← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 176

Sashe 41

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tun da Kaka taga ta shigo É—akin a fusace tai shiru bata tanka mata ba, tana kallo ta wurgar da dardumar da É—ankwalin tai cikin É—aki da qur'ani a hannunta, ko sallama ba tai ba.
Kaka ko ta girgiza kai a fili tana faɗin,"Allah ya shiryaki, banda me ƙaunarki wane zai miki wannan gatan na ɗaukar ɗawainiyar yi miki karatu kullum, karatun ma na qur'ani, kuma ba biyansa kike ba, ya kashe uzurinsa da lafiya ko babu yazo ya koyar dake, shi ɗin ma dai da zai iya kenan, idan wani ne tuni bai rabu dake da wannan halin naki ba...kina asibiti yaron nan sai daya zama kamar marayan da bai da gata".

Maijidda ta shigo bakinta ɗauke da sallama, Kaka ta amsa mata. a tunaninta ko Fillo bata dawo daga karatun da take ɗauka a wurin Amir ba ne shiyasa ma batai maganarta ba. ta zauna nan kusa da Kaka suna hira, Kaka tace,"ke ni fa tunda muka baro asibiti lissafin karɓar aikinmu ya kubce min, Yami bata ce miki komai ba?".

Maijidda tace,"ku zaku karɓi na rana yau, amma naji kamar Yami na cewa ma yau ba za'ai girkin sadaqa anan ba, daga can masarauta za'a kawo".
Kaka tace,"ohh ke haka ne fa, jiya Hajiya ta aiko a faÉ—a mana kinga na manta".

suna hirar Maijidda na duba agogo tana kallon ƙofa da jiran shigowar Fillo, amma ganin har tara da rabi ta wuce bata shigo ba yasa tace da Kaka,"Fillo daga wurin karatun zata wuce aiki?".

Kaka tace,"ai zatona faÉ—an ma dake akai da naga baki yi zancenta ba". Maijidda tace,"a'a ba muyi faÉ—a ba, me kika gani Kaka?".
Kaka tace,"tun É—azu fa ta dawo daga wurin karatun, tana shigowa ta shige É—aka bata fito ba, Allah masanin fushin nata".
Maijidda ta miƙe da azama tayi cikin ɗakin, tana shiga taga Fillo tsaye ta kifa kanta da bango, jikinta sai karkarwa yake yi. haka take ita, indai ranta ya ɓaci duk haƙuri da lallashin da za'a mata ba zasu yi tasiri ba sai tayi kuka ko kuma tayi masifa, idan ba haka ba ba zata huce ba, haka ba zata kwana a tsaye ne tana ta fizgar numfashi da karkarwar jiki, babu me iya controlling ɗinta.

Maijidda ta kalli wayar hannunta dake ringing, tunaninta ko Dr Yusuf ne ya ƙara kira dan sau biyu yana yana kira a safiyar nan yana cewa ta haɗasa da Fillo tace masa bata dawo daga wurin karatu ba, to sai taga ma ba shi bane Amir ne.
ta kalli Fillo ta kalli wayar, ya zatayi dole masifar dai akanta za'a juyeta ta sani, ai ba yau farau ba, tasan halin Æ´ar'uwarta, idan tana cikin irin wannan yanayin ko magana bata so ayi mata, ita kuma ba zata iya barinta haka ba tunda Kaka ba sauraronta za tai ba, in akai haka kuma Fillo da wartsakewa sai dai gobe.

"Fillo wai menene?, wa ya ɓata miki rai?". Maijidda ta faɗa. Fillo tai shiru ba motsi balle amsa. ta ƙara cewa,"to kiyi haƙuri kinji, fushi fa na abokan sheɗan ne, ki zauna muyi kukan tare to, ni bana son ganinki a haka Allah". Maijiddan ta faɗa in breaking voice.

nan ma dai babu amsa babu motsi. hakan yasa Maijidda ta dafata,"ni ce fa nake baki haƙuri Fillo, Hassanarki, Hussaina Hassanarki ce fa, ko kina so na mutu ma barki ke ɗaya?".

Maijidda dai kamar me magana da gawa ko kuma gunki, ta yarfar da hannu kamar zatai kuka, ta ƙara kallon kiran Amir dake shigowa a karo na uku, ta dafa kafaɗar Fillo zata juyo da ita tana cewa,"kinga fa Amir ne ke ta kiranki, kar...".

ai bata ƙarasa ba Fillo ta ɗago a harzuƙe cikin fusata tai wurgi da hannun Maijidda dake kan shoulders ɗinta, wayar Yami ta faɗi a ƙasa ta wargaje, ƙashin hannun Maijidda yay wata ƙara kamar an karya shi.

a zafafe kuma cikin amon muryar da ya cika ɗakin Fillo ta ce mata,"dilla Malama ki rabu da ni, ki ƙyaleni, babu ruwanki da ni, ki matsa daga kusa da ni in ba haka ba duk abinda na miki ke kika jawa kanki".
tana faɗin hakan kuma sai ta fashe da kuka, Maijidda cikin jin zafin hannunta ta matso ta rungume Fillo, sai suka durƙushe a ƙasan wajen, sosai Fillo ke kuka Maijidda kuma na tayata, Kaka dai na daga falo tana jinsu bata bi ta kansu ba.

sai da aka ɗan ɗau lokaci sannan Fillo ta fara samun sauƙi cikin ranta, har daga ƙarshe ma ya zama ita ke lallashin Maijiddan. itama kuma a sannan sai taƙi yin shiru, taci gaba da zubar da hawayenta a kafaɗar Fillo.

Fillo na shafa bayanta tace,"ke Hassana wai mene haka, ki daina mana". Maijidda tace,"to ai kece, na faÉ—a miki bana so kike bari ShaiÉ—an yana tasiri akanki akan fushi".
Fillo tace,"to ba na daina ba, idan kuma ba zaki shirun ba sai mu ci gaba dan kin san dai ba zan zuba ido kina kuka ina zaune ina kallonki, zuciyata ba zata É—auka ba".
Maijidda tace,"nima ai baki saurareni ba a farko har ma kika ji min ciwo". ta faÉ—a muryarta na daÉ—a bayyana kukan da take yi.
muryar Fillo ta karye tace,"to kiyi haƙuri, idan kuma ba zaki daina ba shikenan sai mu fasa auren miji ɗayan".

sai a lokacin Maijidda ta ɗago suna gogewa junansu hawaye, Kaka na daga falo tace da su,"ke Maijidda kin san dake za'aje gidan sarki ko, ke kuma idan kinga dama ki fito kije kiyi musu aikinsu, in ba za ki ba kuma ki faɗa min sai na miƙe".
Fillo tace,"to Hajiya Kaka gamu nan".

sai da zasu fita sannan suka lura da aika-aikar da suka yiwa Yami, Maijidda tai salati tana rufe baki da faÉ—in na shiga uku. Fillo tace kin shiga uku ko mun shiga uku, yau akan akwalar wayar nan Yami ba sai ta cinyemu a É—anyanmu ba.
Kaka da ta jisu tace,"zan kuwa faÉ—a mata".
hannu na rawa Fillo ta É—au wayar tana haÉ—eta suka fito falo.

"yanzu Yami sai tace mun cuceta mun datse hanyar da zasu ke gaisawa da bazawarinta". 
Maijidda ce ta faÉ—a, Kaka tai dariya, Fillo dai duk ta tsure sai É—aure kyauraye takeyi, fatan ta É—aya tana É—ora batirin wayar ta tashi.

bakinta faɗi yake,"kece me Jidda ki kai magana da ƙarfi, da Kaka bata ji ba ai sai mu ajiye a kusa da ita bata sani ba muyi ficewarmu, Yami ba zata ce komai ba ƙarƙari tace da Kaka Ƙawata to ya za'ai babu komai ai, da saninki ai ba zaki fasa ba". ta faɗi maganar tana kwaikwayon muryar Yami.

su duka sukai dariya, kuma cikin sa'a tana saka batirin ta kunna sai ga wayar ta kama. a tare suka sauke ajiyar zuciya. lokacin kira ya shigo da sabuwar lamba, ta miƙawa Maijidda tana miƙewa. ita kuma tace da ita,"ki ɗaga Dr Yusuf ne, tun safe yake kira wai na haɗaku, yama dai ce na masa kwatancen gidan nan nayi masa, ƙila ko zuwa zai yi".

Fillo ta harareta tace,"yazo yayi me?". tace,"haka nace miki zai zo?, ce fa nayi ƙila zuwa zai yi, ki ɗaga kiji koma menene daga bakinsa".
ta aje wayar a cinyar Maijidda ta tashi sai Kaka tace,"babu kyau dai wulaƙata mutum, musamman wanda ya taimaka maka a rayuwa, ba masu gidan nan ne kaɗai suka taimaka miki ba, harda shi likitan, dan shima ya bada jininsa an zuba miki".

Fillo na ɓata fuska tace,"to Kaka yanzu sai kiji yace ai wani magani ko wata allura ya kawo".
Kaka tace,"to ki É—aga mana kiji dai me zai ce tunda ya neme ki, in allurar ce tunda ba shi ne zai yi miki ba ai sai kin so za'ai, abu da kece Halimanki, tun kan ki shigo nan zaki jefar da ita, sai kace kwanciyar asibiti tasa kin manta wacece ke".

ba dai haka Fillo taso ba, sai dai bata son jayayya da Kaka, ta karɓi wayar ta ɗaga, tana yin sallama Yusuf ya ɗauki muryarta. daga cikin motar da yake ya kwantar da kansa jikin kujera sannan ya amsa sallamar.
Fillo tace,"ina kwana, ya kake?". maimakon ya amsa mata sai taji yace,"ai na shanyu har na bushe, daka ni kawai ya rage ayi".

taso yin dariya amma sai ta maze tace,"kaman ya?". yace,"kamar yanda Sister ɗinki bata faɗa miki ba, na kirata nace zanzo na duba jikinki before na bar gari tace min to, ta ban address kuma nazo inata kiranta taƙi ɗagawa, at the end ma sai ta kashe wayar, nayi zuciya zan tafi kuma sai na tuna da saƙonki nace to lallai ko zan kwana anan ba zan tafi ba".

bakin Fillo a gaba tace,"saƙon me?, kuma ai ba daidai tayi maka kwatancen gidanmu ba".
yay murmushi yace,"tambaya har guda biyu a jere, duk ranar da kika zama lauya ai sai ki ɗaure mutum. to da fari dai address daidai aka ban, domin kuwa gani a ƙofar gate ɗin gidan Alƙali Dikko, kuma gate na ɓangaren ma'aikatan gidan, gani ina kallon me gadi baƙi ɗan lukuti kamarki. saƙo kuma sai kin fito kya gani".

da ƙosawa tace,"na san saƙon allura ne kuma bana so kuma ma bama gidan mun tafi ƙauyenmu, sai ka tafi".
cikin kwaikwayon muryarta Yusuf yace,"kuma ma ba allura kaɗai bace harda magani, kuma ma da wuƙar farke ciki, kuma ma me gadi yace min kuna nan ba kwa fita, kuma ma ba zan tafi ba har sai kin fito".

a wannan karon dai sai da sautin ƙaramar dariyar Fillo ya fito, Yusuf ya gyara zamansa yana sosa kansa wanda yasha sabon aski yace,"kinga Malama ki fito kawai nai miki tiyatar nan a wuce wurin, ni ban haƙura ba har yanzu nafi gane ai miki bakinki acikinki sai a ɗinke wannan bakin tsiwar da Maijidda tace yana isarsu".

tasa hannu ta rufe fuskarta cike da kunya, sai kuma tace da shi,"to ka shigo kawai me gadin ba zai hanaka ba, sai kace masa wajen Kaka kazo".
Yusuf ya kalli gate É—in sai kuma yace,"a'a dai ki fito É—in kawai, ba jimawa zanyi ba akan hanya nake". tace,"tom".
Chapter 41 · 0% Book details