ɗora hannu akai agogon ɗakin ya buga ƙara, sai ya ɗago kansa a kaikaice ya kai kallonsa ga inda agogon yake.
Ƙarfe 9 na safe shi ne lokacin da ya buga, Mutumin da yazo cikin kansa a wannan lokacin shi ne Bello Ƙaraye, ko bai faɗa ba yasan yanzu yana can yana mita shi kaɗai na barinsa da yay yana jiransa. Sai kawai ya motsa leɓensa sannan ya ɗauki hular ya saka. Ya zauna a bakin gadon dan saka takalmi wayarsa ta shiga ƙara, ringtone ɗin i love you Maama ya karaɗe duka ɗakin.
Ya miƙa hannu ya ɗauki wayar kuncinsa na murmusawa. bai picking call ɗin ba har sai da ya yanke tukunna yabi bayan kiran, bugu ɗaya aka ɗaga tare da yin sallama. Allah ɗaya yasan me yaji acikin zuciyarsa a wannan lokacin, bai amsa sallamar ba sai da ya lumshe idonsa tukunna.
"Babana".
Sautin muryar Hajiya Madina tayi amo a cikin kunnensa, Sunan da ta kirasa da shi ya fama masa wani ciwo da ke manne a zuciyarsa, ciwon da ba zai taɓa warkewa daga gare shi ba har san da numfashinsa zai tsaya, ya riga ya san da wannan, kuma kowa ma ya san da shi.
Lokaci ɗaya yaji wani dunƙulallan abu ya tsaya a maƙogoronsa ya hana yawu wucewa, bai san lokacin da ya ɗaga wayarsa ya daki goshinsa da ita ba. Irin hucin da yake jerawa ya ankarar da Hajiya Madina situation ɗin da yake ƙoƙarin shiga, dan haka da sauri tayi ƙoƙarin dakatar da hakan ta hanyar kiran sunan da ita kaɗai ke kiransa da shi, kuma shi kaɗai ne sunan da za'a faɗa masa ya faranta ransa.
"Me babban suna, be patient please".
Lokacin da tayi furucin kwanciya yay a jikin gadon yana fuskantar P.O.P, yatsun hannunsa na hagun a saman karan hancinsa yana murzawa da ƙarfi, yayinda idanuwansa ke a kulle har yanzu basu bar raɗaɗi ba.
"Ina kwana Maama".
"Ka tashi lafiya?".
"lafiya lau, ina fatan duk kuna lafiya?".
"muna lafiya lau, Ya wurin aikin naka?".
"Aiki mun gode Allah, yanzu nake shirin fita".
"Glad to hear that, Allah ya taimaka ya bada sa'a da nasara".
Daga kan dining ɗin da Hajiya Madina ke zaune, ta kai glass cup ɗin da ta ɗauka bakinta ta kurɓi lemun ciki na five alive, sannan ta ƙara cewa da Turaki.
"When are you coming back home?".
"Ina kan hanya zuwa wani satin Insha'Allahu, munyi magana da Baffa jiya".
Jin yace mata sunyi magana shi da Baffa ta murmusa kuncinta kamin tace,"To shikenan Allah ya dawo min da kai lafiya".
"amin ya Allah Maama".
"ina fatan Baka da matsalar komai ko?".
"Babu Maama".
"to Allah yayi maka albarka...Make sure you eat your breakfast before going to office".
Ya kai hannu ya shafo gefen fuskarsa inda gashin sajensa yake kamin ya amsa da,"insha'Allahu Maama".
Taso su tattauna wani batu amma saboda wani dalili nata sai ta fasa, Basu yi sallama ba sai da tayi masa adu'a sosai tukunna. Kuma kiran nata na katsewa kiran Bello Ƙaraye ya shigo a lokacin, ya ɗaga da guntun murmushi a fuskarsa, sallamar da yay sai da Bello Ƙaraye yayi kamar ba zai amsa masa ba.
"Ba zaka fito bane yau?".
Turaki na dariya ƙasa-ƙasa yanda Bellon ba zai ji ba yace,"ehh kamar dai hakan".
"naga dukkanin alama ai". Bello na faÉ—ar hakan ya katse kiransa, bayan ya jawa Turaki tsaki na É—an rainin hankali kawai.
Gaba É—aya Turaki bai yi niyyar yin break fast ba, amma saboda abin da Maama tace haka dole yaja ya tsaya da ya fito parlo. Ya nemi kujera ya zauna tare da janyo center table gabansa, dama already yasa wani É—an aikensa yay masa order na chips tun 6, kuma da yaga zai yi late sai ya yanke shawaran idan yaje office yaci, to amma babu yanda zai yi tunda Maama tayi magana.