← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 176

Sashe 15

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

leɓensa na talewa da murmushi yace,"ummm to kinyi kyau sosai...kinyi break fast?".

Ta gyaÉ—a masa kai,"tare zamu yi da kai".

Ya hurar da iska daga bakinsa,"to ai Maama bata sakko ba har yanzu, ni kuma bana so ki zauna da yunwa. ko muje kitchen É—in mu dafa tare kinga mun hutar da ita?".

ta ɗaga masa kai alamar ehhh, hannunsa na riƙe da nata suka miƙe tare, kai tsaye kitchen suka wuce, su na shiga ƙamshin egg ya shiga hancinsu, idonsu kuma ya kai kan wanke-wanken cikin sink, Zaytuna ta dube shi, shima ita ɗin yake kallo idonsa na haskawa da irin abinda nata ke haskawa.

"but yaushe Maama ta sauko har tayi girki ban sa ni ba?".

"may be bata san ka shigo ba, ko ka shiga É—akinta?".

"nop, time É—in da na shigo bata tashi ba ai".

Fitowa suka yi daga kitchen É—in, Zaytuna ce ta kula da Fillo bayan da Turaki ya haye upstairs, ta kalleta da murmushi a fuskarta tace,"sannunki".

Da yake Fillo ta shaidata ta duƙa har ƙasa ta gaisheta, Zaytuna ta amsa tana tambayarta lafiya tayi tsaye anan.

"Kaka ce bata da lafiya shine na amsheta".

"ohh kece jikartata dama?".

ta gyaÉ—a kai,"eh ni ce".

Zaytuna ta sakko daga step na farko da ta hau, ta dafa kafaÉ—ar Fillo tana kallon fuskarta, haka kawai taji yarinyar ta burgeta.

"sannunki, kina da kyau sosai...amma jikin Kakar da sauƙi ko?".

"ehh na dai barta tana bacci".

"Allah ya bata lafiya".
Zaytuna ta faÉ—a tare da kai kallonta kan dining É—in, tana buÉ—e plate tace,"ke kika girka?".

"a'a Hajiya ce, babu jimawa ta hau sama. tana ta yi min bayanin wanda zai ci abincin to ban gane ba ne".

Zaytuna na murmushi ta ƙara dafa shoulders ɗinta tace,"na Hammah ne, ba ki lura da shi ba ne a zaune?".

Fillo tace,"nayi zaton Alhajin gidan ne".

Zaytuna da Nihal wadda ta shigo yanzu taji abinda Fillo tace suka saki dariya tare.

"Lallai kuwa Alhajin gidan, yau an maida Hammah tsoho...ke sai kace mara gani sosai ki kasa banbance dattijo da matashi".
Nihal ke faÉ—a.

zata hau upstairs ta ke cewa da Zaytuna.

"Adda kije Baffa na kiranki".
"oak, to kice da Hammah ya sakko ga breakfast É—in nasa".

Nihal ta haye upstairs ita kuma Zaytuna ta fita, suka bar Fillo tsaye a wurin. da jikin bango ta jingina har sanda Hajiya Madina suka sakko ita da Nihal da Turaki, da shirin fitarta ta sakko hakan yasa tayi mata adawo lafiya, babu jimawa Turaki ya dawo daga rakiyan da suka tafi yi mata.

yana waya da Bello Ƙaraye ya shigo, ya zauna kan dining ɗin ba tare da ya taɓa abu guda na abincin ba. har sanda ya gama wayar Fillo dai na nan tsaye kamar soja, wasa kawai take da yatsun hannunta, hanakalin na can wurin Kaka, tana ta zullumin wannan bawan da har yanzu bata sami kallon fuskarsa ba ya samu ya sallameta tayi tafiyarta.

Turaki na danna waya ya ɗago ido ya kalleta suka haɗa ido, tayi saurin ɗauke nata, shi kuma ya kalli kayan abincin sannan ya ƙara kallonta ta gefen ido. maganar Maama na dawo masa cikin kansa, wai ita tayi helping nata da greating taruhu da yankan albasa, to ta ya ma zai soma cin abicin da wannan yarinyar ta saka hannu?.

wani ɓacin rai ya ziyarce shi, ai ko abincin restaurant ba kowanne yake ci ba, balle kuma na wannan abar. yau bai san me ya sami Maama ba, ita da ta ke haƙura da ko menene akan buƙatarsa kawai, amma yau akan wani meeting har tana haɗa dafuwar abincinsa da ƴar aiki.

murya a tamke yace da Fillo,"ja kujera ki zauna".

Ba dan tasan su biyu ne kawai ba da sai tayi zaton ko da wani yake, tunda babu wata alama da ta nuna da itan yake. kuma duk da hakan dai sai ta tsaya, domin tasan kujerar da yake magana tafi ƙarfin zamanta.
Ita duk rayuwarta ma bata taɓa ganin irin kujerun ba ma.

kusan 2minutes da maganar tasa ya ƙara ɗago ido yana mata wani duban yatsine, yay saurin kauda kansa a tsawace yace,"do you want me to repeat my self before you sit?".

Saurin rufe ido tayi tare da ƙanƙame jikinta, sai rawar jiki ta ke yi kamar me jin sanyi. A rayuwarta ta tsani tsawa, bata sonta ko kaɗan, tsawa na firgitata, tsawa na sakawa ta kusa fita a hayyacinta, tsawa na sakawa ta tuna wani moment da bata son tuno shi a rayuwarta, tsawa na sawa har suma tayi, dalilin da yasa a ko yaushe ta ke guje duk abinda zai sa ayi mata tsawa.

tafi minti uku kafin ta dawo normal, da ƙyar ta iya haɗiye yawun bakinta, a hankali ta buɗe ido ta sauke su akansa, irin kallon da yake yi mata gani ta ke kamar zai duke ta...idonta ya ciko da ruwan hawaye, ta shiga ƙiftasu gudun kar su zubo, ta kama jan yatsun hannunta tana danasanin zuwanta, da wannan abun da yayi mata ai gwara ta yiwa Kaka gardamar ba zata zo ba.

ta kalle shi suka haÉ—a ido, ta yi saurin É—aukewa tana jin faÉ—uwar gaba.
Muryarsa har cikin kanta ya ƙara cewa,"Do I look like someone who would talk to you and ignore?".

Da ƙyar ta iya buɗe ido tana kallon yatsunta, shi wai bai san bata jin wannan yaren ba ne da yake ta ɗaga mata murya da shi. ita bata san ba ma ko abincin ma ba ya ci da kansa sai an ba shi, ƙilan shi yasa yake tayi mata wannan ihun, to ai ba laifinta bane laifin babarsa ne da bata yi mata wannan bayanin ba, kuma ma ya za'ai ace wannan ƙaton ba zai iya cin abinci da kansa ba, banda dai lalacewa.

in cool voice da ke rawa tace masa,"kayi haƙuri ka daina ɗaga muryar, ni ban san me kake cewa ba shi yasa, bana jin wannan yaren".

Yay ma ta wani uban kallo kafin yace,"na farkon ma ba ki ji ba?".

tace,"wanne?".

Ya galla mata harara bai ce komai ba, haka kawai taji tana tsoronsa, yanda taga ya jijjiga kai bata san me zai aikata ba, saboda haka hannunta na shaking taja kujeran ta zauna a É—arare.

"na zauna". ta faɗa tana kusan ƙwarewa.

ta wutsiyar ido yake kallon hannunta da ke rawa akan plate, yana da tabbacin yarinyar nan bata da isashshiyar lafiya.

Muryarsa a kausashe yace,"buÉ—e abincin kici".

ta wani waro ido waje ta kalle shi, cikin sanyin jiki tace,"na ƙoshi".

rufe bakinta ya haɗe da wani mugun kallo da ya watso mata, bata san lokacin da ta damƙe plate ɗin abincin ba.

Turaki kuwa kallon ƙasusuwan jikinta kawai yake, ina alamar ƙoshi anan?, kamu ɗaya zai yi mata ta ɓalle gaba ɗayanta, idan kuwa yace zai yi mata kallon tsab sai ya ƙirge duka ƙashin jikin nata, kuma a hakan ta ke ikirarin ta ƙoshi.

ya karkato kanta murya a ɗage yace,"kin ci abincin nan ko sai na miƙe kinga asalin tsayina?".

babu shiri Fillo ta kai hannu cikin plate É—in zata fara ci, ya dakatar da ita cikin tsawa da cewan,"É—au spoon".
[8/9, 19:47] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*©️Halima h.z*

*10*
wannan tsawar da Turaki ya sakar mata ita tasa ta rikicewa gaba ɗaya, she was completely out of her mind, spoon ɗin da ta ɗauka ya faɗi ƙasa ya bada sautin wata ƙara wadda sai da Turaki yasa hannu ya toshe kunuwansa.

haushin hakan yasa shi damƙo hanunta cikin zafin nama, wanda bai san lokacin da yay hakan ba. ɓacin rai ne kawai, jin mugun riƙon da yayi mata sai kawai ta fashe da kuka tana ƙara rumtse idanuwanta da kyau, ta shiga girgiza kanta a hankali cikin zubar hawaye masu zafi.

muryarta tayi can ƙasa, amma hakan bai hana lafuzan bakinta shiga kunnansa ba, thats why he focuse attention on something she is saying.

"dan Allah kar kiyi mata komai".

ya so yaji dukkan abunda tace sai dai hakan ya gagara, sai wanda kawai ya tsinta, kuma daga shi ɗin tayi shiru, bata sake cewa komai ba sai shashsheƙar kuka da ta ke yi.

ya ƙura mata ido kawai yana dubanta da kyau da kuma mamakin fitar hayyacin da tayi a lokaci ɗaya, ba sai an faɗa masa ba da ganin yarinyar yasan bata da isashshiyar lafiya. lokacin da ta dawo cikin natsuwarta ta shiga buɗe idanuwanta a hankali ta sauke su akan hannunsa da har yanzu ke riƙe da nata gam.

ƙirjinta banda up and down babu abinda yake, idonsa na kan dining table ɗin da alama wani abu yake tunawa, hakan yasa bai san da buɗe idanuwan nata ba sai jin maganarta yayi.

"Hannuna". ta faÉ—a muryarta na fitowa a hankali.

ya ɗago ido ya kalli hannunsu da ke haɗe, sai kawai yasha mur sannan ya kalleta yace,"ba ki da hankali da za ki sakarwa mutane cokali yayi wannan uwar ƙarar, kuma kukan na uban mene?".

bata ce da shi komai ba tayi shiru, ƙoƙarin ta janye hannunta ta ke amma yaƙi sakinta, ta matse ido kaɗan ta buɗe tare da cewan,"ka matse min fata".

sai a lokacin ya ankare ya sakar mata hannu, ta wutsiyar ido ya kalli yanda fatar wurin tayi jawur.
ita dai tunda ya sakar mata hannun sai ta kama wajen tana shafawa a hankali saboda zafi, so take ta gama hucewa ta miƙe ta tafi inda tafi kauri, tafiyar da ba zata ƙara dawo da ita nan ba, wannan zuwan nata shine na farko kuma shine na ƙarshe ba za'a kuma wani ba.

ta miƙe zata bar kujerar ya ɗaga kai ya kalleta, murya a tamke, fuska a ɗaure yace,"koma ki zauna, in kinga kin tashi a wurin nan to kin cinye wannan ƙazantar taki".

ta kalli abincin ta kalle shi, ta É—an haÉ—e fuska sannan tace,"Hajiya ce ta girka bani ba ai".

yanda muryarta ta kumbura wajen faɗa sai ya zamana kamar da rashin kunya ta faɗa, hakan yasa yay saurin ɗagowa, da miƙewarsa tsaye da kai hannu fuskarta zai mareta duk bai san lokacin da yay ba. banda Allah ya taimaka tayi saurin yin ƙasa da fuskarta da sai ya sharara mata maruka.

ya yiwa dining table ɗin wani mugun duka hannunsa na dunƙulewa akai.
Chapter 15 · 0% Book details