Sashe 42
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ita da Maijidda suka fita, hannayensu saƙale dana juna, hijab ɗin jikinsu iri ɗaya komai da komai. yana cikin motarsa fara BMW, sai da suka isa wurin sannan ya fito. jikinsa shadda ce ƴar ubanta dark blue, ta amshi farar fatarsa, tunda ya fito yake ƙarewa girman gidan kallo tare da jinjina kai, yasan wannan gidan ko filoti goma sha albarka, har ƙasa suka tsuguna suka gaishe shi.
hannayensa harɗe a ƙirjinsa yace,"Hassana da Hussaina". su kai murmushi kawai basu ce komai ba. Fillo ta lura yana da magana, hakan yasa tace,"Kaka tana gaisheka, kuma muna da aiki a cikin gida".
yace,"ina amsawa, nima yanzu zan tafi ai ba sai kin kore ni ba, saboda nan da minti 20 jirginmu zai tashi. kawai ji nayi ina so nazo naga mara lafiya ne".
Fillo tace,"ai naji sauƙi". yace,"ehh naga alama ai, Allah ya daɗa lafiya". ta amsa da amin, sai kuma duk suka yi shiru.
Yusuf yace,"ranar da zaku bar asibiti baki bari na baki amsar tambayarki ba kika gudu". ta ɗago ta kalle shi tace,"amsar me? aini ban tambayeka komai ba". yace,"ehh bakinki bai faɗa ba amma ƙwayar idonki ta faɗa...kina jin kamar kin taɓa sanin me wannan fuskar ƴan gayun ko". ya faɗa dan raha yana shafa fuskar tasa. bata ce komai yace,"ko ba haka bane?". tace,"nayi mamaki daka fahimta".
sai yay murmushi yace,"zaki iya tuna watarana?, lokacin baki kai haka girma ba, time ɗin gidaje uku ne kawai a estate ɗin nan, kin fito yawo kika ji ciwo kika zauna kan yashi kina kuka, wani bawan Allah me tausayi yazo ya sameki yasa ki kai shiru da ƙyar, yace ki nuna masa gidanku ya kai ki kika ƙi kika ce Kakar ki zata dukeki saboda bata san kin fito ba, yace to ki tsaya ya ɗauƙo first aid a mota ya wanke miki ciwon kamin ya dawo kika ɓuya a bayan bulo, kuma ya durƙusa yana haɗa hydrogen kika felle da siraran ƙafafunki kika bar wajen, kina gudu kina waige saboda kar ya kamoki".
Maijidda ta ƙyalƙyale da dariya, Fillo kuma kunya ta kamata tasa hannu ta rufe fuska tana murmushi, Yusuf ma murmushin yake.
tace,"kuma baka manta kamannina ba har wannan lokacin?". yace,"to yaushe akai abin?, shekara ɗaya da rabi ne fa kawai. kuma ai ba wani girma kika ƙara ba da za'a kasa ganeki, kin dai ɗan ƙara wayo ne kawai, sai abinda ba'a rasa ba, amma ai nasan ko yanzu kika ji ciwo zaki tirje a tsakiyar layin nan ki ta kuka abinki ke ɗaya har sai kinga me allura zaki gudu".
murmushi bai bar fuskar Fillo ba har lokacin, taji hirar na tafiya da ɓacin ran da Amir ya haifar mata. Maijidda tace,"gaskiya baka da mantuwa". yace,"ai duk randa zan wuce ta wurin nan ai sai na tuna, kin ga fa haka ta riƙe ƙafa tana kallon ciwon tana ta tsala kuka kyace yanke ƙafar akai, kuma abin takaici ciwon fa ɗan ƙaɗanne ba me yawa ba". ya faɗa yana kwaikwayon yanda takeyi a lokacin.
ya basu dariya sosai, yana da fara'a da barkwanci, Maijidda tace,"wallahi na tuna lokacin, ai in faÉ—a maka ciwon nan anfi wata guda ana jinyarsa, haka take ko ya taga jini a jikinta sai ta hargitse".
yace,"kice da idonta biyu aka kaita asibiti ran na da mun shiga uku, ƙila duk patients namu sai sunce a sallamesu dan babu me iyawa da kukanta".
Fillo ta harari Maijidda tace,"sharrin Hassana ne fa".
Yusuf yace,"zan yarda ai, kece fa".
ya kalli agogo yace,"kun ce zaku yi aiki nima kuma zan tafi, bara na ƙyaleku kar na cika ku da surutu, ina da yawan hira da ƙannena, ina son sisters mata musamman kamarku, amma ku ɗin sai naji kuna burgeni sosai".
suka ce,"mun gode". yace,"nima na gode, amma ya kamata dai aje ayiwa Kakata godiya na dubiyar dana zo nayi".
Maijidda tace,"tom shikenan kayi mana kwatance, sai mu zo wataran". yace,"yaushe kenan". tace,"ehh tou sai mun sami damar fita idan kamar Yami ta aikemu gidan sarki".
yace,"to ai kuma ƙila lokacin bana nan". Fillo ta sami kanta da tambayarsa,"ina zaka je?".
yace,"ai a kano nake da zama, nan nake zaune ni da matata, nan garin kuma gidanmu ne da Inna Wuro ta samu tayi bake-bake acikinsa ta hanamu sakat, ta mayar da gidan kamar nata...saboda haka idan zaku zo ku tabbatar kun fesa turare kamar zai yi magana, kun kuma kai mata ƙunshin leda ko da babu komai aciki in ba haka ba kun shigesu da sababi".
Maijidda tace,"Kakarku ce Inna Wuron?". yace,"ita ta haifi Dad namu amma ta zamar mana ciwon kai, kowa ya gaji da ita...nima dan dai ita ta raine ni banda haka tuni na É—inke bakin maganarta".
sukai dariya su duka, Fillo ta katse hirar da cewa,"tom bari mu tafi, mun gode sosai Allah ya kai ka gida lafiya".
suka faÉ—a a tare suna niyyar wucewa.
sai ya tsayar da su. "tsaya ki karɓi alluranki Malama, ki kaiwa ɗaya Kakar taku da kuke cewa Yami wadda kike ɗan tsoro ta dinga tsira miki".
Fillo ta ɓata fuska tana kama hannun Maijidda dan su tafi.
sai gani sukai ya fito da fararen ledoji guda biyu manya, Fillo na ganinsu ta gane irin ledar kantin da Zaytuna ke yin siyayya ce. ya miƙawa Maijidda yace,"ga shi duka na na mara lafiya ne amma kema idan kina so ana iya tsira miki ko guda ɗaya ce, tunda naga da amana a tsakaninku".
Maijidda ta karɓi ledojin tana masa godiya, shi kuma ya zagaya ɓangaren driver seat ya buɗe motar, idonsa na kan fuskar Fillo da ta cukule, sai haɗe gira takeyi kamar zata yi kuka, tana ta harar Maijidda.
ya shiga motar yana ta smiling, ya zuge glass na ɗayan kujeran me zaman banza ya leƙa da salon tsokana yace,"Auta ya dai? a saki ran please kar Kaka tace na taɓa mata Hussaina, kuma dan Allah banda kukan allura kinji, kinga kin girma".
Fillo da ta gama kumbura tai tafiyarta ta bar Maijidda a baya, yana kallon Fillo har ta shige cikin gida, haka kawai yake jin yarinyar ta tsaya masa a rai. ya kuma kasa gane dalilin hakan, tun randa suka bar asibitin yaji kamar zuciyarsa ta shaƙu da yarinyar, kamar yana ya dinga ganinta kullum, kamar dai yana so ya fahimci wani abun amma ya gagara.
sai daya tabbatar da shigarsu gidan sannan ya bar layin yana ji a ransa yana so ya ƙara kasancewa da yarinyar.
*Please Vote, Comment, and Share.*
[8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
*21*
Maijidda ce ta wuce da ledar kayan, Fillo na faɗa mata karta soma ta ambaci sunanta idan Kaka ta nemi ba'asin karɓan kayan Dr Yusuf. ai tasan an hanasu shine yana miƙowa ta amshe.
Maijidda na ɗan jin tsoro tace,"to ni ai nai zaton da gaske alluran ne shiyasa na karɓa".
Fillo na dariya tace,"kinga ke dai kije kisha faÉ—anki ke É—aya, ni na tafi aiki. da nasha faÉ—an Kaka gwara na sha na Hajiya Madina".
tana faɗa ta ƙara saurin tafiyarta tana taiwa Maijidda dariya, ita kuma nata jin shakkar shiga da kayan, ji take kamar ta koma taga idan Dr Yusuf bai tafi ba ta basa kayansa, to amma tasan zuwa yanzu ya tafi kam, dan ko ɓata lokacin da suka yi a wurin duba kayan tasan yaje inda zai je.
tun shigowarsu gate Fillo ta dage sai sun wuce inda ake zubar da bolar gidan sun zubar da maganun, wanda zatonsu abinda ya faÉ—a hakan yake. kuma sai da suka je zasu zubar ne suka tsaya suna kallon uban kayan da mamaki.
leda ɗaya tulin kayan ƙwalama ne kamar hauka, madara, snacks da choculates da lemukan kwali, tarkace dai iri-iri. sai ɗayan ledan kuma kayan makeup ne aciki, shower gel manyan roba guda biyu wanda mutum sai yafi wata yana wanka da roba, sai lotions da su powder, duka dai dangin kayan kwalliya, kuma da gani kuɗi ne ba na wasa ba aka kashe wajen sayayyar.
Fillo ta shiga parlon da sallama tana tafiya a hankali, kanta a ƙasa sai jan yatsun hannunta take yi, Hajiya Madina na zaune akan kujera, ƙafafunta duka biyu akan tum-tum, Sameer na zaune a gaban ƙafafun nata ya tankwashe ƙafa yana yanke mata farcen ƙafarta. sai Nihal dake ɗaya kujeran a zaune tana duba wata handout, daga dining area kuma Zaytuna ce a zaune tana danna waya.
Fillo ta ƙarasa ta durƙusa a gefen kujera tana gaida Hajiya Madina. Hajiya Madina ta ɗauke idonta daga karanta story book ɗin da take yi ta kalli Fillo tana amsa gaisuwar tata.
"Halimatu anji sauƙi kenan". tace,"ehh Maama na wartsake gaba ɗaya". "to masha'Allahu, Allah ƙara miki lafiya. kina da ƙwarin dai da zaki iya aiki ko?". Fillo tace,"ehh Maama".
Hajiya Madina ta gyaÉ—a kanta, tai shiru for some seconds sannan tace. "to jiya an kawo miki Æ´ar'uwa da zaku ke aikin tare, ta kammala komai tun É—azu, yanzu sai ki tashi kije lesson teacher É—in ku yazo, idan kuka kammala ke sai kiyi aikin rana".
wani daɗi ya mamaye Fillo, ko babu komai burinta na yin karatun boko zai cika, abunda mahaifinsu ya kasa yi musu yau wasu bayin Allah zasu mata shi. tunaninta ya tafi can wani lokaci baya, tana wannan tunanin taji Hajiya Madina na ƙara cewa,"dan Allah ku mayar da hankali kunji ko, abunda za'a muku a makaranta shi zai muku, kuɗi masu yawa aka biyasa, akwai percentage ɗin da za'a ke cirewa a cikin kuɗin aikinku, so idan kun mayar da hankali akan karatun kanku kuka taimaka, idan kuma kunƙi kunwa kanku asara babba".
Fillo tace,"insha'Allahu Mama zamu mayar da hankali, insha'Allah ba zan baku kunya ba zanyi abinda kuke so nayi". Hajiya Madina ta jinjina kanta. a lokacin sabuwar maid É—in da aka kawo ta iso wurin ta tsuguna kusa da inda Fillo take. tace,"Hajiya gani".
Maama tace,"yauwa ga ƴar'uwar aikin naki nan. ki bata nata reading materials ɗin da Zaytuna ta baki ɗazu, sai kuyi maza ku wuce me karatun na can na jiranku, awa biyu zaku dinƙa yi, da zarar kun kammala ku yo cikin gida, a kama kai bana son shashashancin banza if not zan sallami yarinya".
duka su biyun suka amsa da,"to". sannan Fillo tace,"aina zamu sami Malamin?".