Sashe 37
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta sakar masa tana faɗin,"kai da yake ai kasan darajar babba. na gode Allah yayi maka albarka ya raya maka iyali, yasa ka gama da duniya lafiya, Amadu na dawowa zansa shi yay maka kyauta wallahi. ni ko zamu koma kanon ma ai ba zan bari a tafi babu kai ba, wa zai so ya rabu da ɗan arziƙi irinka".
nan ya barta tana ci gaba da surfa mita, ta zubawa gate ido tana ta Allah Allah motar Yusuf ta shigo. Mai gadin ya dawo ya bata basket ɗin ta wuce tana ta ƙara gode masa.
tazo wucewa ta ɓangaren Ammi ta saki basket ɗin ya faɗi ƙasa, babu shiri ta saki salati tana ɗora hannu aka.
"la'ila ha'illallahu Muhammadu Rasulillahi". Ammi ta dakata da shiga parlonta ta juyo tana kallonta. kamar ba za tayi magana ba, yanda taga Inna Wuro ta É—ora hannu aka yasa dole ta magantu har tana dawowa da baya don ganin lafiya.
"me ya faru?". cewar Ammin tana bin wurin da kallo. Inna Wuro ta sunkuya ta ɗauki durstbin ɗin tace,"a'a babu ruwanki, yaushe rabon da magana ta haɗani da ke, tunda azumi ya fita kika ƙulla gaba da ni, sai yanzu ne da kika ga ina neman cutuwa sannan za ki kulani, to gaskiya matsa daga kusa da ni bana son munafurci...duk wanda yay na gari dai kansa, ni ɗin dai wallahi ba abar banza bace nafi ƙarfin wulaƙancin bawa tunda ni na haifin me ƙaton gidan nan".
jin haka Ammi tayi tsaki a ƙasan ranta tayi wucewarta, dama tasan ba wani abin arziƙi ba ne, bai wuce abinta da ta saba. Inna Wuro ta bita da ido ta taɓe baki, bata ce komai ba ta wuce side ɗinta, cikin ranta sai masifa take yi Yusuf bai dawo ba har yanzu.
tana shiga ta tarar da Kursum ta fito daga É—akinta. tayi saurin ajiye durstbin ta cire mayafinta ta aje. tabi hannun Kursum da ido har tazo ta zauna, idonta akan bowl da Kursum ta ciko da alkaki tace.
"babu masifar da ta wuce haihuwar ɓeraye wallahi. to ni Safiyya mene marabar ƴaƴan Amadu da ɓeraye?, ka ajiye aje a ɗauke babu neman izini. to ba zan iya ba, Allah ya dawo da shi lafiya, ko ya min gidana daban ko kuma ya katangeni a gefe ɗaya, ba zancen haɗa mana ƙofar shigowa ɗaya da ku...ban son fitina ban iyata ba, Allah kuma ya rabani da ita, ku kuma naga tashin hankali kuka fi so to can ya ƙare akan ku".
tana cikin wannan sababin Nuratu ta miƙe tayi hanyar ɗakin Inna Wuro da sauri tana rufe bakinta da amai ke shirin zubowa.
Inna Wuro ta koma da ba ya tayi wani zaman dirshen akan kujera, ta kama kanta ta riƙe tana girgiza shi.
"wowowo, tashin hankali kala-kala a cikin gidan nan. tayi ta zabga amai babu ƙaƙƙautawa duk ta lalata min bandaƙi. to Yusuf ɗin yazo yau dai zamanki ya ƙare a ɓangarena, ya kwasheki ya mayar da ke gidanki ko dai yasan yacca zai yi da ke. banda ma dai kar yay min kallon mara mutunci ai kamin ya dawo zan kai miki kayanki waje".
sai kuma tayi ta gumi,"wannan masifa duk ni na jawowa kaina da nace ki dawo wajena da zama, shegen shishshigi irin nawa dai...in nasan hakan kike laulayi wallahi da ban soma ba. gwara can Uwarsa ta riƙe ki, tunda ita ƙanwar Uwar taki tasa ƙafa ta bar gidan, ace aikin Umara har yanzu ba'a gama ba kusan sati uku...wa ma yasan inda ta kaɗa".
*Vote, Comment, and Share.*
[8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
*©ï¸Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
*19*
Yusuf na zuwa gida ko horn bai yi ba balle ya tsaya jiran wani abu shi buÉ—e gate, ya fito daga motar cikin sassarfa. yasan yana da patient, matarsa dake É—auke da juna biyu mai wuyar laulayi, yau lafiya gobe babu lafiya, shi yasa duk hankalinsa ya tashi tunda yaji irin salatin da Inna Wuro ta zabga, duk wanda yaji wannan salatin ya san ba lafiya ba kamar yanda ta faÉ—a.
jinsa yake kamar ya ɗauki kansa ya dire a parlon Inna Wuro, ƙaramar ƙofar gate ɗin a buɗe take dan haka yana zuwa turawa yayi ya shiga. mai gadi dake daga cikin ɗakinsa a zaune yay masa sannu da zuwa, a sama ya amsa masa ya wuce kamar zai tashi sama gabansa sai faɗuwa yake.
hango Ammi yay zata shiga motarta, ya bita da kallo for some seconds, atleast dai zuciyarsa ta sami natsuwa ko ya ya ne, dan shi abunda yake hasashen ya faru daban ne, to kuma tunda yaga Ammi taci kwalliya kuma bai ga wani alamun tashin hankali tare da ita ba sai ya fara nutsuwa.
but still dai gabansa bai daina faɗuwa ba, ba zai yi la'akari da yanayin Ammi ba akan ba wata matsala bace babba, komai ma zai iya faruwa ba tare data sa ni ba, idan ma ta sani zata iya yin banza taci gaba da sha'aninta, ranar nan ma haka tayi da akazo aka ce mata Nuratu ta faɗi, baki kawai ta taɓe ciki-ciki tace Allah bada lafiya, Ko da aka kwantar da Nuratun bata je asibitin ta dubata ba, zallar ƙi take nunawa aurensa da Nuratu babu ɓoye-ɓoye ga kowa.
yana wannan saurin tafiyar ne dan ƙarasawa side ɗin Inna Wuro sai yaji wayarsa na ringing, yasa hannu a aljihu ya ɗauko. yana ganin sunan Ammi ƙirjinsa yay wani irin bugawa, da ƙyar ya iya ɗaga kiran a lokacin da yake dab da katsewa.
kasa cewa komai yayi daya É—aga wayar but still bai daina tafiyar ba, sai dai ya rage saurin tafiyar tasa, jin bakinsa yake kamar ba zai iya cewa komai ba.
Ammi tace masa,"shawaran da zuciyar taka ta yanke maka kenan Yusuf?". mamaki ya kama Yusuf, taya akai ta gansa?, a hankali ya juyar da kansa gefe yana kallon inda take sai yaga bata wajen, ba abin yace mata ba shi bane tunda dai ta riga ta gansa É—in.
ya buɗe baki zai yi magana ta tari numfashinsa,"yau da safe baka shigo inda nake ka duba ni ba sannan ka dawo kana ganina amma kasa kai ka wuce saboda banda mutunci yanzu a idonka. idan Falmata ce ka isa kai mata haka?, ko sallah kaga tana yi a compound ɗin nan ai sai ka jira ta idar tasa maka albarka tukunna zaka wuce. to ni dai Allah ya isa rabani da akai da kai wallahi, ba'a san irin baƙar wuyar dana sha kafin haihuwarka da lokacin haihuwarka ba, ba yafewa zanyi ba. kuma kaje duk wanda zai saka maka albarka wallahi bata kai tawa ba, a banza a wofi, kai da ka san darajar uwa ma da baka fifita kishiyata akaina ba, shashashan banza marar hankali kawai, idan baka sani ba ka sani uwa tafi gaban wasa".
muryar Yusuf a hankali kuma da ladabi yace,"kiyi haƙuri Ammi amma ba yanda kike tunani ba ne, yau da safe ko gidan nan banzo ba Allah".
taja tsaki tace,"aikin banza. to ka juyo ka kaini unguwa in ka dawo kaje duk inda zaka je".
yasa hannu ya shafa kansa tare da rufe idonsa bai ce komai ba kuma bai motsa daga inda yake ba. Ammi ta ƙara cewa,"baka ji me nace ba ne?".
yace,"naji Ammi". tace,"ba zaka kainin ba ne?, ko kuma izinin uwar taka zaka fara zuwa ka nema?".
ya ƙara sosa kansa yace,"ai Umman bata dawo ba Ammi".
da a kusa da ita yay maganar da babu abinda zai hanata buge masa baki, cikin zafin rai tace,"zan zauna zaman jiranka ne ko ya?".
yace,"Ammi dan Allah ki kira Aliyu, Inna Wuro ce ta kirani Nuratu babu lafiya zan ɗauketa mu wuce asibiti...". tun bai ƙarasa ba ta dakatar da shi,"ai nasan da Aliyun ban ce shi ba sai kai. Yusuf matarka ko mutuwa zata yi ba zaka je wurinta ba a yanzu sai ka kaini ka dawo, na faɗa maka in ba haka ba kuma zaka sha mamakina, zan maka abinda baka taɓa tsammani ba daga gareni".
ƙasan zuciyar Yusuf yaji babu daɗi, bai san ya zai kimanta mata abinda yake ji ba, shi ta barsa yaje yaga kawai halin da Nuratu take sai ya fito ya kaita, hakan ne kaɗai zai basa natsuwar yin driving ɗin da take so, to amma yasan ko me za'ai ba zata yarda ba, kamar yanda ta faɗa ne ko mutuwa Nuratu zata yi, sannan kuma uwarsa ce, jayayya da ita ko bijire mata ya ɗaukowa kansa hanya ta taɓewa ne.
dabara ta faÉ—o masa yace,"Ammi na bar motata a hospital".
a fusace tace,"ko da motarka ma kazo ni ba zan shiga cikinta ba, ina da tawa a ita zaka kaini. motarka ai sai Falmata amma ba ni ba, kuma ni dai na faɗa maka ƙafarka ka ɗaga kayi cikin gida to ban yafe ba, idan kaga dama kai ta tsaiwa muna dragging muna ɓatawa junanmu lokaci".
Yusuf ya kulle idonsa ya fesar da iska me zafi daga bakinsa, ya katse wayar yana kallon side É—in Inna Wuro ya koma da baya ya nufa wurin motar. a cikin motar ya sameta a zaune, ya buÉ—e driver seat ya shiga, bai juya ya kalla back seat inda take ba yace,"Ammi ina yini, kuma ina zan kai ki?".
Ammi tace,"gaisuwarka dai ka riƙe, inda zaka kaini kuma kowanne store ya kama, wurin dai da zan samu abinda na fita saya, dawowarmu kuma sai Allah yayi".
tana yin shiru yay ma motar key, yay reverse har tayar motar na amsawa, wanda inda ace wajen da ƙasa sai ƙura ta tashi.
suna fitowa daga cikin gidan kamar ance ta É—ago kai daga kallon wayarta taga motarsa. tace,"kace a hospital ka bar motar?".
sai daya kulle ido sannan ya iya ƙaryar cewa,"dama nace da Mujahid ya kawo min ne".
tai murmushi kawai tare da girgiza kai bata ce komai ba.
store wurin huɗu suka je, ba dan tana rasa abunda zata saya a kowanne ba, sai dan kawai ta ɓata masa lokaci, dalilin da yasa ta dinƙa gutsira sayayyar kenan, har yamma tukunna suka ɗauko hanya.
sai da suka shigo cikin anguwarsu sannan ta ƙara ce masa,"nace maka gida zamu wuce ne direct?, to kai reverse ka kaini gidan Kawun ka".