Sashe 108
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajiya Madina tace,"a'a yi mata a hankali, da gaskiyarya ai, dan shi yana so kuma shikenan ita ba za'aji ta bakinta ba?".
ta kalli Turaki tace da shi,"ka zo ka nemi yarda Æ´ata da amincewarta akanka, kwana biyu na baka, idan ba kai nasara ba za ayi duk abinda take so".
tana faÉ—ar hakan taja hannun Fillo suka fita, wacca ke ta faÉ—a mata ita dai asa ya saketa yanzu ba zata zauna da shi ba.
bayan fitarsu Baffa yay adu'a aka watse, ya rage daga shi sai Turaki, on serious note Baffa ke kallonsa kamin yace,"kenan ita Fillo itace uwar gida?"
kansa a ƙasa yace,"ehh Baffa".
ya numfasa ya sake cewa,"to ya zaman nasu zai kasance?, haÉ—e su zaka yi ko ya?".
yay É—an jim kamin yace,"yanda kace Baffa".
"ahh wannan kuma ai kai zaka yi making decision, sai dai in shawara ta kama sai in baka".
yace,"tom Baffa ka bani shawarar".
"ka bari sai mun zanta da hakimi tukunna, now you can leave, sai da safe".
*Vote, comment and share.*
[9/3, 18:03] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
*42*
Jar mota ƙirar rangerover ta sauka daga kan titin ta gangara gefe tayi parking a gaban tebur ɗin masu sayar da fruites.
matashin saurayin dake daga cikin motar ya zuge glass yay wa me siyar da pineapple sallama, mutumin ya amsa yana barin wajensa ya ƙaraso gun motar. zuwan nasa yasa Hamid miƙa masa hannu suka gaisa, me pineapple ɗin yace da shi,"ta nawa za'a zuba yallaɓai?".
Hamid yace,"sako guda goma, kar a yanka kowacce". mutumin ya juya yaje ya zubo pineapple É—in a cikin leda har guda biyar ya dawo, Hamid ya buÉ—e masa booth ya saka a ciki, kwata-kwata ba ita yay niyyar siya ba kawai dan mutumin ya rigada ya saka rai ne.
mutumin ya dawo yana goge hannunsa da durster yace,"ranka ya daÉ—e an gama sakawa".
Hamid ya juya bayan motar ya kalla mahaifinsa daga kishingiɗe kamar me bacci amma ya san ba bacci yake ba, sannan ya juyo ya ƙara cewa da me pineapple ɗin,"bamu apple". cikin sauri yaje ya dawo.
Hamid yace,"nawa ne kuÉ—in?". yace,"ka bada dubu takwas". Hamid yasa hannu a aljihu ya É—auko ya basa, yana shirin barin waje ya tsayar da shi da cewan,"yauwa kaga dan Allah tambaya nake dama".
mutumin yace,"to Allah yasa na sani".
Hamid yace,"gidan Alƙali Dukko nake nema".
mutumin yace,"ohh gidan uban marayu zaka ce". sannan ya shiga yiwa Hamid kwatance yanda zai gane, Hamid yay masa godiya sannan yaja motar ya bar wajen bayan ya ɗau apple ɗaya ya miƙawa Mahaifin nasa yana roƙonsa akan ya daure yaci ko ya ne.
tafiya kaɗan ta kawo su ƙofar gidan Alƙali Dukko, dai-dai lokacin da motar Maama ta shiga gidan, Hamid ya fito yana ƙarewa girman gidan kallo sannan ya ƙarasa yay knocking gate.
me gadi ya buɗe ƙofar ya fito suka shiga gaisawa da Hamid, bayan sun gama gaisawa Hamid ke tambayarsa dan Allah ko akwai Hajiya Rabi anan gidan.
Me gadi yace,"a'a wallah babu Rabi, wani yay maka kwatance da nan É—inne?".
Hamid yace,"ehh tou, daga can gidan sarki aka kwatanto mana nan É—in, da tana aiki acan sai akace ta dawo nan gidan".
Me gadi yace,"ohh ai nan ɗin main gate ne na gidan, da yake ɓangaren ma'aikatan gidan daban, daka zagaya ta baya zaka ga gate ɗin irin wannan ne".
Hamid yay masa godiya sannan ya koma mota, yana zagawa É—aya gate É—in ya faÉ—awa me gadin sunan Kaka na ainihi shima yace gaskiya bai san wannan sunan ba, sai dai bari ya kira masa shugabar ma'aikatan.
ba jimawa Yami tazo wajen, tana kallon Hamid tace,"kar dai jikanmu ne kai". ta faÉ—a saboda tsananin kama da Fullo da ta gani a fuskarsa kamar an tsaga kara.
yace,"ehh to indai wadda nake nema É—in ita kike nufi to ni jikanta ne".
Yami na murmushi tace,"Allah sarki, ai da yake ma ta kwana biyu da tashi daga nan É—in, amma bari sai muje yanzu na raka ka gidan da suka koma dake ba anan unguwar ba ne".
Hamid ya jira Yami ta koma ta sanyo mayafi sannan suka tafi, ita bata ma lura da wanda ke bayan motar ba saboda tana nufar shiga baya Hamid yace da ita ta dawo gaba.
sunyi tafiya me nisa kamin su isa gidansu Fullo, motar tasu ta shigo layin a sanda Fullo ke fita daga layin tana sanye da uniform da kuma niƙab zata wuce islamiya.
ƙofar gate ɗin a buɗe take dan haka bata tsaya knocking ba, Yami ta shiga dan sanarwa da Kaka, a parlo ta sami Kaka ita ɗaya tana kallo, suna gaisawa tace da ita,"taso ƙawata, taso taso".
Kaka na bin ta da kallo tace,"lafiya dai Ƙawata?".
Yami tace,"lafiya lau Ƙawata, ke dai fito da sauri kiga abin mamaki abin farin ciki".
cikin azama Kaka ta miƙe akan kujerar ta ɗauka hijab ɗin Ummi dake kan kujera tabi bayan Yami da sauri hankalinta duk ba'a kwance ba dan taga Yami a hargitse take.
Fitowarsu bakin gate Kaka tayi saurin dafe ƙirji asanda tayi tozali da Hamid jingine a jikin mota.
"me idanuna suke gane min?". wani farin ciki da jin daÉ—i suka mamaye Hamid ya baro jikin motar yana zuwa ya rungume Kaka.
ta ɗan ture shi a jikinta tana faɗin,"Hamid kaine ka zama mutum haka?, dama zan ƙara sanyaka a idanuwa na?, Hamid dama kana raye baka taɓa nemana ba?".
Hamid ya sauke numfashi yace,"kiyi haƙuri Kaka Allah ne bai nufa ba, amma wallahi kina raina, ta ya zan manta dake bayan kece silar zuwan mahaifiyata duniya".
Kaka ta share hawayen farin ciki tana bin motar da kallo kamin tace,"to ya akai kazo nan Hamid?, kar dai wani abu ne ya faru mara daÉ—i?, wannan motar kuma ta waye?".
Hamid yace,"Kaka ai ban manta da kina aiki a gidan sarki ba, na faÉ—a miki tsawon shekarun nan Allah ne kawai bai nufa ba sai yanzun".
tace,"dan dai kaga bana tare da abu me muhimmanci a wurinka ne shisa ka kasa nemana".
yaga tana kallonsa tana ƙara bin motar da kallo yace,"mota ta ce, ba zai yiwu mu shiga daga cikin gidan ba ne?".
Kaka na kallonsa tace,"zai yiwu mana Hamid, ai shiga cikin gida ma dole, gidanku fa kazo taho muje".
ta faÉ—a tana juyawa ya dakatar da ita,"Kaka mota ba zata shiga ciki ba ne?".
tace,"to sai dai ka duba tunda mu ba mota garemu ba, tun zuwanmu dai ta wannan ƴar ƙofa muke shiga".
ya ƙarasa ya duba yaga gate din ba me zugewa ba ne, hakan yasa yace mata,"Kaka to bari na fito da shi".
tace,"waye?".
yay É—an jimm damuwa na bayyana a fuskarsa sannan yace,"tare da Abba muke, ba zai iya tafiya ba sai na taimaka masa".
idanun Kaka a waje tace,"kana nufin Babanka Hayyo?".
ya É—aga mata kai,"ehh Kaka".
da mamaki sosai tace,"to me ya sami ƙafar tasa da ba zai iya takawa ba, ko wani mulkakken ya zama?".
ya sauke numfashi yace,"jarabawar ubangiji".
Kaka ta taɓe baki tace,"Alhaki dai yake bibiyarsa".
bai ce komai ba ya ƙarasa mota ya buɗe booth ya ɗauko wheelchair sannan ya buɗe bayan ya taimakawa Hayyo ya fito ya ɗorasa akan kujerar, tun fito da shi Kaka tayi masa kallo ɗaya taji mugun tsoro ya kamata kamin bala'in tausayinsa ya biyo baya, indai gani take yi da kyau ya rame kamar me cutar ƙanjamau, mutumin da yake jayent son kowa ƙin wanda ya rasa, mutumin da bama a gane girmansa ko ada amma yanzu girma ya bayyana ajikinsa sosai kace me shekaru ɗari.
Hamid ya turo shi suka ƙaraso inda Kaka ke tsaye cike da tsoron duniya, hoton abubuwan da suka faru a baya suna ta haska mata a ido, ita dai banda Hamid ya faɗa mata yace Abbansa sai ta rantse tace ƙarya ne ba shi bane, dan gaba ɗaya ya fita daga kamanninsa tsabar wahala, kamar ba wannan ƙaƙƙarfan namijin da ke zage dukkan ƙarfinsa ya zane mata ƴarta ba.
ta girgiza kai tana ƙara jin tsoro na al'amarin sakayyar wanda aka zalunta, a hankali tace da shi,"Hayyo".
ya ɗago da wuyansa da ƙyar wanda ya laƙwashe.
ya kalleta ya buɗe baki yace,"nannnnaaammm Daddddda". ya faɗa cikin ƙinƙinar da sai kayi da gaske zaka gane, kuma cikin murya kamar ta masu koyon magana.
kawai sai Kaka ta fashe da kuka sosai tana ambaton,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".
ta ƙara kallonsa tace,"Hayyo kai ne ka koma haka?". ta tambayesa tana tuna zaƙin maganarsa ada, wanda daɗin amon muryarsa na ɗaya daga cikin abin da yake jan hankalin mata garesa, dan ƙarya ne Hayyo yayi magana kana wajen baka ce kaji daɗin muryarsa ba.
hawaye ya sakko a idonsa yace,"Kakkkkaaa dddddaaa Allllahhhh kikkki yaaafeeee miiiimmmmnn, dddda Allllahhhh kiiii neeemmmooo minnn Haliiimaaaattttuu".
sai da aka ɗauki cikakken minti ɗaya da ƴan kai sannan ya iya faɗar kalmar da za'a faɗeta cikin sakanni biyu, yana maganar bakinsa na rawa, haƙoransa na daddatsewa akan harshensa.
Hamid yasa handky yana goge masa uban yawun da ya dalala ajikinsa ya ɓata gaban babbar rigarsa kamar an sheƙa masa ruwa.
ƙafafunsa suka shiga rawa akan wheelchair ɗin ya kamo hannun Hamid yana faɗa masa,"zaazzzzzannnn saukkkkkaaaa innnneeee miiii yaaaaaffiyyarrrr Dddddaaaada".
kaman yanda Kaka ke hawaye haka ma Yami, saboda ƙarya ne ace kaga halin da Hayyo ke ciki baka zubar da hawaye ba.
Hamid na kallon Kaka yace,"wai yana so zai sauko ya nemi yafiyarki".
tace,"Hayyo ba sai ka sauko ba na yafe maka, ni baka min komai ba dama".
ta dubi Hamid tace,"mu shiga". tai gaba suka biyo bayanta, Yami ta tura ƙofar. suna nufar entrance na parlon gidan Ummi ta fito, Kaka ta fara gani wadda ke aikin goge hawaye, bama ta lura da sauran ba, tai saurin ƙarasowa wajenta tana faɗin,"lafiya Dada?, na fito naga ba kya parlon me ya faru?".
Kaka bata iya magana ba dan har yanzu a girgiza take, kuma kamin tayi mata nuni da su Hayyo, Ummi taji hannayen mutum a ƙafafunta da ɗigar ruwan hawaye.
ta kai idonta kan Hamid dake zube a gabanta ya riƙe ƙafafunta, ba fuskarsa ta kalla ba, saman kansa kawai ta kalla ta shaida ɗanta, sai taji wani abu ya tsarga mata, ta kulle ido tana jin taruwar ruwan hawaye aciki.