← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 176

Sashe 23

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

to amma dai yake Allah ya tsara cewar Lateef shi zai hau kujerar mulki, duk irin yanda Adam ya kai ruwa rana wajen ganin ya hana faruwar hakan shi da muqarrabansa amma Allah bai ba su iko ba. daga ƙarshe haka dole suka haƙura suka zubawa sarautar Lateef ido wadda yake gudanar da ita cikin gaskiya, tausayi gami da jin ƙan al'umma kamar yanda mahaifinsa ya aiwatar a lokacin nasa mulkin.

Sarki Lateef ya gaji mahaifinsa ne wajen auren mace É—aya tun auren da mahaifinsa yayi masa na Rumana, kuma lokacin da Sarauniya Rumana ta haifi É—a na uku Allah ya yiwa Sarauniya Falmata rasuwa.

bayan rasuwartata ne wannan ɗan guntun haɗin kan dake tsakanin ƴaƴanta wanda yake na dole a gare su saboda ganin idonta sai ya ƙarasa rugujewa, don tana rasuwa kowa ya kama gabansa, da yake dai shima Yarima Adam Allah ya rubuta dole zai riƙi sarauta haka ya zuba uban dukiya aka ba shi sarautar yankin Funakaye, yankin da Babban ɗansa ke mulka a yanzu tun bayan rasuwar Sarki Adam.

sai a wannan lokacin Sarki Lateef ya samu lafiya, aka sarara da bi masa ta ƙarƙashin ƙasa, kwanciyar hankali ta samu a gare shi.
Allah ya azurta Sarki Lateef da yara huɗu, babban ɗansa Abubakar wanda yaci sunan Kakansa Sarki na biyu a wancan zamanin,  suke kiransa da Yarima Babba, sai dai a yanzu Ƴaƴa da Jikoki na kiransa da Alhaji Babba, kuma a yanzu shi ne Hakimin Kaltungo.

sai É—ansa na biyu da yaci sunan mahaifinsa Hashim suke kiransa da sarki na uku, kuma Hashim shine wanda ya gaji sarautar mahaifinsa Sarki Lateef tun bayan rasuwarsa.
a lokacinsu ba'ai wannan tashin hankalin ba na nuna son mulki ga kowannensu, hasalima mahaifiyarsu Sarauniya Rumana ita ta bada zaɓin cewar shine zai maye gurbin mahaifinsu, kuma daga wannan maganartata babu wanda yaja balle a tsaya ja'inja aka tsaya akan abinda tace.

sai ɗansu na uku Habib suke masa alkunya da Dikko, wanda yake babban alƙali a cikin ƙasa da wajenta, wanda gwamnatin tarayya ke ji da shi, kuma mahaifiyarsa ke alfahari da shi saboda gaskiyarsa.

Falmata(Faɗima) itace autar Sarauniya Rumana(Boɗejo), wacca aka haifeta bayan rasuwar mahaifinsu daya tafi ya bar Rumana da cikinta. ya kuma bar wasiyyar cewar indai an haifi mace a saka mata sunan mahaifiyarsa Falmata, kuma kar a ɓoye mata suna a dinga kiranta da wannan sunan. hakan kuma akayi sai dai Ƴaƴa na sakayawa suce mata Inna Falmata, mahaifiyarta kuma tace mata Sarauniya.

bayan biyo ɗan shirun da aka samu a falon na Hakimi wato Alhaji Babba, akan faɗan da yake ta yiwa Turaki na batun ƙin amincewarsa akan auren da iyayensa suke so yayi, yaci gaba da cewa.
"to mu ba mutanen banza bane ya kamata kasan da hakan Turaki, babu yacca za'ai ace mu ƙyaleka akan ra'ayinka na cewar kai ba zaka yi aure ba, wannan ma zancen banza da wofi ne...idan ka manta to ka tuna su waye mu, saboda haka wallahi ƙaryarka ka bar mana abin kunya a tarihin sarautarmu...na san idan ta ra'ayin mahaifinka ne sai da ya zuba maka ido, to mu ba zamu zuba maka wannan idon ba kaji ni da kyau".

A wannan lokacin idanuwan Turaki a kulle suke, kansa a duƙe yake, yana zaune ne a gefen ƙafafun macen da duk duniya baida kamarta Hajiya Madina. itace ta kawo ƙararsa ba kowa ba, aure take so yayi ya riga yasan da wannan batun ba tun yau ba, ya sa ni shine burinta akansa. to amma me yasa?, me yasa a matsayinta na wadda ta isa da shi bata gindaya masa umarnin hakan kai tsaye ba sai dai ta kawo ƙararsa gaban wanda cin mutumci shine abin yinsa?.

wani dunƙulallan abu yaji ya tsaya a maƙoshinsa, zuciyarsa ta katse da raya masa abubuwa a sanda Hakimi ya ƙara yin magana.
"Turaki ko dai baka da lafiya ne?, idan kasan akwai wannan matsalar a tare da kai to ka faÉ—a tun wuri a maganceta, duk da cewar abu ne da kamar wuya namiji kamarka ace yana da matsala makamancin hakan".

Boɗejo dake gefe tace,"ah tou dai nima shi na gani. wannan zance dai na batun ba shi lafiya ma ƙarya ne, ni nafi ga wani algungumin ne ya jefe mana shi, tunda dai kaga maitar ibadar nan da yake ma yanzu fa duk ya daina, kuma wallahi ko waye Allah ya isa bamu yafe ba...yanzu duk wani dogon zance ba shi bane, a tashi tsaye a nema masa magani kawai idan aka biye ta uwar tasa da uban nasa ba zasu yi masa wannan abin arziƙin ba".

Turaki ya buɗe idanuwansa ya zube akanta, magana ta ke tana ƙara kambaba zancen asiri ne akansa. bai san lokacin da bakinsa ya buɗe ya katseta da faɗin,"Boɗejo ke kuma komai ya faru shikenan sai kice aikin asiri asiri".

tayi masa wani kallo ɗaya sannan ta maida kallonta kan Hakimi tace,"me na faɗa maka Yarima Babba tun kamin ayi zaman wannan kotun?, ai sai dai idan ban faɗa ba amma yaron nan sai ya tanka, baka ga kallon da yake min bane kamar ma zai tashi ya rufeni da duka...haka fa ubansa ya koya masa kuma alhalin ni ba irin rainon da nayi muku ba kenan, wallahi duk irin son da yake ma yaransa bai kama ƙafar wanda Ubanku Allah ya jiƙan rai ya nuna muku ba, amma ku dai baku san wani abu wai shi raina na gaba ba, hasalima wallahi baku san babba na magana ku saka baki ba, amma su dai Ƴaƴan Dukko halinsu kenan Babba na magana su nuna bai kai ba...to alhamdulillahi daɗin abin Turaki bani na kawo ƙararka ba Uwarka ce gata nan a kusa da kai, kuma billahillazi da ace lokacin da nake sarauniya ne sai kasan na faɗa ka saka baki".

Turaki yay É—an guntun tsaki, ya É—ago kai ya kalli Hajiya Madina, suka yi ido huÉ—u da ita. a kallon da yay mata ya gano expression É—in dake tare da ita.
sai yayi saurin kai hannu wuyansa ya shafo shi, ɗabi'arsa ce hakan. yawanci Boɗejo kance wani ƙullin yake shafowa.

ya sauke numfashi, muryarsa ta fito a hankali, cikin girmamawa da biyayya yace da Hajiya Madina. "Maama ba sai kin kai ƙarata wani wurin ba. kin isa da ni, kin isa ki bani umarni na bi ko ina so ko bana so, kin isa kija layi kice kar na shata na haƙura dan dole na, bin zaɓinki dole na, yacca kike so nayi haka zanyi muddin hakan zai faranta ranki...".

bai ƙarasa ba amon muryarta ya fito da faɗin,"aurenka nake son gani Me babban suna, ina so kayi aure tun ina da rai Hammansu, ka sani ina sonka fiye da numfashina, babban burina a yanzu shine naga aurenka, naga matar da zaka aura, naga jikana, naga kalar rayuwar jin daɗi da kwanciyar hankalin da zaka shimfiɗa da iyalinka...Hammansu wannan auren da baka so shine mutumcin mutum, kuma shine ƙarshen jin daɗin rayuwa...ita rayuwa nan guda ɗaya ce Hammansu, haka ran ɗan adam guda ɗaya ne. lokaci tafiya yake baya jira, so kai enjoying rayuwarka tun lokacin bai ƙure ba, ya zamana kazo baka mori dukkan jin daɗin rayuwar ba...babu wanda aka yiwa alƙawarin kaiwa gobe a wannan duniyar, tsari kawai muke da hange, kuma zata iya yiwuwa mu matu a lokacin da muke ta shirin tsare-tsaren gobenmu, and that will be the end of us, ni kuma ina so mu tafi ne a lokacin da muka bar masu tunamu a kowacce daƙiƙa. da zarar ance babu kai shikenan duk wasu memories daka bari suma sun tafi, amma ɗa fa?, shi ɗaya ne memory da zaka tafi ka bari a kasa mancewa da kai, hakan yasa nake so kayi aure tunda sauran lokaci, auren nan daga zuriya mai ƙarfi irin zuriyarmu, *SARAUTA*, ta yadda zaka bar bayanka, wannan kawai shine burina akanka Hammansu".

idanuwan Turaki a ƙasan carpet suke, amma ƙwayar idonsa wasu yatsu ta ke hangowa sirara da suke karkarwa kamar waɗanda ake girgiza su. ya haɗiye wannan yawun dake saman harshensa zuwa cikinsa, sannan ya rufe idonsa ya buɗe a lokaci ɗaya. laɓensa na sama da na ƙasa suka tale, harufan bakinsa suka fito da faɗin.

"Aure! zanyi aure Maama, zanyi yanda kike so, kuma insha'Allahu sai na cika miki dukkan burinki akaina, kuma insha'Allahu ba za'a wayi wata rana da za'ace kin rigani tafiya ba, ni nake so na rigaki tafiya Maama, ni nake so, bana so ki tafi ki barni, rayuwar zata yi min tsanani, zan daina jin daÉ—inta kwata-kwata, zan dinga jinta ne kamar ana min feshi da ruwan dalma, dan Allah Maamaaaa".

maganar yake da kakkaryewar kowanne harafi, kuma maganar tasa ta katse gaba ɗaya a sanda yaja sunanta wajen faɗi. lokaci ɗaya ya nemi ya fita hayyacinsa. sautin kuka kawai yake ji acikin kansa, wannan sautin kukan na yarinta da na jarirai, saboda haka yay saurin saka duka hannayensa ya toshe kunnuwansa, tare da kifa goshinsa akan ƙafafun Hajiya Madina da ke zaune tana hawaye.

har zuwa lokacin da ya daina jin ihun kukan acikin kunnensa sannan ya ɗauke hannunsa, ya shiga sauke numfarfashi, gaba ɗaya yanayinsa ya sauya, kamar ma ya burkice ne, hannayensa masu rawa a yanzu suka damƙe zanin Hajiya Madina.
a jikinta ta ke jin irin rawar da jikinsa yake yi, jikinsa na rawa amma ita a wannan lokacin tata zuciyar ce ta ke rawa, so take itama ta taya shi kukan, irin kukan da yake yi, so take ta taya shi ko yaya ne, ko da sau É—aya ne.

Zaytuna dake kusa da Boɗejo ta taso cikin kyarmar jiki, ta dawo gabansa ta durƙusa, sannan ta shige jikinsa gaba ɗaya itama nata kukan na ƙara ƙarfi, Turaki yay mata wata runguma da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma na riƙe ne da zanin Hajiya Madina da yake jin kamar a lokacin ƙwace musu ita za'ayi.

wani tausayi ya ratsa zuciyoyin duk wanda yake zaune a parlon banda zuciyar mutum ɗaya da ke ƙissima tarin abubuwa acikinta.
lissafi take, lissafin yanda komai zai tafi, lissafin yanda komai zai warware, lissafin yanda baya ba zata taɓa gogewa ba, lissafin yanda komai zai tafi akan nata tsarin lissafin.
Chapter 23 · 0% Book details