Sashe 74
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fillo tace,"tom Maama sai kin dawo". har Hajiya Madina ta fita a motar sai kuma ta dawo ta miƙowa Fillo wayarta tace,"bana son zaman shiru riƙe wayan ko ƙur'ani kya karanta, ko kuma za ki biyoni ne?".
Fillo ta girgiza kanta tace,"a'a Maama sai kin dawo É—in". ta faÉ—a tana amsar wayar.
game É—in da take yawan ganin Maama nayi ita ta shiga, tana cikin yi sai ga kira ya shigo wayar, ganin sunan,"My Husband". na yawo jikin screen É—in yasa ta fita daga motar tace da drivern bari ta shiga ta kaiwa Maama.
sai da ta fito taji garin so silent, babu ma inuwar mutane dake giftawa, tana shiga ta bawa Hajiya Madina wayar ta fito.
duk da tana hasko motarsu dake tsallake haka ta taho a ɗan tsorace ta tsallaka, sai dai sanda tazo bakin motar ta buɗe ƙofar motar zata shiga taji wani abu mai sanyi a wuyanta, sanyi irin na ƙarfen wuƙa.
da sauri tayi yunƙurin juyawa bayanta jin numfashin mutum akanta, nan da nan taji numfashinta na seasn, sai kuma taji murya dai-dai kunnenta cikin raɗa da kakkausan amo ance,"wallahi kina ihu ko wani motsi sai na yanka maƙoshinki da kaifin wuƙar nan dake wuyanki".
ai sai tayi ɗiff ta fasa yin ihun da tai niyya, idonta ya maƙale a driver seat sai taga drivern baya ciki, dan haka ayanzu bata da wani zaɓi da ya wuce umarnin da aka bata.
tayi tsilli-tsilli da idanu tana jin yadda sanyin kaifin wuƙar ke wucewa har cikin zuciyarta. ta runtse ido sosai zuciyarta na tsananta bugawa, cikin kanta ya haska da kalmar mutuwa!, sai kuma gefen ƙwaƙwalwarta ya karanta mata ya ya Kaka zata ji labarin mutuwarta?, wanne hali Amir zai ji a sanda aka faɗa masa ta mutu?.
tana ji mutumin yasa tsumma ya toshe bakinta sannan ya shiga janta har suka bar bakin motar, ita dai idonta wurgawa yake yana kallon ƙofar store ɗin da Hajiya Madina ke ciki, so ta ke ta hango fitowarta in yaso ta san ta yadda zata ƙwace bakinta ta ƙwala mata kira, sai dai har suka baro bakin motarsu aka zo da ita wajen da bata san ina ne ba, bata ga kowa a wurin ba ko da kuwa Maama.
taji an buɗe motar da suke kusa da ita a yanzu an buɗe ƙofar baya. tana jin sanda wata murya daban da wacce ke riƙe da ita yace,"sakata aciki".
duk wannan abin da ake har yanzu wuƙar na wuyanta motsi kaɗan suke jira tayi su fille kan.
suka zirata acikin motar, tana kallon wanda ke front seat fuskarsa lulluɓe cikin bakin ƙyalle, wanda ke riƙe da ita yana shigowa ya rufo ƙofar, sannan ya ɗauke tsumman da ya rufe mata baki da shi, daidai da buɗewar bakinta zatai ihu, daidai kuma da juyowar na gaban ya danna mata wani tsumman da ya rufe hancinta da bakinta.
take ta shaƙi ƙamshin wani abu a jikin tsumman, bata da ilimin sanin chloroform balle a yanzu da taji ƙamshinsa tayi ƙoƙarin ɗauke numfashinta, kuma wannan ƙamshin abin da ta shaƙa ya wuce har cikin kanta sai taji kamar zata mutu, ƙirjinta kamar ana rura wuta tana ci bal-bal, lokaci ɗaya kuma sai taji numfashinta ya sarƙe gaba ɗaya, ta kasa shaƙar iska, a hankali kuma sai jinta da ganinta suka ɗauke duka, nan take kuma tai laƙwas ta tafi luuu tana faɗawa jikin na kusa da ita.
ba tare da ɓata lokaci ba motar ta bar wajen cikin speed ɗin da ba za'a taɓa zargan muggan mutanene acikinta ba. har sanda zasu wuce driver da ya dawo daga fitsarin da yaje ya bi motar da kallo, yana jin kamar bai yarda da motar ba har ta ɓacewa ganinsa. dai-dai nan kuma ya ɗaga kansa yana ganin me tahowa daga bayansa...
     Â
   *LULLUÆIN BIRI don catch fire.......*
*comment, vote and share.*
[8/30, 09:42] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
'''DAGA MARUBUCIYAR'''
1-Sirrin Æoye
2-Al'amari
3-Hidaya Noor
4-Alhussain
5-Sanadin Talauci
6-Ƙaddarar So
7-Prince Khaleed
Da sauran su.....
*32*
ganin Hajiya Madina yasa drivern tafiya wurinta da sauri ya karɓi ledan kayan dake hannunta, a gaban mota ya aje manyan ledan kayan kusan guda 5, da gani kasan ba siyayya bace ta jarirai kamar yanda ta faɗa, siyayya ce ta musamman tayita don yin kyauta ga Fillo.
drivern ya buɗe mata back seat ta shiga, sai dai tun kamin ya zagayo ɓangarensa har Hajiya Madina ta kula da rashin Fillo cikin motar. hakan yasa ta buɗe motar ta leƙo kanta tana faɗin,"Ɗan Usaini ina ƴata?, ina Halimatu taje?".
ÆŠan Usaini ya dakata da buÉ—e motar yace,"Hajiya ai taje kai miki waya ni kuma naje É—an yin uzuri".
Hajiya Madina tace,"ban gane nufinka ba".
yace,"ruwa naje kamawa, to ban san ba gaskiya ko ta dawo na dai barta ta shiga ciki kai miki waya".
lokaci É—aya Hajiya Madina ta fito a motar gaba É—aya,"ka daina cewa ta kai min waya. kai wayar tun yaushe ne?, kusan fa minti biyar kenan, tana bani ta fito".
ÆŠan Usaini na waige yace,"to ko ta zo ta tarar bana ciki sai ta koma, bari na duba cikin store É—in".
ya faɗa yana barin wajen, Hajiya Madina tabi bayansa. lokacin hankalinta duk bai tashi ba amma dai ta tsorata, ina Fillon zata je?, idan cikin store ɗin ta koma ai tana shigowa zasu yi clashing tunda tana daga bakin ƙofa tana biyan kuɗi.
daga cikin store dai har wajensa babu Fillo, a wannan lokacin hankalin Hajiya Madina ya fara tashi, haka suka dinƙa zagayen arean wajen suna kiran sunanta suna dubawa amma ba ko alamarta.
Ɗan Usaini na tare da me gadin store ɗin yace da Hajiya Madina,"ƙilan ko da ta shiga kai miki wayar makuwar hanyar fitowa tayi".
Hajiya Madina dai tana tsaye ta kasa cewa komai, saboda yacca take jin numfashinta na neman yankewa, iska ce a wajen ke ta kaÉ—awa amma ita zata iya rantsewa hucin zafi take ji ajikinta, zata iya rantsewa kamar ji da ganinta ya É—auke.
ƴar mutane ta ɓta ata sanadinta?, me zata ce da Kakar yarinya?, me zata ce da wanda ke shirin aurenta?. lokaci ɗaya kanta yay wani mugun sarawa kawai sai ta fashe da kuka, staffs dake cikin store ɗin suka fito dai anata ƙara lalube, tsawon kusan minti 30 inuwar Fillo ma ba'a gani ba.
da ƙyar Hajiya Madina ta iya picking call ɗin Baffa, ta faɗa masa halin da take ciki, sai dai kamin yace komai Hajiya Madina ta yanke jiki ta faɗi a lokacin, dalilin abinda taji Ɗan Usaini na faɗawa me gadin wajen.
"to ni dai bana ce hakan ba ne, zargi kawai nake da hasashe. kaga bakin bishiyar can anan naga motar tayi parking, kuma wallahi tun lokacin da zan tafi fitsarin naji hankalina bai kwanta da motar ba, to kuma sanda nake dawowa sai naga motar na barin wajen, sai na bita da kallo har ta ɓacewa ganina, kasan Allah ba wai don saboda ɓatan yarinyar nan ba, jikina kawai naji bai aminta da motar ba, Ya Rahmanu dai yasa ba ƴan garkuwa bane suka yi gaba da yarinyar nan".
da hanzari akai kan Hajiya Madina, da ƙyar aka iya kamata aka sakata a mota sai asibiti.
Tunda suka isa asibitin aka karɓe ta aka shiga bata taimakon gaggawa saboda yanayin yadda ta ke a sume, su na tsaye cirko-cirko a ƙofar ɗakin aka shiga da ita suna jiran suji me likitan zaice in ya fito, ba'a fi mintina biyu ba ya fito yana ƙarasa zare gloves ɗin hannunsa a lokacin ne kuma Baffa ya iso wajan da hanzarinsa.
ganinsa yasa ÆŠan Usaini nufarsa, sai dai ko ta kansa Baffa bai bi ba yay wajen likita.
"Likita ya jikin matata?" Baffa ke tambaya yana kallon likitan da yake goge hannunsa da hand sanitizer.
ya kalla Baffa yace,"Patient É—in ku jininta ya hau sosai, akwai abinda ya firgita ta lokaci É—aya shiyasa BP É—inta yayi high, wannan dalilin ya saka ta suma, but yanzu an saka mata drip kuma da izinin Allah da ta farka zata dawo dai-dai."
Ɗakin Baffa ya shiga ya tarar da ita a kwance tana bacci, ya zauna gefenta ya kamo hannunta yana ta kallonta, tausayinta yayi matuƙar kama shi, ya sa ni fiye da hawan jini ma za'a iya faɗa indai akanta ne, saboda ita macece da bata iya saka abu a ranta ba, tana da saurin ruɗewa nan da nan musamman akan ƴaƴanta, haka ma akan wanda ta damu da shi, ta kan kasa juriya da dauriya.
ya san tana matuƙar son Fillo, dan ko da yaushe suka zauna tana yawan masa labarin yarinyar, irin tarbiyar yarinyar da hankalinta da natsuwarta da kamun kanta, har ta kance masa ita ina ma ace yarinyar ta zama rabon wani acikin Khalil ko Turaki.
kuma sau tari tana faɗa masa insha'Allahu zata yi iyakar bakin ƙoƙarinta wajen ganin yarinyar ta samu wadataccen ilimi domin itama rayuwarta ta inganta, yarinyar ba kalar yaran da za'a banzatar da rayuwarsu ba ne.
Hajiya Madina bata farfaɗo ba sai bayan sallar isha'i, kuma tana farkawa idonta ya sauka akan Baffa dake waya da wani police yana shaida masa ɓatan Fillo, sai dai suna haɗa ido yay saurin sallama da police ɗin gudun kar taji a ƙara samun matsala.
ta kama hannunsa tana faɗin,"Baffa yarinyar mutane, ƴar mutane ta ɓata a hannuna Baffa, me zance da iyayenta Baffa?, me zan faɗawa mijin da zata aura Baffa?, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wallahi wallahi banda masaniyar inda tayi, Baffa wallahi da nasan hakan zata faru ba zan fita da ita ba".
daga yanayin yanda take maganar kasan bata cikin hayyacinta.
sai kuma tayi shiru tana kallonsa kamin cikin sanyin murya tace,"Baffa an ganta ne?, ÆŠan Usaini ya nuna motar mutanen?". ta faÉ—a tana sakin kuka me ban tausayi.
Baffa Ya kama hannunta sosai, ya kwantar da murya yace,"Please stop crying, Insha'Allahu za'a ganta very soon, ba wai ɓata tayi kamar yanda muke tunani ba insha'Allah".
tace,"Baffa ta ya?, ÆŠan Usaini fa yace yaga motar da bai yarda da ita ba, kuma fa lokacin ne ta fito ta kawo min wayata, Baffa me kake tunanin ya faru?".