Sashe 85
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bai ma san tana yi ba becouse he is totally getting out of control, ƙwaƙwalwarsa ta shiga faɗa masa anger ɗinka ba zai yi amfani yanzu ba, just relax and control your self.
ya buɗe idonsa da ya rufe in just 10seconds, yaja leɓensa ciki ya cije da ƙarfi sannan a hankali ya sauke dogon numfashi, ƙwayar idonsa da ta sauya kala ta dawo yanda ta ke.
ya ɗauko wayarsa a aljihu ya ɗauki lambar tasu, sannan ya bi bayan kiran nasu da suka katse. bugun farko suka ɗaga, cikin kwantar da murya Turaki yace,"muna jinku, me ku ke da buƙata?".
mutumin yay dariya sosai yace,"kun tabbata za ku bayar da komai muka ce?, idan kun san baku shirya karɓan ƴarku ba karku sa mu ɓata bakinmu wajen yi muku bayani".
Turaki ya ƙara rumtse ido yace,"duk abinda kuke so na tabbatar da zaku sa me shi".
mutumin ya kuma dariya yace,"good. ga yaronku nan yana ta kuka kullum yana so yazo ya ganku, amma munce ba zamu sake shi ba sai an bayar da miliyan ɗari biyu tukunna mu barsa ya dawo gida da ƙafafunsa".
zuciyar Turaki na bugawa fat-fat yace,"you got additional of 300million, zan baku miliyan ɗari biyar muddin baku taɓa lafiyarta ba wannan alƙawari ne, ta ya zaku karɓi kuɗin?, or throught bank za'a tura maku".
mutumin yay dariya sosai yace,"zaka kawo mana kuÉ—in da hannunka". nan ya shiga korawa Turaki bayanin inda zai je ya kai kuÉ—in ya ajiye. Turaki ya tabbatar masa da cewar zai zo É—in in the next few minutes amma su tabbatar ba su yiwa Fillo komai ba.
mutumin na bushewa da wani dariyar yace,"ga yaronku kuyi magana dan ka tabbatar yana lafiya, idan kunji jishi yana kuka ba komai bane akayi masa, soro ne kawai da yake ciki".
daga can inda mutumin ke zaune kan kujera ya É—orawa Fillo wayar a kunnenta a tsawa ce yace,"yi magana da father naki".
cikin matsanancin kuka tace,"Kaka".
Turaki ya ƙara matse hannun Maama da har yanzu ke hannunsa, muryarsa a hankali yace,"Fulaniii". sai kuma ya fesar da iskar bakinsa me zafi yace,"kina jina?".
a wahalce tace,"Turakii, dan Allah kazo ka cece ni, kashe ni zasu yi sun ce, wai zasu yi amfani da ni, ka faÉ—a musu Kaka bata da kuÉ—in da suke nema". ta faÉ—a cikin kukan da duk wanda yaji sai ya zubar mata da hawaye.
Turaki ya tattaro jarumtarsa da yake jin tana neman barinsa yace,"kiyi shiru ki daina kukan kinji, zan zo in É—auke ki yanzun nan. babu abinda suka isa suyi miki in har bakinki bai gushe da ambaton Allah ba, amma na faÉ—a miki ki daina kukan kinji Fulani".
wannan jarumtar tasa ta maza yaji ta ƙwace, bai san sanda ya zube a gefen gadon Kaka ba, idonsa na cika da tarin hawaye, ya buɗe baki yana jin kamar ba zai iya magana ba, acikin zubar hawayen da babu wanda ya lura da shi a fuskarsa yace,"karki bari suyi miki komai kinji Fulani, i know who you are, i know you can protect your dignity, dan Allah karki bari suyi miki komai, dan Allah".
yanda take sauke numfashi a wahalce kawai yake jiyowa, ya matse idonsa sosai yana jin zuciyarsa na wani mugun matsewa, yace ta sassauta kukan tace,"to zaka zo yanzu?".
yace,"yes, i will come right now, just some minutes kinji". ƙit yaji wayar ta katse, ba tare da yabi ta kan kowa dake jiran cewarsa ba ya ratsa ta tsakiyar Maama da Yami ya fice daga room ɗin cikin sauri.
yana shiga mota yay dialling number D.P.O yace masa,"ranka ya daÉ—e kun fara tracing numbern?". yace masa,"yes, before wayan naku ya katse har mun gano a inda suke, yanzu haka yara sun É—au hanya. ka tsaya ka É—auke ni a hanya".
Turaki nasa hannu ya sha re zufar goshinsa yace,"please ka faÉ—a musu suyi a hankali kar suja su cutar min da ita". da haka ya katse wayar sannan ya kira wayar Khalil yace,"Bro i need five hundred million naira in cash right away, kaje Zenith Bank wurin Faisal, on my way to meet you there in the next 10minutes".
acikin motar Turaki da yake sharara mahaukacin gudu akan hanyar zuwa ƙauyen pindiga, lokacin ƙarfe bakwai da rabi na dare har tayi, waya ce maƙale a kunnensa yana tabbatarwa da kidnappers ɗin cewa shi ɗaya ne ba tare da kowa ba kamar yanda babu wanda ya shaidawa maganar..
sai dai a dai-dai wannan lokacin da yake wayar da su, a dai-dai wannan lokacin Fillo ta samu damar zare igiyoyin jikinta ta miƙe tana bin hanya saɗaf saɗaf ta yanda babu me jin motsinta, kuma ta tabbata har ta fice babu wanda zai ganta kamar yanda mutumin nan ya faɗa mata.
sai dai kuma me?, sanda ta ke zuwa gab da ƙofar zata fita, dai-dai jikin windown wani ɗaki, bala'in tsoron dake tare da ita sai ya koma zuwa tsantsar mamakin abinda kunnuwanta ke jiyo mata, muryar wanda ta ke ji da kuma sautin dariyarsa da abinda yake faɗa na saka jijiyoyin jikinta tsinkewa.
ta ja ƙafarta a hankali ta isa jikin window tana leƙawa ta yanda ba za'a ganta ba, tana tsaye a wurin kunnuwanta na ci gaba da jiye mata abubuwan da yake faɗa, maganganun nasa da take jinsu tamkar ɗigar dalma ajikinta, in one time sai taji jikinta gaba ɗaya ya zama kamar na statue, ko hannunta ta kasa motsawa, ko idonta ta kasa ƙiftawa, zata iya rantsewa cewa zuciyarta kanta ta tsaya da aikin buga jini zuwa sassan jikinta.
a sanda ƙyar idonta tayi tozali da shi ta siririyar ɓular, zaune tsakiyar mutanen wanda ya tabbatar mata shine Babban Oga da taji suna ta ambata, kuma yana ɗaya daga cikin mutanen da suka shigo ɗazu har tabi su da kallo.
sai ta koma da baya ta lumshe idonta tana jin zuciyarta kamar ta zama ƙanƙara tana narkewa ruwan yana taruwa acikin idanunta, taji duk wani tsoro nata yana bin iskar wajen dake kaɗawa, taji kamar duk wani abu da yake cikin kanta yana farfashewa a ƙasan wajen da ta ke, taji duniya gaba ɗaya tayi mata zafi. sai ta ƙara matsawa da baya tana saka hannu ta goge hawayen da ya taru cikin idonta amma sai taji ƙamas babu komai, idonta a bushe yake kamar famfon da ya shekara guda babu ruwa, haka ma fuskarta.
"Amir!". taji zuciyarta ta furta da wani irin amo kamar ba nata ba. "Amir ta ke gani anan, Amir ta ke ji yana faÉ—ar shi zai fara keta haddinta kamin kowa, shi ta ke ji yana faÉ—ar ya cika burinsa na shekara da shekaru ya gama handame musu komai, har yana faÉ—in bai zama lallai ma su barta da rai ba".
gaba ɗaya sai taji jikinta ya ɗauki rawa kamar an jona mata electric shock, haka ma zuciyarta na harbawa fat fat kamar zata faso ƙirjinta ta fito, numfashinta na fita da ƙyar tana jin kamar ana zare ranta.
ta jingina kanta da bango tana kasa rufe idonta, komai da ta ke ji ta ke gani kamar mafarki ba gaske ba. ta ƙara dafe bangon wurin tana rumtse idonta tana girgiza kanta da ɗan sauran kuzarin da take jin tana da shi, cikin ranta tana addu'ar Allah yasa ta buɗe ido taga ba Amir ta gani ba, Allah yasa idan ta buɗe idon taga mafarki ne ta ke yi ba muryarsa ta ke ji ba acikin azzaluman mutanen da tasan babu makawa sai wutar Allah ta ci su. Ta shiga buɗe idonta a hankali tana mai tsoron buɗewa bugun zuciyarta na ƙara tsananta.
a lokacin ta ƙara jinsa yace,"ba zata san ni na tsara komai ba kuma na shirya ba har sai bayan na gama da rayuwarta. zanje yanzu dan ana kan hanyar kawo kuɗin fansarta...in ance ma nasan mutanen nan a shirye suka da yin komai akanta da tun farko ba'a ɗauki tsayin wannan lokacin ba, da ban tsaya na jira na gama haifar da tashin hankalin da bai da misaltuwa ba a wurin Kakarta, da a yanzu kuma bamu ambaci miliyan ɗari biyu ba, da 2billion naira zan ambata musu".
Fillo ta buɗe baki tana ƙoƙarin furta kalmar innalillahi a fili amma sai taji ta kasa sarrafa harshenta, sai bakinta da ke rawa kawai, cikin fitar hayyaci ta juya da gudu ta buɗe ƙofar ta fice tana jin kamar numfashinta zai ɗauke.
gudu take sosai acikin duhun daren, cikin jejin da take gani kamar ba'a duniya ba, ko gabanta bata iya gani sosai, sai da ta tabbatar tayi nisa sosai sannan ta duƙa tana haki a wajen da ta ke, wucewar daƙiƙa biyu ta ɗago ta ɗora daga inda ta tsaya, tun ƙafafunta na ɗaukarta har taji suna dab da dainawa, kuma a lokacin da ƙarfinta ya ƙare lokacin taji tayi karo da abu, karo da abu kamar mutum.
tsoron da ya barta tun a É—azu sai ya dawo sabo a sanda ta É—ago ido tana kallon halittar dake gabanta, da sauri taja da baya tana dafe kanta cikin ranta tana jin anya kuwa yau itace?, anya bata yi gamo ba?, anya zamanta a wajen can bai sa aljanu sun shiga jikinta sun rikita mata tunani ba?.
sai ta juya tana kallon bayanta kan ta juyo ta ƙara kallon matar da ke gabanta wadda ta ke duk a firgice, firgicin da zata ce ya ninka nata, kuma mafaka take nema, inda zata tsira da ranta ta ke nema.
sai taga matar ta ɗaga hannunta biyu tana haɗe tafun hannunta alamar roƙo, ruwan hawaye na bin idanunta, jini ya taru a ƙwayar idonta, a cikin rawar murya irin wadda ta sa ni taji tace mata,"dan Allah ki taimaka min zasu kashe ni, amma dan Allah kema karki cuce ni".
ta faÉ—a acikin yaren fulatanci muryarta na shaida tsananin tsoro da kuma tashin hankali.
hasken farin watan da ya hasko su ya haskawa Fillo sarƙar da aka ɗaure hannun matar da ita, ya kuma haska mata abayar dake jikinta wadda taci ubanta da mugun dauɗa sai wani kalar wari ke fita a jikinta, yalwataccen gashin kanta a barbaje ɗauke da tsirarrun furfura duk ya tuttuje.