← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 176

Sashe 19

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusuf yace,"Mommi hawayenki babban tashin hankali ne a wurinmu, dan Allah ki daina, ko menene kike tunawa zai zama tarihi da izinin Allah...and ina da yaƙinin 100% komai naki ya kusa daidaituwa duk da cewar bamu san me ya faru dake ba har kika zo ƙasar da babu wani naki acikinta, fatanmu Allah ya baki lafiya domin musan ta inda zamu fara".
shima É—in maganar yake cike da tausayinta.

Mommi ta sake su daga rungumar da tayi musu, tasa hannu zata goge hawayenta Yusuf ya riƙe hannun nata tare da saka handky ɗinsa ya goge mata.
ta sakar musu murmushi, irin murmushin da ake kira na ƙarfin hali, sannan ta jinjina musu kai na ƙara godiya a gare su tare da nuna jin daɗin kasancewarta tare da su.

su biyun suka taimaka mata ta sauko daga kan bed, Yusuf ya fice ita kuma Nuratu tayi mata rakiya zuwa toilet. bata wani jima a wankan ba ta fito dafe da bango.
Nuratu na ajiye mata kayan da zata saka tai saurin bari ta taho tayi mata jagoranci suka ƙaraso ta zauna kan wata kujera.

Nuratu ce tayi mata komai, tun daga kan shafa cream har saka kayan. abaya ce white da adon stones masu ƙyalli. sai hijab ɗin peach ta ɗora mata akai wanda yake daidai ƙirjinta. kasancewar Mommi fara ce sosai sai kayan suka amsheta matuƙa, idan ba wanda ya sani ba sai ka iya rantsewa balarabiyar ƙasar ce dan tayi kama da su sak.

"Mommi ending this week zamu wuce Saudia muyi Umarah for 1 week daga nan sai mu wuce naija, Excellency ya gama gudanar da aikin daya kawo shi, aikinsa zai koma can nigeria gaba É—aya".
Nuratun ta faɗa tana bata kubza a baki haɗe da black tea, Mommi taunar ta ke yi da ƙyar saboda jin wani nauyi a ƙirjinta kamar an ɗora dutse.

magana Nuratu ke tayi amma hankalin Mommi gaba É—aya ya bar jikinta, tunaninta ya tafi can wata duniya ta daban, ita É—aya ta san me ta ke tunani, kuma ita É—aya tasan me zai iya faruwa. halin da mahaifiyarta ke ciki shi tafi so ta sa ni kamin azo kan kowa da komai.
ta rufe ido kaɗan ta buɗe ta ɗorasu kan Nuratu, sai tayi dauriyar maida ƙwallar data cika idonta sannan ta matso ta sumbaci Nuratu a goshi.

Yusuf na parlo zaune da waya kare a kunnensa yana sauraron maganganun da Umma keyi masa. tsawon lokaci kafin ya numfasa yace,"Umma please don't let Ammi knows munyi waya dake".

daga inda Umma ta ke ta galla harara kamar yana gabanta, tai shiru kamar ba zata ce komai ba, tana shirin yin magana ya rigata.
"please Umma". tayi hanzarin katse shi,"tana part É—inta ina part É—ina how will she know?, ko da yake aini ce aku sarkin surutu".

yanda yaji muryata yasa shi sosa kai tare da cewan,"ba haka nake nufi ba Umma". dai-dai lokacin Nuratu ta ƙaraso wajen ta zauna saman cinyarsa tare da kwantar da kanta bisa kafaɗarsa, shi kuma ya zira ɗayan hannunsa acikin rigarta yana shafa cikinta, har zuciyarsa ji yake tamkar babynsa yake shafawa a zahiri. Nuratun ma ta ɗora nata hannun akan nasa suna shafa cikin tare.

komai na ubangiji ne, kuma komai lokaci ne, shekararsu biyu da aure Nuratu bata taɓa ɓatan wata ba, maganganu har sun fara tashin ai bata haihuwa, ya kamata ya ƙara aure tun kamin ya mutu baiga ɗansa ba. cikin masu maganganun harda Ammi mahaifiyarsa, da yake dama ita ba ƙaunar auren ta ke ba, kasancewar Nuratu ƴar Yayar kishiyarta ce wato Umma.

lokacin daya gama service É—insa ta aika shi har abuja yaje yayi kwanaki a gidan best friend É—inta Hajiya Habiba don yaga yarinyarta. amma Yusuf na dawowa a lokacin ya tarar da Nuratu da tazo hutu shikenan sai yace shi fa ita yake so, duk yanda Ammi tayi yace shi Nuratu kaÉ—ai zai aura, kuma da yake mahaifinsa ba mai takurawa Æ´aÆ´a bane, abunda suke so shi yake so haka dole aka bi abinda Yusuf ke so.

Ammi tayi kamar tai hauka a lokacin, ita baƙin cikinta akan me zaisa ya auri jinin kishiya banda yana so ya tozartata a idon duniya.
to fa shikenan kuma sai ya jawo ta É—auki fushin duniya ta É—ora akansa. dama can ana Æ´ar hakan saboda tana jin haushin shirinsa da Umman.

sam Ammi bata son Nuratu, kuma Nuratu yarinya ce me hankali. dan ko sau ɗaya ma bata taɓa nunawa Yusuf rashin jin daɗin tsangamar da ta ke samu daga wurin mahaifiyarsa ba. hasali ma idan yana bata haƙuri sai dai tace masa its matter of time hakan zai zama kamar ba'ai ba.

hatta wani lokaci da Ammin taje har gidansu Yusuf baya gari ta wanke Nuratu tass akan sun asirce mata ɗa, da kuma cewar Allah ya isanta da ta aure mata yaro alhalin tasan ita juya ce. Nuratu bata taɓa danasanin auren Yusuf ba sai a ranar, saboda wankin babban bargon da Ammi tai mata na maganganu marasa daɗi da tsayawa a rai.
hakanne ma yasa bayan tafiyar Ammin ta kira Umma tace ita kam tasa Yusuf ya saketa bata iya ci gaba da zama da shi, tunda dai haihuwar nan ba itane zata bawa kanta ba.

ta kwashe duk abinda Ammi tayi mata ta faɗawa Umman, silar inda faɗan gaba me tsanani ya shiga tsakaninsu kenan. Umma bata biyewa faɗan kishi na Ammi, amma akan wannan abin har sai da Daddy yace shi ba zai iya da jarabarsu ba sai ya maka su a kotu. dalilin samun sauƙi kenan shima kuma dan Umman tana bagararwa ne, amma da saboda Ammi ne har gaba da kotu sai dai akai su.

maganar Umma ta katse su Yusuf daga abinda suke ƙoƙarin yi, sai lokacin Yusuf ya farga ya amsa kiran sunansa da tai.
"ina Nuratu?". Umman ta tambaya da É—aure muryarta.

"ga ta nan". "to bata".
ya cire wayar daga kunnensa ya ɗora akan kunnen Nuratu, ta wani narke tana shagwaɓewan Umman.
"ba dai ki da wata matsala ko?". Umman ta tambaya da tsansatar kulawa.

tayi kamar za tai kuka tace,"Umma ni so nake mu dawo, anan bana samun duk kayan kwaÉ—ayin da nake son ci".
Umma tace,"kai Nuratu".
tace,"Allah Umma, nan fa babu irin su goruba, tsamin gaye, kuma fa har Farar ƙasa ma babu Umma, ga shi duk abunda naci ni ba sonsa nake ba sai ya dawo".
ta ƙarashe maganar tana fashewa da kukan taɓara.

daga inda Umma ta ke tai murmushi. "ai ke kika dage sai kin bisa, amma kiyi haƙuri kinji, haka ƙaramin ciki yake Nuratu. ai kun kusa dawowa, idan kun dawo ma nan gida za ki dawo ba zan barki ke ɗaya ba...yanzu dai zan san duk yanda za'ai na aiko miki abubuwan da kike so kamin dawowar taku, kiyi list sai ki turo min".

"tom Ummana. ina su Kursum?".
Umma tace,"suna bedroom É—in su".
"kice ina gaida su kuma nayi fishi tunda basa nemana...kuma ko É—ansu yazo ba zan basu shi ba".

Umma tace,"ai kina da wayarsu ki kira su mana". sannan ta É—aure murya tace,"ina Yusuhun?".

lokaci ɗaya Nuratu ta nemi hawa bori ajikinsa akan Umma tace Yusuhu, dan ita bata son sunan ana ɓata masa suna ya koma na ƴan ƙauye. ita kuma Umman duk lokacin da Yusuf ya ɓata mata rai ko ya ya ne sunan da take faɗa masa kenan.
"bana son iya shege Malama bawa mijinki".

tana ɓata fuska tace,"don Allah Umma ki daina cewa Yusuhu idan wasu suka ji sai su ɗauka".
Umma tace,"to sai kizo ki faÉ—awa ubansa ai yay masa sabon yanka".

sai around uku na yamma tukunna suka fita outing, Mommi nata jin daÉ—in fitar tasu saboda yanda suke ta ma ta hira su biyun, kowa so yake ya nuna bajintarsa na É—ebe ma ta kewa tamkar wasu Æ´aÆ´anta. basu suka dawo gida ba sai after isha'i.

*Nigeria, Gombe, Dikko resident.*
kan Fillo duƙe tana yankan farce suna magana da Kaka, wadda ke ta yabon Turaki saboda mutumcinsa.
Fillo dai bata cewa komai, dan ita duk da halin kirkin daya nuna bata jin zai wani burgeta. saboda haushinsa ma ta ke ji gaba ɗaya, har ga Allah ta tsani mutum me ji da kai, wannan yasa tun a wancan ranar da ta fara zuwa aiki ɓangarensu taji ko kaɗan bata ƙaunar ma hanya ta ƙara haɗata da shi ko bisa kuskure.

ita bata ma yi tsammanin yana da halin ƙwarai har haka ba da zai iya taimakawa wani, tayi mamakinsa sosai. sai daga baya taga ashe tayi masa bahaguwar fahimta ne, bata san da yaje duba Kaka da jiki ba sai daga baya, tun ranar farkon aikin nan nata daya kira waya a ɗakin baya da akace ta zauna, bata ɗaga ba saboda baccin daya fara ɗibarta.

da kansa yazo ɗakin ya sameta tana bacci, yana shirin juyawa ne ta farka, ta tambaye shi akwai buqatar wani abu ne fuskarsa a tamke yace mata babu, sai kawai ya fice daga ɗakin. kuma babu jimawa ya ƙara dawowa ya tambayeta ina tsohuwar da ta samu anan, tace masa ai ko da tazo babu kowa a ɗakin.

kamar bai yarda da abinda ta faɗa ba lokacin, saboda ɗan jim yayi kamin ya fice a ɗakin. sai bayan isha'i da ta koma ne ta tarar da uban cartons jere a falonsu, maltina, madarar gwangwani da ruwa da kayan marmari kala-kala, ga kaza gasashshiya, abun ya bata mamaki sosai, duk da zuciyarta ta raya mata ko Amir ne ya kawo, to amma iya ƙoƙarinsa dai tasan baida kuɗin wannan uban sayayyar.

tana tambayar Kaka tace mata ai Zaytuna ce suka zo ita da Yayanta suka kawo mata, a lokacin bata kawo cewar Turakin ba ne dan haka kawai godiya tayi tana daɗa faɗawa Kaka kirki irin na Zaytuna da Hajiyarsu, Kakan itama na ƙara faɗar nata kirkin da ta san Zaytunan da shi a ɗan tsukukun zaman jinyar Turaki da tai.

Sai da Fillo ta shiga ɗaki taga ledar drip da tarin magani akan katifarsu sannan tai saurin fitowa daga ɗakin, tsayawa tayi kawai tana kallon Kaka kafin ta iya buɗar baki tace,"Kaka wa akaiwa ƙarin ruwa?".
Chapter 19 · 0% Book details