← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 176

Sashe 171

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai ya kalli jaririyar da kukanta ya fara yawa yace,"Allah'n mu ka tausaya mana, don Allah Allah ka juya wannan ƙaddarar, ka ganta Allah tana buƙatar nonon mahaifiyarta a halin yanzu, idan kace ka ɗauketa bata da me bata abincinta, Allah ko ba don ni ba, don jariran nan Allah ka tausaya mana, Allah jarabawar tayi mana girma, a sauya mana, a dawo da Fulani a ɗauƙe ni Allah".

sai yayi ƙarfin halin miƙewa ya hau kan gadon ya zauna, zama sosai har da miƙe ƙafa, ya ɗaga mayafin da aka rufeta da shi ya buɗe fuskarta, da farko daskarewa yayi a yanda yake, sai kuma yayi blinking idonsa, saboda ganin kamar likitocin sun yi makuwar saƙon da suka faɗa masa, domin wannan ba fuskar gawa ba ce, wannan fuskar ta me bacci ce, gata nan fess da ita, ta ƙara yin wani irin kyawun da bata taɓa yi masa ba, fuskarta ta ƙara yin doguwa, hakama hancinta kamar ba nata ba, ya ƙara yin tsaho sosai, fuskarta sai annuri take.

a sanda ya lura da rashin motsin bugawar zuciya a ƙirjin matarsa, a sannan ya kamo hannunta ya ƙanƙame a ƙirjinsa ya haɗa da jaririyar, yana jin irin yanda zuciyarsa ke huci tana huda ƙirjinsa tana neman fashewa.
shi musulmin ƙwarai ne ya san mutuwa, ya yarda da ita, so dole yay accepting jarabawarsa, dole ya yarda da ƙaddadararsa, yanzu ya tabbatar da likitocin ba ƙarya suka yi masa ba, ta mutu, ta tafi in da Maama ta tafi, ta tafi in da ba'a dawowa.

sai kawai ya kwantar kansa akan ƙirjin gawar tare da rufe idonsa, yana jin wani irin bala'in kaɗaici ya lulluɓe shi, yana jin mugun tausayin kansa, yana jin tamkar shi ɗaya ne ɗan Adam ɗin da yay ragowa yanzu a duniya, sai yaji ina ma shi ma tasa zuciyar ta daina motsawa tamkar ta Fulaninsa, shi ma ya koma gawar ko ya daina jin raɗaɗin da yake ji a zuciyarsa, yana jin kamar ya zama gawar ya bi bayan matarsa masoyiyarsa, ya bi bayan macen da ta dinƙa kasada da ranta domin ceto rayuwarsa.

a haka yay kissing ƙirjinta, tabbas wani tashin hankalin yafi gaban kuka, domin a yanzu ya kasa yin kukan, alhalin kuma kukan yake so ya yi.
wacewar mintuna ashirin da biyar, a lokacin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, acikin parlon na Hajiya Ramla, gawar da aka rufe na shimfiɗe akan carpet, in da a hankali sautin wasu muryoyi ke fita da kuka wajen sanar da mutuwar da akayi.

a wannan lokacin Hajiya Ramla da Baffa da Boɗejo da Ilham na kan Turaki, wanda ya sume tun a dawowar su, tun a lokacin da suka dawo gida yake tsammanin zai ga Fulaninsa ta fito da ƙafafunta, amma sai yaga an fito daga mota wasu na ɗauke da gawarta, a lokacin ya san kallonta kawai yake yi, sai kuma yaji kukan jariran da ke hannunsa na tashi, kukan da ya ƙara haddasa bugun zuciyarsa, kukan da ya kaishi ƙololuwar tashin hankalin da har bai san lokacin da yanke jiki ya faɗi ba, ya san dai tare da yaran ya faɗi, amma bai san wanne hali shi da su suka shiga bayan faɗuwar tasa ba.

don haka tun bayan faɗuwar tasa tsawon minti goma kenan a yanzu, ƙoƙari ake tayi wajen ganin ya dawo hayyacinsa, kuma da taimakon Dr Yusuf ya farfaɗo, sai dai kana kallonsa kasan baya cikin hayyacinsa, idonsa na tsaye ne a waje ɗaya ƙyam ya zama kamar gunki, cikin ransa ji yake ina ma bai farfaɗo ba shi ma ya mutu, har cikin zuciyarsa ji yake ina ma yabi bayan Fulaninsa da Maama, duk da cewa baya so ya rabu da yaransa, to amma bai san ta yanda zai fara rayuwa tare da yaran ba alhalin mahaifiyarsu bata raye, yana tsananin tausayin su, don haka a yanzu babu abin da yake so illa ya mutu shi ma, baya so yaci gaba da rayuwar sam.

kamar daga sama mutanen parlon suka jiyo muryarsa na faÉ—in,"Wannan wacce irin jarabawa ce ubangiji yake yi min?, laifin me na aikata da za'a jarabce ni irin haka?...".

Baffa yay saurin saka hannu ya rufe masa bakinsa.
"kar ka yi saɓo Muhammad, kar ruɗani yasa ka fita daga imaninka, kayi haƙuri, ka yi tawakkali ka roƙi Allah ya baka dangana, kayi haƙuri komai muƙaddari ne, ka roƙi Alah ya baka ikon cinye jarabawarka".

Turaki ya shiga sauke numfarfashi, ya shiga jan mazaunansa har ya ƙarasa gaban gawar da yake gani, ya ɗaga mayafin ya ruƙo hannunta.
"Fulani Nah! don darajan Allah da Annabinsa ki tashi, na yarda ki tashi ni sai na tafi, ko kuma mu tafi tare, ba zan iya rainon yaranmu ba ni É—aya, ban san me zan ce musu ba idan suka tambaye ni ke".

sai kuma ya kifa kansa kan gawar yana ambaton,"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".

faɗa yake yana ƙara maimaitawa, yana girgiza gawar, gani yake tamkar idan yana hakan zata farfaɗo, kamar zata dawo duniyar su ci gaba da rayuwar su tare, su raini ƴaƴan da Allah yaba su ciki kyakykyawar kula da tarbiya, idan yaji yaran sun yi kuka sai ya shiga girgiza kansa yana faɗin Allah ka sassauta min, Allah tayi min tsauri, Allah kaji tausayina.

duk sai ya koma kamar wani taɓaɓɓe, sai maganganun kawai yake yi, idan aka ce yay haƙuri yay ƙoƙarin cin jarabawarsa sai yace ba zai iya ba, tayi masa tsauri, da farko an ɗauke masa Maama, mutuwarta bata gama sakinsa ba an ɗauke masa Mata, sannan an bar shi da marayu, marayun da ko nonon uwarsu ba su samu damar sha ba, to ta ina zai iya ɗauka?, ta ya ma zai iya cinyewa?

haka akaita rarrashinsa amma inaaaa, a lokacin da ya rasa Maama ganin yake idan aka cire Mum to duk wata mutuwa da zata zo masa zai É—auketa, zai iya É—auka, but a yanzu da ya rasa matarsa, uwar Æ´aÆ´ansa sai yaga abun ba haka ba ne, da wuya, da zafi, ba zai iya da wannan jarabtar ba me tsayawa a zuciya.
a wannan dare dai waɗanda suka sami yin bacci ƙailan ne, hatta Ilham sai ɓarawon bacci ne ya ɗauketa, domin sosai mutuwar ta taɓata, a ɗan sabon da suka yi Fillo ta shiga ranta, don tun bayan da Allah ya ganar da ita ta koma yiwa Fillo kallon ƙanwa ta jini ba wai kishiya ba.

Hajiya Ramla kuwa na kan ɗanta, idan tayi rarrashin tayi rarrashin sai taji tana taya shi kukan da ya kasa yi. haka suka kwana ba su runtsa ba, yana riƙe da hannun gawar, yayin da jariran ke jikinsa su na bacci, waɗanda aka rarrasa da ƙyar suka daina kuka har baccin ya ɗauke su, waɗanda har gari ya waye ana tunanin wanda zai shayar da su.

washegari ƙarfe goma na safe an gama haɗa gawar Fillo, gawar tana tsakiyar parlon na Hajiya Ramla cikin sutturarta, cikin wannan farin ƙyallan da ke jiran duk wani mai rai, mahaifiyarta da Yayanta da Kaka da Dada su na gaban gawar su na kuka, musamman Ummi wacca ake ta cewa su yi sallama, tayi mata adu'a domin wannan ita ce sallama ta ƙarshe da za su yi.

"Allah ya jiƙanki Halimatu, Allah ya yafe miki kurakuranki, Allah ya baki Aljannatul firdausi, Allah ya karɓi shahadarki, Allah ya karɓi ruhinki cikin daraja, Allah yasa Manzon Allah ya karɓi baƙuncinki, Allah yasa mutuwa ta zamto hutu a gareki, Allah ya lulluɓeki da rahamarsa da gafarsa, haƙiƙa ba ki yi min komai ba, na yafe miki duniya da lahira, abin da kika bari Allah ya kula miki da su, Allah ya basu haƙuri da juriyar rashinki. sai mun taho muma".

aka shigo da Turaki, ya zauna shi ma agaban gawar, yana jin sautuka na shiga kunnensa, sai dai a lokacin babu abin da ƙwaƙwalwarsa ke iya ganewa, har yanzu ya kasa karɓar mutuwar matarsa, ganin komai yake yi tamkar shirin wasa, tamkar shirin film aka haɗa don kawai a girgiza shi, don kawai a gwada irin ƙarfin soyayyar da yake yiwa Fulaninsa.

"Muhammad ka yi mata adu'a, kuyi sallama Muhammad kaji".

tun daren jiya, tun lokacin da labarin mutuwar matarsa ta riske shi, da zaman kwanan da yay agaban gawar, zuwa wayewar garin yau da ya ƙara tabbatar da ya rasata, sai a yanzu da ake cewa yay mata adu'a suyi sallama ya ji idonsa ya cika, saɓanin jiya da yake a bushe, har yana jin kamar ba zai taɓa zubar da ruwa ba, amma a yanzu tarin ruwan da ya cika a idonsa ba ya jin zai iya dakatar da su, saboda haka sai kawai ya kifa kansa akan ƙirjin gawar, hawayen ya ƙwace, kukan ya kubce, ya shiga rero kuka tamkar ƙaramin yaro, yana kukan jikinsa na girgizawa kamar yanda zuciyarsa ke yi.

adu'ar da ake ta cewa yayi ya kasa yi, sai da ƙyar aka iya raba shi da jikin gawar, aka miƙar da shi aka riƙe shi, yana kallo aka ɗauki gawar aka fita da ita, da sauri ya bi bayan su, ya tarar da su suna saka gawar a cikin makara.
abinda ya saka shi ƙara rikicewa, sai ya tsinci kansa da yiwa Allah godiya da ƴaƴansa ba su tsinci ganin wannan lokacin ba.

ƙarfe sha ɗaya dai-dai aka yiwa Fillo sallah, a cikin ƙaton compound ɗin gidan Alƙali Dikko, bayan gama sallar gawar aka ɗauƙi makarar aka fita da ita daga gidan, Turaki na sahun gaba, ƙafafunsa ke jansa ba shi ne yake tafiyar da su ba, yayin da hannunsa guda ɗaya yake cikin na Bello ya riƙe shi da kyau, saboda gudun faɗuwarsa.
Chapter 171 · 0% Book details