← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 163 OF 176

Sashe 163

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fillo na murmushi ta kalli cikin da ke jikinta, haka Hajiya Madina take yi, aikinta yanzu bai wuce tasa Fillo a gaba ba tayi ta magana da cikin tamkar a gaske, in anyi dariya sai tace ai ita tana jinsa su ne basa ji, kuma idan ya fito zai ba su labari ne.

haka É—aya yau zuciyar Fillo taji tana so ta yafewa wannan mutumin da ta manta a rayuwarta, kamar ta yafewa Amir, sai ta rumtse idonta ta hura iska a bakinta ta fita daga kitchen É—in.
tana tayar da mota kiran Ummi ya shigo wayarta.

"Auta kina lafiya?".

"lafiya lau Ummi".
"masha'Allah, ina zaune naji ina kewar ki".

"wallahi nima Ummi jira nake naje gidan su sai muyi vedio call da ke, yau kawai ina ta kewarki sosai fiye da da. Ummi na yi mafarkin Abba ma, yace in gaida ke, sai naji kamar na bi shi Ummi".
[9/7, 02:37] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*59*
idan mu ka duba fuskar rayuwa, zamu ga gaba É—aya tana tafiya ne based on yanda Allah (SWT) ya tsara mana.
rayuwar mu na tafiya ne daidai da yanda ubangiji ya rubuta mana tun kafin zuwan mu duniya. duk hasashenmu, duk lissafin mu, duk yanda muke so, duk yanda muka tsara, duk yacca muke tunani, duk yanda ba ma so, duk yanda muke gudu, duk yanda muka yanke, to haƙiƙa yanda ubangiji ya rubuta mana hakan ne zai kasance, kuma na ubangiji shi ne daidai.

sau tari idan muka duba fuskar rayuwa, zamu ga duniya tana yiwa wanda ya jima yana aikata laifi talala, zai ta aikatawa yay ta aikatawa, kafin ya ankare sai ya farga lokacin tuba ya ƙure masa, wani Allah zai iya nufar sa da tuba kafin mutuwa, wani kuma ba zai sami wannan damar ba, haka zai wuce lahira da tarin ɗumbin zunubi.
haka sau tari zamu ga rayuwa ta rufta da wanda zai aikata laifi sau ɗaya tal a rayuwarsa, nan da nan sai ya fuskanci hukunci abin da muke tunanin me aikata babban kuskuren shi ya kamata ya karɓa.

haka zalika idan mu ka ƙara duba fuskar rayuwa, abin da duk mu ka sani shi ne asiri gaskiya ne, tun da har yaci shugaban mu fiyayyan halitta Annabi Muhammadu (SAW), kuma tasirin adu'a ya warka da shi, har aka gano wanda yay wannan sihirin.
sai dai abun da yake da akwai a tamu rayuwar, ba ko da yaushe Allah ya ke tona asirin waÉ—anda suka zalunci wasu bayin Allahn ba, sai dai ubangiji yay wa bawansa sakayya kawai.
idan mu ka ɗauki ɓangaren masu aikin asiri ga wani wanda bai ji ba bai gani ba saboda son zuciya da tsantsar zalunci.

zamu ga a yayin da suka yi asiri sun yi nasara, sai dai ƙarfin adu'a kan karya wannan asirin na su komin tsayin shekarun da za'a ɗauka, yayin da wasu za su sami waraka suci gaba da rayuwar su ta yau da kullum, yayin da wasu kuma warakar zata zama ajalin su.
sai dai fa abin da yake da akwai ko da asirin ya karye to bai zama tilas dole ba a san wanda yay wannan asirin har kuwa duniya ta naɗe, duk da cewa a yanzu ubangiji ya daina barin wannan ladan gabar, sanda za'a barka kayi ta yawo da hakkin mutane har ka mutu sai anje ƙiyama tukunna.

a'a! a wannan rayuwar da muke ciki ta yanzu, tun a duniya Allah yake wulaƙanta mutum, rayuwa tayi kacakaca da shi, tayi masa ɗaurin goro, wataƙila ma ya faɗa tsananin wuyar da ta fi ta wanda ya jefa a ciki, har sai ma ubangiji ya so ka da rahmarsa sannan zai baka damar roƙon yafiyar wanda ka zalunta, idan kuwa aka yi rashin dace ubangiji bai baka damar fallasa kanka ba, balle har ka nemi yafiya, to lallai wata shari'ar sai dai a yi ta kuma a lahira.

a lokacin da motar tata tayi parking a compound ɗin gidan, ta fito daga ciki riƙe da babban flask na abinci a cikin basket, ta jingina da jikin motar domin numfasawa, saboda yanayin nauyin cikin jikinta.
Auwal ɗan me gadin gidan ya ƙaraso wajenta cikin sauri, bayan sun gaisa ya karɓi flask ɗin domin taimaka mata, bata hana shi ba saboda ita ma tana buƙatar ataimaka mata ɗin, duk da flask ɗin ba wai nauyi ne da shi ba, kawai dai ko ƙaƙa abu yake yana yi mata nauyi a yanzu.

part É—in Mum tana fara nufa, a parlo ta sameta tana kallon news da ake yi, ta zauna suka shiga gaisawa Mum na tambayarta yanayin jikin nata.
a lokacin da Fillo ke kallon Hajiya Ramla tace,"Mum lafiya dai ko?". tayi tambayar duba da yanayin Mum É—in da ta gani, fuskarta da damuwa sannan ga jikinta kamar a sanyaye.

"babu komai Daughter, kawai yanayin garin ne na yau".
tana faÉ—in hakan kuma sai ta É—auki wayarta ta kira lambar Hajiya Madina, har kiran ya katse bata É—auka ba.

sai ta miƙe tana cewa da Fillo,"na bar ki anan ko zamu je tare?".

"ina Mum?".
"wajen Maaman ku. naga tun safe ban ji ɗuriyarta ba, ƙafana na ciwo ban sami damar leƙawa ɓangaren nata ba, ina ta kiran wayarta kuma bata ɗaga ba".

Fillo tace,"ai ba mu jima da gama waya da ita ba Mum, ita ma ta kira ni ai".

Hajiya Ramla ta sauke numfashi, tayi gaba yayin da Fillo ta bi bayanta.
shigar su parlon Hajiya Madina kiran Turaki ya shigo wayar Fillo, tana É—aga yace da ita.

"Fulani Nah kin ƙarasa gidan?".
"na je Jannaty, lafiya naji ka kamar a damuwa".

"babu komai. yau É—in ne kawai nake jinta duk babu daÉ—i, ina Maaman?".
"yanzu ai na shigo ɓangaren nata, ban hau saman ba".

"kowa a gidan yana lafiya?".
"Jannaty wai...".

"just answer me".
"kowa lafiya lau, Mum ma muna tare da ita".

ya sauke numfashin da ta jiyo har cikin dodon kunnenta.
"ina kan hanya ne go slow ya tsare ni. amma insha'Allah yanzu babu jimawa zan ƙaraso gida".

san da ta shiga ɗakin Hajiya Madina ta tarar da Hajiya Ramla na taɓa jikinta, a yayin da take yin magana da Nihal tana tambayarta,"kuma bata ce miki bata jin daɗi ba?".

"a'a Mum, ba ma fa ta jima da kwamciyar ba ai, lafiyarta lau".
"to masha'Allah, idan ta tashi ki ce ta kira ni a waya. zan je saboda baƙin Haɗeja da za su zo".

"tom Mum".
Hajiya Ramla ta fita, Fillo ta ƙaraso ciki ta zauna a gefen gadon da Hajiya Madina ke kwance tana bacci.
ita ma tasa hannu ta taɓa ƙafar Maaman sai taji babu zafi kamar yanda kowa ke tunanin ko zazzaɓi ne ya sata yin baccin rana haka.

"Allah yasa ba ciwon kai ba ne".
Fillo ta faɗa tana cire mayafin jikinta ta ajiye, tare da naɗe ƙafarta ɗaya ta ɗora akan gadon gaba ɗaya.

Nihal da ke kan kujera tana aikin project a system tace,"lafiyarta fa lau, ko 10minutes bata yi ba da kwanciya, tace idan kin zo ki tashe ta".

"ta fita aiki ne yau?".
"a'a haka kawai ta tashi da gyaran part É—in Baffa yau, nace yau dai soyayya ake ji".

Fillo tayi dariya tana faÉ—in,"amma dai kin tayata?".
"ina zuwa ma ce tayi in bar mata ɓangaren miji ita ɗaya take so ta sami ladan".

shiru ya gimla na kusan mintuna biyar, Fillo ta miƙe taje ta ɗauko basket ɗin abincin, a ƙasa ta zauna ta buɗe ta zuba iyakar wanda zata ci a plate, Nihal ta taso ta zo ta zauna su ka shiga ci a tare.

"gaskiya yayi masifar daɗi, no wonder Maama tace ba zata ci komai ba sai kin kawo mata, bari na tasheta yasin tun zafin flask bai jiƙa shi ba".

"no barta tayi baccinta please, abu da an kusa la'asar, lokacin sallah nayi za ki ga ta tashi".

bayan wucewar mintuna goma hannayen Turaki su ka murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin, ƙafafuwansa suka shigo cikin ɗakin yayin da sanyin Ac ke ratsa shi.
ƙwayar idonsa bata sauka akan kowa ba sai Maama da ke kwance kan gado tana bacci.

A lokaci guda yaji jikinsa yayi wani irin sakayau tamkar an zare masa lakar jikinsa, abun da bai yi tsammani ba sai yaji yawun bakinsa ya bushe, Me ke shirin faruwa ne?.
ya saki handle ƙofar da yake riƙe da shi, ya kasa ɗaga ƙafarsa yana jin wani abu ya wuce ta maƙogwaronsa, wani irin abu mai nauyin gaske, yana jin yanayin bugawar zuciyarsa na sauyawa, yana jin faɗuwar gabansa na ƙaruwa.

ya san da cewa don mutum yayi bacci ba wani abu ba ne, dan bacci wani abu ne da É—an adam ke yinsa a kowanne dare, to amma ba zai iya cewa ga ranar da Maama tayi bacci ba da rana, iyakar tsayin rayuwarsa zai iya faÉ—in hakan, ko da ace kuwa tana cikin halin jinya ne, baccin rana ba ya daga cikin al'amarin rayuwarta.

to amma yau ɗaya, rana guda, rana ta farko kawai sai ta kwanta irin haka?, ƙarfe ɗaya da rabi na rana, har tayi irin baccin da bata ji buɗewar ƙofar tasa ba, kuma a lokacin da ya san tana zama tayi lazimin sallar azahar?.
kawai sai ya ji wani abu ya motsa a ƙasan zuciyarsa, yaji kamar rauni na shirin kama shi, sai dai kamar ko da yaushe a rayuwarsa, yayi ƙoƙarin tattaro dukkan nutsuwarsa da dauriyarsa tare da dakiyarsa, ya maida ƙofar ɗakin ya rufe.

"me ya sami Maama?".
ya jefa tambayar ga Fillo da Nihal yana tsaye a gefe guda.

"bacci take yi, aiki tayi ta gaji".
"aiki!?, ina ma su aikin?".

"part É—in Baffa ne fa Hammah, ka san bata barin Æ´an aiki su je can".
"gajiya bata sakata baccin rana, tasha magungunanta?".

"lafiyarta fa ƙalau Hammah, kawai muna zaune muna hira tace bari ta kwanta kafin ta gaban goshinta ta ƙaraso".

ya shiga girgiza kansa, ƙafafunsa na ɗagawa da ƙyar, haka ɗaya Maama ba zata yi baccin rana ba, no matter what bata baccin rana, bai yarda da wannan baccin nata ba.

"kar ka damu lafiyarta fa ƙalau, ban da yanayin ciwon kai da sai ka tashe ta".
kunnuwan Turaki su ka tsinci muryar Fillo a cikin iskar É—akin.
Chapter 163 · 0% Book details