← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 176

Sashe 20

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kakan tace,"ni ce, ai da suka zo dubani ɗinne sai shi Yayan Zaytunan ke cewa ina da buqatar asamin ruwa domin na samu ƙwarin jikina. yana zaune anan ya kira likita yazo ya dubani shine har ya biya kuɗin waɗannan magungunan, ina ji likitan yana lissafin kusan dubu takwas Halimatu...ai yaran nan sunyo halin iyayensu".

a lokacin hannu Fillo tasa ta goge hawayenta bata ce wani abuba. kuma tun daga ranar kullum sai Turaki yazo ya duba jikin Kaka sati guda kenan. ita bata ma san shine Turakin da tai kasada akansa ba sai ranar da Hajiya Madina ta aikata ɓangarensa tace tai gyara. anan ne tana shiga taga lafcecen enlergment ɗinsa a jikin bangon bedroom ɗin wanda daka shiga shi zai fara maka maraba.

kuma a sannan babu hoton abinda ya shiga haskawa a idonta sai na sunansa dake jikin wannan farar takardar da ta ƙona, kamar yanda akai rubutun manya ajikin hotonsa haka ma yake a jikin takarda. tarin tambayoyi da mamaki suka maƙale a kwanyar tunaninta.
tambayoyin da ta ƙudurcewa ranta son sanin su nan kusa bada jimawa ba in har taci gaba da zuwa aiki, tunda Hajiya Madina tace ko da Kaka taji sauƙi ba zata dawo ba ita zata ci gaba da aikin.

dan sosai Hajiya Madina ke sonta, tunda ko da akace za'a ƙaro wasu ƴan aikin tace a'a a barsu ita Halimatunta kawai ta isheta yanzu, inma zaa ƙaro to a ƙaro ɗaya saboda kar aikin yay mata yawa, kullum cikin yabonta take tace bata taɓa ganin yarinya me hankali da natsuwa ba irinta, hakan yasa ta ke jin daɗin aikin sosai.

ko a ƴaƴanta ma da Samha ne kawai basa wani ɗasawa amma ko Khalil idan ya ganta ya dinga tsokanarta da Sojan Rana. kuma sau tari indai Hajiya Madina na parlo sai tace itama ta zauna ayi kallon tare da ita, Turaki ne ma ta fuskanci kamar baya so talaka ya raɓe shi, shi yasa fuskarsa kullum ɗaure ta ke akanta, ko da yake ba ita ɗaya ya kewa hakan ba har ƙannensa idan aka cire Zaytuna da Khalil.

saurin da ta ke yanzu ta gama yankan farcen ta wuce don taji Hajiya Madina na faÉ—in yau zasu unguwa duka gida.

Kaka ta katse shirunta da cewar,"kin kuwa É—auki namanki?".
ta É—ago tace,"aina?".
Kaka tace,"a'a na aje miki nama cikin farar robar nan, da za ki wanke-wanke ba ki gani ba?".

"ni banga komai aciki ba, ƙila Maijidda ta shigo ta wawashe shi...wa ya kawo miki nama dama?".

Kaka ta dire wani hijabi da ta ke linkewa tace,"Yayan Zaytuna ne ya shigo jiya da daddare, ba ki jima da kwanciya ba lokacin...nace masa ai ma na gama warwarewa lafiya ta samu dan jibi ma zan dawo aiki shine yace a'a nai zamana na ƙara hutawa tunda akwai me taimaka min, koma da babu a nemo wata".

Fillo ta miƙe ta ɗauko tsintsiya tana share wurin da ta ɓata tace,"an gode masa...yana ta abu na masu kirki alhalin ba haka yake ba".
Kaka dai shiru tayi, ita kuma ta ɗauki hijabi tana ce mata. "zan tafi Kaka. yau babu kula da buƙatun ɗan gwal da wuri zan dawo dan naji Hajiya tace zasu je unguwa".

Kaka tace,"sai kin dawo ki gaida Hajiyar".
tana fitowa haraba sukai kiciɓis da Maijidda, Fillo ta tsaya tana kallon yanda ta ke jera hamma daga gani kaga wadda ta taso a bacci.

Maijidda tace,"yauwa dama wajenki za ni". ta faɗa tana miƙa mata wayar hannunta tace,"Amir ne ke kira tun asuba".

Fillo ta kallesu ita da wayar kafin tace,"kuma ai sai kice masa bama tare". Maijidda tayi hamma sannan tace,"ai yaƙi gane wannan bayanin, ni dai ungo idan kin gama kya kawo wallahi mugun bacci ke idona".

ba tare da Fillo ta karɓa ba tayi gaba abinta da cewar,"sai ki faɗa masa kinzo ba ki sameni ba".
Maijidda tabi bayanta da kallo tana faɗin,"ni ban iya ƙarya ba, Allah haka zan faɗa masa kince idan yazo ya sameki acan".

a parlo ta samesu kaf ɗinsu, ita kam rayuwarsu na burgeta. ta durƙusa ta gaida Hajiya Madina. Hajiya Madina ta ajiye hisnul muslim ɗin dake hannunta a gefenta, sannan ta zare medical glass ɗin dake a idonta ta saka shi cikin box ɗinsa. ta kalli Fillo da fara'a tace,"Halimatu kin shigo?".

kan Fillo a ƙasa tace,"ehh Hajiya, Kaka na gaishe ki".
tace,"ina amsawa, jikin nata da sauƙi dai ko?".
"ehh taji sauƙi ai, tama ce zata shigo gaida ki zuwa anjima".
"a'a ita da ba ƙwarin jiki ba, zan shiga na dubata insha'Allahu...yanzu maza ki fito da break fast naga already Zaytuna ma ta kammala komai".
ta amsa da,"tou". sannan ta miƙe ta wuce kitchen din bayan duk ta gaida yaran.

a kitchen ta sami Zaytuna tana ɗauraye hannunta, ta ƙarasa tana yi mata sannu da aiki. Zaytuna tace,"yau kinyi late".
Fillo tai ɗan murmushi tace,"na tsaya yima Kaka aiki ne zata yi baƙi".
"oh Allah sarki, jikin nata dai da sauƙi ko".
"ehh taji sauƙi sosai".
"to Allah ya ƙara mata lafiya".
"amin ya Allah".

ta nufi drower ta taka kujera ta É—auko babban tray, Zaytuna na goge hannu a towel tace,"na kammala komai fito da su kawai za ki...kiyi da jiki dan Allah zamu fita ne har da Baffa".
"tom Adda".
Zaytuna ta dakata daga fitar da zata yi ta tsaya tana kallonta, ta girgiza kai kawai sannan tace,"wannan jiki naki Fillo anya ba sai mun nemi magani ba, komai kike salalo salalo kamar mara jini ajiki".

tana faÉ—ar hakan ta juya zata fita ta bar Fillo da Æ´ar dariya. Turaki ya shigo kitchen É—in ko maganar da Zaytuna ma ke yi bai tsaya sauraro ba. ya wuce kai tsaye wajen drink trolly ya É—auki mug, Fillo na shirin É—aukar tea flask ta É—ora akai muryarsa ta tsayar da ita, ita bata ma san da shigowarsa ba.

yo ita me ta sani da wani wait É—insa da zai ce mata wani wait, mutumin da ba zai yi hausa zalla ba dole sai ya haÉ—a da yaren da ita bata iya shi ba, ko da yake taga duka haka suke, shi yasa wataran suke shanyata a tsaye idan suka faÉ—i abinda bata sani ba, banda late da Zaytuna ta saba faÉ—ar mata shi har ta fahimci me hakan ke nufi to me ta sani bayansa.

dan haka kawai sai ta kuma yunƙurin ɗaukar tea flask ɗin, Turaki da idonsa ke kan hannun Flask ɗin da zata kama yace,"Wae ankam a iri 6iddo toi kam a nanako volwanego?". (wai ke wacce irin yarinya ce da ba'a faɗar magana kiji ne?)

kakkausar muryarsa a sama ya doka mata tsawar da ta saka ta ture flask ɗin ba tare da saninta ba, ya zamo zai faɗi ƙasa yay saurin isowa ya tare shi. kamar yasa hannu ya bibbigeta don haushi, shi haushinsa da yarinyar saurin rikicewarta akan abindai bai kai ya kawo ba. ga shi ya tsana yaga da anyi magana jikinta ya hau rawa, shi yasa ya cewa Maama su kaita asibiti a binciki lafiyarta.

ta ɗauki tsawon 2mints jikinta na rawa kamin ta daidaita, ta buɗe idonta da ta rumtse gam ta sauke kan dogayen yatsun ƙafarsa, sannan ta sauke hannunta daga kare fuskarta da tayi.
sai lokacin ta ɗago ido ta kalle shi, ita yakewa wani irin kallo da bata son gani a wannan ƙwayar idon nasa da bata kama da ta mutane.

muryarta kamar zata yi kuka tace,"Wadu munyal mi anda be min a vondi on". (kayi haƙuri ban san da ni kake ba).

ya zabga mata harara ya bar wajen, ya ƙarasa ya buɗe coolers ɗin da Zaytuna ta zuba kayan soye-soyen da tayi, ya zuba chips a plate sannan ya zuba tea a mug ya fice. Fillo tabi bayansa da ido kawai, ita bata tasa ta ke ba, burinta yanzu bai wuce ta sami damar ahiga ɗakinsa ba, ba tare da sanin kowa ba ta gudanar da abinda zata yi.

shi yasa ta ƙagu suyi-suyi su fice.
[8/12, 08:00] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*©️Halima h.z*

*12*
bayan ta gama jera komai a dining tazo ta tsuguna gaban Hajiya Madina. "Maama ko mai ya kammala". sunan da yaranta ke kiranta da shi itama da shi ta ke kiranta, Hajiya Madinar ta faɗa mata haka a watarana, sanda ta ke ce mata. "Fillo ban taɓa ƴar aikin da nake jinta tamkar ƴar cikina ba irinki, saboda haka daga yau Hajiya ya fita daga bakinki, ki dinga kirana da Maama kamar yanda kika ji ƴaƴana nace min kinji".

Hajiya Madina ta shiga kallonta ta wutsiyar idonta ba tare da ta amsawa maganarta ba, Fillo kuma dai har yanzu tana nan durƙushe bata motsa ba, kuma tunaninta bai bata ko Hajiya Madinar bata ji ba ne, a'a tasan taji kawai dai a jininsu ne basa amsa maka nan ta ke sai sun ɗan ɗau lokaci.

"oak tom, kije ki zuba naki kici". abinda Hajiya Madina tace da ita kenan. Fillo ta miƙe ta wuce, sannan suma suka nufa dining, by the time Turaki har ya gama nasa, yana zaune wajen yana aikin danna waya.
suna cikin yin breakfast ɗin ne wayar Nihal tayi ƙara, ganin sunan dake yawo jikin screen ɗin wayar gabanta ya faɗi, jikinta na rawa ta kai hannu tana gyara zaman medical glass nata, ta cikinsa ta ke kallon Hajiya Madina wacce ta dakata da cin abincin tana yi mata wani duba ta ƙasan ido.

duk ta dabarbarce, tsoronta Allah tsoronta kar tace ta miƙa mata wayar. saboda haka tayi saurin kai hannu tai mute na ringing ɗin, sai dai kamin ta ɗauke hannunta daga kan wayar sabon kira ya ƙara shigowa. babu shiri ta haɗiye wani dunƙulallan yawu tare da rufe ido.
sai dai kamin ta buÉ—e maganar Hajiya Madina ta shiga cikin kunnuwanta.

"give me the phone". kamar zata yi kuka ta ɗauki wayar hannu na rawa ta miƙa mata.
Hajiya Madina ta kashe wayar gaba ɗaya sannan ta miƙawa Khalil, ya karɓa ya saka a aljihunsa.
har suka kammala breakfast ɗin babu wani wanda yay motsi na hira ko kuma tsokanar juna kamar yanda suka saba da mahaifiyar tasu, saboda yanayin da ta tashi da shi yau sun kasa gane kanta, ga shi Nihal ta ƙara dagula musu ita.
Chapter 20 · 0% Book details