Sashe 77
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sai dai tana ajiye wayar yaji tana faɗawa mahaifinsa halin da ake ciki, dan haka nan da nan brothers ɗinsa suka watse akayi gida dan fara karatu da adu'oi. faɗar dai tsananin tashin hankalin da Amir ke ciki ba zai misaltu ba, don lokaci ɗaya har ya faɗa kamar wanda ya jima yana jinya, Dr ma har yana cewa in ba'a kiyaye an nema masa abinda yake nema ba zuciyarsa zata iya taɓuwa.
a daren wannan ranar dai Kamar yadda Fillo bata iya runtsawa ba, haka ma Hajiya Madina, Kaka, Maijidda da kuma Amir, dan Amir saura kaÉ—an ya rage ma ya bar asibiti a daren ya fita nemanta.
Tashin hankali dai duk bai bar kowa ya runtsa ba, yaran Hajiya Madina kansu sun kasa bacci saboda halin da mahaifiyar su ke ciki, shi kansa Baffa har sannan yana kan matarsa yana bata baki.
at the end dai Baffa yaga zaman kukan duk ba shi bane, dan haka yace kowa yay sallah ai adua, a haka suka raya wannan daren daga masu sallah sai masu karatun qur'ani sai masu tasbihi haka har asuba da tayi.
bayan sunyi sallar asuba Anty Zulfa ƙanwar Hajiya Madina da tazo ita ta zauna tana jero Adduo'i kowa na amsawa, cikin adu'ar suna roƙon Allah ya kare Fillo a duk inda take, ya kuma dawo da ita garesu cikin amincinsa, da ameen suka amsa har ta idar suka shafa, suka shafa aduar a daidai sanda Baffa ya turo ƙofa ya shigo.
ya zauna akan kujera idon kowa akansa, ya numfasa sannan ya shiga yi musu bayanin abinda police suka ce game da report É—in da aka shigar.
yace,"ku kwantar da hankalinku dan Allah tunda dai har Police sun riga sun shiga maganar, kuma yanzu zasu ƙara bazama gurin nemanta".
ya kalli Kaka yace,"na basu hotonta da shi saurayin nata ya bamu, kuma duk an baza shi a lunguna da saƙunan garin nan, an miƙa cigiya gidajen rediyo da talabijin duk an baza hoton nata".
cikin kuka Hajiya Madina tace,"to amma me yasa zasu shigo da tunanin cewar Kidnappers ne suka ɗauketa. Baffa idan sune ai da tuni sun kira waya, mun kwana na biyu fa kenan Baffa, Kidnappers ba zasu yi shiru har haka ba. dan Allah Baffa a dai ƙara bincikawa ƙila wani wurin tayi, idan kuma kidnappers ɗinne a nemo su, su faɗa mana abinda suke so". ƙarfin kukanta ya katse maganar tata.
to wasa-wasa dai har tsawon kwana uku lamarin Fillo shiru, Kidnappers ɗin da aketa tunani suma shiru basu kira ba, wannan ya ƙara ɗaga hankalin kowa, aka kuma bar tunanin cewa kidnapping Fillo akai, dan idan shine tuni sun kira waya, abin dai yafi kama da ɓata, Kaka na batun ita gwarama taga gawarta ta huta.
adu'a kawai ake ta ko'ina, sadaƙa kuwa a gidan Alƙali Dikko babu dare babu rana.
Amir kuwa yana can ba ci babu sha saboda tsananin damuwa, musamman idan ya zauna yana tuna moments É—insu shi da ita.
lamari fa ya ƙara ta'azzara, dan tun ana lissafin kwanaki aka daina aka shiga sati, to abu kamar wasa daga sati ɗaya sai gashi an tafi sati na biyu har an shiga na uku.
daga nan kowa ya saddaqar da cewar an rasa Fillo har a bada, kuma duk wannan bidiri da ake Turaki bai sani ba, da ya kira waya Zaytuna kawai shaida masa tayi sunyi tafiya ita da Kaka zasu yi wata guda.
amma tun ranar da sukai waya da Maama yaji hankalinsa bai kwanta ba, tace masa kar ya damu ciwon kai ne ba wata matsala ba, ya zauna yay concentrating kan sabon project É—in da Baffa yasa su.
haka kuma dole ya haƙura ya maida hankalinsa kan aikin da Baffa yasa su, sai dai zuciyarsa ta kasa natsuwa, rabin tunaninsa na kan Fillo, so yake yaji ko da muryarta ne, amma babu hali, tunda har Zaytuna yasa ta tambayi Yami ko suna gaisawa da su kaka ta waya, Zaytuna tace masa Yamin tace itama wallahi duk ta rasa ta inda zata same su.
kuma randa Fillo ta cika kwana 21 cif, ranar kidnappers ɗin suka kira wayar Yami suka shaida musu suna buƙatar naira miliyan 5 cas,idan kuma babu to su yanka musu ƴarsu su turo musu da namanta a kwali, suka kuma bada gargaɗin cewa in har suka sanar da wani batun hakan to ko da sun kawo kuɗi lallai sai sun yake ƙafafun yarinyar, aka kuma saka musu muryar Fillo dake ta kuka tana roƙon Kaka akan azo aceceta zata mutu.
wannan batun yasa Kaka da Yami suka yi É—iff ko Maijidda basu bari ta sani balle su Hajiya Madina da sun tsab zasu iya sanar da police.
Kaka ta kira Amir a waya yazo, ita da Yami suka bincike É—aki tsab suka kwaso takardun filayen Fillo da Abdulhamid, filaye guda huÉ—u da kuma takardar wata gona, ta bawa Amor tace dan girman Allah yay shiru aje a siyar duka ayau azo aje akai kuÉ—in nan.
cikin sa'a kuwa Amir na zuwa gaba ɗaya abinda aka saya filayen da gonar miliyan ɗari huɗu da hamsin. dan haka ko da ya kawowa Kaka kuɗin sai aka ƙara ɗauka shanu guda uku akaje aka siyar har kuɗin yayi making yanda aka nema.
kuma Amir shi ya ɗau kuɗin yaje ya kai inda Kidnappers ɗin suka buƙata, bai dawo gida ba sai wajen biyu na dare cike da tsoron dajin da yaje ya ajiye kuɗin, har ya kasa bacci saboda firgici.
su Kaka kuwa ana can anata zabga adu'a, Kidnappers É—in sunce da an kai kuÉ—in zasu saketa ta dawo gida a lokacin, amma har sallar asuba har wayewar gari babu ko da inuwar Fillo.
hakan ya ƙara ɗaga hankalin su Kaka, suka kasa tsaye suka zaune ita da Yami, sai zagayen ɗaki suke yi, ana hakan wayar Yami dake ƙugu a soke tayi ƙara, da sauri jiki na rawa ta ɗauko ta kara a kunne, abinda ya doki kunnenta a lokacin shine Kukan Fillo.
tace,"Fillo kina ina?".
tace,"Yami sunce ba zasu sake ni ba, wai kuɗin yayi musu kaɗan sai an ƙaro. Yami karku ƙara musu ko biyar, ni na saddaƙar mutuwa zanyi, ki faɗawa Amir kar ya ƙara zuwa dan sun ce zasu karɓi kuɗin kuma su kashe shi, He has done so much for me that I can not repay him, bana son rasa shi Yami, kar ya ƙara zuwa dan Allah, gwara ya rayu ni na mutu, Yami ki kula min da Kaka bata da kowa sai ni sai Allah". ta faɗa tana kuka sosai, kuma me taɓa zuciya.
ƙit kamin Yami tace wani abu an kashe wayar.
Amir yazo gidan jikinsa duk a sanyaye don tuni Kaka ta kira ta shaida masa, ko da ya shigo ɗakin zubewa yayi daga bakin ƙofa, har tsawon minti biyar ya kasa cewa komai, sai da ƙyar ya iya buɗe bakinsa yace,"Kaka ko dai mu sanarwa da su Hajiya?, tunda sunce a a shirye suke suyi duk abinda ya kamata".
Kaka tai saurin girgiza kanta tace,"a'a Amir, ana faÉ—a musu zasu kai lamarin ga hukuma, su kuma mutane nan kaji abinda suka ce muddin hukuma ta sani sai sun kasheta".
Amir ya haɗiye wani abu a maƙogoronsa da ƙyar sannan yace,"shikenan Kaka, zanje yanzu akwai wani filina acan ƙauyenmu zan siyar da shi, shima kuma gidan da zamu zauna zan siyar da shi. gaba ɗaya in Allah ya yarda za'a iya samun ko miliyan biyu ce, sai a haɗa a ƙara basu". daga yanayin yanda yake maganar in ka kalle shi sai kayi masa kuka, bakinsa duk ya bushe, gaba ɗayansa ya wani firgice ya zaftare saboda rama.
Yami da Kaka suka haÉ—a baki wajen ce masa,"a'a karka sayar da komai Amir".
ya miƙe kamar zai faɗi yace,"Kaka bamu da wata mafita da ta wuce wannan. gobe zan dawo in Allah ya yarda, kuma a gobe zasu saki Fillo da izinin Allah, fatana ku kwantar da hankalinku kuyi ta adua".
Kaka tace,"to Amir a haÉ—a da sauran shanun can guda 5 da suka yi saura, akwai awaki ma guda 10 duk ka siyar sai a haÉ—a".
da kansa kawai ya iya amsa mata sannan ya fice jiki duk a saɓule, yana tafe yana layi kamar wanda yasha ƙwaya, bacci ne fal a idonsa da wata azababbiyar yunwa da yake ji, amma baya jin cikin biyun ɗa zai iya samuwa, shi da cin abinci da bacci kuma sai Fillo ta dawo.
kuma a safiyar ranar ne Turaki ya kira Khalil yake tambayarsa ga me da jikin Maama. dan shi har yanzu bai yarda da lafiyar da take ta faɗa dan bai ji a voice ɗinta ba, kuma taƙi yarda suyi vedio call.
Khalil mutum ne shi da baida wani ɓoye-ɓoye, ko saƙon mutuwa ne kai tsaye yake sanar da shi, dan haka kai tsaye Khalil yace masa,"Hammah ai yau kusan 3weeks kenan ana cikin tashin hankali, zancen da nake maka yanzu haka Maama bata cikin hayyacinta, ta fita ita da ƴar aikin nan Fillo an sace ƴar, har yanzu shiru babu labarin yarinyar, shisa ka kasa jin Maama a yanda kake so".
Turaki ya ɗauke wuta, ya daskare daga zaunen da yake, wayar ta silale daga hannunsa ta faɗo ƙasa, maganar Khalil ta shiga tariya acikin kansa. yarinyar ta ɓata, an saceta, 3weeks ba'a ganta ba, babu labarinta, ba'a san ina take ba.
hannunsa ya dunƙule ya naushi kujerar da yake zaune, ya dinƙa karanto innalillahi wa'inna ilaihi raji'un har Bello yazo ya sa me shi a sanda idanuwansa suka kaɗa suka yi jawurr.
*Vote, Comment & Share.*
[8/30, 20:26] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
```DAGA MARUBUCIYAR```
1-Sirrin Æoye
2-Al'amari
3-Hidaya Noor
4-Alhussain
5-Sanadin Talauci
6-Ƙaddarar So
7-Prince Khaleed
Da sauran su.....
*33*
*Switzerland*
sanya take cikin rigar sanyi mai kauri sosai, dogon wando ne fari a jikinta sai p-cap red colour da ta saka, wanda shigar ya amsa farar fatar jikinta sosai. yanayin fuskarta kaɗai zai shaida maka cewar bata cikin walwala da annuri, haka kuma ƙwayar idonta na shaida rashin nutsuwar da take da ita a zuciyarta a kullum a ko da yaushe.
a tsaye take daga jikin window tana leƙan waje, tana kallon yacca ruwan sama ke sauka, sanyin garin na ratsowa har cikin ɗakin yana shiga jikinta.