Sashe 168
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
murmushin tayi sannan yace,"to ka san june?, tunda nake a rayuwarta ban taɓa hango kaina a matsayin uwa ba, ban taɓa tunanin zan ɗauki ciki ba balle har akai lokacin da zan haife shi".
sai tayi shiru, yace,"ehen ina jinki lukutar Gombe".
murmushi ya kasa ɗaukewa a saman fuskarta, tana kallon bayansa ta ƙara cewa,"sai ga shi Allah ya ƙadarta min ganin samun cikin, har zuwa watan haihuwarsa, zan haife ƴaƴa biyun da nagartaccen mijina ya bani su, na ƙagu in haife su Jannaty, ina tsananin son su fiye da kaina".
cikin sigar zolaya yace,"har ni kin fi son su akaina?".
ta ɗan taɓe baki tana kallonsa, da irin wasan da ke tsakanin mata da miji tace,"waye kai?".
ya ƙaraso ya zauna kusa da ita ya mintsinin leɓenta, ya ɗora hannunsa a saman nata dake kan cikin.
"yau kin ji sun juya?".
ta ɗaga masa rigar tana faɗin,"kalla fa yanda suke ta ƙiriniya, duk sai duka suke kai min ta ko'ina, suma ai sun gaji da zaman".
Turaki bai iya cewa komai ba illa shiru da yayi yana ta kallon cikin dake motsi, yana jinjinawa girman ƙudirar ubangiji. gaba ɗaya sai yake jin tamkar yasa hannu ya buɗe cikin ya ɗauko yaran, Fillo kuwa kallon cikin kawai take yi a gefe guda zuciyarta na saƙe-saƙen yacca rayuwar zata juya, yanda komai zai koma saɓanin tunanin su da hasashen su, yacca komai zai faru anan gaba kaɗan, nan da ɗan lokaci kaɗan ba me yawa ba, hakan take taji a jikinta.
"ba fa na so yarana su yi kama da mijin lukutar gombe saboda bana so su yi muni, ka daina kalle min su".
ya rungumota jikinsa yana cewa,"wallah ki roƙi Allah su yi kama da ni kiga yanda za'a dinƙa miki layi a ƙofar gida, in kuwa su kai kama da ke to kin shige su, ƙila sai dai mu ke kulle su a store".
bayan fitarsa ta zauna a gefen gado, ta rufe idanuwanta a hankali, yayin da hannayenta ke ɗore akan ƙaton cikinta, ita ɗaya ke ta saƙawa wai yanzu halitta ce a cikin cikinta, halittar da ya girma kuma zai fito nan ba da jimawa ba, shikenan da zarar sun fito ita ma ta samu nata babies ɗin, irin wanda take gani daga nesa don bata iya ɗaukar jariri, za su fito a matsayin nata, yayin da zata amsa wannan sunan mafi daraja na Uwa, ƴaƴan su ita da Turaki, Ƴaƴan su ikon su.
sai taji ƙwalla na neman taruwa a cikin idonta, ƙwallar da take ta zallar farin ciki da wani bala'in jin daɗin da ba zai misaltu ba.
ta lumshe idanunta, ƙwaƙwalwarta na haska mata hoton yaran acikin kanta, ana jibi Hajiya Madina zata rasu ana scaning sai taji tamkar ta ɗauko su a wannan lokacin, babies ɗin su na kwance a cikinta gwanin sha'awa, ga sunan clearly a jikin screen cikin hoton black and white, kansu a haɗe su na ta watsal-watsal yayin da hannun kowanne ke gefen bakinsa, idanunsu a buɗe tarr tamkar kayi musu magana su amsa maka.
kawai sai ta fara hasko yanda kammanin babies ɗin zai kasance, bata san ya Allah ya tsara halittar kamannin nasu ba, wataƙila su yi kama da su, wataƙila kuma su ɗauko kamannin su daban, sai dai a son samunta duk su ɗauko kamannin Turaki, ta yan da zata dinƙa kallonsa a fuskarsu idan baya gida, ba ya ga hakama idan suka ɗauko kamanninsa zasu fi kyau, irin wannan kyan da sai ta dinga tofe su da adu'a a kaɗawar kowanne sakan na agogo.
tashi tayi akan gadon, ta isa gaban dressing mirror ta ɗauko diary ɗinta, sannan ta duƙa ta ɗauki riyon kayan babies, ta fita a ɗakin Turaki ta isa zuwa nata. wadrobe ta buɗe ta ɗauko wasu set ɗin kayan sanyi da Hajiya Ramla tayo mata aiken su a jiya, sannan ta fita ta nufi ɗakin kusa da na Turaki, ɗakin da suka ware domin yaran su, ɗakin da Turaki ya rufe mata ido ya shigar da ita sannan ya buɗe yana nuna mata yana faɗin for our coming kids.
ɗakin tamkar already dama yara na rayuwa acikinsa, domin anyi decorating ɗinsa da duk wasu kayan wasan yara, komai na cikinsa pink and white, kayayyakin da almost siyayyar Marigayiya Hajiya Madina ne, sai ta isa gaban gadajen guda biyu, a wannan lokacin babu abin da ƙwayar idonta ta haska mata irin hoton yaran a zahiri, ta gama ba su nono ta zo ta kwantar da su tana yi musu wasa, idan zata yi aiki sai ta saka musu karatun alƙur'ani kafin ta fita.
yayin da suka girma su fara kiranta da Ummi, mahaifin su kuma su kira shi da Abie, ƙwayar idanunta ta ƙara haska mata lokacin da zata fara shirya su cikin kayan makaranta, ta ba su lunch box na abincin su, sannan tayi driving ɗin su zuwa makaranta, yayin da suka dawo ta zauna domin yi musu home work ɗin da aka ba su, idan weekend ya zo sai su dinƙa yada zango a field su na yin wasa tare da ita, ko kuma suke shiga cikin swimming fool.
ita dai ta riga ta gama tsara yacca rayuwar jin daɗi zata kasance tsakaninta da ƴaƴanta, ba zata zamto ɗaya daga cikin irin uwayen nan da basa jan yaran su a jiki ba, ita zata zam yaranta na liƙe da ita ne ko da yaushe, ta dinƙa jin damuwar su suma su na jin tata, zasu zama manyan aminanta kamar yanda zata zame musu.
sai taji kamar zuciyarta ta ƙara girma da tsiron wata sabuwar ƙauna ta daban, ƙaunar abinda ke cikinta ya mamaye dukka ilahirin jikinta, irin wannan ƙaunar ta ɗa da uwa, irin ƙaunar da zaka ji kamar zuciyarka na fitar da tiriri na son tabbatar da abinda kake so, Allah shahidi, shi zai yi mata shaidar irin son da take yiwa yaran, tana ƙaunar su fiye da ranta, a yanzu su ne rayuwarta, in har babu su tabbas babu ita.
har ƙarfe uku tana ɗakin yaran a zaune, sallolinta duk anan tayi, abinci ma da aka kawo mata anan taci, ko ƙwalli ɗaya bata bari ya zuba ba gudun karta ɓata musu ɗaki.
zuwa lokacin kuwa sun yi waya da Turaki yafi sau goma, bini-bini sai ya kirata yace ga shi nan yana hanya, kuma taji gaba É—aya hankalinsa a tashe yake tun san da tace masa tana jin mararta na ciwo sosai, kamar dai zata fara labour.
cikin mintunan da ba zasu wuce biyar ba bayan wayar su ta ƙarshe sai ga Turaki ya dawo, yana shiga ɗakin yaran ya ganta zaune akan darduma tana goge hoton enlargement ɗinsu ita da shi, fuskarta ta washe da murmushi, wani murmushi da Turaki zai iya cewa bai taɓa ganinsa a saman fuskarta ba.
"welcome back".
ya ƙarasa ya zauna a gabanta yana tankwashe ƙafafunsa, ya ƙura mata ido sosai yana ganin yanda take cije fuska, tana so ta ɓoye masa zafin ciwon da ke cinta, tana so ta ɗauko ƙarfin hali domin ta nuna masa babu komai, babu wani abu da yake damunta, babu wata matsala, duk saboda hankalinsa ya kwanta.
"kin ci abinci?".
"na ci, me ka taho min da shi?".
ya matso da ledar da ya shigo kusa da ita yana buÉ—ewa. "irin naman da kike so".
ai ko nan da nan ta warci ledar, ta miƙa masa enlargement ɗin tace,"maƙala musu wannan, an manta jiya ba'a saka shi ba, mp3 ɗin su na karatun alƙur'anin ka bar shi a ɗakinka, ka ɗauko sai a ɗora musu a saman wancan table ɗin, ungo wannan diary ɗin sa min shi cikin wadrobe ɗin su, kasa shi ƙasan kayan Aayan".
duk maganar tayi ne a lokacin da ta fara cin naman, Turaki ya miƙe yayi duk abin da tace, san da ya kammala har ta gama cin naman, ya shiga tsokanarta da kura, kasancewar naman yana da yawa sosai.
sai da suka ƙara kimtsa ɗakin sosai sannan suka zauna a tsakiyar gadajen biyu, suka shiga hira, wata iriyar hira suke yi mai ratsa jiki, hira da zasu ce ba su taɓa irinta ba a tsawon zaman su, hirar da ta yiwa kowannensu daɗi matuƙa. kan Fillo na saman ƙirjinsa yayin da yake shafa gashin kanta, duk hirar da suke yi muryarta na fitowa ne tana ratsa dukkan ɗakin a hankali, cikin wani amo na rauni da ya gaza ɓoye dauriyar ciwon da ke cinta.
ana sallar magriba ciwon naƙuda me tsanani ya ɓallewa Fillo, lokacin tayo alwala kenan ta fito daga banɗaki, tayi saurin dafa bango tare da duƙawa a wajen tana dafe bayanta, a lokacin wata azaba ta tsarga jikinta, sai taji numfashinta kamar ya tsaya cak a maƙogoronta, taji kamar duk wani ɓurɓushi na halittar jikinta yana barinta gaba ɗaya.
ta rumtse ido na tsawon mintuna tana ambaton Allah cikin wata rarrauniyar murya, wani sabon bala'in zafi taji ya fara bin dukkan jijiyoyinta, sai taji ina ma ta kwasa a guje ta bar cikin ɗakin ta fita waje ko zafa sami sauƙi acan, sai dai ko yatsanta guda ta kasa motsawa, ji take yi tamkar an saka ƙaton dutse an danneta.
muryarta tun tana fita da ƙarfi har ta zo ta daina fita, lokacin Turaki ya shigo ɗakin kamar an hankaɗosa, dama tun san da zai tafi masallaci yaji hankalinsa bai kwanta ba, yaji gaba ɗaya ba ya so ya tafi masallacin gwara yay sallarsa anan, amma sai ta hana shi, ta tilasta masa akan sai ya tafi masallaci ya sami jam'i.
cikin tsananin tashin hankali ya ƙaraso in da take, cikin bala'in ruɗu na farat ɗaya yace,"kin gani ko, sai dai na faɗa miki ba zan fita ba".
"ka kaini a cire min su Jannaty, ba zan iya ƙara kwana a haka ba, don Allah ka taimaka min, zan mutu..."..
Sauran harufan suka katse sakamakon wani sabon ciwon da ya murÉ—a mata, taji kamar an saka kibiya an soketa a tsakiyar cikinta da mararta.