Sashe 65
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"wallah zan baka 25k daga baya zan cika maka sauran, amma kayi haƙuri ka sakar min hannu da zafi wallahi, ƙashina ma har ya ɓalle ina jin".
tsabar ƙuluwa Turaki bai san lokacin da ya dunƙule hannunsa ya daki bakinta ba ya fashe, shi zata faɗawa ya sakar mata hannu bayan ita halalinsa ce?, and ta iya barin wani ƙaton banza can daban da ba muharraminta ba ya riƙe mata hannu ba tare da ta hanasa ba?.
Fillo ta fashe da kuka sosai tana sa gefen mayafinta ta danne leɓenta da ya fashe. "ni me nayi maka a rayuwa ka tsane ni, ban taɓa cutarka ba haka ban taɓa munafurtarka ba, amma kai kullum burinka ka ƙuntata min, akan me?, saboda ina ƴar talakawa?, ina yi maka biyayya iyakar iyawana matsayinka na wanda nake a aiki a ƙarƙashin iyayensa, mahaifiyarka bata taɓa min kallon banza ba balle har ta nuna min tsana, amma kai ko da yaushe ka ganni burinka bai wuci kasa na zubar da hawaye ba, a wanne dalili?, idan har nayi maka wani laifi ne bisa kuskure da ban sani ba sai ka faɗa min na baka haƙuri, ba wai ka dinga muzguna min ba duk sanda ka ganni. yanzu ka karya min ƙashin hannu ka fasa min leɓe duk saboda me fisabilillah?".
kuka take sosai tayi maganar, idon Turaki manne akanta yana hasko tsayuwarsu da Amir, cikin jin zafi a heart ɗinsa ya kulle idonsa, yaja motar with high speed kamar duniya zata tashi, tayoyin motar suka bada sautin ƙuuuuu akan kwalta, wannan ƙarar ta haddasa tsoro na bala'i a zuciyar Fillo, kuma tsananin tsoron yasa farat ɗaya ta ɗago da kanta dake kan cinyarta, ganin yanda yake zabga mugun gudu akan titi tayi jikinsa a rikice ta riƙosa tana faɗin,"kayi a hankali dan Allah zamu yi accident fa, ka daina nufar bishiyan can".
*Please vote, comment and share.*
[8/28, 19:06] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
*29*
motar Turaki bata tsaya a ko'ina ba sai a compound na cikin company nasu, ƙarfe biyar na yamma a lokacin, and at that time an ma yi closing, bai san exact abin da ya shigo da shi ba, kawai ɓacin ransa ya kaisa.
yay parking yana daɗa tabbatar da duka glasses na motar a rufe suke, ya kunna karatun qur'ani sannan ya buɗe lock. ya kalli Fillo da har lokacin kanta ke kife a gefen kafaɗarsa, tun san da ta ke roƙon yay driving nasu a hankali taga baida hankalin dainawa shikenan sai tayi shiru, kuma tsoron da takeji shi ya hanata ɗagowa a kafaɗar tasa.
wucewar 20seconds yana kallonta, yana jin yanda numfashinta ke sauka a hankali, a tunaninsa duk bacci ne take yi, nan kuwa tsabagen zuciya ce tasa tai luff kamar wadda baccinta yay mugun nisa, wani irin zafi take ji a zuciyarta kamar ana rura wuta, in ace ta ɗago a ɗazu da tabbas babu abin da zai hana hannuwanta shaƙe Turaki, in yaso suyi accident ɗin da gasken gasken.
kafaɗarsa ya janye nan take kanta ya ƙwalu da kujeran, ta buɗe ido a hankali tana kallon inda suke, bata ko motsa ba har ya fice daga motar, tana kallo ya saka lock ya wuce ya barta, ita kuma ta rakasa da ido.
tana ganin yacca Æ´an tsirarrun staffs da basu wuce ba kowa na gaida shi, shi kuma yana É—aga musu hannu.
duk ƙoƙarin da tayi don ganin lock ɗin motar ya fita ta kasa, kenan rufeta yayi a motar ya tafi ya barta?, koma me zai faru da ita ya faru da ita?, to me yake nufi da ɗaukota ɗin?, ga shi ya kashe Ac balle ta samu sauƙin zafin gari da na zuciyarta da take ji.
wani malolon baƙin ciki ya tokare mata zuciya, sai ta kifa kai da gwiwa ta fashe da kuka, kuka take sosai har tana jin kamar zata shiɗe, ga kanta na uban sara mata, ga zufa duk ta wanke mata jiki, sai da tayi me isarta tukunna ta ɗago tana goge hawayen, tana jan majinar hancinta ta ƙara trying buɗe motar amma taƙi buɗuwa.
sai kawai ta jinginar da kanta jikin kujerar ƙirjinta sai bugawa yake, ta cikin glass ɗin ta fahimci magriba ta gabato saboda yanayin yacca garin ya lulluɓe, zuwa lokacin duk staffs sun ɗaɗe sai me gadi kawai da take iya hangowa ta cikin mirror. ta rufe idonta tana bin suratul Yusuf dake tashi cikin ƙira'ar Yousuf Kalo.
Turaki kuwa tunda ya shiga office É—insa zama yay kawai ya rufe idonsa, yayi hakan ne kawai saboda temper É—insa yay cool, dan in yaci gaba da kasancewa tare da ita a yanda yake mugun jin haushin abin da tayi ba abin da zai hana sa illata ta. sai da ya É—auki tsawon awa guda bai motsa a yanda yake ba, yana kallon kira daga different numbers na shigowa wayarsa amma babu É—aya da yay picking.
Fillo dai har sannan tana zaune sai wurga idanu kawai take yi, Allah É—aya yasan yanda take ji a cikin ranta, taja Allah ya isa tafi kai ashirin, in ace da wani abu da zata iya fasa glass É—in tuni ta fasa ta fita ta windown.
tana cikin tunani a ranta sai taga Turaki ya fito daga wani building daban da inda ya shiga É—azu, cikin sauri yake tafiya yana sauke hannun rigarsa da ye tattare, da alamu alwala yay zai wuce masallaci tunda ga ruwa nan a fusakarsa.
bata ɗauke idonta akansa ba har sai da ta daina ganinsa, bayan minti goma sai taji lock ɗin motar ya fita, kuma kamin ta kai ga buɗe murfin idonta taji ƙofar side ɗin da take ta buɗe.
"out". taji muryarsa ta shiga kunnenta san da take buÉ—e idonta duka.
kamar tayi banza da shi sai kuma taji tana tsoron yin hakan, Allah shahidi bata tsoron uban kowa a duniyar nan amma tana mugun shakkar Turaki.
ta tattaro mayafinta tana ƙudundune jikinta sannan ta fito a cikin motar ta tsaya a gefensa, tana fitowa ya rufe yay gaba yana cewa da ita,"follow me".
tabi bayansa tana É—an kalle-kalle, sai yaba kyan company É—in take yi, daga waje ma kenan ina kuma ga an shiga ciki.
suka shiga cikin office ɗinsa sannan suka wuce cikin wani ƙaton parlo, inda anan ne yake Turaki ke hutawa.
"kiyi sallah". abinda yace mata kenan ya wuceta ya zauna kan ƙaton farar cushion.
Fullo ta kalla haɗuwar parlon ta ƙara kallo tana me jinjina uban yawan dukiyar da aka kashe wajen ginin company ɗin da kuma abinda aka zuba acikin office ɗin, wato kuɗi dai suna inda suke, talaka da baida su ne yake ganin kamar babu su kwata-kwata.
kanta a ƙasa ta fuskanci kujerar da yake zaune, muryanta a hankali tace,"banda alwala".
yanda tayi maganar kawai yasa shi ɗago da kansa yana kallonta, ko kurma yaji sautin murayar nata yasan da ɓacin rai aciki. sosai yake kallonta da son gano abin da yasa tayi uban hasken da yake gani ajikinta, ba haka yasan asalin hasken fatarta ba, to daga ina wannan mugun farin?.
jin yay shiru ta ɗago kanta karaf suka haɗa ido, ta tsuke fuska da baki tana ƙara ɓata rai. shi kuma yay mata nuni da hannu yana mata nuni da toilet.
bata motsa ba kawai ta tsaya, ita ba zata iya shiga toilet yana zaune a wurin nan ba, sai dai in su shekara a haka, in yaso daga baya ta rama sallolin.
da kansa ya gane manufarta, hakan yasa ya miƙe ya fice bayan yace mata,"don't waste my time".
yana fita ta shiga toilet ɗin, cikin toilet ɗin kansa mugun ƙamshi yake kamar ba'a shigarsa. tai alwalan ta fito, mayafinta ta yafa ta tayar da sallah akan darduman da ta gani.
la'asar da magriba tayi a haɗe, bayan ta idar ta duƙar da kanta saboda mugun sarawar da taji yana yi, ga jikinta ya fara zafi alamun fever na son kamata. ita kanta ta san ma dole tayi zazzaɓi da ciwon kai ko saboda kukan da tasha a yau.
minti 1,2,3 har minti ashirin suka wuce Turaki na zaune office yana jiran fitowarta amma shiru. cikin ransa ya ayyana duk yanda akayi jira take ya koma yace mata ta fito, tsaki yaja ya tashi ya koma cikin parlon.
zaune ya ganta har sannan akan darduman kaman me lazimi, to amma jin motsinsa bai sa ta ɗago ba, alhalin ya santa da shegen tsoro, ya tsaya yana kallonta yaga dai durƙushen kanta kamar ba na lafiya ba tukunna ya ƙarasa ciki ya zauna kan kujerar dake kusa da ita.
yasa hannu ya ɗago kanta looking at her innocent face da yay ja, with the other hand ya taɓa forehead nata yaji zafi rau. ya rufe idonsa kaɗan ya buɗe yana ganin yacca hawaye ke suntiri akan kumatunta, kallon hawayen yake yana hango lokacin da yake zaune a gaban Hayyo yana faɗa masa cewar,"ehh kamar uba nake a wurinta amma ni ba mahaifinta ba ne, wannan yarinyar da kake gani ai ƴar zina ce, ƙwarai ƴar gaba da fatiha ce ranka ya daɗe, mahaifiyarta ma mahaukaciya ce, garin haukar nata ta gudu shekaru da yawa har yanzu bamu ganta ba, kuma har yanzu ni ban saketa ba. amma dai saboda a rufawa yarinyar asiri indai da gaske kake sonta ranka ya daɗe kawai ka biya sadakinta yanzu a take, batun sauran kayan al'ada da ake yi duk ba sai kayi mata ba, tunda dama ba faɗar addini bace, sadakin dai nata kawai ka kawo itama idan an bata babu hankalin riƙe su, tunda dama ni ne maɗaurin aurenta, babu wanda ya san danginsu tunda a titi na tsinci uwar naji tausayinta na aureta. ita kuma tsohuwar da kake cewa Yarinyar na hannunta gaskiya to ban ma san wace ba, ƙila ma ko irin tsaffin nan ne macuta".