Sashe 117
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya kwantar da kansa a kafaɗarta yace,"almost 1week fa Mum ko gaisuwana bata amsawa, ban san laifin da nayi mata ba wallahi, and taƙi bani damar ma da zan bata haƙuri, na mata sending apology through text message and letter duk tayi ignoring ɗina, kuma ina so nayi magana da ita Mum".
Hajiya Ramla na kallonsa da tsananin tausayi tace,"and duk ina ina hakan ta faru?".
ya kama hannunta cikin sanyin murya yace,"kinyi busy da yawa a office Mum, kuma kinga Baffa ya hanani zaman gidan nan".
ta sauke numfashi tace,"tashi muje".
yace,"Mum ko munje fa ba zata saurareni ba, korana take yi".
ta kama hannunsa kawai suka fita zuwa side ɗin Hajiya Madina, suna shiga parlo tana saukowa daga upstairs, taiwa Turaki kallo ɗaya ta ɗauke kai ta wuce kan kujera ta zauna, yabi bayan Mum suka ƙarasa ya zauna kusa da ƙafafun Hajiya Madina.
Hajiya Ramla tace,"ina bayar da haƙuri a madadinsa Madam".
Hajiya Madina ta kalleta tace,"bai faÉ—a miki laifinsa ba?".
yay karaf yace,"ki faÉ—a min Maama zan gyara".
nan da nan ta fara masifa tana cewa da Hajiya Ramla,"yaron nan saboda baida mutunci yana so ya mayar damu ƙanan mutane yaje dubai ince idan sun tashi dawowa ya taho da trollys amma ya kawo min guda goma sha biyu kacal, ba wannan ba ma!, nace ya haɗo lefe but sai ya turawa Zaytuna 1ML wai ta siya abin da taga ya dace, wato gamu faqararru da miliyan ɗaya zamu haɗa lefe ko?, in tambayeka ma! zatonka Fillo ƴar aiki daka sani a baya zaka kaiwa lefe da zaka kashe 1ML kacal?, to in haka ƙwaƙwalwarka ke faɗa maka ta yaudareka, Fillo ƴar aiki daban Fillon da zaka kaiwa lefe daban, in ka manta ka tuna gidan da kaje kayi gaisuwar mahaifinta, ka tuna irin mutanen da ka samu, ka san da cewa kenan tafi ƙarfin naira miliyan ɗayanka, Fillon yanzu ƴar gata ce gaba da baya kuma ƴar gidan manyan mutane, beside wallahi ko da ace Fillo ta nan a yanda ka santa tun farko baka isa ka kawo min lefenta na miliyan ɗaya na karɓa ba, kai ka san da cewa taimakonka da tayi tafi ƙarfin dukka arziƙin ubanka har da naka.
to make it short, kaje ka sami ubanka Alƙali Dikko ka tambayesa lefen nawa suka haɗawa ƴarsu daga nan sai kayi abin da ka san zai ɗaga mutuncinmu ba wanda zai ja mutuncinmu ya zube ba, dan mu ba marowata ba ne".
kansa a ƙasa yace,"Maama kiyi haƙuri amma wallahi bani na tura kuɗin ba, time ɗin account ɗina ya sami matsala kuma kaina ya ɗau caji da damuwar Boɗejo shine nasa Bello ya tura mata, kuma wallahi sai da nayi masa magana yace ai hakan ya isa wai almubazzaranci babu kyau".
Hajiya Madina ta zare ido tana doka masa tsawa tace,"rufe min baki shashasha, shi Bellon da zai haÉ—a nasa lefen da 1ML ya haÉ—a da har ya mayar da kai É—an iska, me yasa baka tuna masa check É—in da na basa yaje ya haÉ—a nasa lefen ba?, ko kuma baka faÉ—a masa gidan da kaje ka sami Fillo a yanzu ba?, to wallahi wallahi ba zan kai iyaka akwatu sha biyu ba, kuma ba zan kai lefen miliyan É—aya ba, tashi ka bar min parlo".
ya ɗago ya kalleta kamar zai yi kuka, ya marairace yana roƙonta akan tayi haƙuri.
tace,"fitar min a parlo tun ina ganinka da gashin ido, ai ba iyakarta kenan ba, nace kaje ka gano lafiyar matarka kaƙi zuwa yau kwana hamsin da wani abu, wanne kallo kake so mutanen nan suyi mana?, amma na lura da hakan bai dame ka ba saboda kana tare da zaɓin ubanka acikin gidanka ko?, kai kasan maganganu marasa daɗin da Boɗejo tazo ta yiwa mahaifiyarka yanzu kuwa?, kuma duk akan Ilham, me ta-ke nufi da mu?, auren nan muma da muke iyayenka muka haƙura da yanda kaje kayi gaban kanka balle ita, ta bar yarinya ta tare a ɗakinta amma ta hana kowa kwanciyar hankali, ba'a zama da kishiya ita uwar yarinyar ta zauna da kishiyoyi, haba dan Allah tun yaushe ake abu ɗaya, abu mitsitsi yaƙi ci yaƙi cinyewa, comon tariyar da za'ai lokaci ɗaya a wuce wurin ta hana rawar gaban hantsi, tabi tasa mahaifinka ya takura maka saboda kai baka da uwar da zata baka umarni ko me?, but shikenan zan yiwa tufkar hanci, idan ta san wata ai bata san wata ba, yanda ɗanta yake bin umarninta haka kaima zaka bi umarnin taka mahaifiyar, ai uwa bata fi uwa ba".
ɓacin ranta na ƙara tsananta ta waiga gefenta ta ɗauko jotter, ta falli takarda ta jefa masa da biro tace,"umarni nake baka ba ja'inja nace muyi ba, ka saki Ilham saki ɗaya".
yay saurin É—ago kai yana kallonta,"Maama in saketa kuma?".
ya kulle ido yana jan ajiyar zuciya,"Maama itama fa Fulani Kakarta tace sai na saketa".
ta buga masa tsawa tace,"ba batun Fillo nake yi ba yanzu, ka fara sakar musu Æ´a tukunna".
sannan ta kalli Hajiya Ramla tace,"umarninki ne a matsayinki na wacce ta ɗau cikinsa wata tara ta kuma haife shi da wuya bata sauƙi ba, kamar yanda itama take jin ta ɗauki cikin wata tara ta haife bata sauƙi ba, idan ta cije ki fita cijewa, kin sa ya saki Ilham kuma ba zai saki Fillo ba".
ta ƙara maida kallonta kan Turaki tace,"nace ka sakar musu ƴa ko".
babu shiri ya shiga rubutu, _Ni Muhammad Habib Dikko na saki Rumana Hashim saki É—aya._
ya gama rubutun daidai da faÉ—owar BoÉ—ejo parlon, kuma daidai da shigowar kiran Dada a wayar Hajiya Ramla....
*Comment, share and vote.*
[9/4, 18:52] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
*45*
Boɗejo ta ƙara ɗaure fuska a sanda take isowa kan Turaki ta tsaya.
"mara mutuncin banza da wofi, kai har nawa kake da zaka raina ni?, har ni ina maka magana ka yi banza da ni ka ƙaro gaba wato ga ƙatuwar shashasha na yi maka magana ko?, ko da yake babu komai, ba ni karaina ba ubanka ka raina".
ta gyara zaman gyalenta tana saka hannu ta ɗago kansa sama,"wallahi bari kaji na faɗa maka kayi kaɗan kace zaka wulaƙanta min Ilham, sanin kanka ne kaf jikokina na fi ƙaunarta, ba'a haifeka ba ba'a haifi uwar da zata haifeka ba, ɗan iskan banza yaushe kaciyarka ta girma har da kake jin kafi ƙarfin kabi umarnina da na ubanka. kai ka sa ni dai Ilham tafi ƙarfin wulaƙancinka, domin kuwa ta fika gata, ita ɗaya a wajen uwarta bata taso ta san wata aba damuwa ba, saboda haka baka isa kace zaka haɗata da kishiya ba, kishiyar ma mara aji ƙasƙantacciya wadda tayi aiki a gidanku, haba dai cin mutunci haka har ina!, a wanne garin mahaukatan ma ka taɓa jin an yiwa mace kishiya alhalin ko shekara bata rufa ba, ka tambayi uwarka kaji shekarun da ta rufa bata taɓa ɓatan wata ba kafin ayi mata kishiya, duk da dai na san cewa ba kowa ke zugaka ba illa waɗannan munfukan marasa yafiya da haƙuri".
ta faÉ—a tana nuna Hajiya Ramla da Hajiya Madina da baki tana bin su da harara.
"kuskure uban waye ba ya yinsa, haka laifi uban waye ba ya yinsa, ku waye ya san adadin laifin da ku ka yiwa ubangiji kuma ku ka roƙe shi ya yafe muku. dan uwar yarinya tayi masa laifi ai ba yana nufin yarinyar ce da kanta tayi masa ba, ku wa yasan kalar mutanen ma da ku ka yiwa sharrin da yafi wanda tayi masa, kuma naga dai anyi shekara da shekaru da yin abun, kuma ke Madina bace kika yi kun yafe ba, amma saboda dai zuciyarki baƙa ce sai yanzu za ki wani fa-ke da abunda aka riga aka manta da shi, saboda dama kina baƙin ciki da gatan da Allah ya yiwa Ilham wanda ƴaƴanki basu samu ba, to kuwa sai dai ki haɗiyi zuciya ki mutu domin gata da mulki da jin daɗi da ilimi da tarbiyya Ilham ta yiwa ƴaƴanki zarra, har a naɗe duniya kuma ba zasu samu abunda ta samu ba".
ta maida hankalinta kan Turaki,"mara imani wanda bai da tausayi, yarinya bata da lafiya amma ka iya tsallaketa kasa ƙafa ka bar gidan saboda ga ka baƙin mugu azzalumi, to idan ba ka sa ni ba ka sa ni, akan Ilham ina iya ɓatawa da uban kowa, in nace uban kowa har da nata uban kuwa, ka ga kenan naka uban ba komai ba ne a idona. saboda haka yanzu tun muna ta lafiya lafiya ban ja abinda zai hana kowa kwanciyar hankali ba to ka miƙe ka wuce muje ka kaita asibiti, shege ɗan banza ka samu ka ɗirkawa yarinya ciki shi ne za ka watsar da ita, to miƙe mu tafi, alhakin kulawa da ita ai akanka ya ke yanzu ba'a kan iyayenta ba".
shi dai kansa har lokacin na ƙasa yana ta kallon rubutun sakin da yay, ya rasa gaba ɗaya me ma yake ji a tare da shi, tsabar bala'in ciwon da kansa ke yi masa ji yake kamar zai bar jikinsa.
sai da Boɗejo ta kai bakin ƙofa tukunna ta waigo tana ƙara cewa,"wai kuwa ba zaka taso ba?, ka san Allah in har wani mummunan abu ya sami Ilham sai nasa an ɗaureka".
tayi ƙwafa tana bin su Hajiya Madina da wani kallo na ban haushi tace,"algungumai duk ku biyun da ba ku da aiki sai saka yaro agaba kuna kimtsa masa yanda zai bijirewa umarnin ubansa, yau zan gani sai dai ko ni ko ku acikin gidan nan muddin ba'ai abunda nake so ba, dan ya zama dole yau a saki waccan yarinyar, domin a yanzu dai Ilham ba zata zauna da ita ba har sai ta haife abinda ke cikinta, zan nuna muku na isa zan kuma nuna muku kaf a ƙasana ku ke, munafukai biyu masu son raba zumuncin ƴan'uwa, abokan sheɗ...".