← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 176

Sashe 24

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

****
Komai na É—akin abin kallo ne, ko da ace baka san kuÉ—in kaya ba kallo É—aya da za kai ma É—akin da kayan da suke cikinsa zaka san cewa tabbas an narka dukiya wajen siyan kaya da kuma tsara É—akin.
ko da ace za'a É—auki tsawon shekara 10 zuwa sama ba'ai renovating É—akin ba, ba za'a gane cewar komai da yake ciki ya jima ba.

lokacin da Fillo ta buɗe ɗakin zata gyara shi, tsayawa kawai tayi tana mamakin abinda za'a gyara, ina ƙurar da Hajiya Madina ta ke faɗi?, babu, infact irin ƙamshin dake tashi a ɗakin ko ɗakin da ake gyarawa kullum albarka, saboda haka ne tama rasa ta inda zata fara, gani ta ke sai dai ta ɓata ba dai ta gyara ba, dan komai tsaf tsaf, ɗakin yafi ƙarfin basirar gyaranta.

amma a hakan dai ta gyara dole, tunda umarni aka bata, kuma sai bayan da ta gyara ne ta fahimci ashe da gasken yana biɗar gyaran. komai ya ƙara zama fes-fes, adon ɗakin dark blue and silver ne, kalar da ta burgeta kuma tasan ta dace da mamallakin ɗakin.

a sanda ta gama gyara komai, sai ta shiga binciken abinda ta daɗe tana roƙon Allah yayi sanadiyar shigowarta ɗakin, wannan asirin da akace an saka shi a ɗakinsa, ba ɗakin da yake kwana ba, wannan ɗakin da zai koma da kwana bada jimawa ba, yes taga asirin, ta ganshi a inda taji sunce sun ajiye, ƙasan gadon, a mulmule yake kamar yanda taji sun faɗa, sam ba wari yake ba, wani irin daddaɗan ƙamshi yake yi, irin ƙamshin nan da ba zaka so ka daina shaƙarsa ba, irin ƙamshin nan dake motsa zuciya ta faɗa cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa.

hasalima da ta ɗauko sai ƙamshinsa ya gauraye duka ɗakin, ya kore ƙamshin air freshner da turaren wutan da ta yiwa ɗakin.
tunaninta guda ɗaya ne a lokacin asirin na menene?, to dama asiri yana ƙamshi?, ai tayi zaton asiri wari yake yi?, anya wani bai ganta ba a lokacin da ta laɓe yasa suka faɗi wannan maganar domin a ɗana mata tarkon ɓera?.

ta tsorata da wannan tunanin, amma ko menene dai ba zata taɓa barin wannan dunƙulallan abin ya ƙara zama a ɗakin ba balle har Turaki ya kwana tare da shi.
saboda haka cikin hanzari ta yunƙura ta miƙe zata fice, kwatsam idanuwanta suka sauka akan takardun da suka faɗo ɗazu da zata shiga ƙarƙashin gadon tace sai ta fito ta mayar da su.

ta kama gefen zanenta ta ƙulle wannan abin da har yanzu zuciyarta taƙi yarda da cewar asiri ne, babu ko ɗigon tsoron zai iya cutar da ita, ta durƙusa ta kwashe takardun ta buɗe drower ta zuba su, sai dai cikin rashin sa'a wata takarda me duhu ta faɗo.
daga tsayen da take kawai ta tsaya tana kallon takardar, baƙa ce, duk da duhunta hakan bai hana hoton abinda ke jikin takardar bayyana ba.

dai-dai take gani ko kuwa gizo ne idanuwanta ke yi mata?, kalmar Tashin hankali dai tayi kaÉ—an wajen kwatance da halin da ta shiga a lokaci É—aya.
ƙafafuwanta suka tafi a hankali gwiwoyinta na zubewa a ƙasa gaban takardar, waɗannan siraran yatsun nata na rawa ta ɗauko takardar, sai bayan ta ɗauko ne taga ashe harda wata ƙaramar takarda anyi stapling ɗinta ajiki.

ƙwayar idonta ta manne akan ƙaramar takardar dake ɗauke da sunan asibitin *As-Salam International Hospital*, Assalam ɗin kawai zuciyarta ta iya karanta mata banda international Hospital ɗin.

*Nile Corniche, Athar an Nabi, Old Cairo, Cairo Governorate 4220501, Egypt.* kamar haka address ya biyo bayan sunan asibitin, bin kowanne rubutu ta ke da ido ba don zata iya karantawa ba, har tazo inda ta ke da ilimin karantawar, karatun da ta samu daga wajen Amir, *NAME* zuciyarta ta faɗa, sannan ta ƙara faɗar sunan da ya ke rubuce akan siririn dogon layin da aka zana dan rubuta sunan majinyaci, *MUHAMMAD TURAKI HABIB*.

ƙasan sunan kuma wani dogon layin ne da aka rubuta *KIDNEY FAILURE*. A duk cikin tarin rubutukan da takardar ke ƙunshe da su, suna uku zuciyarta ta iya karantawa, As-Salam, Name da kuma Muhammad Turaki Habib.
kuma ta ke zuciyartata tayi wani girgiza da karanta sunan nasa, ba kamar ranar farko ba da bata ji komai ba sanda ta karanta sunan nasa.

sai kuma ta maida idonta ga haƙiƙanin hoton dake jikin baƙar takardar, ta taɓa riƙe irin takardar nan, wasu shekaru baya da suka wuce, kamar haka ne ba zata manta ba, likita ya basu takardar dake ɗauke da hoton ƙodar da akayi.

_"tana ɗauke da ciwon ƙoda"._ ba zata manta ba haka likita yayi musu bayani a wancan lokacin.

allon ƙirjinta ya girgiza lokaci ɗaya, me hakan ke nufi kenan?, shima wanda sunansa ke rubuce ajikin wannan takardar yana ɗauke da irin ciwon da ya kashe mata Adda?.
bata san lokacin da ta shiga girgiza kai da sauri ba, ai bata manta ba ta faɗa a baya, anyi an gama, ba zata ƙara rasa wani mutum da ya samu gurbin motsi a zuciyarta ba, kuma wannan alƙawari ne ta ɗaukarwa kanta.

kuma shikenan sai ta shiga rera kuka, zaman durƙushen da bata tashi daga shi ba kenan har zuwa yanzu, tunda ta tuna irin baƙar wuyar da Addanta tasha kafin ta mutu, bayan sun gama sa rai da cewar ta sami lafiya, a wankin ƙoda na arba'in da huɗu(44) da akayi mata, ashe tsawon lokacin da ta ɗauka tana fama ciwon ajali ne.

Hawayen dake bin idanunta ya gangaro ya sauka akan takardar dake riƙe a hannunta, wadda ta tsirawa ido babu ko ƙifce. _"Mutuwa zai yi shima"._ wani ɓangare na zuciyarta ya faɗa mata hakan.

a lokacin idan ka ga Fillo zaka iya rantsewa hankalinta ya gushe gaba ɗaya daga jikinta, dalilin ambatar kalmar mutuwa da zuciyarta tayi mata, allon ƙirjinta ya ƙara yin wani duka a karo na babu adadi, wata tsawa ta ziyarci cikin kanta, tsawar da ta haɗe da kiran daya shigo ta cikin wayar ɗakin wadda ke manne ajikin bango.

_Idan Ayyukan da suke gabana na ɗaya daga cikin abin da ke hana ni yin typing, to tabbas rashin comment ɗinku shi ne maƙasudin abin da ke saka na ɗauki tsawon lokaci banyi ba...ko da na zo yin typing ɗin ma sai naji banda wannan ƙwarin gwiwar, tunda ko nayi babu masu tarbarsa hannu biyu, saboda haka ku daina ganin laifina, har da na ku laifin...amma idan har kun gyara la shakka nima zan gyara...Ina baran adu'anku akan jarabawar da na kammala a yau don Allah._
[8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*©️Halima h.z*

_nace muku i love you ko na bar kayata?...kai aradu sai na faɗa ko me xaku yi sai dai kuyi😏, idan na faɗa sai na ruga da gudu yanda ba zaku iya kamani ba😝...nace ba *I LOVE YOU MY FANS* 🏃‍♀._

*15*
tunda taga Turaki ne ke tunkarota tayi ƙasa da kanta, ta shiga wasa da hannunta, haka kawai kuma sai ta tsinci kanta da mugun faɗuwar gaba, saboda haka a hankali ta shiga karanto innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, hasbunallahu wani'imal wakil.
_laifin me ta aikata?._ shine tambayar dake yawo acikin ranta, dan ita dai ta sa ni tsawon lokacin da ta ɗauka a gidan nan bai taɓa ambatar sunanta ba, to amma yau kiran nata na menene?.

tana cikin wannan saƙe-saƙen yazo ya wuce ta gefenta, ta ɗaga kai tabi bayansa da kallo tana ganinsa har ya shige part ɗin Boɗejo, sai a sannan ta sauke ajiyar zuciya me nauyi.
maganar Khalil da ta ƙaraji a gabanta ita tasa ta baro da kallonta daga entrance na boɗejo.

"ina za ki?". Khalil ɗin ya tambayeta yana kallon hannunta dake karkarwa tana ƙara damƙe box na glass din, ya lura kamar tana so ta hana hannuwan nata karkarwa ne amma hakan ya gagara.

tace,"BoÉ—ejo ce ta aikeni É—akinta zan ajiye mata idon baturenta".
Khalil yay murmushi yace,"kema ta koya miki idon bature kenan...to amma me ya samu ƙafarki?".

ta ɗan kallesa da mamaki amma sai ta kawar, bayan ta kalli ƙafartata tace da shi,"babu komai".

sai kawai ya jinjina kansa yace,"to shikenan tunda babu komai je aiken".
ya faɗa yana tsare ƙafafun nata da ido, sai ta tsaya bata tafin ba, ya ɗago ido yaga shi take kallo, da murmurshi ya ɗaga mata gira ɗaya yace,"ehen je ki mana". ya faɗa ba tare daya nuna mata so yake ya ƙureta ba.

ta juya zata tafi sai kuma ta ƙara juyowa ta kalle shi, ya ɗauke kansa yana kallon sama as in idonsa ba'a kanta yake ba. tana fara tafiya taji yace,"babu komai?, to shi wannan jan ƙafar na menene?, ko wani laƙanin ne nima a sammin?".

ba tare da ta juya ba ta girgiza masa kai bata ce komai ba, ta rumtse ido tana so ta ɗaga ƙafar ya ƙara cewa,"to jan ƙafa dai babu kyau, idan ma dai da kyau to kika ci gaba da janta ƙafarki faso zata yi ki rasa mijin aure, dan babu me kaiki gidansa kina yaga masa ledar ɗaki".

bata san lokacin da ta saki dariya ba, ta É—an waigo tana kallonsa tace,"Hammah Khalil kana da ban dariya".
hannayensa a aljihu yace,"ke kuma kina da ban mamaki".

tace,"mamaki kuma?".
yace,"yes, banda haka ace mutum na ciwon ƙafa kuma yaƙi faɗa kuma a tambaya ya mu sa...to faɗa min, magani kike tsoro ko kuma allurar?".

ita kam bata san taya akai ya lura da ita ba tun farko, duk yanda ta dinga ɓoyewa ashe sai an iya ganewa. fuskarta tayi narai-narai kamar me shirin kuka, yana lure da ita da hakan, ya fiddo da hannunsa daga aljihun sannan yace,"je ki kai aiken kizo mu wuce asibiti". ta ɗago ido ta kallesa sai dai bai bata damar magana ba ya ƙara cewa,"ina jiranki a mota".

yana faɗin haka ya juya ya bar wajen, ita kuma ta juya ta ƙarasa part ɗin Boɗejon.
Khalil ya kira Hajiya Madina a waya ya sanar mata zancen ciwon ƙafar na Fillo wanda itama bata san da shi don tunda suka dawo bata ganta ba.
Chapter 24 · 0% Book details