← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 176

Sashe 109

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hamid". ta kira sunansa da amon sautin da ya tafi ya taɓa har zuciyar Hayyo.

"me kake nema a ƙafafuna Hamid?, laifin me kayi min?, tashi tsaye na ganka ɗana".

Hamid ya miƙe yana hawaye, Ummi ta rungumosa jikinta suna kuka tare, wucewar daƙiƙa biyu Hamid ya zare jikinsa daga nata yana bin mahaifiyar tasa da kallo, wadda yaga ta ƙara kyau da girma kamar ba ita ba.

"ya akai kazo nan Hamid?, wa ya faÉ—a maka inda muke?".

tambayoyin da tai masa kenan, kuma kamin ya bata amsa idonta ya sauka akan halittar da duk lalacewar da tayi ba zata kasa ganeta ba a kallo ɗaya, tai saurin ɗauke ƙwayar idonta daga kan mutumin da take jin ta tsane shi tsana mafi muni.

Hamid ya buɗe baki zai yi magana tayi saurin ɗaga masa hannu cikin fusata, ta kulle idonta tana huci na tsawon daƙiƙa ɗaya, ta buɗe su a sanda ƙwayar idonta ta kaɗa tayi jawur, wannan damuwar da take tare da ita na tsawon shekaru ta taso tun daga can ƙuryar zuciyarta ta mamaye saman fuskarta.
da tsananin ɓacin rai a muryarta tace da Hamid,"tunanina duk sanda zan ganka zan zama ina me farin ciki ne".

ta faɗa tana ƙara ɗaga muryarta da faɗin,"me yasa kazo min da wannan abin cikin gida?, to idan baka sani ba ka sani, bana so kuma bana ƙaunar sake haɗa ido da azzalumin mahaifinka har in bar duniya, dan haka tun ina shaida kai ɗana ne ka fitar da shi daga gidan nan".

tai maganar cikin zafin rai tana yi masa nuni da gate, Hamid ya dubi mahaifinsa da tausayi wanda ke ta kokawa da wheelchair yana so ya sauko, ya koma ya kalla Ummi yace,"dan Allah Ummi...".

bata barsa ya ƙarasa ba ta doka masa tsawa.
"Hamid ka fita da shi na faÉ—a maka, ka fita da shi tun ina iya kallonka ina shaida kai É—ana ne, Hamid ina me rantse maka in baka fitar da wannan matsiyacin mutumin daga gidan nan ba zan tsine maka".

Kaka tayi saurin shiga maganarta da cewa,"kul, kul Halimatu, shi me yayi miki da zaki nemi ki sauke fushinki akansa".

Ummi tace,"wallahi tallahi in har don inci gaba da kallon wannan azzalumin mutumin a inda nake ne to gwara in yafe Hamid muddin bai fitar da shi daga gidan nan ba, na tsani mutumin nan na tsani ganinsa, inata roƙon Allah kar ya ƙara haɗani ko da ace da inuwarsa ne shine Hamid saboda ba ya ƙaunata zai ɗauko shi ya kawo shi inda nake salon zuciyata ta buga".

Yami tace,"kiyi haƙuri Ummin Fillo, ki tsaya ki saurare shi har yanzu shi ɗin mijinki ne, kuma kar ki manta shi uban ƴaƴanki ne, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana, to kuma ina laifin wanda ya gane kurensa yazo neman yafiyarka".

ta girgiza da kanta cike da takaici da ƙunar rai,"Yami baki san waye wannan mutumin ba, wannan da kike ganinsa azzalumi ne, mugu ne, macuci, dan Allah ku fitar da shi daga gidan nan tun ban faɗi na mutu ba".

sai kawai ta fashe da kuka me cin rai, tana jin wani abu me É—aci na taso mata, tana jin kamar ta shiga ciki ta rarumo duk abinda ta gani tazo taita rotsawa Hayyo.

faɗowar Hayyo daga kan wheelchair yasa hankalinsu ya kai kansa, Hamid ya tafi da sauri ya ɗaga kujerar da ta danne shi, jikin Hayyo duk karkarwa yake, yana jan jikinsa a ƙasa yana so ya ƙarasa gaban Ummi, Hamid ya fara hawaye ya ɗagosa ya mayar da shi kan kujerar, sannan ya turasa ya kaisa gaban Ummi.
gwanin ban tausayi hawaye ke sauka akan fuskar Hayyo ya haɗe hannayensa alamar roƙo, bala'in nadama da danasani shimfiɗe a fuskarsa, cikin ƙinƙina mesa zuciyar mutum ta tsinke yace,"dan darajan Allah ki yafe min Halima, ki tausayawa halin da nake ji, ke kaɗai kika rage ki yafe min acikin waɗanda suke raye, kuma muddin ba ki yafe min ba nasan ba zan gama da duniya lafiya ba, domin nasan na aikata miki abubuwan da Allah ba zai barni ba, dan Allah ki yafen ko na samu sassaucin bala'in da nake ji a tare da ni".

Ummi na kallonsa da tsantsar tsana tace,"kai yanzu Hayyo har kana da idon da zaka kalleni ka buɗi baki kace in yafe maka?, yaushe kasan Allah da yau kake roƙon wani da shi?, to bari kaji na faɗa maka, banda idon da zan dubi halin da kake ciki in tausaya maka balle na yafe maka, ka cire batun yafiya tsakanina da kai dan ko da ace yafiyata ta rage maka shiga aljannah Hayyo ba zan yafe maka ba".

Kaka, Yami da Hamid su kai ta roƙon Ummi akan ta yafe masa, amma sam taƙi, ƙarshe ma sai ciki ta shiga ta ɗauko mayafi ta fito tana kallon kowa tace,"in har ba zaku ɓadda shi daga inda nake ba to ni zan bar muku gidan".

sannan ta kalli Hamid tace,"kai kuma ko a mafarki ka ganni karka nuna ni a matsayin mahaifiyarka, tunda kaima baka tausayina".

tana zuwa bakin gate Fillo na turo ƙofa ta shigo, niƙab ɗinta a hannu tana yamutsa fuska alamun ta gaji, farat ɗaya hankalinta ya tashi ganin Umminta na kuka, gabanta ya faɗi tana tunanin me zaisa mahaifiyarta kuka a yanzu kuma?, ai tayi zaton zubar hawayenta ya ƙare kuma tunda har ta rabu da Hayyo.

sai ta ƙanƙance ido tana bin kowa da kallo, ta tsayar da idonta bayan Hamid da bata ga fuskarsa ba, zuciyarta bata gama tunanin ko waye ba ya juyo, ta ware ido tana faɗin,"Hammah". ta faɗa murmushi na ƙwacewa a fuskarta, harta ɗaga ƙafa zata wuce wurinsa sai kuma idonta ya sauka akan mahaifinta dake kallonta yana murmushi da hawaye, alamun na yaji daɗin ganinta, lokaci ɗaya ta haɗe rai ta ɗauke idonta daga kansa.

ta kalla Ummi dake ƙoƙarin raɓata ta wuce, ta kama hannunta zasu fita maganar Hamid ta tsayar da ita.

ta juyo tana kallonsa tace,"Hamma dana ganka sai naji farinciki ya kamani, amma da naga wannan masifar a tare da kai sai naji kamar in haɗiyi zuciya in mutu, saboda na san ba komai ya samin Ummina kukan da ta jima bata yi ba, dan haka gwara mu bar muku nan ɗin dan ba zamu ƙara zama da masifar da zata hanamu farinciki da jin daɗin rayuwa ba".

tana rufe bakinta Hamid ya É—auketa da mari, kuma bai sauke hannunsa ba Ummi ta zabga masa marin shima.

"ƙarya tayi ba masifar bane shi da har zaka ɗaga hannu ka marar min yarinya, to wallahi ka kiyayeni kar kaja ɓacin rai yasa bakina ya zama silar lalacewarka a duniya, kuma na fasa tafiyar kaje ka gangaro shi kuzo ku fita a gidan nan tunda ba uban wani ya gina mana ba".

maganar Hayyo ta shiga kunnen Fillo a sanda yake cewa,"dan Allah dan Annabi Æ´ata ki yafe min, ki tausayawa halin da nake ciki, wallahi na san alhakinku ke bibiyata shisa na faÉ—a cikin wannan mawuyacin halin".

Ummi tace,"ai baka ga komai ba, kaÉ—an ma ka gani, kuma insha'Allahu nan gaba maganar ma sai ta gagareka, da izinin Allah sai kowa ya gujeka ya barka kai É—aya a halin da yafi wannan muni".

Hayyo ya kulle idonsa yana ƙara roƙon su Ummi su yafe masa, tasa tazo ƙarshe su taimaka masa kar ya tafi lahira da alhakinsu, Fillo na kallonsa cikin ƙunci tana tuna voice ɗinsa da taji a wayar Turaki tace,"mu yafe maka kake cewa?, ka manta san da kake saka Ummina a ɗaki ka kulle kayi ta dukanta?, ko kuma ka manta san da kake bin ta har waje ka duketa a gaban mutane kana zaginta?, ko manta yacca ka azabtar damu da yunwa kayi?, ko kuma ka manta sheganta ni da kayi da har kake kirana da ƴarka?, to idan ka manta duk waɗannan abubuwan mu ba zamu manta ba, kuma tsakaninmu da sai Allah, da yardar Allah ba zaka mutu ba sai kaga shiga matsanancin halin da yafi wannan".

a tsawace Kaka tace da ita,"kul ɗinki Fillo, kar ki ƙara wani furuci anan, wannan lamarin tsakanin iyayenki ne, duk lalacewar uba uba ne shi, uba ba abin wasa bane ki san da wannan, kamar yanda kike ganin mahaifiyarki da mutunci ya zama dole shima ki gansa a mutunci muddin kina son gamawa da duniya lafiya, ke ba dan shi ba ai da baki zo wannan duniyar ba, ki iya bakinki akansa kafin duniya tayi watangaririya da ke".

Fillo tasa kuka tana faɗawa jikin Ummi tace,"ni wannan ba Babana bane, shi da ya sheganta ni a duniya ta ya za'ai ya zama ubana, mutumin da ya kasa bani ilimi da tarbiyya shi ne zai zama mahaifina?, ni dai ba Babana ba ne kuma ba zan taɓa yafe masa abunda yay mana ba".

tarin da Hayyo ya fara babu qaqaautawa yasa Fillo haÉ—iye sauran maganganunta tayi kansa da sauri, Kaka tace da Hamid ya tura shi su shiga daga ciki, Ummi na tsaye tana jin zuciyarta nayi mata wani iri tabi bayansu da kallo.
cikin ƙanƙanan lokaci dai Hayyo ya fita a hayyacinsa, tari kawai yake yana a basa ruwa ya sha, Fillo ta ɓare jarkan faro jikinta sai rawa yake yi ta zuba a kofi ta tallafi kansa ta basa ya sha, Kaka ta ɗauka lambar Dr Yusuf ta kirasa a waya yace gashi nan zuwa nan bada jimawa ba.

cikin mintunan da basu wuce biyar ba Hayyo yasha ruwa yafi roba huɗu, da yasha zai kuma cewa a ƙara masa, kuma duk Fillo ce take basa, idan ta kai kofin bakinsa sai ya haɗa harda hannunta ya kama tukunna yake shan ruwan, hawayenta kuwa dake zuba ajikinsa jinsu yake kamar wuta, in ace ya san haka Ƴaƴa suke da tausayi da jin ƙai da bai wulaƙanta ƴaƴan da Allah yabasa ba balle ya wofuntar da su, bai san Ƴaƴa rahama bane sai da ya shiga wannan halin, lokacin da babu macen da zata kula da shi, haka kuma babu ƴaƴan da zasu zauna su basa kulawa, in ace babu Hamid bai san kuma ya zai yi ba, wataƙila da tuni ya mutu ya ruɓe ba tare da kowa ya sani ba.
Chapter 109 · 0% Book details