Sashe 156
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Samha ta amshe da cewa,"ai wallahi jiya na so da ni aka je da sai nayi masa rashin mutunci. ni yanzu Nihal ma aina zan ganta, da ƙyar ma idan bata ƙwace tayi gidan Hammah ba fa".
a lokacin ne dattijiuwar da ta shigo tana laluben Hajiya Ramla ta ƙaraso wajen.
Hajiya Ramla tace da ita,"sannun ku da aiki Maga".
"yauwa Hajiya, wai da ma masu yankan nama ne suka ce Baffa ya kira waya yace a ƙara yanka raƙumi da raguna guda uku, sai akai raƙumin gidan Hakimi".
"sun yanka ne?".
"a'a da ma nace bari na zo na fara shaida miki".
"to kinga garzaya ki faɗawa Madina, ki dubata a ɓangarenta ko ɓangaren yaran nan".
"to shikenan, batun funkason can fa ya za'ai da shi?".
"ai da kun gama ku kai gidan Babana, ɓangaren Fillo za ku kai, nata ne aka yi mata saboda baƙin da ke can".
"to shikenan".
Maga ta juya ta fita a parlon, yayin da Hajiya Ramla ta ƙarasa wurin mutanen da ke zazzaune a parlon, waɗanda mafi yawan su abokan aikinta ne.
"sannunku fa". ta faÉ—a a sanda take zama akan É—aya daga cikin kujerun, kusa da wata aminiyarta Hajiya Shamsiyya.
"yo ke uwar amarya haka ake sai ki shige É—aka ki barmu zazzaune anan".
murmushi ya ƙwace a fuskar Hajiya Ramla tace,"haƙuri zaku yi, ƴar taku ce ta sakani gaba tana kuka".
ta faÉ—a a lokacin da take bawa wata tsohuwa umarnin inda zata ajiye kulolin soyayyan naman da ta shigo da su.
sannan ta ƙwalla kiran Ɗausiyya da sabuwar ƴar aikin da suka yi bayan auran Fillo, me su na Maraƙisiyya, cikin sauri sai ga su sun zo sun durƙusa a gabanta.
"ku É—auko farantai ku fara rabon naman nan, kowanne plate ku zuba yanka goma sha biyar".
sai kuma ta kalli tsohuwar tace,"Yaya kun kai ɓangaren Madina kuwa?".
"ehh Hajiya yanzu Yami ta tafi kaiwa".
"to masha'Allah, sannunku da aiki".
sannan ta ƙara cewa da ita,"Yaya don Allah ce da Madina ta bayar da maƙullin store, sai a samu waɗanda za su ɗebo lemuka aciki, a ɗebo katan arba'in, akai katan sha biyar gidan Babana, sai a bar sauran anan".
cikin sauri tsohuwar ta miƙe ta fita, sai da ta fara zuwa ta duba wajen aikin suyar ta su sannan ta wuce ɓangaren Hajiya Madina.
nan ɓangaren ma cike yake da mutane waɗanda mafi yawansu ƴan'uwa ne, duk sai ka kalla fuskokin su zaka shaida ashe Hajiya Madina ƴar dangi ce, saboda kusan duk kamannin su ɗaya.
"Hajiya tana sama ne?". tsohuwar ta tambaya a sanda ta shiga parlon.
"kamar dai ta shiga kitchen". wata acikin mutanen dake zaune akan kujera ta faÉ—a.
"ta fito ta koma sama fa, yanzu suka wuce ita da Zaytuna".
Tsohuwar ta miƙe cikin hanzari ta hau upstairs, ta tsaya a ƙofar ɗakin Hajiya Madina domin jiran iso bayan tayi sallama.
a sanda babu wanda ma ya jita saboda akwai Æ´ar hayaniya acikin É—akin.
Hajiya Madina na tsaye a gaban madubi tana ɗaura sarƙa a wuyanta, a lokaci ɗaya kuma tana bayani ga Maga.
"kinga ba wani nama da za'a kai gidan Hakimi, shi ya siyo mana, ko a gidansa ake taron, mu da aurar da ƴaƴa shi da karɓe nama. wani lokacin ma dai Baffa ya fiya neman suna, ya mayar da Hakimi kamar wani ubansa, to kice su yanka a haɗe gaba ɗaya da na gida, in Baffan ya dawo ace masa mantawa aka yi".
Maga ta miƙe tana ƴar dariya ta fita, Yaya ta shigo ita ma, ta durƙusa tana cewa,"Hajiya wai ki bayar da maƙullin store za'a ɗebo lemuka".
"Zaytuna duba drower ɗin nan ki miƙo mata maƙulli".
sai kuma ta dubi Yayan ta ƙara cewa,"don Allah da an ɗebo a rufe saboda jiya sai da akayi mana ta'adi".
Umman Nadiya ta shigo É—akin a lokacin.
"ke Madina da ma Turaki aure ya ƙara?".
Hajiya Madina ta kalli fuskarta a cikin madubi tare da yin murmushin takaici sannan ta ce,"wa ya guntsa miki wannan maganar?, to ba sabon aure yayi ba tsohuwar matarsa ya mayar, ita ma kuma don fitinanniyar Kakarsa ta ƙara tayar da rigima ne, yauwa biyayya ya ƙara yi a karo na babu adadi, don Allah a bar ɗana ya huta a daina yawan zancensa ana faɗar masa da gaba, haba tun jiya da akace an ɗaura aure da shi ake ta ƙwala kiran sunansa acikin gidan nan kamar wanda yay sata, to idan ma auran ya ƙara zunubi ya aikata ko me?, ina ruwan wani?, ko ba mata huɗu aka halasta masa ba?, haba mutane da shegen gulma da tsugudidi".
Umman Nadiya tace,"to jarababba Allah ya ba ki haƙuri, ni tambaya nayi ba wani abu ba".
Hajiya Madina dai bata ƙara tanka mata ba, ta haɗe rai ta juya kan Zaytuna tana yi mata faɗan kukan da take tayi tun jiya da aka ɗaura aure.
"ni dai ina ga sai na haɗa miki da duka tukunna, haba kuka yaƙi ci yaƙi cinyewa abu tun jiya, to ki shiga hankalinki da ni".
Umman Nadiya tace,"to ai dole tayi kuka, ita kaÉ—ai ce fa acikin su zata yi nesa".
"yo nesa abu da ba ƙasar zata bari ba, Allah na tuba ina nan ina Abuja, shi ma ɗan banzan Bellon da ya biyewa Baffa ya mayar da shi can abujan, ai sai da na faɗa masa ya dage ya barsa su ci gaba da aikinsu anan. ban ma san munafikin dai da ya bayar da shawarar buɗe wani kamfani ba tare da saninmu ba, ko da yake yanzu ai mu ƴan banza ne a wurin Baffa, duk ya mayar mu ƴan wofi, wannan fitinanniyar tsohuwa duk ta bi ta hargitsa mana zama, Allah ya shiryeta kawai, yanzu tun da dai an mayar da auren sai ta bar hankalin kowa ya kwanta".
ta kamo kunnen Nihal da ke shigowa ta murÉ—e,"ke, ke, ke, ki kiyaye ni fa".
"Maama wallahi Hammah É—in ne fa ya koro ni, wai daga nace ba za'a bawa masu jeran kayan Ilham abinci ba".
"mtsww Allah ya sauƙa, to Mum ɗin ku tace ki wuce ki karɓo mana kayanmu tun ranki bai ɓaci ba".
"ehh yanzu zan tafi, Maama to sauran kuÉ—in ai za ki cika min".
"nawa ne?".
ta ɓoye ƴar dariyarta tana leƙo jakar Hajiya Madina dake saman gado ta ce,"jiya na ƙara kai ɗinki na set uku, su zan saka ranar da za'a kai amare, balance ɗin dai har na ku yace 35k za'a bayar".
"idan kuma babu naki fa?".
"20k".
ta zauna bakin gadon ta ɗauko jakarta, ta ƙirgo kuɗi 20k ta miƙawa Nihal ta ce,"ga namu ɗin, naki kuma bari nayi miki kwatancen ɓangaren Baffa ko kuma na ba ki lambarsa kawai, sa 08065....".
kowa a ɗakin yasa dariya hatta Zaytun da ke kuka tun ɗazu, Nihal ta fara shagwaɓa tana zama kusa da Hajiya Madina ta shiga yi mata kirari da kalallameta.
Umman Nadiya ta ce,"gaskiya ya kamata dai a bawa Auta kuɗi ta karɓo nata ɗinkin ita ma, ba wani sai taje gun Baffa".
Hajiya Madina ta ce,"wannan ƴar fa da kike gani tun da biki ya taho ta fara fashin kuɗi, daga shekaranjiya zuwa jiya kawai tayi min fashin kuɗi sun kai kusan 100k. tsabar rashin sanin darajar kuɗi jiya makeup ɗin 20k akayi mata, ɗaurin aure kawai ba wani event ba. her Excellency kuwa ce tayi sai jiya ta ankare da ATM ɗinta, ta manta shaf ta bawa Nihal tun ranar da aka je jeran kayan ɗakin Samha, ƙarshe dai ta talauta ta babu ko sisi a account ɗin nata, to ni dai na bata shawara nace ta makata a kotun alƙali Dikko kawai, ina dalili yarinya duk ta bi ta yashe mu".
"Allah Maama kina da kuÉ—i, to ki ban 5k sai Mum ta cika min 10k É—in".
"yo Nihal ko da Kakar ki BoÉ—ejo uwar masifa kike tafe ai biyar ba zan ba ki ba, don haka ki tashi ki kama gabanki kawai, kije can wajen Uwaki ta ba ki".
Zaytuna ta ce,"ke yarinyar nan wai me kike yi da kuÉ—i?, Maama É—a zu ma fa tasa Hammah Bello ya turo mata 20k, ina jinta kuma again tana bin Khaleel tana yi masa Æ´ar murya".
Nihal ta tura baki gaba ta ce,"daga yau ba zan ƙara tambayar mijinki kuɗi ba balle ki zo kina min tonon silili, kina terere da ni mijinki ya ban dubu ashirin. shi ma Hammah Khaleel ɗin da ya ban sai da ya faɗawa duniya ya bani, shiyasa zan mayar masa da kayansa, to wai ma idan baku bani ba waye zai ban? Hammah ne kaɗai a gidan nan zaka tambayrsa kuɗi ya baka kai tsaye babu ƙurewar tambayoyi".
Hajiya Madina tace,"ba kya tambayar na hankali ne shiyasa, tambayar Æ´an fashi kike yi, ban san ba kuma ko jari za ki kafa da kuÉ—aÉ—en mu".
"Maama to ki ban don Allah, haba Maaman Hamman'mu, Maama me haƙorin maka guda biyu, Maama ƙawar Boɗejo, Maama ta hannun dama na".
Hajiya Madina tayi dariya ta make hannunta dake kan haɓarta,"zan ci gidanku Nihal, naga alama kin mayar da ni Kakarki".
sai kuma ta ɗauko kuɗi a jaka ta bata ta ce,"ga 5k nan daga haka ba zan ƙara ko ficika ba".
Nihal ta rungumeta tana yi mata kiss,"Allah ya bar min ke uwar marayu har ma da masu uba, i love you so much. Allah yaja mana da ranki".
lokacin Samha ta shigo ɗakin, bayanta wasu yara ne su uku ke biye da ita, Hajiya Madina ta bita da kallo, cikin sigar tsokana ta ce,"don Allah Umman Nadiya kin taɓa ganin amarya mara kunya irin wannan?".
ta nuna Samha da ta wuce wadrobe ta buÉ—e tana É—ebo kaya.
"ina irin ƴar ƙwallar nan da ake yi ta ranar ɗaurin aure, to in faɗa miki yarinyar nan dai bata yi ba, jiya Zaytuna na kuka ita tana wage haƙora talatin da biyu a waje, duk sai ta bani kunya...".
Samha ta katse maganar Hajiya Madina da cewa,"kai Maama, ni yaushe akayi hakan, Allah ma nafi Adda kuka".
"yo camera ai ba zata yi ƙarya ba, za'a kawo bidiyo ko bayan raina Umman Nadiya za kice na faɗa".
Samha tayi murmushi ta ce,"Maama ina tawa atamfar?".
"ki ka bani ajiya?".