← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 176

Sashe 124

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"ko ke fa, adu'armu itace Allah ya baku zaman lafiya, Allah yayi muku albarka ya albarkaci rayuwar aurenku, Allah ya baku zuri'a É—ayyiba, ya kauda fitina tsakaninku ya haÉ—a kanku ke da abokiyar zamanki".

kowa da ke É—akin ya amsa da,"ameen".

a lokacin Dada ta shigo, itama ta bata wani ruwan tofin adu'ar ta sha, sannan ta ba ta wani magani na su da kuma wani turare da ta fesheta da shi lungu da saƙo, ta kuma bata wata ƙaramar kwalba itama da ke ɗauke da turare aciki ta ce,"karki yarda taje hannun kowa har ki shiga ɗakinki, ki shafa turaren ciki a lokacin da zai shigo ɗakin, karki yi wasa da duk abin da muka faɗa miki da kuma abubuwan da muka ba ki, so muke kiyi zarra, ki zama tauraruwar da ke haska cikin gidan mijinki".

Dadda da Adda Asma su ka kamata a tare suka fita da ita, ɗakin Hajjah aka wuce da ita inda nan Ummi ta ke da zama yanzu ita da su Kaka da sauran ƴan'uwanta, ana shigo da ita Ummi kawai sai ta fashe da kuka, aka ƙaraso da Fillo gabanta ta durƙusa.
Ummi ta zura hannunta cikin alkyabbar ta kamo hannunta ta riƙe anata, sai a lokacin Fillo ma ta saki nata kuka da bai zo ba tun ɗazu.

"Yanzu kin zama matar aure, kin bar ƙarkashinmu kin koma ƙarkashin wani bawan Allah wanda Allah ya zaɓa miki matsayin mijinki, haka zalika aljannarki ta koma ƙarƙashin mijinki, bauta za kiyi, bautar da za ki saka a ranki cewa ba Muhammad Turaki za ki bautawa ba Allahnki za ki bautawa, biyayyar mijinki a yanzu ita ce gaba da komai a gurinki in banda addininki, in dai har za ki yi ma mijinki biyayya to za ki shiga aljannah, faɗar Allah ce ba tamu ba, ki kula da abincin mijinki ki kula da shimfiɗarsa, karki wasa da tsafta, ki zama me haƙuri, karki ko yi rashin juriya da kawar da kai, in har kin riƙe waɗannan abubuwan riƙo me kyau to kuwa za ki kama mijinki a tafin hannunki, kina da kyau ki ƙara da wanka ƴata, Allah ya yi miki albarka Halima, biyayyar da ki ka yi min Allah yasa kema naki ƴaƴan da za ki haifa su yi miki. Allah ya sa wannan aure da ki ka yi anyi kenan sai mutuwa ce zata raba ku, Allah ya yi riƙo da hannayenki ƴata, Allah ya dasa tsananin tausayinki da ƙaunarki a zuciyar mijinki, Allah ya ba shi ikon yin adalci a tsakanin ke da abokiyar zamanki, don Allah ki zama me haƙuri a gidan aurenki kinji, da auren so da auren ƙiyayya duk sai anyi haƙuri sosai ake jin daɗin zamansa, ki girmama iyayen mijinki wannan zai ƙara ba ki fada a zuciyar mijinki, kar ki zamto me yi masa jayayya da ƙorafi hakan zai sa mijinki yaji kin fita a ransa, ki kula da duk haƙƙoƙin mijinki, ki dage da ibadah da kuma yawaita adu'ar tsari da zaman lafiya tsakanin ke da mijinki da abokiyar zamanki, kin san ba ki da lafiya dan haka ki nesanta idanuwanki da kunnuwanki da dukkan abinda zai zamar miki damuwa balle ki jawa zuciyarki matsala, sannan abu na ƙarshe da zan jaddada miki shi ne ki zama busy akan yawaita karatun ƙur'ani, wannan zai hana zuciyarki samun lokacin biyewa zugar shaidan, Allah ubangiji yayi miki albarka, ya baku zaman lafiya ya kauda fitina a tsakaninku, na yafe miki dukkan abin da kika yi min".

rabuwa dai tsakanin mahaifiya da ƴarta sai ya zama abu me wahala, dan ƙam Fillo ta riƙe Umminta tana kuka me taɓa zuciya, kuma da yake itama Ummin tana da raunin zuciya sai su ke ta kukan tare, sai da ƙyar aka samu aka cire Fillo daga jikinta.
suka fito aka wuce da ita part ɗin Maudo, shi da Dottijo ne zaune a parlonsa, anan aka zaunar da ita kowa ya fita ya rage daga ita sai su, Maudo ya ɗora hannunsa akanta ya dinƙa kwaranyo adu'a yana tofa ma ta, ya gama nasa Dottijo ma ya yi ma ta, sannan suka shiga yi ma ta faɗa da nasiha me ratsa zuciya, kukanta sai ya ƙaru, kuma lokacin kewar mahaifinta ta kamata, sun jima su na ma ta nasihohi kafin a fito da ita.

ko ƙafar gida ba'a fito da ita ba anan ƙaton tsargidan akayi parking da motar Maudo me shegen tsada a gabanta aka shigar da ita, ana ta busa algaita da sarewa kamar wata ƴar sarki, Dadda da Inna Baraka yayyan Hayyo sai wata cousin ɗin Ummi me suna Innah Hajar su ne suka shiga motar amarya, sauran motocin kuma da mutane shida kacal suka bi bayansu, motar amarya tayi airpot sauran biyun kuma suƙa ɗauki hanyar Gombe.

a gidan Alƙali aka yada zango, dan su da kansu suka turo motar ɗauko amarya a airpot, su Dadda sun sami tarba me kyau a wajen su Hajiya Madina, sun ga mutunci da karamci tsurarsa, lokacin da su Dadda zasu damƙa Fillo a hannun Mum sai ta girgiza kai tana yi musu nuni da Hajiya Madina ta ce,"ai ga mahaifiyar tasa can".

Inna Hajar ta miƙa hannun Fullo akan ƙafafun Hajiya Madina tana faɗa ma ta ga amanar ƴarsu, Maama na murmushi me faɗi da jin daɗi take shaida musu sun karɓa, kuma insha'Allahu ɗan su ba zai bayar da kunya ba, Fillo sai ta rinƙa jin kamar ayau ne ta fara shigowa gidan Alƙali, kuma kamar ayau ne ta fara sanin su Maama dan duk sai take jin su sababbi a wurinta, a cikin hular alkyabbar da ta rufe mata ido banda kuka babu abin da take yi, ƙwayar idonta baƙin rubutun da ke ɗauke da adadin sakin da Turaki ya yi ma ta kawai ta ke haskowa, tana jin muryarsa na ƙara karanta ma ta a kunnenta.

sai wajen ƙarfe uku sannan ƴan taraba waɗanda Dada ta zaɓa zasu zo Dinner suka zazzo, ciki kuwa har da ita kanta, tasha wanka na kece raini kamar ba tsohuwa ba, less ɗin jikinta kansa abin kallo ka ƙara kalla ne.
sai ƙarfe takwas na dare tukunna aka fara shirin tafiya Dinner, faɗar haɗuwar da amarya tayi ma ɓata lokaci ne, alƙalami ma ba zai iya ba, ta yi kyau iyakar kyan da ƙaryar baki ya ce zai iya faɗa, wata arniyar doguwar riga ce da Maama tasa Samha tayo order ɗin ta daga europe aka taho da ita, kana kallo kasan kuɗi aka sa ba kaɗan ba aka saya rigar, shigar pink aka yi ma ta wanda hasken fatarta yayi bala'in ɗaukar colour ɗin, abin ba'a cewa komai sai dai masha'Allah.

sabuwar mota fil wacca Mum ta bawa Turaki a ita zaa ɗauketa, Raudha da Maijidda su kai ma ta rakiya har bakin motar da Bello ne ke zaune a driver seat, aka buɗe mata bayan motar ta shiga, san da zamanta ya daidaitu lokacin balaƴaƴƴan ƙamshin turaren da ta san shi kaɗai yake amfani da shi taji ya doki hancinta, ta yi saurin ɗago kai tana kallonsa, ta gan shi yana kallon gefe guda da alama ma bai san da shigowarta cikin motar ba, Fuskar nan kamar an aiko masa da mutuwa, ya fito sak a asalin Turakin da ta fara sani a rayuwarta, sai dai duk da wannan ɗaure fuskar da ya yi hakan bai hana fito da azababben kyan da ya yi ba acikin arniyar suite ɗin da yasa, black da ratsin pink colour irin na jikinta.

tuna cewar ita fa ba matarsa ba ce yasa tayi saurin ɗauke idonta akansa, tana me tuna haramcin hakan, idanuwanta suka ciko da ruwan hawaye suna ƙoƙarin zuba, sai dai ba ta basu damar hakan ba dan sam bata so yaga weakness ɗinta a yau balle ya alƙanta hakan da zafin sakin da yay ma ta.
ta kafe ƙunshin hannunta da kallo tana jin ƙaguwar su tafi aje ayi ayi a gama taron ta daina ganinsa a kusa da ita.

da ga Bello dake driving har su kowa zuciyarsa a cunkushe take, Maijidda ce kawai da bata san damuwar komai ba take jin zuciyarta wasai sai kallon titi takeyi, Bello kuwa bini-bini sai ya daki stearing yana jan dogon tsaki.
can da tafiya tayi nisa Fillo taji kallon dake jikinta ya yi yawa ta ɗago ido, karaf ƙwayar idonsu ta tsarƙe ata juna, tasha murr fiye da yanda ya haɗe tasa fuskar, kwatakwata ba ta san lokacin da bakinta ya suɓuce da faɗin,"kana da buƙatar ƙara sanin addini da kyau, domin na lura sam baka san yanda shari'ar musulunci ke tafiya ba".

tayi maganar a ƙasa yanda su Bello da ke gaba ba zasu ji ba.

Turaki ya dinƙa kallonta da mamaki tsantsa, kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce da ita,"kin fini buƙatar komawa makaranta ke da kika kasa ba da takardar sallamar da aka ba ki".

ya faɗa daidai da isowar motarsu event center, suka yi parking a bakin ƙofar shiga gurin sannan suka yi zaman su a mota, Bello bai ko waiga ya kalli Turaki ba balle yay masa magana, ya fita ya tsaya jikin motar sai jera uban tsaki yake yi.

sai da duk mutane suka gama shiga cikin hall sannan aka zo aka fito da Turaki da Fullo, Bello ya yi gefe abinsa kamar bai da wata alaƙa da Turaki, aka zagayo da Fillo side ɗin da Turaki yake nan da nan sai ruwan camera akansu, ƙememe suka ƙi riƙe hannun juna duk da ɓata ran da Anty Rahinatu(ƙanwar Mum) ta nuna musu, suka jera kamar ƴan ƙauyen ƙayayau.
su Amatullah da suka zama ƙawayen Fillo su ne suka fara shiga a layi na hannun dama da ga nan sai iyayen gayyar a tsakiya, sannan abokan ango da Turaki bai sa a inda Bello ya kawoso su ba suka ja nasu layin a gefen hagu, abin dai gwanin burgewa, ba zaka taɓa kallon fuskar Turaki da Fillo ba kayi zaton ransu a ɓace yake, ko damuwa, hakan yasa duk hoton da aka ɗauke su sai sunyi kyau, ita dai tayi ƴar ƙarama a kusa da shi dan ita kanta sai nauyi take ji.
Chapter 124 · 0% Book details