← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 166 OF 176

Sashe 166

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hannun Turaki ya shiga cikin maƙarar, ya tallafo kan gawar, yasa ɗaya hannun ya yaye linkafanin ya tsayar da shi daidai wuyanta, inda fuskarta kawai suke iya gani, fuskar da suke gani tamkar zata yi musu magana.
muryarsa ta fito cikin sanyi, ya shiga jero tarin adu'oin da ya san su na cikin kansa, yi yake yi yana ƙara maimaitawa, har tsawon lokacin da bai san ya ɗauka ba me tsayi, har sai da Baba Nafi'u yasa hannu ya dafa kafaɗarsa yace,"ya isa haka Turaki".

shi kaÉ—ai ne ya iya yi masa magana domin ko Baffa ba zai iya ba a wannan lokacin, shi kansa ya kifa kansa yana hawaye kamar yanda Hajiya Ramla da Æ´aÆ´an suke yi.

"ke kam taki tayi kyau Madina, tabbas ke É—in Æ´ar aljannah ce, ki yafe min Madina, don Allah don Annabi ki yafe min".
muryar Boɗejo suka ji ta amsa acikin ɗakin, a sanda take isowa wajen, kuma kukan da yaci ƙarfin ya hanata ƙarasa abun da zata faɗa.

har aka yi sallar jana'iza Turaki da Khalil basa cikin hayyacinsu sosai, a tsaye kawai suke, hannayensu sarƙe dana juna, yayin da idanunsu ke kafe akan makarar da ke ɗauke da gawar dake gabansu.
da ga bayan su kuma tarin ɗumbin jama'ar da ba zasu ƙirgu ba ne, don jama'ar gari yara da manya sun halarci jana'izar.

ƙarfe shida na yamma aka kai Hajiya Madina ƙabarinta, inda ɗumin jama'ar da suka fi ƙarfin ƙirga suka yi mata rakiya zuwa gidanta na gaskiya.
acikin shirun da ya ratsa maƙabarta, babu sautin muryar da kake ji na tashi sai na manyan mutanen dake cewa.

"yauwa bismillah ku biyo ta nan".

"yauwa jama'a a É—an gyara".

"ku riƙeta sosai".

"to ku miƙota nan".

"yauwa to ku ajiyeta nan, masha'Allahu!".

mutanen da suka ratso ɗauke da gawar ta cikin tarin ƙaburburan dake jere a cikin maƙabartar. suka ajiye makarar a bakin ƙasar da aka tone, kusa da ramin da yake gida matabacci, kuma gida na ƙarshe ga kowanne bawa, gidan da ke jiran duk wani mai rai, gidan da yake iri ɗaya da na me kuɗi da na talaka.

Turaki da Khalil na tsaye kusa da juna, tsayinsu kusan ɗaya, zuciyar kowanne na tunani kala-kala a game da mutuwar da ta riske su a yau. abun da basu taɓa zato ba, abun ba su taɓa kawo shi nan kusa ba.

"Bismillah".

Muryar limamin masallacin unguwar ta janyo Turaki da Khalil daga dogon tunanin da ƙwaƙwalwar su ta faɗa, suka juyo a tare suka kalle shi, sannan suka kalli gawar dake gabansu, wadda aka fito da ita daga cikin makara, a lokaci ɗaya suka tsinci kansu da tarin ruwan hawayen da ya bar idon su tun ɗazu.

a hankali Turaki ya durƙusa daidai kan gawar ya tallafo kan, Khalil da Samir da Baffa da Wan Hajiya Madina da Liman suka tallafi sauran jikin, sannan suka haɗu wajen zura gawar a cikin ramin ƙabarin.

lokacin da suka zura gawar acikin rabin ƙabarin, zuciyar kowannen bawa dake wurin ta matse da ƙarfin imanin dake ƙaruwar a ƙirjinsa, tabbas duk wanda bai yarda da Ubangiji ba yayi asara, asara mai girma kuwa, haka duk wanda bai tuba ba kafin mutuwa tabbas yay babbar asara.
idanuwan Turaki suka tsaya cak akan farin likkafanin, yana kallon yacca ake mayar da ƙasar da aka haƙe ana rufe gawar gawar da ke ciki, har sai da hasken likƙafinin ya dusashe, yayin da tukwane da tudun jar ƙasa suka shafe shi gaba ɗaya.

daga wannan lokacin kuma ƙwaƙwalwarsa bata ƙara wani tunani ba, komai da ke cikin kansa ya zame yabar shi.
abin da zai ce yana iya jiyowa a duniyar da yake jinsa kamar ba'a cikinta ba, tarin adu'oin dake fitowa daga bakin liman, kafin a hankali kuma ya fara jin sautin wani abu na shiga kunnensa, sautin takun ƙafafu su na juyawa su na barin wajen.

sai ya kalli nasa ƙafafun, sai yake ganin tamkar ba zai iya ɗaga su ba, tamkar sun ƙame anan kenan har sanda tasa mutuwar zata zo ta riske shi.
yaji an riƙo hannunsa, da ƙyar ya iya ɗauke idonsa akan ƙabarin, ya juya ya kalli Baffa da Khalil, kafin ya ɗaga ƙafarsa a hankali ya fara tafiya da baya, a haka ya dinƙa tafiya da baya har ya bar cikin maƙwabartar, yana tafiya yana barin Hajiya Madina, yana kusantar gidan da zai koma a yau rana ta farko ya riske bata cikinsa, rana ta farko da zai koma bai ji muryarta ba na kiransa da wannan sunan da ita kaɗai ta raɗa masa, kuma ita ɗaya take kiransa da shi, Me Babban Suna!.

yaji wani uban gumi ya keto masa, ya wanke masa dukkan ilahirin jikinsa, a hankali kuma ƙwaƙwalwarsa ta karanto masa kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
shikenan sun yi tazara, tazarar da ba zasu ƙara kusantar junansu ba.

a lokacin da suka koma gida, tsakanin Khaleel da Turaki sai aka rasa wanda ya riga wani shiga É—akin Hajiya Madina, an dai gansu sun shigo sun tsallake tarin mutanen dake zazzaune.

a cikin ɗakin na Hajiya Madina, Khalil na zaune a ƙasa, idonsa na manne akan gadon inda tayi baccin ƙarshe a duniyarta, yau rana ta farko da ya shigo ɗakin bai ganta ba kuma ko da ya zauna zaman jiranta ba zata shigo ba, shikenan ta tafi tafiya ta har abada, sun zama marayu, yanzu ba su da uwa, wannan jigon na jin daɗin duniya.
a hankali yaji hawaye na sauka akan kumtunsa, masu ɗumi da yawan da yaji kamar an buɗe bakin famfo, kukan da bai yi ba tun a ɗazu shi ya taho a yanzu, kawai sai ya ajiye dukkan dauriyarsa, yay ƙasa da kansa, ya runtse idonsa da yake ganin hoton mahaifiyar tasa na haska masa, don haka saiya shiga rero kuka babu ƙaƙƙautawa, kuka tamkar ƙaramin yaro.

a wannan lokacin kuwa Turaki ya kifa kansa akan gadon, ƙamshin Maamansa na fitowa daga kan gadon na ziyartar hancinsa, yayin da yake damƙe da wannan ƙaton zanin da take cewa zanin goyon jikanta ne.

_"kwana ashirin da biyu ya rage Edd É—in nata ya cika ko?, to Allah ya raba su lafiya. kaga Me Babban suna waÉ—an su gadaje na jarirai na gani da suka fi wanda na siyo kyau, mu sauya shi ko?"._

maganartata ta haska acikin kansa, shekaran jiya suka raba rana su na hira da ita, kuma yawancin hirar duk akan jikokin da taƙe ta burin ganin zuwan su ne, har daga ƙarshe ma take ce masa.
_"to ni ina ta lissafina ma, wa ya sani ko ba lallai ba ne na kai wannan lokacin, Allah dai ya san adadin shekarun da ya É—iba mana a rayuwa, ni dai idan na tafi ku yafe ni Me Babban Suna ko da nayi muku laifi bisa kuskure"._

sai kawai yaji ya rasa dukkan dauriyarsa, ya manta shekarunsa, yana tunawa cewar shi fa ɗan Maamansa ne, kuma Maaman ta rasu a yau, bai san lokacin da wani matsanancin kuka ya kubce masa ba, ya shiga rero shi tamkar yaro sai dai gaba ɗaya babu sauti, illa tarin ruwan hawayensa da ke sauka su na jiƙa bedsheet ɗin.

har aka tura ƙofar ɗakin aka shigo tsakanin Turaki da Khalil babu wanda ya sani balle ya ɗago.
Fillo ta ƙarasa ta zauna akan gadon, tana zama kuma Turaki ya ɗago kansa ya ɗora akan ƙafafunta, ya damƙe cinyoyinta yana wani irin girgiza.

sai taji sabon kuka yazo mata, tunawa da tayi Nihal na can an rirriƙeta sai surutai take yi. saboda haka sai ta nutsa yatsunta acikin kansa tana motsa yatsun.

*BAYAN SATI BIYU.*
[9/7, 03:10] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*60*
*Jarabawa daga Mahaliccin mu.*

Rayuwa tana cike da nasara da kuma faɗuwa, kuma akwai lokutan da gwaje-gwajen da ake yi mana kamar ba za su ƙare ba.
A cikin Alkur’ani me girma, akwai ayoyi da dama da Allah ya yi magana a kan hanyoyi daban-daban da za a gwada mu, amma kuma ya ba mu ƙunshin kulawa da zai taimaka mana mu bibiyi waɗannan lokutan masu wahala a gare mu.

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce:“Babu wata musiba da za ta samu musulmi face Allah ya kankare masa wani abu daga cikin zunuban shi, ko da kuwa tsinuwar ƙaya ce”. (Bukhari Wa Muslim).

haƙiƙa jarabawa ba azaba ba ce daga Allah, tana daga cikin rahamarsa marar iyaka.
Musulmi ko wanda ba Musulmi ba, babu makawa kowannen mu yana fuskantar jarabawa a rayuwarsa. Rayuwa ba gadon wardi bane ga kowa, Akwai mutanen da ke fama da talauci, akwai masu fama da lafiyarsu, sannan akwai masu fama da danginsu, akwai masu fama da mutuwa a jere a jere.

Jarabawar ubangiji ta bambanta ga ɗaiɗaikun mutane daban-daban, an yi su ne bisa la'akari da irin ƙarfinmu da rauninmu. Abubuwan da suka zama kamar gwaji a gare ni, wataƙila ba za su dame ku ba, nima akasin hakan.
tambayar gama gari da kowa ke yi a lokacin da ya shiga wani hali shi ne; me ya sa Allah ya sa na shiga cikin wannan halin? Me ya sa ba zan iya zama mai farin ciki a ko yaushe ba?, Menene na yi don cancantar wannan jarabawar? Me yasa Allah ya jarraba ni?.
kuma rashin sanin amsar waÉ—an nan tambayoyi wani lokacin yana iya nisanta mutum daga imaninsa.

jarrabawa na iya haifar da mummunan tunani mai tayar da hankali wajen mutum ya aikata saɓo, kamar faɗin Allah ba ya so na!. ko ma mafi muni mutum yace Allah ba ya yi mini adalci(astagfrullah). Amma Allah shi ne Al-Adl, Mai adalci, kuma shi ne Ar-Rahman, Mai jin ƙai, wanda ba ya ya nufin cutarwa ga bayinsa, face yana son alheri a gare mu.

Akwai hikima a yanayin da ya ke sa mu a ciki, duk abin da muke buƙata mu yi shi ne haƙuri.
Akwai dalilai da yawa a cikin Alqur’ani da hadisi da suke taimaka mana wajen amsa tambayar dalilin da ya sa ake jarraba mu.
Chapter 166 · 0% Book details