Sashe 55
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cikin muryar kukan da bai gama sakinta ba tace,"Maijidda ke kike ganin ban rasa komai ba tunda Kaka ta tsaya min, amma a zahirance ni nayi babban rashi tunda har na rasa uba, ba wai don ya mutu ba, yana raye amma na zama kamar banda uba a raye, tunda uwata ta haife ni ban sami soyayyar uba ba irin wacce ko wanne É—an halak ke samu, ban sami gata ba irin wanda kowanne É—an halak ke samu daga wurin mahaifi, ban samu tarbiya ba daga wajen ubana, ban sami ilimi ba daga garesa, ban sami kulawarsa ba, ban sami farin ciki daga wurinsa ba balle naji daÉ—i daga garesa, ya kirani da suna shegiya, ya kirani da Æ´ar zina alhalin akan shimfiÉ—ar sunnah ya samar da ni...".
muryarta ta harɗe tana kifa kanta akan cinyar Maijidda tana ƙara fashewa da sabon kuka.
"Maijidda banyi dacen uba ba, ni kaɗai ce nayi rashin sa'ar uba, ta dalilin baƙin cikinsa har yau ban san inda Ummina take ba, bamu san ina ta tafi ba, ki tayani adu'ar duk inda take Allah yasa tana cikin kariyar ubangiji, jikina na bani Ummina bata rasu ba tana raye, amma Kaka wai sai tayi ta ce min Ummi ta mutu".
kukanta ya ƙaru sosai, kuma daga ita har Maijiddan kukan suke yi. "Maijidda i wish ace ana sauyawa tuwo suna dana sauya Hayyo a matsayin ubana, i wish Hayyo is not my father, I wish I could take revenge for what Hayyo did to me and my mother. but i can't, i can't do that Maijidda, duk da lalacewarsa i still feel his love in my heart".
da ƙyar kukan Fillo ya tsaya bayan da ta ɗau tsayin mintuna tana bawa zuciyarta haƙuri da kalar tata ƙaddarar.
tana riƙe da hannun Maijidda tace,"ina key ɗin motar Turaki da na baki ajiya?".
Maijidda tace,"yana ƙasan kayanmu. amma Fillo ba kya tsoron garin mayarwa a ganki".
tana kallon wani side na daban tace,"idan ma an ganni there is no problem, and ba ma komawa É—akinsa zanyi na ijje ba, Maama zan kaiwa".
Maijidda tayi ajiyar zuciya tace,"gaskiya Hajiya Madina ta dabance, ni tunda kika ban labari na rasa ma abinda zance, nayi matuƙar girgiza da lamarin".
Fillo tace,"ni kaina farko ban yarda ba sai da kunnuwana suka jiye min...kiji fa wai a tsinke burkin motar, wai sai ta kira shi tace yaje ya É—aukota a anguwa motarta ta lalace, wai in ya taho sai me tirela É—in yasha gabansa kawai yabi takansa".
Fillo ta rumtse ido gam tana jin kanta kamar zai buga. "Maijidda wannan masifa har ina?, ace ka dinga harin jinin ɗan'uwanka?, me ya yi musu?, Allah da ƙyar ƙafafuna suka iya ɗaukata suka kai ɗakinsa, ke yanda na tafi a rikice ko a hannunsa naga key ɗin motar sai nayi kokawa da shi na ƙwace, ko kuma na faɗa masa komai kowa ya huta, saboda Hajiya Madina yasa kawai ban faɗa masa ba amma wallahi nayi niyya, to kawai dai ina tausayin halin da Maama zata shiga ne. kuma nayi rashin dabarar na faɗa mata ma tun a daren, dan da wuya in babu spare key da zai ce zai yi amfani da shi".
Maijidda tace,"to Allah dai kar ya tsare shi daga dukkan shirinsu". "amin".
Sabira wacca itama jika ce a wajen iya Hanne abokiyar aikin su Yami tazo wajen ta zauna. taci kwalliya daga yanda ta riƙe jakar hannunta kasan shirin fita tayi.
tace da su Maijidda,"nan kuka yo ashe?". Maijidda tace,"ehh, nan É—in yafi iska".
Sabira tace,"duk yanda akayi ba'a sanar da me gidan nan wutar ɓangaren nan ta lalace ba, ji fa kwana huɗu muna cikin duhu da zafi".
Maijidda tace,"ita kanta Hajiyan bata sani ba, kwana biyu basa zama. amma naji Yami tace sun faɗawa incharge zai bar mata saƙo". tace,"gwara haka, cikin daren nan duk sai ka kasa bacci wallah, ga zafi ga sauro".
cike da tsokana Fillo na kallon Sabira tace,"uwar yawo sai ina aka dosa?". Sabira ta ƙara turo ture kaga tsiyanta gefe ta tauna cingom dake bakinta, bayan ta karkaɗa ƙafa tace,"ni zan so ma ki rakani, dan wannan shirin nawa da kika gani bana wasa ba ne".
Fillo tayi Æ´ar dariya tace,"rufani ki saya, ke dai da yawonki amma ba dani ba, sai dai ko Maijidda gata nan itace uwar yawo irinki".
Maijidda tace,"balle ma ba zuwan zanyi ba".
Sabira tace,"ko zaki je ma ba zaki bini ba dan abinda zanje yi ba da irinki sanyi ƙalau ake zuwa ba, dan sai ki lalata min aiki. Fillon dai itace daidai da tafiyata".
Fillo tace,"wai ina zaki haka, naga sai wani faman cika kike kina batsewa".
Sabira tace,"ruwan masifa da bala'i zanje na juye". ta jijjiga kanta tana yin ƙwafa me ƙarfi,"ai na rantse yau idona idon kishiyar Anty Jummai sai na rotse mata kai".
sai ta karkato tana facing su Fillo da kyau ta shiga basu labarin kishiyar Yayarta. "wai fa kawai dan Anty Jummai tana da haƙuri, kuma ita ƴar talakawa ce shikenan kullum sai cin kashin da kishiyar taga damar yi mata. tayi ta zaginta wai ƴar matsiyata kyace ita ubanta haifarsa akayi da kuɗin, ga shegen haɗa makircin tsiya tayi ta jawa Anty Jummai Faɗa a wurin me gidan, jiya Allah ne ya taƙaita bai saki Anty Jummai ba".
Fillo da tausayawa tace,"kishiya dai kowacce kala ce bata da daÉ—i, Allah kai mana tsari da sharrin kishiya dan ni har ga Allah a duniyata inda abinda na tsana bai wuci kishiya ba wallahi".
ta ɗaga hannu sama tana roƙon Allah,"ubangijina na roƙeka ba don nafi kowa ba Allah karka sa mijin da zan aura yay min kishiya, ko na shiga na tarar ko a shigo a tarar da ni".
Maijidda tace,"ki dai roƙi Allah ya haɗaki da abokiyar zama ta gari shine kawai, ba wai batun kar a miki kishiya ba, in haka ne ina kike so akai sauran matan?".
zuciyar Fillo na sosuwa tace,"mu bar zancen nan kawai, zan iya haɗiyar zuciya a wurin nan. kishiya fa! ni Fillo da kishiya?, to ta ina ma za'a fara zaman?, in ke ganin abinda nake so tare da wata?, Allah karka nunan wannan ranar. Maijidda cewa fa kike wai kishiya ta gari, ke a duniyar nan har akwai kishiya ta gari?, hmmm yarinya baki san wace kishiya ba, amma kishiya babu ta kirki, ba sai na faɗa miki ba tunda kin riga kin san tarihin gidanmu, kin san baƙar wuyar da na sha hannun kishiyar uwa...ke Allah ya tsinewa kishiya kowacce kala ce ma".
Maijidda tace,"to Allah ya kyauta". Sabira ta miƙe tana faɗin,"bari naje, dan zuciyata azalzalata kawai take yi". Fillo tace,"je ki wallah ki ƙwatarwa Yayarki ƴanci, ki tsaya tsayin daka karki fito a gidan nan sai kin nunawa kowa Antynki na da gata, ke idan ta kama ma kiji wa Anty Jumman ciwo ki fito waje kina kururuwa, waye bai iya makirci ba ai sai in bai so ba, karki yarda ki taho sai an garƙame shegiya a cell, ke inta kama ma ki ɗau wuƙa ki saka a hannunta kafin akawo ɗauki, ana shigo kice gata can da wuƙa wai duk sai ta kasheku".
da gaske Fillo ke ta maganarta, bayan tafiyar Sabira Maijidda tace mata,"yau ba zaki je aiki ba?".
Fillo tace,"tun ranar dana fasawa Turaki turarensa nake shakkar komawa, so nake a bamu albashi tukunna sai na siyo masa tsiyarsa. shisa naiwa Maama ƙaryar banda lafiya".
Maijidda tace,"to yau dai Dr Yusuf yace zai zo, ki tashi mu san abinda zamu yi masa".
Fillo ta kalleta ta taɓe baki,"ni ba abinda zanyi tunda ba gayyatarsa nayi ba".
sukai shiru for some seconds sannan Maijidda ta katse shirun da faɗin,"Fillo Amir fa?, ya kamata ko me yayi miki kiyi haƙuri ke kam, tsakanin harshe da haƙori ma an saɓa, kuma shi dama zaman tare zo mu zauna zo mu saɓa ne. zatonki zaki samu masoyi kamar Amir?, karki zama butulu ki mance da irin halaccin da yay miki a rayuwa, ni dai dan Allah ko mene yayi miki kiyi haƙuri ki manta, tunda ni kinƙi ki faɗa min".
Fillo tai guntun murmushi na takaici,"shi bai faÉ—a miki abinda yayi min ba?".
Maijidda tace,"ni ba abinda yace min, kuma bana so na sani tunda har ke kika kasa faÉ—a min, abinda nake so kawai shine ku dawo daidai komai ya wuce..".
Fillo tai saurin tarar numfashinta,"har gaban abadan, igiyar soyayyar da ke tsakanina da shi na datseta har mutuwa, kije ki faÉ—a masa hakan, in ma yana wani lissafin rayuwa tare da ni ne to ya daina deceiving kansa, domin ni Halima na barsa har gaban abadan, wallahi ko Amir ne kaÉ—ai ya rage namiji a duniya ba zan auresa ba".
sai kuma ta fashe da kuka,"idan har da gaske Amir sona yake tsakani da Allah ba zai taɓa goranta min ba, duk da banga laifinsa ba. laifin Hayyo ne da ya sheganta ni da bakinsa, in ace Hayyo bai kira ni ƴar Zina ba yau da Amir bai buɗi baki yace min ƴar gaba da fatiha ba...".
furucinta na ƙarshe yasa Maijidda tayi zumbur ta miƙe,"kika ce me?, Amir ɗin ne ya faɗi haka?".
cikin matsanancin kuka tace,"Allah shahida idan nayi masa ƙarya Allah kar ya ɗagani anan wurin, kije ki tambayesa. daga nace bana so naje gidansa babu kayan ɗaki gudun gori shi ne ya tashi ya juya min baya yana faɗa min wai kar na manta ni ƴar zina ce, saboda haka ko ba'a min gorin kayan ɗaki ba ana iya min gorin an haifeni without marriage. Maijidda wanda nake so da aure ya faɗa min haka tun ban auresa ba, just imagine anyi auren, waɗannan kalamai kike tunanin zai dinga gaya min?".
Maijidda ta sauke numfashi da matuƙar mamakin ace Amir ne zai faɗi haka. ta rasa abin faɗa saboda tayi matuƙar girgiza, idonta kawai Amir ɗin yake hango mata, bata taɓa tsammanin zai iya faɗawa Fillo haka ba saboda bala'in son da yake yi mata.
Fillo dai kuka kawai take yi babu ƙaƙƙautawa, har sai da wayar hannun Maijidda tayi ƙara ta ɗaga suka gaisa da Dr Yusuf yace musu ga shi a waje, sannan Fillo ta goge hawayenta ta shi suka tafi bayan ta wanke fuskarta.