← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 176

Sashe 54

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zuwa lokacin tayi kuka ta gode Allah. muryarsa a tamke ba tare da ya duba irin zafin ciwon da take ji ba yace,"tashi ki gyaran waje, saura ki ƙara saka hannu tunda baki da hankali".
ta miƙe sai sheƙar kuka takeyi ta ɗauko tsintsiya ta tattare wajen. tana kammalawa ta nufi ƙofa zata fita taji ya ƙara saka key ya kulle.

"na gama ai". ta faÉ—a tana kallonsa a É—arÉ—arce. ba tare daya kalleta ba yace,"kin san tsadar turaren da kika fasa?".
da sauri ta girgiza kai tace,"a'a, amma don Allah kayi haƙuri bada sani na bane".
ya É—auke idonsa daga kan wayarsa ya É—ora akanta sannan yace,"balle ma da saninki kika fasa É—in, dan haka abu É—aya na san da shi sai kin biyani turarena, kuma a yanzun anan wajen ba sai anje ko'ina ba, if kika biyani sai ki sami damar fita daga room É—in nan".

maganarsa yasa ta ruɗe ta shiga ba shi haƙuri tana roƙonsa. tayi mugun basa tausayi amma ya ɗauke kansa kamar baya jinta.
wucewar mintina biyar sai yaji shiru ɗakin, kukanta ya ɗauke kamar ɗaukewar ruwan sama, tun before ya juyo da kansa ya kalli bakin ƙofar ya fara tunanin ta yanda akayi ta fita after yasa key, sai dai yana juyowa ɗin sai ya ganta ta ɓingilar da kanta ajikin ƙofa baccin kuka ya ɗauketa kamar jaririya.

zai iya cewa bai san lokacin da leɓensa ya tale da murmushi ba, banda yasan abubuwa da dama ba, to tabbas zai rantse wannan rigimammiyar yarinyar ba itace hatsabibiyar dake cusa kanta cikin haɗarin da ba nata ba.
ya jima yana kallonta a hakan, matsawar ya barta ta ɗauki tsawon lokaci tana bacci a haka wuyanta sai yayi ciwo sosai saboda yanda ya barƙale, hakan yasa ya sakko a gadon yazo ya ɗauketa ya dawo ya kwantar da ita akan gadonsa, yaja blanket ya rufeta yana jin zuciyarsa na matsewa.

for few minutes yana daga kishingiɗe ajikin pillow daga ɗayan side ɗin, tunani kawai yake yi kala-kala acikin ransa, daga bisani ya miƙe ya bar ɗakin, yana fitowa yaci karo da Bello na niyyar shigowa, ganin junansu yasa duk suka ɗaure fuska.
Bello na ƙoƙarin ya ture shi ya shiga room ɗin, shima Turaki na ƙoƙarin ya turasa baya ya nuna masa hanyar da ta fi dacewa da shi.

"Malami ban hanya". Bello ya faÉ—a cikin tamkewar fuska yana sa hannu ya ture Turaki gefe, ya murÉ—a handle ya shiga bed room É—in.

sai dai yana shiga ya fito da sauri yana dakatar da Turaki daga tafiyar da yake yi zai sauka daga benen. "Turaki me nake gani a É—akinka?".

a fusace Turaki ya juyo yace da shi,"uban wa ya kai ka shigar min É—aki dama?".
shima Bellon a fusace yace,"da sai da izininka nake shiga?, ko kuma dama Baffa ce yayi É—akin naka ne kai É—aya?...ba wannan ne a gabana ba Muhammad, faÉ—a min me na gani a É—akinki?, warware min komai tun ban fara shakku akanka ba".

Turaki yaja tsaki ya sauka a benen ba tare daya ce masa komai ba. Bello yayi ajiyar zuciya yana sa hannu a aljihu ya É—auko wayarsa ya kira lambar Zaytuna.

*Masarauta Kaltungo.*
"nifa duk bayannan naki a banza nake jinsu, shekaru ba su zasu hanani cimma alwashin dana É—auka ba Jakadiya, tunda har naga bayan Ramla to babu abinda zai hanani ganin bayan Madina, ki rubuta wannan ki ajiye, ko bayan raina zaki faÉ—a cewar ni Fulani nace duk wata mace da Dikko zai aura rayuwarta a hannuna take".

furucin da Fulani tayi kenan a sanda idanuwanta ke sauka a ƙasa, tana jin zuciyarta na zafi da tafarfasa, tana jin yanda zuciyarta ke kuka, kukan da ta ɗauki tsawon shekaru masu yawa tana yi kuma har yanzu bata daina yinsa ba.

ƙafarta kawai take kallo wadda tasha adon sarƙa na gwalagwalai da azurfa, kallon ƙafar tata take yi a zahirance, amma a baɗini ƙafar Alƙali Dikko take kallo, ƙafarsa take kallo tana tuno yanda ta riƙe ƙafafunsa a wancan lokacin tana roƙonsa akan kar ya rabu da ita ya aureta ko da bayan auren zaisa wuƙa ya kasheta, da kuma yadda ya fizge ƙafafunsa ya fita daga ɗakin ya barta ba tare da ya waigo ya kalleta ba, waigen kallon da bai ƙara yi mata ba har yau tsawon shekaru 37, duk da kasancewarta matar Yayansa Mai Martaba Hashim.

ta rumtse idonta sosai tana jin zafi a zuciyarta, ganewa ne kawai mutane ba su yi ba, amma zafin so yafi ƙarfin kwatance, ita zata iya cewa zafin so yafi zafin wuta zafi da raɗaɗi, muddin wanda kake so bai bar tasirantuwa a zuciyarka ba. Allah ya sani har duniya ba zata taɓa daina son Alƙali Dikko ba duk da cewar akwai igiyar auren wani akanta, auren ma da har suke da rabon ƴa a tsakani, ƴa me shakaru 21 a duniya, son Alƙali Dikko ba daga gareta bane, so ne daga Allah.

taja wani dogon numfashi ta sauke, a sannan ta buɗe ido ta sauke akan ƙaton tray ɗin dake gabanta.

Jakadiya Haulat tace,"ranki ya daɗe ki ƙara haƙuri akan wanda kike yi, Allah ya huci zuciyarki uwar gijiyata...yanzu kamata yayi kisha furar nan domin ki samu kiji sanyi a ranki, tun safe babu abinda kika sa a bakinki...batun Hajiya Madina da Ɗan Ramla tamkar tsoma allura ne acikin ruwa, kisa a ranki lokacin kawar da su daga rayuwar Alƙali Dikko yazo ƙarshe, zasu barshi kamar yanda Ramla ta barsa".

Fulani tayi murmushin takaici me ciwo, sannan ta ɗago ido ta yiwa Jakadiya kallon tsab kafin nan tace,"ban taɓa yin wani shiri akan Madina ba, kasantuwar nasan Dikko ba sonta yake ba, zatona a lokacin Mai Martaba zai sawwaƙe min daga nan sai na maye gurbin Ramla, ashe duk lissafin da nayi akan hakan da ƙazamin tunani nayi shi...dukkan wani shirina ina yinsa ne akan ɗan Ramla, shirye-shiryen da nayi akan na tarwatsa yaron nan yafi ƙirgen yatsu, sai dai har yanzu na kasa ganewa Jakadiya, na kasa fahimta, na rasa dalilin da yasa cikin tarin ƙullin da nayi akan Turaki babu wanda yay tasiri, amsa ɗaya nake so daga bakinki ba daga bakin boka ba, haka kuma abu ɗaya nake so na sani daga wajenki ba daga wajen boka ba, meke warware aikin Malam?, menene ke warware duk wani ƙulli da nayi?, waye yake lalata min dukkan shirin da nayi?".

sai kuma ta miƙe tsaye a fusace, ta ɗaga murya cikin tsawa tana nuna Jakadiya tace mata,"faɗa min gaskiya, kina aiwatar da aikin da na saka ki ko kuma cin amanata kike yi?".

cike da tsoro da rawa jiki Jakadiya tace,"wallahi, wallahi Ranki ya daɗe ina sawa a aiwatar da duk abinda kika ce, wallahi kuma ko kaffara ba zanyi ba waɗanda na saka suyi ba zasu ci amanarmu ba, ni kaina ina matuƙar mamakin yanda komai ke warwarewa acikin sauƙi, sai dai ina tunanin ƙarfin adu...".

ai tun Jakadiya bata ƙarasa ba Fulani ta ƙara ɗaga murya wajen dakatar da ita acikin tsananin fushi da ɓacin rai,"dakata munafuka, tabbas sai naga bayanki Jakadiya domin babu wanda yake cin amanata na ƙyale shi...karki ƙara buɗe baki kice zaki faɗa min zancen banzan da ba yarda zanyi da shi ba, ƙarya kike yi kice tasirin adu'a zai karya aikin asirin da nake ɓarnatar da kuɗi akai, aikin boka tumbutsu ne ba aikin wani galhonaho ba, bokan da yake aiki tamkar yankan wuƙa, kuma tunda har aikinsa yayi tasiri akan Ramla ƴar Turakin Taraba, bana tunanin aikinsa zai ƙi cin wani tsiyatattan halitta Turaki, don haka kamar yanda na ɗauki alwashin ganin bayan Madina da Turaki a wannan ƙarnin, haka kema sai naga bayanki Jakadiya tunda har kika ci amanta".

Jakadiya ta zube gwiyoyinta a ƙasa ta shiga roƙon Fulani cikin tsananin ruɗewa, ana cikin haka Ilham ta turo ƙofar ɗakin ta shigo. cike da shagwaɓa ta faɗa jikin Fulani ta sakin kuka da cewar,"dan Allah Mami ki barni naje, Allah ba zan jima ba zan dawo...sau biyu kenan Hammah Turaki na ciwo bana zuwa na duba shi, kuma yana ta min complain ɗin hakan".

Fulani ta tureta daga jikinta, ta fita rai a ɓace daga turakar tata. Ilham ta buta da kallo kafin daga bisani ta zube akan gado tana sakin kuka.
tana cikin kukan wayarta ta shiga ringing, ta ɗau wayar tana kallon screen ɗin, ganin sunan Turaki na yawo a jiki yasa ta sakin wani kyakykyawan murmushi sannan ta ɗaga tana cewa hello cike da shagwaɓa.

daga ɓangaren Turaki ya sauke ajiyar zuciya sannan yace,"ba ki damu da lafiya ba right?".
Ilham ta ƙara narkewa da muryar shagwaɓa tace,"Hammah yau zan zo insha'Allah".

Turaki yace,"ba sai kin zo ba, ni gani na zo. ina ɓangaren Abbas...but ba zan jima ki hanzarta".

*Comment, Share and Vote.*
[8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*©️Halima h.z*

_not edited._

*27*
Fillo ce zaune akan dakalin bayan É—akinsu, daga yanda ta zabga tagumi kasan tunanin wani abu takeyi wanda ke damun ranta.
ƙwayar idonta ta kaɗa tayi jajir, idon kuma ya ƙara girma. Maijidda ta ƙaraso wajen tana faɗin,"na tsani wannan tagumin naki wallahi".
Fillo ta ɗago ido tana kallonta, bata iya cewa komai ba saboda zafin da zuciyarta ke yi mata, tun ɗazu take so tayi kuka ko ta sami relief amma kukan yaƙi zuwa.

"kwana nawa kina kuka?, zatonki kuka na maganin damuwa?, to idan baki sani ba kuka baida amfanin komai, damuwarki ya wuci ki kaita gaban Allah, akwai me yaye miki sama da shi ne?, amma sai kiyi ta faman kuka kuma ayi tambayar duniya kiƙi magana, da me kike so Kaka taji?, bafa isassan lafiya ke gareta ba. kuma ke har me kika nema kika rasa a duniyar nan da zaki ɗau damuwa kisawa ranki kina ƴar ƙaramarki, salon dai jawa kai matsala".

Maijidda tayi shiru a sanda taji Fillo ta riƙe hannunta gam, tasan ba komai bane illa kukan da take so tayi, ta janyo Fillon jikinta ta kwanta a kafaɗarta, tuni kukan da Fillo ke jira tun ɗazu yazo mata, saida tayi me isarta tukunna ta yakice daga jikin Maijidda tana goge hawayenta.
Chapter 54 · 0% Book details