← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 176

Sashe 93

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a taƙaice dai Maama da iyalanta duk sai suka manta da batun wata Fillo saboda tsabagen farin cikin da suke a ciki. kuma haka suka zama ababen kallo a wajen dan tuni akai caa akansu ana kallon ikon Allah.
gaba É—aya sun cikwikwiye Hajiya Ramla sun kasa jin ma abinda ta-ke cewa na,"ina da patient kuyi a hankali". but inaa duk wannan batu da take yi babu wanda ya jita hatta Turaki dake manne a jikinta.

kuma a lokacinne Kaka suka shigo ita da su Yami da Khalil waɗanda yaje ya ɗauko daga asibiti, sai dai me?, zuwan su wajen kawai suka ga Fillo a guje ta fito tana ƙwala kiran,"Kaka ga Ummina, Kaka Ummina ta dawo".

*Vote, Comment, and Share.*
[8/31, 01:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

_😂😂yau dai ina typing ina gyangyaɗi, so duk baragadar da ku ka ci karo da ita ku gyara da kanku kawai🤣🤣._

*37*
gaba ɗaya Fillo sai ta rikice ta firgice ta nemi fita a hayyacinta, ba don komai ba sai dan tsananin murna da kuma mamakin ganin mahaifiyarta a lokacin da bata tsammata ba, tsabar farin ciki ji take kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. ganin komai ta ke yi tamkar mafarki ko kuma ba daidai take gani ba, lokacin da ta farka da matsanancin ciwon kai ta tashi, amma buɗe idon da zata yi ƙwayar idanunta suka sauka akan Ummi dake zaune a gefenta ta kama hannunta ta riƙe tana hawaye.

da farko tai zaton gizau idonta yay mata, dan haka tai saurin maida murfin idonta ta rufe sannan ta ƙara buɗewa, kuma a wannan buɗewar ne ta tabbatar da abinda ta gani ɗin gaskiya ne, Umminta ce a gabanta, wannan macen da tafi gwal, tafi zinare, tafi lu'u lu'u girma da daraja, wannan macen ce da bata da tamkarta a duniyarta, tauraruwar da ke haska duniyarta, mahaifiyarta ce mafi soyuwa a ranta, jarumar da tai fama da rainon cikinta tsawon watanni tara, jarumar macen da ta tsaya tsayin daka akan ibadarta da iliminta da kuma tarbiyarta, jarumar macen da ke sadaukar da farincikinta domin ƴaƴanta, jarumar dake ɓoye zafin ciwon rashin lafiyarta gudun tashin hankalin ƴaƴanta, jarumar uwar da ta kan iya haƙura da loma ɗaya na abinci da zata sa a bakinta ta rabarwa ƴaƴanta, tabbas itace, ba zata mantata ba ko da ace tana cikin ciwon hauka ne, har a naɗe duniya ba zata kasa gane ɗumin jikinta ba, ba zata manta wannan farar fuskar da bata iya bacci ba har sai ita tayi, abu ɗaya da ta san yake dahir shine uwa dabance, daban take da kowacce irin halitta a duniya, soyayyarta dabance da ta kowa, ƙaunarta ma haka, mahaifiyarta itace ranta itace jininta itace duniyarta.

hawaye ta dinƙa ji yana bi ta gefen fuskarta, dama tasha faɗawa Kaka cewar Ummi bata mutu ba tana raye, kuma da izinin Allah zamu gana da ita, sai ga shi yau ta ganta, sai ga shi ta ganta a ranar da wani macuci, azzalumi ya dasa baƙin ciki a zuciyarta wanda ba zai taɓa gogewa ba, to mai ma zai ci gaba da zamar da wannan baƙin cikin alhalin ga mahaifiyarta ta dawo a sanda take tunanin babu me iya share mata hawayen baƙin cikin da Amir ya haifar mata?, ai babu wani sauran baƙin cikinsa kuma, ta san in ace bata sami ganin mahaifiyarta ayau ba, to tabbas baƙin cikin abinda Amir yayi mata shi zai zama ajalinta.

zata iya cewa bata san lokacin da ta yunƙura ta miƙe zaune ba daga kwancen da take, jinta tayi kawai ajikin Ummi tayi mata wata tsatstsaurar runguma, Ummin ma ta kewayeta da dukkan hannayenta tana daɗa matseta a jikinta, Fillo taji saukar wannan ɗumin na daban wanda ajikin uwa kawai aka halicci yana ɗumama jikinta, tana jin wannan soyayyar mahaifiya ta daban tana ratsa jini da sassan jikinta, sai kawai suka fashe da kukan farin ciki a tare, babu wanda ya lallashi wani acikinsu har sai da suka yi me isar su tukunna.
cikin muryar kuka tace,"Ummina ina sonki sosai".

kuma abinda taji Ummin ta fara ce mata shine,"Auta wa ya kawoki nan garin?, me ya sa me ki haka?". ta tambayeta É—in tana janyeta daga jikinta tana dubanta, tana yi mata kallo me cike da tausayi da kuma fargabar abinda bata fatan ya kasance a rayuwar Æ´arta, domin tasan rashin uwa a tare da Æ´aÆ´anta babu halin da baya jefa su, balle kuma su da basu yi sa'ar uba ba, wanda ko kallonsu ba yayi balle ya kula da rayuwarsu.

a lokacin sai kawai ta faɗa ƙirjin Ummi tace,"Ummi kullum sai nayi kukan rashinki, Ummi ko me nake yi tare dake nake yinsa a zuciyata, Ummi duk sanda naga ƴa da mahaifiyarta sai nayi ta kuka in kasa ko da cin abinci. Ummina me yasa kika tafi inda ba zamu ganki ba?, me yasa baki ci gaba da wannan haƙurin naki ba?, me yasa kika bari takaicin ɗa namiji da baƙin cikinsa yasa kika nesanta kanki da ƴaƴanki da kowa naki?, Ummi kin san kuwa tsananin son da nake miki?, muna fa yi miki so me zafi, Ummi kin san buƙatar rayuwar ƴaƴa shine mahaifiyarsu, amma mu sai kika ƙaurace mana na tsawon shekaru da yawa, Ummi ba kiyi tunanin in ta gayyara ba?, ba ki yi tunanin...".
bata ƙarasa ba Ummi tasa hannu ta rufe mata baki, hawaye na zubar mata tace,"tambayar da nayi miki daban, zancen da kike min daban".

Fillo ta ƙara matseta tace,"kiyi haƙuri Ummina". tace,"ban san amsar tambayata".
Fillo ta rumtse ido tace,"ai tun sanda kika tafi na dawo wurin Kaka. wannan halin da kika ganni a ciki kuma wanda zan aura ne sila".

lokaci É—aya jikin Ummin ya hau kyarma ta É—ago Fillo ajikinta tana bin ta da kallo tace,"ya zamo silar me?, me yay miki?, ina Kakan?". tace,"garkuwa yayi dani Ummi after all na basa dukkan yarda".
ta faÉ—a tana fashewa da kuka sosai, muryar Ummin ta fita a hankali da cewar,"ina fatan bai cuce ki ba?".
bata iya amsawa da baki ba sai Kai da ta ɗaga kawai. anan taji Ummin ta sauke ajiyar zuciya me nauyi, kafin ta furta,"Allah ya daɗa kare min ke, ya kareki daga sharrin duk wani abin ƙi. dan Allah kiyi haƙuri ƴata da abinda nayi muku, ban da bakin ce muku komai domin nasan ni ɗin me laifi ce, amma yanzu na dawo gareku sai mutuwa ce zata raba mu, ina roƙonku dan Allah ku yafe min, ki yafe min Autata".

Fillo tace,"ni ba kiyi min komai ba Ummina".
sai ta ɗago kai tana kallon Ummin tace,"Ummi to ya akai...". kuma karantar fuskarta kawai Ummin tayi ta bata amsa ba tare da ta ƙarasa ba.
"Dr Yusuf, shi ya shigo da ni nan yay min nuni da ke, shine sabon ɗan da Allah ya bani wanda ya kula da ni shi da matarsa kusan shekara guda, ba ƙyama, ba hantara, sun ɗaukeni kamar mahaifiyarsu, duk da ni nayi musu laifi na ɓoye musu cewar ina magana tsawon lokacin da muka ɗauka, haka nayi ta wahalar da su da aikin rubutu a takarɗa kuma basu taɓa ƙosawa ba".

maimakon kallon Ummi sai Fillo ta koma kallon Dr Yusuf, babu ko ƙyafta ido, kenan shisa watarana da yazo hira wajenta yace mata yana ganin me kama da ita sak, in ace zata yarda da ya kaita ta ganta, tave masa ba wani nan wasa yake yi, ashe Umminta ce ma, Umminta ya taimakawa har yake kyautata mata da irin halin karamcinsa.
_"sun ɗauke ni kamar mahaifiyarsu"._ haka Ummin ta faɗa, ƙwarai yau ta ƙara tabbatar da cewa Dr Yusuf na musamman ne, kuma ya zama dole ta saka masa da taimakon mahaifiyarta da yayi, kamar yanda ta san cewa yafi ƙarfin duk wani abu da zata basa, haka bata san irin kyautar da zata yi masa ba domin nuna masa godiyarta, but zata tambaye shi kyautar da yake so tayi masa ko da ace za'a kai ga matakin da sai ta ɗaga zoben azurfarta ta siyar.

Dr Yusuf ya sakar mata murmushi, itama ta mayar masa tana sauke idonta ƙasa tace,"Ubangiji Allah yay maka sakayya da gidan aljannah akan taimakawa Mahaifiyata da kayi, Allah ya rabaka da iyaye lafiya"...haka ta dinƙa jera masa adu'a kafin tace masa,"dan Allah Dr a wurin da ku ka tsinto ni ba kuga wata mata ba?".

Dr Yusuf yace,"ai ba tsinto ki mukai ba, kawo ki akayi". ta ɗan dube shi da mamaki tace,"bai gudu ba?". yay murmushi kafin yace,"ƙanina ne yanzu haka yana waje tare da su Daddy nah, itama matar da kike magana tana waje, ƙila zuwa yanzu ma su Kaka sun iso dan anyi musu waya tuni".

ai rufe bakinsa kenan t a saki hannun Ummi ta diro akan gadon tana ce da Ummi,"ba inwa Kaka albishir".
bata jira cewarta ba ta fito da gudu daga ɗakin tana ƙwala wannan kiran sunan na,"Kaka ga Ummina". ba tare da ta lura da jama'ar da suke cike a wajen ba balle tabi ta kan dalilin da yasa akayi wannan dandazon.

kuma cikin sa'a tana fitowar tayi karo da su Kaka na shigowa, idonta a rufe ta doka wani uban tsalle ta É—afe Kaka tana ihun murna tana faÉ—a mata Ummi ce.
Kaka lamarin sai ya nemi ya bata tsoro dan sai take ganin kamar ko Fillo ta samu matsala ne, ta tafi zata faɗi dalilin ɗafe jikinta da Fillo tayi sai taji an saurin riƙota ta gefe.
Chapter 93 · 0% Book details