Sashe 26
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ƙarfe sha biyu da minti goma sha biyar na dare a lokacin, motar Turaki akan hanyar da bai san ya akai ya biyo cikinta ba. hanyar tayi duhu dulum sai haushin karnuka dake tashi. gefe da gefen hanyar shukoki ne na masara da shinkafa da alama dai gonaki ne a wajen.
ya rasa me yake damunsa gaba É—aya, shi dai yana zaune yaji kawai yana so ya fito yasha iskar gari, kuma da har ya wuce Lambu sai ya koma ya É—auki key É—in motarsa ya fito.
da farko gidan Mai Martaba yaso ya nufa, sai kuma zuciyarsa ta sauya masa ra'ayi, ya dinga bin titina yana sauka daga wannan zuwa wannan. tuƙin kawai ba dan ya san inda hankalinsa da tunaninsa yake ba, shine har ya shigo wannan layin da bai san ina motar ta kawosa ba, dan ba shi ya kawo kansa ba..
wuri ya samu yayi parking ya fito ya jingina da jikin motar yana fuskantar inda shukar shinkafar take, idonsa akan Shukar yake amma ba ita yake kallo ba, ba kuma tunani yake yi akanta ba, wucewar minti goma ya kalli agogon wayarsa yaga ƙarfe sha biyu da rabi a lokacin.
sai kawai ya buÉ—e motar ya koma ciki, ya kuma nausawa cikin gonar ba tare da tsoron daren ba.
driving É—in yake with high speed kamar me shirin barin gari, ba ganin gabansa yake da kyau ba a lokacin duk da fitilar motar daya kunna. yasa hannu a rigar kujera zai É—auki glasses É—insa sai ya tuna É—azu da zai karanta jarida yasa Nihal ta É—auko masa.
yay guntun tsaki kawai, jin komai yake babu daÉ—i, cikin kansa kamar babu komai, kamar ma ba'a cikin duniyar yake ba.
da hakan yasa hannu ya daki stearing da ƙarfi, horn ya kama nan wani Kare dake gefen wata bishiya ya tashi da gudu ya tsaya a tsakiyar hanya, ganin hakan yasa Turaki ƙara danna horn da ƙarfi, nan karen ya bar wajen da gudu. tsaki kawai yake jerawa, ya jera yafi ƙarfin ƙirgen yatsu, bai san meke damunsa ba, bai san meke masa daɗi ba, bai san me zaiyi ya samu salama ba.
kawai sai ya tsinci idonsa da haska masa wasu shafuka acikin al-qur'ani, da haka kuma zuciyarsa ta fara karanta abunda ƙwayar idonsa ke haska masa.
sannu a hankali yaji yana samun relief, nan ya kai hannu ya kunna alqur'ani, ƙira'ar Shuraim ta fara tashi acikin motar.
ba tare da ya sani ba, haka kuma ba tare daya ankare ba yaji ya daki abu. gabansa ya faɗi, bakinsa ya furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, duhun idanunsa ya washe lokaci ɗaya, yayi mugun taka burki babu shiri ganin yana neman bi ta kan abinda ya buge wanda bai san mene ba a lokacin, ƙarar taka burgin ya bada wani ƙara ƙuuuu, tunaninsa ɗaya ne wata dabbar ya kaɗe.
sai dai me zai faru?, a lokacin daya fito daga motar cikin hanzari sai kawai yaga mutum yashe a ƙasa cikin jini, macece, amma kamar ba mutum ba haka zuciyarsa ta faɗa masa.
saboda haka kamin ya kai ga tsugunawa gaban wadda yake da tabbacin ta riga ta zama gawa sai daya kalli ko'ina da ina, yaga babu kowa kuma babu alamun kowa, sannan ya tsuguna yana mai jin fargabar kai hannu ya taɓata.
bakinsa ɗauke da tarin adu'oi yasa hannu ya juyo da ita daga kifen da take, jini duk ya wanke mata fuskarta, babu ta yanda za'a ganeta. ya janye gashin kanta daya baje akan fuskar. ya ƙara furta innalillahi sannan ya kama hannunta wanda yake a damƙe kamar ta riƙe wani abu, ya taɓa yaji artery ɗin wurin na motsi.
ya sauke ajiyar zuciya, ji yayi kamar yayi hamdala a lokacin.
kansa ya ƙulle da tunanin ma me zai yi, kuma tana ina zai fara, kuma me ya kamata yayi.
yana riƙe da hannun tsawon wucewar wasu daƙiƙu sannan ya miƙe da sassarfa ya buɗe bayan motarsa, ya kunna fitilar motar sannan ya dawo ya ɗauketa ya sakata a motar, yarinya ce ba wai babba ba, hannunta guda ɗaya ya sauka akan kafaɗarsa, ya ɗauke yana kallon hannun nata da yake a damƙe.
ƙwayar idonsa ya tsaya cak a kanta, wacece?, me ta fito yi a irin wannan lokacin?, daga ina ta ke?. zuciyarsa ta ƙara ɗarsa masa anya kuwa mutum ce?, sai yayi saurin ɗauke idonsa daga kanta ya sauke ajiyar zuciya. ya rufe bayan ya dawo mazauninsa yana ƙara volume na karatun daya kunna.
yana kunna motar ya ɗauki wayarsa ya kira lambar Hajiya Madina, dai-dai lokacin daya hau kan titi ta ɗaga wayar. muryarta tattare da tarin bacci ta kira sunansa tana mai mamakin kiran nasa a irin wannan lokacin ƙarfe ɗaya na dare.
daga ɓangaren da take ta miƙe zaune akan gadonta cikin faɗuwar gaba ta kunna bedside lamp. "Hammansu". ta kira sunansa cikin wani amon sauti da bata san tana da shi ba.
a wannan lokacin Turaki kamar zai yi kuka, ya juya baya ya kalli yarinyar sannan muryarsa dake É—auke da tashin hankali yace,"Maama na kashe rai".
"what?, ban ji da kyau ba Hammansu". tayi maganar a É—age tana durowa daga saman gado babu shiri.
"Maama ban san ya akai ta shigo gabana ba, its like kamar jefota akai". a rikice yay maganar kamar yanda yake a rikice.
Hajiya Madina da ta faÉ—a toilet tana wanke fuska don ta wartsake daga mafarkin da take tunanin tayi tace,"kana ina Hammansu?".
yace,"ban san inda nake ba Maama, ina dai kan wani titi. har yanzu banga wani wuri dana sa ni ba, banga asibiti ba ko ɗaya Maama...kamar da sauran ranta ina tsoron karta ƙarasa mutuwa".
muryar Hajiya Madina a É—age tace,"wai wacece ne? kuma me kake so ka faÉ—a min?".
ya ƙara juyawa ya kalli bayansa sannan yace,"accident nayi Maama, kuma ban san wa na kaɗe ba".
tace,"na shiga ukuna, to da yaushe ka fita daga gida ban sa ni ba?, daka fita ma ina zaka je me Babban suna?".
ya kulle idonsa sannan yace,"Maama duk ba wannan ba, bana so ta mutu ta sanadina, bana cikin hankalina wallahi ban san lokacin dana kaÉ—eta ba, na kasa fita daga inda nake, kamar ma na bar garin gombe gaba É—aya".
Hajiya Madina ta zube a gefen gadon da ta ke ta fashe da kuka. wucewar daƙiƙa biyu ta sauke numfashi tace,"ka nemi wuri kayi parking, ka kunna datarka...zamu bi location ɗinka yanzun nan...kai ta biya innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, zaka samu mafita kamin ƙarasowarmu insha'Allahu, take care kaji, kama kashe motarka kawai".
yayi shiru bai ce komai ba. ta katse shirun da cewar,"Hammansu kana jina?". idanuwansa a rufe yace,"Maama idan ta mutu fa?". yay maganar da tsananin rauni. tace,"i beg you stop negative thinking, ba zata mutu ba da yardar Allah, gamu nan tahowawa".
tana faɗar hakan ta kashe wayar, tabi layin Khalil da kira, kira na farko dana biyu duk bai ɗaga ba sai ana uku, cikin bacci ya kira sunanta. tunma bai ƙarasa faɗar sunan ba tace,"Khalil ta shi a barcin nan muna cikin tashin hankali, tayar da mota gani nan".
Allah ya taimaka Khalil baida nauyin bacci, yana jin haka ko tambayar ba'asi bai jira yi ba ya diro ya zira jallabiyarsa ya fita. Hajiya Madina ma zani ta É—aura akan kayan baccinta sannan ta zura hijabi ta fito da warikan takalma, sai salati ta ke yi.
*Please Vote, Comment and Share*
[8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
*©ï¸Halima h.z*
*14*
Fillo tasa hannu ta goge hawayen dake fuskarta, ta ɗaga kai tana bin wayar dake ringing da ido, tunani takeyi akan taje ta ɗaga ko karta ɗaga, ɗaya ɓari na zuciyarta ya rinjayeta akan taje ta ɗaga ɗin.
saboda haka ta yunƙura ta miƙe tsaye jikinta a mace, bata ma ko iya ɗaga ƙafa sai janta take yi har ta ƙarasa inda wayar take manne a bango.
ta kai hannu ta ɗaga wayar, daga ɓangaren Hajiya Madina ta kaɓe abinda ke jikin zaninta sannan tace,"Fillo". jin muryarta acikin wayar yasa Fillo saurin saita natsuwarta, sai da ta gyara muryarta sosai sannan ta amsa kiran. "Na'am Maama".
Hajiya Madina tamkar tana kallonta ne a lokacin, don tana jin muryartata tunaninta ya bata kamar da wani abu, apple ne a hannunta a lokacin, amma cikin wani irin zullumi ta ajiye tana tambayar Fillo,"kuka kike yi?".
Fillo ta haɗiye wani abu sannan ta ƙara gyara muryarta tukunna tace,"a'a Maama".
Hajiya Madina tace,"but how comes naji muryarki some how?, wani abu ya faru ne?, ko ba kya jin daÉ—i?". ta jero tambayoyin ga Fillo muryarta na fita da sautin dake nuna damuwa da kulawa.
kamar tana gabanta ta girgiza kanta tace,"a'a Maama lafiya lau". ta faÉ—a cike da mamakin yanda akai Hajiya Madinan ta gane kuka acikin sound É—inta farat É—aya, dan har sai da ta kai ga ta kalli wayar ko dai tana kallonta ne.
Hajiya Madina ta ƙara cewa,"tiles ɗin nan yana da tsantsi sosai i forgot to tell you that, Allah yasa ba faɗuwa kika yi ba wajen yin mopping?". duk da cewar bata fahimci ɗan guntun turancin ba amma ƙarashen maganar ya fahimyar da ita dukkan maganar.
tace,"a'a Maama nayi takatsantsan, har na gama ban zame ba". Hajiya Madina tace,"to yayi kyau, kin gama aikin?".
tace,"ehh yanzu nake shirin rufe ɗakin". Hajiya Madina tace,"me amsar saƙon da na baki yazo yana ta jiranki, kije ki kai masa sannan ki ƙarasa aikin...muma mun kusa dawowa muna jira Boɗejo ta shirya ne tare zamu taho". tace,"tom Maama Allah ya dawo daku lafiya".
da haka wayar tasu ta katse, Fillo tabi wayar da kallo tana jin son Hajiya Madina har cikin ranta, a iya É—an zaman da tai ta gama karantar matar, zata rantse duk wanda ya faÉ—i aibun Hajiya Madina to É—an hassadarta ne.
macece da bata da ɗagawa ko kaɗan, bata tunƙaho da arziƙinsu, bata wulaƙanta talaka, bata da ƙasƙanci, kowa nata ne, kowa ganinsa ta ke ɗaya suke, kowa sonsa ta ke yi, mutumta duk wanda yake tare da ita takeyi babu tozarci.