Sashe 63
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
can sai taji Boɗejo tayi shiru, ta ɗago kai ta kalleta, sai taga hanyar bedroom ɗinta take kallo, Fillo ta waiga taga Turaki ne ya wuce, gabanta taji ya faɗi, da sauri ta juyo tana ci gaba da matsawa Boɗejo ƙafarta, fatanta ɗaya Allah ya kawo abunda zai tasar da ita daga wurin nan yanzu, kuma Allah yasa kar Boɗejo tace zata aiketa ɗakin nata, dan sam bata so ta haɗu da Turaki.
Boɗejo tace,"ina faɗa miki to haka ake yi fa idan biki ya tashi, in kika ga yanda ake kashe kuɗi sai kiyi zaton ko ba'a san ciwonsu ba ne. to da yake al'adar gidan sarauta ce hakan, indai za'a yiwa Yarima aure ko kuma Gimbiya to zaki ga yarda ake ɓarin kuɗi kyace ba'a talauci a nigeria, musamman ma ace bikin sarauta da sarauta ce ta haɗu, to ina faɗa miki in aka tashi kai lefe hatta bayin gidan sai an yi musu sutturu an kuma basu kuɗaɗe. kinga lokacin bikina dangin Mamana sai da suka dinƙa cewa ko dai siyar da ni akayi. yanzu dai ai zaki ganewa idonki tunda muna tare, in bikin Ilham ya tashi uban kayan da zaki samu sai kinsha mamaki, har sai kin kyautar kema".
tun farkon fara labarin Fillo batai magana ba, har BoÉ—ejo ke cewa ko tana ciwon baki ne, amma haka kawai da taji ta ambaci sunan Ilham sai ta sami kanta da tambayar,"BoÉ—ejo wacece Ilham?".
Boɗejo tace,"kul Gimbiya za ki ce, ita ɗin ai ƴar me martaba ce, yanzu in a gaban fadawa kika faɗi sunanta haka gatsal ai kin shiga uku, ƙila ma Fulani tasa a ɗaureki...ita aka sakawa sunana ai shiyasa nake masifar sonta, baki taɓa ganinta ba?".
tace,"ban ma taɓa jin sunanta ba".
Boɗejo tace,"kika ce kuma shekararku biyu a masarauta kafin a ƴanta ku ayo nan da ku...ko da yake zai yiwu ɗin ki kasa saninta, tunda uban ita kaɗai ce baya so, tun tana ƙarama ya kaita can ƙasar arna bata dawo ba sai da ta shekara biyar".
Fillo tai shiru ita dai ƙirjinta sai bugawa yake haka ɗaya babu gaira babu daɗi, wayar Yami dake soke a gefen zanenta tayi ƙara, tai banza da kiran har ya katse, lokaci ɗaya taji sabon ɗaci da ɓacin rai a zuciyarta. sanda kira na biyu ke ƙara shigowa sai taji kamar ta rotsa wayar, Boɗejo dai nata zuba labari tausar ƙafa yayi mata daɗi.
can dai ta gaji tana kallon Fillo tace,"ki ɗaga wayarki mana, anata kira kin sha re, yanzu fa idan samuwa ce shikenan kin yiwa kanki. haba ƙila ma ba lafiya ba tunda kika ga kiran yayi yawa haka, kusan sau shida fa ina jin ma ko bakwai".
Fillo ta ciro wayar hawaye na sakko mata, tabi sunan Amir dake jikin screen da kallo. maganar Kaka ta ɗazu ta haska acikin kanta,_"ni dai kawai in har na isa dake to komai da ya faru tsakaninku ya wuce daga nan inda kike, in kuma ban isa dake ba zan gani. kuma insha'Allahu nima zan juya miki baya ata dalilin hakan, wallahi sai na nuna miki ban taɓa saninki ba, kallo wannan sai ya daina shiga tsakanina dake balle har ki samu ikon ci gaba da zama tare da ni"._
ba don waɗannan maganganun da Kaka ta faɗa mata ba, da idan ta ƙara sauraron Amir a rayuwarta shegiya ta ke, ai me zuciya akewa gori ba mai dukiya ba.
tana ɗaga wayar ba tare da ta amsa sallamarsa ba tace,"ba ta gate ɗin ɓangarenmu ba, main gate na gidan". tana faɗar hakan ta kashe wayar ta cillar tana ɓata fuska.
ta yunƙura zata tashi tana cewa da Boɗejo,"zanje Yayana ne yazo yana ƙofar gida".
Murmushi ya sauka a fuskar Boɗejo tace,"Allah sarki, to gaida shi dan Allah. ki buɗe friedge ki tafi masa da fura tana cikin gora, jiya Nihal ta dama min ita da daddare, akwai inibi ma duk ki haɗa masa da shi, ko kuma zaki shigo da shi ciki ne?, ko can ɓangarenku ɗin zai je?, a'a kinga ma kawai shigo da shi nan ɗin mu gaisa, yanda kike da mutumci ai dole a mutunta baƙonki".
ta girgiza kai tace,"a'a BoÉ—ejo sauri ma yake ai, ba zai shigo ba na sani".
BoÉ—ejo tace,"to É—aukar masa abin sawa a baki ki kai masa, ba kyaje haka ba gaskiya hannu na dukan cinya".
ba yanda Fillo ta iya haka dole ta É—auka Furan da inibi saboda takurawan da BoÉ—ejo tayi mata, amma tana fitowa ta bawa me gadi, dan da dai ta bawa Amir gwara ta zubar a kwata, hakan kuma babu kyau.
ta jima tsaye bakin ƙofar gate ɗin kamin tasa ƙafa ta fita saboda bala'in zafin da zuciyarta keyi mata, dole ta fara controlling kanta kamin ta fita.
daga can ƙarshen katangan gidan ta hangosa tsaye jingina akan machine, ta tsaya taƙi ƙarasawa wajen sai shi ya ƙaraso inda take. bata jin zata iya ɗaga ido ta kallesa hakan yasa yana kusantota ta rufe ido da hannunta tana ƙara yin ƙasa da kanta.
Amir na ƙarasowa gabanta sai ya zube a gabanta yana sa dukkan gwiwoyinsa a ƙasa, ya haɗa hannayensa wuri guda alamar roƙo, cikin muryar dake bayyana dana sani da ɗumbin nadama yace,"dan darajar Allah da manzonsa kiyi haƙuri ki yafe min abinda nayi miki, nasan nayi kuskure kuma na karɓi hukuncin da kika min. amma horarwa ta isa haka, da nisanta ni da kanki da kike wallahi tallahi gwara kice na kwanta a akan titi mota tabi ta kaina, and am giving you full assuarance of zanyi hakan domin ba zan iya ci gaba da rayuwa babu ke a tare da ni ba...i know halina ba zai sa ki yafe min ba, but ki ji tausayin Uwar da ta mallaki ɗa guda ɗaya, wannan ɗan nata kuma ya kamu da son mace guda ɗaya, wanda son nata zai iya zama ajalinsa, ita kuma uwar bata so ta rasa ɗanta, ki kwatanta yanda wannan uwar dake son ɗanta zata ji in har ta rasa shi...kiyi haƙuri, kiyi haƙuri, dan Allah da Annabinsa Halima".
kuka ya kubcewa Fillo, ta sauke hannunta daga fuskarta, ta buɗe idonta a hankali tana sauke su akan Amir, da tsananin mamaki ta ɗan ja da baya saboda ganinsa durƙushe a gabanta yana hawaye, kallonsa take sosai tana ganin yanda hawaye ke sauka kamar an kunna famfo.
bata san sanda tace,"na fa yafe maka". ta faÉ—a tana turning around gudun kar wani ya gansu.
Amir bai motsa ba still duka gwiwoyinsa na ƙasa yana hawayen so, jin zuciyarsa yake kamar zata faso ƙirjinsa, anya zai iya ci gaba da rayuwa babu Fillo?.
tana kallon gefe tace,"ka tashi kar wani yazo ya ganka".
acikin muryar da ta jiƙu a maye na so yace,"mene aciki dan wani yazo ya ganni durƙushe a gaban wacce nake ƙauna duk duniya bayan uwata?, ko ban miki laifi ba ni me zube gwiwoyina gabanki ne balle kuma na aikata laifi. Halimatuna ba zan taɓa miƙewa daga nan ba har sai kin dubi hawayena, ko da zaki shiga gida ki barni haka".
Fillo ta ƙara waigawa ko'ina bata ga kowa ba, muryarta a ƙasa tace,"Amir na haƙura, in ban haƙura babu abinda zai fito da ni wajenka".
ya ɗago da sauri yana kallonta, yana ganin yacca hawaye ke sunturi akan kumatunta, sai yaji zuciyarsa ta ƙuntata sosai, yaji wani mugun sonta ya ƙara kamasa, ji yake ina ma there is chance ɗin da zai iya hugging nata da yayi hakan, sai dai babu wannan damar, but he will use another chance yaga ya tsayar da zubar hawayen, to make sure ya goge wannan dattin baƙin cikin da ya haddasa mata.
dan haka sai ya dinƙa jan gwiwoyinsa akan ƙasar wanjen har zuwa gabanta, yasa hannu ya riƙe siraran ƙafafunta da suka shige cikin tafin hannunsa, yace,"kiyi haƙuri don Allah, na tuba ba zan ƙara aikata kuskure makamancin haka ba".
a hankali tace,"Amir na haƙura fa". ya girgiza kansa da cewar,"zubar hawayenki na shaida min baki haƙura ba, kuma baki yafe min ba, kiyi min rai ki daina bari hawayenki na zuba a ƙasa, wallahi tallahi ina jin kamar za'a zare raina ne".
tasa hannu ta goge hawayenta tace,"na haƙura Allah kuwa". ya miƙe yana murmushi, suka haɗa ido tana jin kamar ba zata iya sakin nata murmushin ba, sai dai kuma ƙwayar idonsa da ta shiga cikin tata ta dagargaza alwashinta, taji ba zata iya yi masa komai ba, dan haka ta sakar masa sanyayyan smiling ɗin da sai da Amir ya nemi bango ya dafe.
tai masa harar wasa tana faÉ—in,"duk ka wahalar da ni".
ya kafeta da ido murmushin kan leɓensa yaƙi ɗaukewa, ya bar jikin bangon ya matso kusa da ita sosai har tana jiyo numfashinsa da bugawar zuciyarsa, yay ƙasa da murya sosai saitin kunnenta yace,"please can i hug you?, just a little, don't say no plsss".
da sauri Fillo ta ɗago kanta ta kallesa, taga yanda idanuwansa suka sauya kala, tai saurin juya masa baya tana jin wani irin kunya na rufeta. ganin zata gudu yay saurin riƙo hannunta ya janyota yace,"in baki juyo ba da gaske zanyi hugging na...". ai bai ƙarasa ba ta juyo da sauri tana kulle idanuwanta.
rufe idon nata kuma ya bawa Amir damar ƙare mata kallo tas, ji yake kamar ya ɗora lips ɗinsa a nata, kamar ya tsaga ƙirjinsa ya ɓoyeta aciki, kamar a barsa daga shi sai ita a wannan duniyar, he can't even imagine kalar soyayya da tarairayan da zai nuna mata idan suka yi aure.
a hankali yace,"buÉ—e idonki ki faÉ—a min ni dake wa yafi wani wahala da har kike faÉ—in duk na wahalar da ke".
cike da kunya ta buÉ—e ido tana tura baki gaba tace,"ka sakar min hannu a waje fa muke".