Sashe 28
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
haka sukai ta hira ba tare da sun san lokaci ya tafi ba, Fillo sam ta manta ma a inda suke, sai da mai gadi ya ankarar dasu. cike da kunyar mai gadin ta bar wajen dan idan ta biye ta Amir ba zasu tafi haka ba, yana faÉ—a mata wai yau subscription zai yi.
bin ta yayi a baya yana ta murmushi, tsaye ya sameta a gate ɗin da zai shigar da kai ɓangaren ma'aikatan gidan, tana ta jan yatsun hannunta kamar yanda hakan yake sabonta ne.
ya jingina da ƙofa yana kallonta yace,"wai kuɗi kike lissafawa a jan yatsun nan ko me?".
idonta na ƙasa ta jinjina kai,"ehh kuɗin ɗangoten Gombe nake ƙirgawa".
yay murmushi yace,"Allah ya amsa". itama tace,"amin". sannan ta kalli yanayin garin da magriba ta ƙarato tace,"muyi Sallama su Hajiya na kan hanya, kuma akwai sauran aiki gabana".
yace,"aikin me?". tace,"Adda Samha ta bar min guga kuma tana da yawa, gata bata da sauƙi mafaɗaciya ce".
"barkono ce ita?". tace,"kafi barkono in kaji ana faÉ—a".
ya kalli agogonsa yaga har ƙarfe shida da minti goma, ya sauke numfashi sannan yace,"to sai yaushe?". daga yanda yay maganar sai yay mugun bata tausayi, itama ba dan tana so zasu yi sallamar ba, lokacin da bata fara aikin ba ai babu ruwanta da wani kallon lokaci, ko zasu kwana suna shan soyayyarsu babu mai katse su.
"kawai zance banda lafiya kaga zan huta ranar". ya ɗan zaro ido waje yace,"a'a bana so kiyi ƙaryar ciwo, kawai dai zan ƙara dawowa".
ya faÉ—a yana jan É—an cif-cif É—in gemunsa. "a'a ni kam ban yarda kazo ka ban kunya ba". ta faÉ—a tana kama gefen hijabinta.
yace,"ohh kina jin kunyar kar suga saurayinki ba É—an gayu ba kuma talaka ko?, alhalin ke me kyau ce".
tayi saurin girgiza masa kai yanayin fuskarta na sauyawa,"ko kaɗan ba haka bane, dan Allah karka ƙara wannan tunanin Amir, ba zanji kunyar nunaka a koma ina ne ba wallahi, kai nake so ba gayunka ko kuɗinka ba, kuma so nake maka na tsakani da Allah". tayi naganar kamar zata yi kuka.
"bance ki zubar min da hawayenki ba, kin san suna da tsada...na faɗa ne dan na zolaya, kiyi haƙuri".
tai knodding kanta kawai, kamar ba zasu yi sallamar ba, sai da tayi da gaske tukunna sukai sallamar ta juya ta tafi, kuma tana cikin tafiyar ne ya dakatar da ita da tambayar me ya sami ƙafarta, dan a ɗazu bai lura ba sai yanzu. tace masa babu komai tsayuwar da sukai ne yasa ƙafar yin tsami, ba don ya yarda ba sai dan karya takura mata ya ƙyaleta.
sai bayan isha'i mutanen gidan suka dawo, bata ma san sun dawo ba saboda lokacin tana É—akin Æ´an aiki zaune cike da kewar Kakarta, yanza basa yini tare ko kaÉ—an, da dare yayi sai safiya ta taho aiki.
tayi zurfi cikin tunani taji wayar ɗakin na ƙara, tana ɗagawa taji muryar Zaytuna na cewa da ita,"kina ina ne?".
tace,"laa Adda kun dawo, banji ƙarar mota ba". Zaytuna tace,"to kizo". ta ajiye wayar ta miƙe tana jan ƙafar dan sam bata so a gane ciwon dake ƙafarta.
Boɗejo kawai ta samu a parlon, ta ƙarasa ta tsuguna ta gaisheta. sannan ta tashi zata hau upstairs, Boɗejo ta tsayar da ita.
"kinga ke ƴar nan zo kai min idon baturen nan nawa ɗakin kwana na". Fillo ta rissina ta karɓa, Boɗejo ta kalleta tace,"ke kuma zuwan yaushe?". tace,"ban jima ba". "Allah sarki, to sannu Allah yayi miki albarka". Fillo tace,"amin". Boɗejo tace,"to ɗakin nawa kin sa ni ne?". Fillo ta girgiza kai alamar a'a.
Boɗejo ta ɗora ƙafarta kan tumtum ɗin dake ƙasan carpet tace,"can ɓangaren ƙarshe nake kusa da su Turaki, nan suka wullani wallahi daga ni sai halina, kamar ba saurauniya ba ada".
ta jefa wata choculate a baki ta ƙara cewa,"ai da mijina shine sarkin garin nan, to daya rasu ne kuma ɗana Habibu ya hau kan kujerar...kin ganni kamar ban haɗa jini da sarauta ba ko?, wallah bata dameni ba in faɗa miki ƴar nan, banda ma dai Allah ya ƙaddara da hakan ai bata faru ba, shi yasa ko ƴar izzar nan ma ta masu sarauta banda ita, sha'anina kawai nake ba zan iya takura kaina ba wallahi, ina dalili. me gidan nan aini ya biyo, idan kika gansa ba kyace Yarima ba, shi dai Habib ɗin dama da kin gansa kinga wanda sarauta ke yawo a jininsa, aishi wannan Yaron na gidan nan yayo, umm Turaki ba wallahi kam...sauran yaran Ibrahimu da Samir za ki gansu kamar ƴaƴan tsintuwa".
Fillo dai murmushi take tayi, taji sosai tsohuwar ta burgeta. "ba kya magana ne?". Fillo ta girgiza kai tace,"a'a ina yi Hajiya". Boɗejo tace,"auyo ni fa nace ai da an banu...ba ki da magana dai ina ce ko?, dama ai ba kiyi kama da sauran ƴan aikin ba iyayen zuba kamar tsohuwar kanya, wallah na faɗa miki su nan suke zubewa su sakani gaba inta basu labarin masarauta wai suna so, ita surukar tawa tayi ta jin haushina, itama wannan ƴar Samha taita ɓata rai wai ita ba haka ƴan sarauta suke ba, to ni dai basu isheni kallo ba ma dan bana bi ta kansu, ina dalili ka takura kanka akan wata banzar aba sarauta".
Fillo tayi murmushi me sauti still dai bata ce komai ba, haka kawai taji tana so ta ɗauki lokaci tare da tsohuwar suna hira. sai yanzu Boɗejo ta bata glass ɗin dake cikin box ɗinsa tace,"idan kinje sai kin kunna fitilar ɗakin dan ba lallai bane an kunna min, tunda me ta'adin Sameer baya nan can muka baro shi gidan Hakimi...akan mudubi kawai zaki ɗora min shi kinji ki riƙe da kyau kar ya fashe, na huɗu kenan da Habib yasa akayo min shi daga dubai, da yake acan ake duba min lafiyar idon".
Fillo tace,"to Hajiya". Boɗejo tana kallonta sosai tace,"a'a wallahi sunana Rumana ko kuma kice min Boɗejo kamar yanda jikokina ke kirana. ina wani batun Hajiya anan salon dai a ƙarawa mutum jin kai, ai da Hajjah suke ce min, Mai Martaba na rasuwa na rufe ido nace ko Rumana ko wani sunan, to shine fa baturen yaron nan ɗan gidan sarki Habib ya saka min Boɗejo, da ike shi ne jikana na farko, kai izza acikin yaron nan kamar ba zai taka ƙasa ba".
tana faɗar baturen yaro Fillo ta gane Yarima Abbas take nufi. "kema ɗakin kwanan masu aikin kike?". ta girgiza kanta,"a'a wurin Kakata nake". "can da nisa ne kenan?". "a'a Boɗejo nan ɓangaren ma'aikata, nan muke da zama".
BoÉ—ejo tace,"auyo ce min zaki tsaffin bayina ne ku, to ai shikenan dama ce nake nan kike kwana nace to kizo É—akina mu kwan tare dan sosai na yaba da hankalinki wallahi".
Samha ta faɗo ɗakin rai ɓace, tana jifan Fillo da wani irin kallo tace,"ke dan Uwarki ina aikin da na saka ki?". maimakon bata amsa sai kallo da Fillo ta bita da shi, cikin ranta tana maimaita dan uwarki, kalmar da ta jima bata ji an faɗa mata ba.
"ba magana nake miki ba?".
Fillo ta rufe ido tana jin zuciyarta na suya sannan ta buɗe tace,"Adda Samha ai nayi". "kika yi a gidan uban wa?. bance miki acikin trolly za ki jerasu ba, gobe da asuba zan bar ƙasar". sai taja tsaki tace,"ni ba'a taɓa bagidajiyar ƴar aiki ba sai akanki wallahi, to minti uku na baki kije ki kammala shiryan kaya tun ban nuna miki other side of me ba".
a sanyaye Fillo tace,"kiyi haƙuri don Allah, zan gyara yanzu". ta faɗa tana barin parlon, guntun hawayen dake maƙale a idonta ya sauko, a rayuwar nan ko mene zaka yi mata kayi amma karka sako mahaifiyarta aciki, bata so, bata so ko kaɗan.
kuma ɗazun sha'afa tayi gaba ɗaya, ta gama gugar sai ta zuba cikin wadrobe tana ta sauri saboda ƙafarta da ke mata zafi, amma tana ta alla alla kafin su dawo taje ta gyara.
Boɗejo ta kalli Samha tace,"ki dai dinga bin duniya a hankali, ni wallahi duk kece me ɗaukan duniya da zafi su dai su Zaytuna basu ɗorawa kansu wannan masifar ba...yo Samha kuɗin ubanki ɗin me?, shi ya bawa kansa?, to in gaya miki nan da kika ganni kafin Babana ya zama wazirin Sarki kika ganmu sai kin tsartar da yawu, to amma yau fa?, matar wa na zama kuma yanzu uwar su wa na zama?, kuma wane irin matsayi na taka?...to wallah kaɗan daga cikin ikon Allah kiga ƴan aikin nan da kike narkawa uwar tsawa kullu yaumin sun lula sama ke kuma kina nan ƙasa".
"wallahi ba amin ba, wannan ai mugun baki ne BoÉ—ejo". Samhan ta faÉ—a tana wucewa ta haye sama.
a bakin side ɗin su Turaki, Fillo tazo wucewa zuwa part ɗin Boɗejo, Khalil dake balcony a tsaye yana waya idonsa ya sauka akanta, ya lura da yanda take ta ɗingisa ƙafa tana tafiya da ƙyar.
ya sauke wayar daga kunnensa ya kalli adadin minutes É—in, sannan yace,"please hold on 2minutes". daga haka ya aje wayar nan kan table ya fito.
"Fillo". kiran sunan nata ya dakatar da ita daga tafiyar, muryar Kalil taji, amma ko da ta juyo maimakon ta gansa sai taga Turaki na tunkaro inda ta ke.
*Please comment, Share and Vote pls.*
[8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
*©ï¸Halima h.z*
_avoid any mistake plssðŸ™._
*16*
*Shongom LGA, Gwandum, Yabayo village.*
rubutun da map location ɗin ya zana kenan ajikin wayar dake riƙe a hannun Khalil. with high speed yake drving motar kamar zai tashi sama. adu'a yake cikin ransa Allah ya kaisu lafiya, idan ba haka ba za'a iya samun gagarumar matsala a wannan tuƙin nasa, saboda kukan mahaifiyarsa dake gigita hankalinsa da tunaninsa, da kuma tunanin halin da ɗan'uwansa, Yayansa mafi soyuwa a gare shi yake ciki.
tunda suka taho kuka kawai takeyi, duk wata magana ta kwantar da hankali ya faɗeta amma taƙi tasiri a gareta, ya rasa me kuma zaiyi, yasan dai ba zata taɓa natsuwa ba har sai sun isa inda take da buri, to amma atleast yana so ta tsayar da wannan kukan nata ko dan ya samu yayi tuƙin nan lafiya.