Sashe 25
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a parlon BoÉ—ejo Fillo ta tarar da Turaki hakimce akan kujera ya zubawa tv dake kunne ido, kallo É—aya zaka yi masa ka gane kallo kawai yake amma ba don yana fahimta ba, dan gaba É—aya hankalinsa baya wurin.
tunda tayi masa kallo ɗaya bata ƙara ba, a iyakar wannan kallon ta gane cewar yana ɗauke da damuwa, wata damuwa da yake so ya rabu da ita.
dole ta gabansa zata wuce kafin taje bedroom ɗin Boɗejo, ta durƙusa a gabansa tace,"ina yini". bata sa ni ba ya amsa ko ba amsa ba, ta tashi ta bar wajen.
tana ajiye glass É—in ta fito, zata fice daga parlon taji muryarsa yace,"ban ruwa".
sai kawai ta tsaya tana kallonsa da mamaki, anya kuwa da ita yake?, ba shine rannan yace ko ruwan goran da zai sha ba karta ƙara ɗora hannunta akai ba.
"ba kiji bane?". maganarsa ta katseta daga tunaninta, ta É—ago suka haÉ—a ido da shi, tayi saurin É—auke nata ta nufi hanyar kitchen, lucky kawai tayi amma ba don tasan nan ne kitchen É—in ba, har ta shiga kitchen É—in tana jin idonsa akanta.
ta dawo ta ajiye masa ruwan akan table ɗin dake gabansa, har ya zuba ruwan ya sha bata miƙe daga tsugunawar da tayi ba, kamar wadda yace mata tayi ta zama karta ta shi.
ƙwayar idonta ta jima akan yatsan ƙafarsa, sai can ta ɗan ɗago kai ta kalle shi, yasha ruwan amma still cup ɗin na riƙe a hannunsa, idonsa a rufe, haka kuma ya kwantar da kansa jikin kujera ya tusa ɗayan hannunsa cikin sumarsa yana yamutsawa.
kawai sai taji tausayinsa na gaira babu dalili ya tsarga mata, ta jima tana kallonsa ba tare da saninsa ba sannan ta tashi ta fita daga parlon.
zata shiga ɓangaren Hajiya Madina fitilar mota ta hasketa, tasa hannu ta kare tana kanne ido. sai sannan ta tuna ma da maganar Khalil na zasu asibiti, ita kam ai ko me za'ai ba zata je asibitin nan ba. ai dama ta gama ayyukanta, wurin Kaka zata gudu wadda ba zata takurawa ciwonta ba, dan haka da sauri ta ɗau hanya zata tafi sai ga Hajiya Madina ta fito.
"au baku tafi ba?". Hajiya Madinan ta tambayeta tana tsareta da ido.
tace,"ehh Maama yanzu dai zan tafi, dama nazo zan miki sallama ne".
Hajiya Madina ta tsaya tana kallonta, kamin tai tambayar da zata mata sai ga Khalil ya ƙaraso wajen, yana zuwa yace,"ɗauko mayafinki".
kamar zatai kuka tace da shi,"Hamma Khalil ai naji sauƙi".
baice komai ba Hajiya Madina tace,"me ya samu ƙafar taki dama?".
idanuwanta suka yi narai-narai tace,"gurÉ—ewa nayi É—azu da zan sauko daga bene".
Hajiya Madina tace,"ki dinƙa kulawa Fillo, je ki shirya kuje ya kaiki asibiti, duk ƙanƙantar ciwo bama barinsa sai anga likita".
ba don tana so ba sai dan ba yarda zata yi, saboda bata son yi mata musu.
a mota ta sami Khalil na jiranta, ta buɗe baya ta shiga, nan ma sai shine ya buɗe mata don bata iya ba. ƙamshin cikin motar daya gauraye da sanyin ac ya bata da wani daɗi, ta buɗe ƙananun ƙofofin hancinta ta zuƙe ƙamshin tana jin wani sanyi a ranta.
Khalil nata bin waƙar turancin dake tashi a motar, ita dai tayi shiru sai bin titi take yi da ido tana kallon hanya, rabon da ta fito har ta manta, kullum suna wuri ɗaya idan ba wani taro za'ai a masarauta ba shine har da su ma'aikatan ake tafiya, Maijidda ma ta fita yawo itace Yami ke yawan aikenta, ita kam Kaka da ta aiketa ma gwara taje da kanta.
a harabar asibitin yayi parking, tayi ƙoƙarin ganin ta buɗe motar da kanta, ta fito sannan ya sakawa motar key. "idan munje ki faɗawa likitan harda ciwon baki na damunki".
ya faɗa da sigar zolaya, tai ƴar dariya bata ce komai ba, tabi bayansa zuwa cikin asibitin. wani babban likita ne ya dubata, sai dai tasha kuka sosai saboda matsa ƙafar da akayi, sunan Kaka kuwa ta kira yafi sau biyar.
a wani pharmacy Khalil ya tsaya ya siya magungunan da aka rubuta masu yawa harda allurai.
tunda suka É—auko hanyar dawowa Fillo ke jin kanta na wani mugun sara mata, Khalil na kallon duk wani motsinta ta cikin mirrow, sai cije fuska take yi hawaye na sauka a saman kuncinta, bai ce mata komai ba don duk tunaninsa ko har yanzu kukan allurar ne.
ita kuwa kanta ke mata wani azababben ciwo, yayi mata nauyi kamar an É—ora dutse, ga shi sai take jin tsoron da bata san dalilinsa ba, ji take kamar ana tsoratata acikin kanta, kuma kamar kiranta ake ana tazo.
tasa hannu ta damƙe zanin jikinta, daidai lokacin da Khalil yayi parking a compound.
kusan tare suka fito daga motar, ya bata ledar drugs ɗin yana yi mata sannu. karɓa tayi tare da yi masa godiya sannan tayi masa sai da safe.
ɓangarensu ta wuce bata wani biya ta yiwa Hajiya Madina sallama ba, tana tafe tana haɗa hanya saboda ganinta dake neman ɗaukewa gaba ɗaya, a yanzu ta manta da ciwon dake ƙafarta, ta ciwon kan kawai take yi.
duk da uban hasken fitulu dake gauraye da harabar gidan amma ita wani duhu take gani na daban, ta damƙe kanta haka har ta kai ɗakinsu, kuma sai lokacin ne taji idonta ya washe, ta buɗi baki tai sallama cikin ɗakin.
jin yanda tayi sallamar Kaka ta kafe ƙofar ɗakin da ido har ta shigo, tabi ta da ido har ta nemi wuri ta zauna tana jefar da ledan tulin drugs ɗin. sannan ta ƙara fashewa da wani kukan.
Kaka ta katse lazimin da take yi tace,"ke Lafiya?". tayi shiru bata ce komai ba. Kaka ta É—aga murya sosai,"kin san dai bana son shashanci ko Halimatu, menene ya faru?, wani kuskuren kika aikata?".
ta ɗago tare da girgiza kanta alamar a'a. Kaka tace,"to menene?, wadda kuka baya yi mata wahala". bata yi magana da baki ba sai nuni ta yiwa Kaka da ƙafarta.
Kaka ta kalli ƙafar da ta kumbura tace,"subhanallah garin ya?".
da ƙyar ta buɗi baki tace,"nazo saukowa a bene na gurɗe". Kaka ta kawo hannu zata taɓa tayi ƙara tana janye ƙafa tana cewa,"Kaka akwai zafi fa...yanzu ma daga asibiti muke sun ƙara karyani shine kika ga ta kumbura haka, saura kaɗan na mutu Kaka".
Kaka nayi mata wani kallo tace,"kice gata suka yi miki...to sannu sai ki daina kukan, ke idan ba'ai miki hakan ba kina zaton zuwa safiya za ki iya motsar kafar ne ma, Allahk dai ya sakawa Hajiya da alkhairi". sai sannan Kaka ta kai idonta kan ledar maganin da ta yasar can gefe, tace da ita,"ledar kuma ta mene?".
tana shaƙar majina tace,"wai magani ne". Kaka tace,"wai kuma haka za ki ta shansa ba har sanda Allah zai kawo miki sauƙi".
Fillo taiwa Kaka da maganin wani kallo ta wutsiyar ido, Kaka na ganin hakan ta miƙe ta ɗauka ledar tana faɗin,"jefar da magani a bola ai ba wahala yake miki ba, gwara na ɗauke nayi masa guri tun ba kisa anyi asarar kuɗi ba...dan na san kuɗi ne bana wasa ba aka kashe".
Kaka ta shige cikin ɗaki da ledar maganin dan yi musu wajen ɓuya. kuma tana shiga aka saki wata uwar tsawa a tsakiyar kan Fillo, ta buɗa baki zata yi adu'a da ihu sai taji ta kasa, ta ya zata kwatanta?, wani irin ciwo take ji acikin kanta da ba zai kwatantu ba, ita ɗaya tasan azabar da take ji, ga gefen cikinta ma da takeji kamar ana caccaka mata allurai.
kira kawai take ji acikin kanta, kira daga muryar da bata san ta ko waye ba, kuma muryar da bata taɓa ji ba. _"zo da nisa, maza zo da sauri"_. wannan kalmar ita ake ta faɗa mata, ta kai hannu ƙugunta ta damƙe wannan dunƙulallan asirin da ta ɗauko, kuma kamar wadda aka tsikara tayi zumbur ta miƙe ta fice daga ɗakin.
lokacin da Kaka ta fito daga É—aki sai tayi tunanin ko ta shiga banÉ—aki ne, hakan yasa bata nemeta ba, har ta girgiza kai tana faÉ—ar Allah ya kyauta raki irin na Fillo, bata san ya za'ai ba idan tazo haihuwa.
kuma sai bayan minti goma sai ga Maijidda ta shigo ɗakin neman Fillo, Kaka wadda har ta kwanta a lokacin tace mata,"yo aini nayi zaton wurinku ta nufa, ta shigo tana kukan ciwon ƙafa to nama zaci banɗaki taje, dana ji shiru kuma nace ƙila tayi wajenku".
Maijidda ta zauna tace,"bata je ba Kaka". ta faɗa muryarta na nuna rashin jin daɗi. Kaka tace,"ƙila can cikin gidan ta koma, yanzu ai zaki ganta tunda ba can dai zata kwan ba, yanzu haka tayi mantuwar wani abu ne shi yasa ta koma".
Maijidda dai tayi shiru bata ce komai sai ɓata rai ta ke, Kaka na kallonta dai bata tambayi ba'asi ba, saboda tasan kwanan zancen, akan dai Fillo ne da basa zama tare yanzu shine take ta yin wannan kumburin.
shiru-shiru Fillo bata dawo ba sama da kusan rabin awa, Maijidda lokacin itama har ta fara hamma. ta fara masifar ita wannan aikin bata sonsa sam, zata sa Yami ta nemi wata yarinyar akai musu a ƙyale mata ƙawarta.
Kaka tace,"to wai ke Maijidda iyaka akayi miki da shiga cikin gidan da ba za ki dinga binta ba ko me?, ba sai ma ku dinga yin aikin tare ba".
Maijidda tace,"ni bana son shiga wurin da za'ake min gani gani Kaka, tunda sun san basu É—aukeni aiki ba ina zuwa za'a fara min tambayar yanda Uwata ta haifeni".
Kaka tace,"aiko dai kin yiwa Hajiya sharri dan ba haka halinta yake ba...zaman jira ne kuma sai kita zama karki yi bacci har sai ta dawo, waya san ma ko acan zata kwana tunda har ta kai wannan lokacin...to ni dai na kwanta sai da safe".
Maijidda dai tai zaune jugum tana sauraron radion Kaka dake kunne, har lokacin da gidan radion suka tashi a aiki. daga ƙarshe dai data gaji da jira ta tabbatar Fillo ba dawowa zata yi ba ta tashi ta rufe ƙofar ɗakin sannan tabi Kaka ɗakin ta kwanta itama a inda Fillo ke kwanciya.