← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 176

Sashe 11

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata ce komai ba, Maijidda ta ƙara cewa,"ga furar kisha da sanyi".

"aina kika samu ƙanƙara?".

"Yami ta aike ni É—azu na ganta shi ne na sayo, nasan za ki so".

Fillo tayi shiru, idonta na kallon yatsun ƙafarta.

"ni dai kici abinci kar naci amanar Amir".

"ba zan iya ci ba Maijidda sai Kaka ta dawo".

"haka za ki yini da yunwa kenan?".

"zanci amma idan ta dawo".

"Amma dai kin san sai dare ko?".

Fillo tayi shiru, itama Maijiddan bata ƙara ce ma ta komai ba. For a while Fillo Let out a long sigh of despair, duka tafukan hannunta saman fuskarta tana ƙoƙarin danne kukan da ke neman cin ƙarfinta.

"Maijidda tsawon yaushe idanuwana zasu É—auka kamin Dada ta dawo gare su?".

tausayin Fillo ya kama Maijidda matuƙa, bata iya cewa komai ba sai hannu da ta saka itama tana goge nata hawayen.

****
Sakkowa yake daga stairs a hankali hannunsa riƙe da mug, three quarter ke jikinsa brown colour da white t-shir me coller dark blue. har yanzu ba'a cire masa bandage ɗin goshinsa ba.

yana sakkowa parlon direct kitchen ya wuce, ya zuba sugar a cikin tea ɗin, sannan ya fito ya ƙarasa kujera ya zauna.
Kaka wadda ya barota a kitchen ta fito da sauri, ta ƙaraso inda yake, da rissinawa ta ke faɗin.

"sannu ya yallaɓai".
Turaki ya amsa mata yana É—an runtse ido saboda zafin ciwon dake kafaÉ—arsa.

Kaka ta saka masa pillo daga bayansa sannan ya jingina da kujerar.

"sai me kake da buƙata Yallaɓai?".

Ƙafafun Kaka a ƙasa lokacin da ta ke tambayar tasa. ya ɗan rufe ido yana jin tausayin tsohuwar a ransa, tukunna ya buɗe yana kallonta ta wutsiyar ido yace,"babu komai, kije ki huta haka don Allah".

tace,"to Allah ubangiji ya ƙara maka lafiya, ina bayan kitchen idan da buƙatar wani abu".

Tana faɗin hakan ta miƙe zata bar wajen, har tayi tattaki zata nufa kitchen ta fita ta baya sai ya dakatar da ita, tsawon kwanaki shidan da tayi a wurinsa sai jiya ya san sunanta a bakin Maama.

"Kaka". ta juyo idanuwanta a ƙasa, tun ranar da ya dawo ta dawo aiki ɓangaren, ita ta ke ta lura da shi da ciwonsa, yana ganin ƙoƙarin tsohuwar sosai, yana jin tausayinta matuƙa a cikin ransa, sai dai bai taɓa jin tausayinta da yawa haka ba sai a yau da yake kallon fuskarta me bayyane da damuwar da ke cikin ranta.

kullum zuciyarsa na gaya masa tsohuwar kamar wannan bata samun hutun rayuwa, to ina ƴaƴanta?, waye a ƙarƙashin kulawarta da ta kasa samarwa kanta hutu a wannan shekarun nata?.

Sai dai tambayar da ke zuciyarsa yanzu damuwar da ke fuskarta ta mene?, ya ƙara ɗaga ido ya kalleta, tana tsaye har yanzu bata motsa ba, ji yake kamar ya tambayeta menene matsalarta amma sai yaga wannan ba huruminsa ba ne.

Saboda haka sai yace,"Kaka tun da yau na sami sauƙi kije kawai ki huta kema".

Har yanzu kan Kaka a ƙasa tace,"to yallaɓai".
ta faÉ—a tana sake juyawa ta nufi hanyar kitchen.

Kamar bata fahimci me yake son ce mata ba.
"Kaka ina nufin ki tafi ki huta sosai".

tace,"Yallaɓai ai kar na tafi kuma wata buƙatar ta tashi".

Kamin yayi magana sai ga Zaytuna ta shigo, ta wuce inda yake zaune tana kara masa waya a kunnensa, ya maida hankali ga wayar ita kuma tace da Kaka.

"ki tafi É—in kawai babu matsala, zan zauna da shi".
da yake taji last conversation É—insu kamin shigowanta parlon gaba É—aya.

Kaka tace,"to Zaytuna na gode, Allah ya ƙara masa lafiya. Kya sanar da Hajiyar".

"tom shikenan babu matsala".
Da hakan Kaka ta bar wajen.

daga ɓangaren Bello Ƙaraye da ke magana ta cikin wayar Turaki yace,"all this while ina ka bar wayanka, i have been calling tana ta ringing ba kai picking ba".

Zaytuna ta sauke cup ɗin tea daga bakinsa, bayan ya haɗiye tea ɗin da ya kurɓa ya amsawa Bello da cewan,"Maama ce ta ɗauke wayan wai na samu na huta da kiran da ake mani, i though ma tayi switch off nata ashe kunne ta barta".

Bello yace,"anyway, how are you feeling now?".

Cikin sanyin jiki yace,"Alhamdulillah".

Bello yace,"hope kana iya cin abinci yanzu ko?".

Yace,"yanzu haka ma am taking tea".

Bello ya ƙara cewa,"Good, batun drugs fa?". Yay tambaya cike da concern.

Turaki yay É—an jim yana tuna yanda Maama tayi ta fama da shi akan shan magani É—azu da safe.

jin shirunsa Bello yace,"i know, ba za'a sami matsala da kai ba a ko'ina sai a ɓangaren shan magani...you should have grow up by now gaskiya".

Turaki yace,"ka kira ka gaya min magana ne na kashe wayana?".

"yo tsakani da Allah ace ka girma amma kana gudun magani da Allura".

"ina ce ciwon jikina yake ko?".

"ai kuma da yake mun damu da kai...by the way zan shigo cikin satin nan".

"Allah ya kawo ka".
Bello yace,"ameen, Allah ya ƙara lafiya...and please ka dinga kulawa kaji"

Turaki ya amsa mishi,"toh".
Sallama Bello yyi masa ya katse wayar, ba'a É—au lokaci ba Maama ta shigo parlon.
[8/8, 19:41] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*©️Halima h.z*

*8*
Idanuwan Turaki da Zaytuna suka ware akan Maama da ta shigo fuska babu yabo babu fallasa, suka bita da kallo har ta zauna kan kujera ta harɗe ƙafafu tana girgiza su. Dukansu suka sauke numfashi mai nauyi dan sun san tunda suka kalla fuskarta a haka to lallai akwai damuwa.

"É—auki wayar nan ki kira min Bello". Muryan Hajiya Madina ta fito da wani irin amon sauti.

Zaytuna ta ɗauki wayar Turaki da ke kan cinyarsa, tabi kiran Bello da suka gama waya da Turaki babu jimawa. ta miƙe ta isa ga kujerar da ta ke ta bata wayar, a kiran farko bai picking ba sai ana biyu, shima sai da ya kusa katsewa tukunna.

Daga ɓangaren Bello yace,"Turaki ya dai?".

Hajiya Madina ta numfasa tace,"Bello ba shi ba ne".

Jin muryarta yay saurin gyara zama daga inda yake, ya gyara yanayin muryarsa, cike da ladabi ya gaisheta, ta amsa masa tare da tambayarsa ya aiki, yace mata aiki alhamdulillah.

Shiru na Æ´an sakanni ya biyo baya, Turaki dai kallonta kawai yake, kiran Bello da tayi na menene?, me zata ce da shi?, to me ya faru ma tukunna?, dan yanayin fuskarta kaÉ—ai yana shaida cewar there most be something behind.

"kana jina Bello?". ta faɗa tana yiwa Zaytuna nuni da dining area, inda a lokacin Zaytuna ta miƙe ta isa wurin dining ɗin, ta ɗauki cup ta tsiyaya watermelon juice aciki, ta ajiye jug ɗin sannan ta dawo ta miƙawa Maama.

"ina jinki Maama".

lemun da ke hannunta ta kurɓa kamin tace da shi,"application for annual leave, ina ce ka miƙa musu ko?".

Yace,"ehh Maama na miƙa tun a washe garin ranar da yay accident ɗin".

Tace,"good, how many months kasa?".

yace,"munyi waya da shi yace na saka just 1 week".

ta ɗago ido ta yiwa Turaki wani kallo na ashe baka da hankali, hakan kuma yasa yay saurin sauke idonsa ƙasa, duk da bai san akan mene kallon ba tunda ba jin abin da Bello yace yake ba, amma wannan kallon yasan ba a banza ba.

Ta kalla goshinsa da ƙaton plaster ke manne a wajen, sannan ta tsurawa kafaɗarsa ido, tana hasko yanda wajen ke nannaɗe da bandage kwanaki biyar da suka wuce kamin jiya a kwance, ai har yanzu hannunsa na hagu baya moving sosai, amma shine saboda bai da cikakken saiti, yay wannan mummunan accident ɗin sannan yace wai hutun just 7days ya ɗauka, which means monday zai koma aiki.

Tayi gajeren tsaki, ta lura Turaki nema yake ya kashe kansa a bautar company kawai, yafi damuwa da aikinsa akan lafiyarsa da rayuwarsa, to ita ba ƴar iskar uwa ba ce. Ko da yake shima Bello ba shi da hankalin ai, yana kallo har kusan fitar da rai su kai da Turaki, basu taɓa zaton zai farka ba saboda mugun ciwukan da ya ji, amma shine har yake biye masa da ɗaukan hutu na kwana bakwai kawai.

Daga ɓangaren Bello so yake yay magana amma yana gudun faɗan da zai biyo baya, dan shima sai bayan da ya kai takardar yaga yayi rashin tunani.

ta katse tunaninsa da cewan,"then write a resignation letter ka ƙara kaiwa".

Turaki da Zaytuna duka a lokaci guda suka ɗago ido su na kallonta da mamaki tsantsa, hatta Bello daga inda yake bai san lokacin da ya miƙe daga zaune ba, yana daɗa tambayarta abunda tace.

"ehh resignation letter nace, takardan barin aiki ba, And if you can't tell me sai na saka Khalil ya rubuta ya kai".

Bello ya haÉ—iye wani yawu yace,"amma Maama hakan sai nake ganin will not be the best solution, we should just add him a days more off...idan ya dawo sai a san zaman da za'ai da Manager to let him know what is going on".

a fusace tace,"kar ka rubuta ka bari zan rubuta sai na bawa wanda na isa da shi ya kawo, kuma ai dama ban kira na faÉ—a maka don neman shawaranka bane, umarni nake baka tunanina cewar na isa matsayin mahaifiyar amininka".

In calm voice yace,"kiyi haƙuri Maama".

Bata ko ba shi amsa ba ta kashe wayar, tana kallon yanda idanuwan Turaki suke kallonta kamar zasu fito waje, amma sai tayi kamar bata san yana yi ba, taci gaba da shafa wayarta har sanda ta nemo lambar Khalil ta kira shi, ringing biyu ya ɗaga. a taƙaice ta amsa sallamarsa ta ɗora da cewa.

"You have Bello Ƙaraye's number right?, Anyway if you don't have i will send it to you now, call him and ask abunda na karanta masa, as early as tomorrow morning ka fara aiwatar da abin da nace before you leave to koma ina ne zaka je".

Bai tsaya yin wani tambaya ba, haka itama bata jira cewarsa ba ta katse wayar ta ajiyeta gefenta.
Chapter 11 · 0% Book details