← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 176

Sashe 34

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

baccin da bata farka a shi ba kenan ba har sai washegari da wajen ƙarfe goma, lokacin su Kaka sunzo, tana buɗe ido akan Kaka ta sauke wacca ke zaune kan kujera ta rafka uban tagumi. Maijidda kuma na tsaye jikin bango kana kallon fuskarta zaka san tasha kuka ta gode Allah, itama duk ta faɗa saboda tashin hankalin da suka shiga. Yami ce kawai me ɗan ƙarfin hali da take ta tausar Kaka akan ta daure ta saka abu acikinta tunda likitan yace zata farka. kuma kwana biyu Kakan banda ruwa babu abinda take sha, shima idan tasha ɗacinsa take ji.

"Yami ba zan iya sa komai acikina ba sai yarinyar nan ta farka, yau fa kwana huɗu kenan, faɗa mana suke tana raye, ni dai ina tantamar hakan, gwara kawai a faɗa min gaskiya a bar ɓoye-ɓoye aini musulma ce na yarda da mutuwa".

Yami dai tayi shiru bata ce komai ba, sai kallonta da ta maida kan Fillon, itama dai ta fara tantama akan maganar likitocin nan, ace kwana huɗu mutum bai farka ba kuma sannan ace yana raye?, to mene amfanin ɓoyewar?. sai kawai ta gyaɗa kai cikin ranta tana faɗin wataƙila kuma ba'a so a ɗora alhakin mutuwar tata ne akan Turaki shiyasa, tasan zasu iya komai tunda suna da uwar kuɗinsu.

Fillo da take jinsu a lokacin ta kira sunan Kaka, wani farin ciki ya baibayesu suka yo kanta. Maijidda tayi mata wata runguma har sai da ƙashin bayan Fillo ya amsa. kuma a sannane Amir yazo, tunda ya shigo ya kafeta da ido, kallonsa take shima kallonta yake, zuciyoyinsu na saƙa abubuwa iri ɗaya dangane da junansu. kalmar da Amir ya fara faɗa mata shine,"za ki iya yin sallah?". kai kawai ta ɗaga masa, Yami ta kamata ta sakko a gadon ta kaita banɗaki. lokacin data fito Amir kawai ta gani har sannan yana tsaye idanuwansa duk sun faɗa ciki, kana kallonsa zai baka matuƙar tausayi.

shi ya shimfiÉ—a mata sallaya, ya tayata saka hijabin, yace mata idan zata iya ramawa duk ta rama, idan ba zata iya ba tayi wasu ta bar wasu sai jimawa. tambayar da tayi masa shine,"kwana nawa yau?". "huÉ—u". amsar daya bata kenan. kuma tunda ta tayar da sallar bata tsaya ba sai data rama duka sallolin dake kanta, har lokacin Amir bai zauna ba yana tsaye.

tana idarwa kuma sannu kawai yay mata, zai fice a ɗakin tabi bayansa da kallo tace,"ina zaka?". "tafiya zanyi". amsar daya bata kenan ya fice daga ɗakin bai jira cewarta ba, jikinta yayi matuƙar sanyi, su Kaka suka dawo ciki ta tambayi Maijidda suka ce ta tafi raka Amir.

Yami ta zuba mata abinci ta ajiye a gabanta, har lokacin tana kan sallaryar ta miƙe ƙafafunta, da ƙyar tayi sallar, ƙarfin dauriya irin nata kawai. "na ƙoshi Yami". kalmar da ta faɗa kenan, kuma kafin Yami tace wani abu an turo ƙofar ɗakin an shigo, Dr Yusuf ne, suka amsa sallamarsa sannan ya umarci Fillo da ta koma kan gadon za'a ƙara saka mata drip.

gadon ta koma ta kwanta, yay mata wasu tambayoyi dangane da yanda take ji tana basa amsa, acikin drip ɗin ya zuba duk alluran da za'ai mata. yana gama saka mata kuma yace da Kaka,"idan ya ƙare a bata abinci taci". da haka ya fita.

sai yanzu su Kaka suka sami natsuwa, Yami ta zuba musu abinci suka shiga ciki, lokaci zuwa lokaci Maijidda na lura da ruwan daya kusa ƙarewa.
bayan wani lokaci hankalinsu ya karkata ga turo ƙofar ɗakin da akayi, ganin wanda ya shigo da sauri Kaka ta miƙe tana yi masa sannu da zuwa tare da amsar ledojin dake hannunsa.

Khalil ya shigo yana ta kallon Fillo, mamakin da kowa yake akanta shine taya akai ta fita acikin wannan daren?, kuma me taje yi a wannan dajin?. shi dai abinda zuciyarsa ke raya masa shine Turaki ne ya É—auketa zai je ya cutar da ita, Turaki ne yay komai, har yau haka zuciyarsa ke faÉ—a masa.

*Plss Comment, Vote, and Share.*
[8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*

_🤔zato dai zunubi ko da ya kasance gaskiya, ku daina ɗaukar hakki babu kyau ni gaskiya nake faɗa muku, ahh tou🤣, yo kowa ya tashi sai ya wani kama cewa Hajiya Madina kaza-kaza, banda ma dai neman magana yaushe kuka taɓa ganin ta cutar da wani daban balle Turaki da ya gama nannaɗe zuciyarta😒...to a daina gaskiya ban so, duk wanda naji ya ƙara taɓata zan hau bori😭😭..._

*18*
After long minutes sai ga Zaytuna itama ta shigo room É—in, har lokacin Khalil yana nan bai tafi ba, yana zaune akan kujerar da Kaka ta ajiye masa.
yana kallon Zaytuna da mamaki yace,"from where?". bayan duk ta gaida su Kaka tare da tambayarsu ya me jiki tace da shi,"bamu jima da shigowa garin ba, so muna sauka a airpot mu kai waya da Hamma yake ce min yana nan".

Khalil ya ƙara tambayarta,"ya Granny ɗin?".

tace,"tana lafiya, duk tana gaishe ku...da ta saka rigimarma sai mun zo tare tana so taga Hammah".

yace,"Allah sarki Granny, insha'Allahu zan matsa masa akan muje, sai mu dawo a ranar tunda dai am sure ba zai kwana ba".

Zaytuna ta cirewa Fillo drip nata da ya ƙare yanzu, itama tana tambayarta yanda take jin jikin tana faɗa mata komai da sauƙi ƙafarce dai har yanzu.
after five minutes Zaytuna ta yiwa su Kaka sallama saboda kiran da Baffa yake yi mata, tare suka fita da Khalil wanda yake ta mamakin yacca akai har yanzu Turaki bai shigo ba.

bayan fitarsu Maijidda ta dafa shoulders É—in Fillo tace,"mene damuwar?".

tace,"me kika gani?".

Maijidda tace,"na san dai ba ki da lafiya amma yanayin fuskarki ya nuna akwai damuwa a ƙasan ranki".

Fillo ta haÉ—iye yawu tukunna ta É—ago ta kalla Maijidda sannan tace,"me yake damun Amir?".

Maijidda ta tashi daga kujerar da take zaune ta dawo gefen gadon kusa da ita ta zauna, ta kamo hannunta ta riƙe acikin nata tace,"me kika gani?".

Fillo ta dake ta hana kuka ƙoƙarin fitowa tace,"sannu fa kawai yace min, ina amsawa yasa kai ya fice".

"kinyi masa wani laifi ne?".

ta girgiza kanta,"a'a ni banyi masa komai ba. kuma ko da ace ma nayi masa ba zai min haka ba tunma da ya ganni banda lafiya".

Maijidda tace,"to kwantar da hankali ba abin da kika masa, kawai yana cikin damuwa ne akan lamarinki. yace ya kasa fahimtar me ke faruwa, yana ganin kamar mutanen ɓoye naso su shafeki ne tun a wancan ciwon da kika yi, amma wannan karon sai yaga kamar ma sun riga sun shigeki...baki gani ba wallahi yanda yake ta sadaƙa yana sauke miki alƙur'ani, anan fa yake kwana kullum ba ya tafiya, abinci sai Innarsa tayi da gaske".

Fillo tai É—an jim kafin tace,"to ai ni banda wasu aljanu, hasashensa ne dai kawai".

Maijidda tace,"to aikuwa abin da kowa ke faÉ—a kenan".

Fillo ta kalli su Kaka da suke can gefe su na maganarsu, hankalinsu ba ya kansu gaba ɗaya. murya can ƙasa tace,"Maijidda ina asirin da nace miki zan ɗauke a ɗakin Turaki?". 

idanun Maijidda a waje take kallon Fillo da al'ajabi, ai dama tunda hakan ta faru ta fara tunanin da wuya idan ba karambaninta ne ya bata damar ɗauke asirin da ta gaya mata zata ɗauke ba. ita kam ta fara tsorata da lamarin ƙawarta, ta bakin Amir aljanu sun shigeta domin mutum dai ba zai yi abin da takeyi ba.

Fillo taja hannun Maijidda da taji tayi shiru,"kina da matsala wallahi, shi yasa wani lokacin da faÉ—a miki abu gwara shiru".

bata bawa Maijidda damar magana ba taci gaba,"na ɗauke asirin harma ya ƙone".

"shima ke kika ƙona shi?".

ta girgiza kanta,"aa wallahi ikon Allah kawai, ba ki gani ba kamar tashin bom haka yayi tushhh, kinji yanda yake ɗoyi kuwa Allah kika shaƙa kayan cikinki sai sun kusa zubowa...kuma kin san me?". ta faɗa tana muskutawa ta gyara zamanta akan gadon inda ta juyo ta fuskanci Maijiddan.

"ina ga wannan asirin ne yake hana Turaki Sallah, ai dama na faÉ—a miki naji Maama na kokawa da hakan. kinga nima fa tun sanda na É—auko shi naji bana sha'awar yin sallah kwata-kwata...bari dai mu bar asibiti zan baki labarin komai".

ita dai Maijidda tsuru tayi tana zubawa sarautar Allah ido, ta É—anja baya kamar tana tsoron Fillo ne.

muryarta itama a can ƙasa tace,"wani lokacin idan muna magana sai naga kamar bake ba, shi yasa bakina ba ya rabo da ayatulkursiyu...to Allah dai ya ba ki lafiya ya rabaki da su lafiya. insha'Allah sai anyi galaba akansu...".

bata ƙarasa ba Fillo ta kai mata duka a kafaɗa ita kuma tayi saurin kaucewa tana dariya.

"Allah ki bar wannan zancen Maijidda bana so, ba wasa bane wannan, wani yaji ai sai ya ɗauka gaske. ƴar wulƙanci kawai".

Maijidda har sannan fuskarta da dariya tace,"yo daga miki abin arziƙi, adu'a fa Haliman Amir?, ina ga ma wannan dalilin Allah ya duba ya aiko Malam Amir gareki, kinga ai sa dinga cin ƙwal uwarsu a hannunsa, dan ba raga musu zai yi ba da adu'a...waya sa ni ma yanzun ko ba ke bace".

wannan maganar tasa Fillo zuro ƙafafunta zata sauko a gadon ta damƙeta, ita kuma tayi wajen su Yami tana ta dariya.

Fillo tayi ƙwafa,"Allah kika ci gaba sai na bugo miki wannan ƙarfen". ta faɗa tana nuna ƙarfen da ake saƙale drip a jikinsa.

Kaka dai idonta na kansu tun É—azun, tana jin zuciyarta na washewa daga damuwar dake tare da ita, sai yanzu hankalinta ya dawo jikinta. ko babu komai tasan Fillo ta sami lafiya, abu É—aya yayi saura, matsalar jinnu da suke tunani sun shafeta.

Fillo ta rafka tagumi tana tunani Kaka ta miƙo mata abincin da bata ci ba ɗazu, ta ɗago tana ɗan yamutsa fuska, murya a narke da shagwaɓa tace,"Kaka na ƙoshi fa".

Kaka tayi mata wani kallo tace,"karɓa kafin ranki ya ɓaci, kin farka za ki ɗora daga inda kika tsaya ko. wadda bata tausayin kanta kawai".

Fillo na turo baki ta karɓi plate ɗin.

"wallahi ki cinye shi kafin na dawo". Kaka ta faɗa tana kaiwa ƙofa.
Yami ta miƙe tabi bayanta suka fita tare.
Chapter 34 · 0% Book details