Sashe 8
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idan yazo zai bawa kowa sadaqa zai ba shi kuɗi dubu uku, sai ma'aikatan gidan maza su bika da kwanon shinkafa, taliya guda biyu da kwalaban farin mai da manja. Judge Dikko ba ya taɓa barin wajen har sai ya tabbatar da kowa ya samu, duk kuwa da uban yawan da mutanen ke da, ba ya gajiyawa kuma ba ya ƙosawa, hakana duk nisan tafiyar da yayi duk irin muhimmancinta zai katse kome yake yi ya dawo alhamis dan kawai waɗannan mutanen da Allah ya ba shi ikon taimaka musu.
Ya faɗa saveral times gani yake idan har ba shi ne da kansa ba to ba za'a riƙe amana kamar yanda ya bayar ba, saudiya kawai yake tafiya ya iya haƙura, shima kuma sai ya kira Muhammad Turaki a duk inda yake ya dawo ya tsaya akan ragamar abun, dan shi kaɗai yake ganin zai iya kwatankwacin abinda shi zai yi da kansa.
Kuma a wannan juma'ar ne ma'aikatan gidan basa samun hutu ko kaÉ—an, dan tun daga safe har dare su na rabon abincin sadaqa.
Ƙarfe goma da rabi Baffa ya dawo cikin gidan daga rabon sadaqar da ya fita, Khalil da ke ƙoƙarin shiga motarsa zai fita ya hange shi, hakan yasa ya rufe motar ya taho da sauri.
Ya rissina a gaban mahaifin nasa cike da girmamawa yana faɗin,"Barka da dawowa Baffa". tare da miƙa hannu don karɓar jakar hannunsa, wadda yake zuba kuɗin sadaqa ya fita da ita.
Baffan ya dube shi yace,"ba fita zaka yi ba?".
"fitar ba wata mai muhimmanci bace". Ya faɗa yana ƙara miƙa hannu don amsar jakar. Baffan ya miƙa masa, shi kuma yana masa sannu tare da adu'ar Allah ya bada lada a irin ayyukan alkhairan da yake yi.
Tare suka jera su na tafiya, su na entrance na shiga parlo Baffa yace da Khalil.
"Muhammadu ya dawo ne?".
"a'a bai dawo ba".
"amma É—azu sai naga motarsa".
"ai dama ba da ita ya tafi ba, da GLK ya tafi".
Baffa bai ce komai ba ya shiga katafaren parlonsa bayan Khalil ya buɗe masa ƙofa. Hajiya Madina coming down from stairs take welcoming nasa. Khalil ya miƙa mata jakar hannunsa tace ya wuce ya kai bedroom ɗin Baffa.
Tana gyara dining area ta ke cewa Baffa, "yau ka dawo da wuri, hala ba'a taru ba yanda aka saba".
"ba haka bane, jikina nake jinsa babu daÉ—i".
"subhanallahi". Ta faÉ—a tana saurin barin abinda ta ke yi ta dawo kusa da shi ta zauna.
Tana taɓa jikinsa looking worried tace,"i hope ba ciwonka ne zai tashi ba".
Tai maganar tana ɓalle maɓallin gaban rigarsa. Sannan ta miƙe tana cewa,"let me reduce the AC".
Kayan breakfast ta ɗauko ta dawo da shi gabansa ta aje saman wani medium glass table. His favorite dish kunun gyaɗa da awaran ƙwai, da kanta ta ke feeding nasa tana jera masa sannu, bayan ya gama ta ba shi drugs sannan ta buƙaci da ya tashi ya koma bedroom yace a'a ta barshi nan.
Ƙasa ya sauko ya zauna kan tattausan carpet ɗin da ke malale, haɗuwar parlon da tsaruwarsa kace turakar sarki, ya kishingiɗa da tum tum ɗin da ke gefensa, in a state of misery yace.
"ban san me ya riƙe yaron nan ba".
Yay maganar yana sosa gashin gemunsa.
Hajiya Madina ta sauke nunfashi kamin tace,"yace yana hanya ai...ka kwantar da hankalinka please ba wani abun damuwa ba ne. Duk yanda akai aiki ne yayi masa yawa".
"to Allah yasa". Ya faɗa fuskarsa na nuni da damuwar da ke ransa, na rashin dawowar Turaki gida tun a ranar da ya dawo ya kirasa ya sanar masa ya dawo gida yana da buƙatar ganinsa.
Suka ci gaba da magana akan rayuwa, a haka har ya fara samun relief na ciwon kan da ya fara gallabansa É—azu.
yay nisa yace,"yaran nan ba su tashi ba ne?".
Hajiya Madina tace,"what is the time now?". Ta faɗa tana duban agogo tukunna ta ƙara cewa,"masu baccin dama Zaytuna da Nihal ne, Samha ta tashi yanzu...itama tana tunanin baka shigo ba ne thats why baka ganta ba, tunda time ɗin dawowanka bai yi ba".
Yay murmushin manyace yace,"da asuba da naje gaida BoÉ—ejo ina jinta ita da Zaytuna".
Ya ƙarasa maganar yana ƴar ƙaramar dariya, yayinda Hajiya Madinan ke taya shi dan lamari indai aka ambaci Boɗejo a ciki to za'a dara.
fararan haƙoransa a waje yake faɗa mata cewar,"da asubar nan fa ko lazimi bata gama ba take mitan Allah kaimu safiya ta bar gidan ita ba zata iya da gorin da ake yi mata ba".
Hajiya Madina ma tayi dariya sosai, lokacin kuma hankalinsu ya karkata kan yaransu da ke shigowa parlon bakunansu É—auke da sallama.
Shigar jikinsu kaɗai zata shaida maka ƴaƴan wani ƙusan ne, ballanta azo ga kallon fatar jiki da zata tabbatar maka da hutu, jin daɗi da gata ya zauna.
Baffa ne ke amsa sallamar tasu yana miƙewa zaune daga kishingiɗar da yay ajikin tumtum.
Samha, Zaytuna da Nihal suka zube a gabansa, cike da tsantsar girmama da ladabi suka gaishe shi cikin taushin murya. ba sai an faÉ—a ba, irin zaman ma da su kai a gabansa shi zai baka tabbacin an gina tarbiyarsu bisa bigere na addini, duk da Judge Dikko É—an boko ne hakan bai sa yay watsi da koyarwar addini da al'ada ta fulani ba ya É—auki É—abi'ar bature ya gina iyalinsa akai.
Idanuwansa na bin kowacce da kallon so da ƙauna da ke tsakanin uba da ɗansa yake amsa musu cikin farin ciki da annashuwa. Adu'a yake jero musu iya adu'a su kuma su na amsawa da amin, Zaytuna wadda ke da idon hawaye tuni idanuwanta suka ciko da ƙwalla, haka ma muryarta tayi rauni wajen amsa albarkar da mahaifinsu ke saka musu.
Da yake shi mutum ne me barkwanci a cikin iyalinsa ya kalla Nihal cike da zolaya yace,"Auta ya naga kinyi fari har kinfi Boɗejo, saura ƙiris ki koma Zabiya".
Babu shiri Nihal tayi dariyar da duka haƙoranta suka bayyana a waje tana rufe bakinta da hannu.
Baffa ya ƙara cewa,"ki sammawa Mamanki abinda kike shafawa ko ta ƙara yin kyau ta koma ƴan mata". Yay maganar cike da barkwanci.
bata bar dariya ba tace,"Baffa ni babu abin da nake shafawa tsabagen hutu ne kawai".
Yay murmushi, Hajiya Madina tace,"yo Allah na tuba ni wa zai ganni ma yace na ajiye maka waÉ—annan yaran...ni jikina ma ai yafi na wata budurwar, man bature kuwa ai sai dai mu barwa wasu danmu da namu farin Allah ya halitto mu".
a cikin amon yanda tayi maganar zaka tsinci tsagoron kishi duk da cewar maganar anyita ne for raha becouse of ayi dariya.
"Zaytuna naga hannun naki". Hajiya Madina tace tana duban inda Zaytuna ke zaune, gefen mahaifinta tamkar zata shige cikinsa. ta taso ta dawo kusa da ita tana nuna ma ta hannun.
"ya fara sauƙi ai...da zafi har yanzu?".
"ehh Maama yana zafi".
"sannu, did you take your drugs?".
Tace,"ehhh".
"To Allah ya sauƙe".
Baffa yace,"to wai ba za'a nemo wata ƴar aikin bane?, kuma ke har kina shirmen me da kika bari ruwan zafi ya taɓa ki".
Hajiya Madina tace,"tsautsayi dai da ba ya wuce ranarsa, ita kasan kamar inji ba son zama take yi ba tai aiki ba ko masu aikin su na nan...amma idan yau Jamilar bata dawo ba sai nayi magana da Yami ta samo wata, ai dama sati É—aya Jamilar tace zata yi".
Sahma tace,"ai Maama a nemi wata kawai, dan bana tunanin Jamila zata dawo, naji Sha'awanatu na cewa kamar aurenta za'ai".
"ai da hakanne zata faÉ—a, ko ta kira waya ta sanar".
Baffa na riƙe da hannun Zaytuna yake cewa da ita,"please Babyn Baffa a daina shiga kitchen kinji, bana so wani abu ya dinga taɓa min lafiyarku".
Sameer da suka shigo shi da Khalil yace,"to wai a yanke hannun mana".
Zaytun tayi masa wani kallo tace,"sai kazo ka yanke ai".
yace,"kar ki bari a barmu daga ni sai ke a gidan nan kiga aiki da cikawa".
Baffa with full of smile on his face yace,"ƙyale shi haushi yake ji hannunki yafi na budurwarsa kyau, kuma nan gani nan bari...". tun bai ƙarasa ba Samha da Nihal da ita Zaytunan suka ƙarashe faɗin,"ɗumamen mayya ba". su kai maganar su na dariya.
Sun ɗau tsawon lokaci su na hira kafin yaran su tashi su tafi, su na fita Baffa ya kamo hannun matarsa yana cewa,"haba ƴar shawalwalata ɓata fuskan kuma na menene?".
Bai jira me zata ce ba yaci gaba,"kema dai ai kin san waɗannan idanun tsufan nawa kallon jaririya ma suke miki ba budurwa ba, me za'ai da wata ƴan mata ina da ke ƴar shila, kin fa riga kin rufe ƙofar tuntuni, to mene kuma wani batu zai sa ki ɓata fuska ummm Babyn Baby, please saki ran karki ɓatan kwalliyan da akayi mani nake kallo ina jin daɗi".
ya ƙarasa maganar yana shafo fuskarta ita kuma tana ƙoƙarin danne murmushin jin daɗin da ke neman suɓuce mata, yanda yake yi mata kamar ƙaramar wata yarinya, har sai da yayi nasarar sakata yin murmushin da ya haɗe da dariya.
"yauwa ko ke fa gimbiyata, sarauniya a fadar zuciyata, ina sonki fa, ina sonki da yawa wallahi...kai Allah dai ya ƙara miki kyau".
Ya faÉ—a yana kamo dogon hancinta.
sai kuma ya kai bakinsa saitin kunnenta yana cewa,"wai yaushe zamu ƙara tafiya honey moon ne?".
Hajiya Madina tace,"da gaske fa nayi zaton ko ka ƙyalla ka gano wata ƴar baturiyar ne".
Yace,"waa nii rufani ki saya, at this age ace idona bai daina gane gane ba, ke É—aya kin ishe ni. Soyayyarmu bata tsufa ba balle ta mutu".
Yana nuna idanuwansa yace,"ai wannan idanuwan babu abunda suke gani sai ke, ke É—aya tallin tal Aina'u ta Habibullahi".
"to yanzu tashi mu koma É—aki ka samu ka rama baccin asuba da baka koma ba...nima na samu na tafi guest parlo kasan yau ranar amsar kukan mata ne".
Suka miƙe tsaye tare yana faɗin,"ai nayi zaton idan munje ɗakin soyayya zamu sha". tayi murmushi ta kama hannunsa.
"to kai dai muje mana Your Excellency". Da haka suka haura stairs.
****
"ni kuwa na godewa Allah, wai ko Allah Fillo ba za ki daina wannan kukan alluran haka ba".