← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 176

Sashe 18

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Rufe bakinta kenan Bafaden ya washe haƙoransa da faɗin,"yo ta jewa Jakadiya da wannan zancen ai sai dai wata ba ita ba. Dan tun a wajen zata zama tarihi kamin ma maganar ta kai ga kunnen Shugaba. Da farko da aka kirawo ki aka tambayeki za ki iya ba ki ce ba za ki iya ba sai bayan da kika gama jin sirrinsu saboda rashin hankali. To wa kike tunanin zai barki da rai?"._

_"ni fa ba wani abu nace ba, hankalina ne kawai yau ɗin naji bai kwanta ba. Dan duk randa asirinmu ya tonu, ko ita Shugabar da muke taƙama da ita ba zata iya ƙwatarmu ba, ƙila ma ta juya mana baya"._

-Da Bafaden da É—ayar matar su kai tsaki a tare. "to idan kin shirya rasa ranki da kuma dubu É—ari biyar É—in da za'a ba ki kina iya juyawa ki tafi, mu ki barmu muyi aikinmu...akan kuÉ—i da kika ganmu babu kasadar da ba zamu iya É—auka ba"._

_su na rufe baki Bafaden ya durƙusa ya shiga haƙe ƙasar da ke wurin, wanda bai tsaya ba har sai da yayi rami mai ɗan zurfi tukunna. Sannan macen da bata da tsoron ta ɗauko gorar ruwa a cikin jakar da ke hannunta ta juye ruwan a cikin ramin. Sannan ta miƙa hannu ta karɓi wata baƙar leda a hannun ɗaya matar ta zira a cikin ramin. Duk abunda suke yi su na yinsa ne cikin saurari-sauri gudun kar azo a gansu._

_Kuma bayan sun maida ƙasar ne sun rufe suka tsaya su na tattaunawa, wanda yanzu da su ke maganar Fillo bata jiyo komai da suke cewa saɓanin maganganun da su kai a ɗazu duk ta ji su._
_Alokacin zuciyarta na faɗa mata ne ta tunkari inda suke dan su san wani fa ya gansu, amma ɗayan ɓari na zuciyarta na hanata aikata hakan gudun karta fito suyi mata illa, duk da bata ga fuskar ko guda acikinsu ba amma tasan ba mutane bane masu imani a zuciyarsu._

_Cikin gudu mai kama da sauri suka bar wajen, sai da ta tabbatar sun bar wajen sannan ta fito, sai dai ko da taje wurin juyin duniya ta kasa gane inda akai haƙan aka binne, dan babu wata alama ta ɓurɓushin ƙasa da zai nuna maka anyi haƙan ƙasa a wajen, wannan ya nuna mata sun ƙware a iya aikinsu, kuma ba yaune farau ba._

_Ta ɗau kusan minti guda tsaye a wurin tana tunanin abinyi sai kawai taji gabanta ya yanke ya faɗi, ƙirjinta kuma na bugawa sosai, zuciyarta na faɗa mata tayi hanzarin barin wajen tun wani bai zo ya ganta ba, dan idan akazo aka kamata ta ina zata fara bayani?, waye zai wanketa daga duk wani kalar zargi da za'a ɗora akanta?, gatanta Allah gatanta Kaka, bata mantawa da lokacin da ɗaya daga cikin yaran gidan yaci abinci yay ta amai, aka ce ai mai aikin da ta kai masa abinci ce ta saka masa wani abun, idan har yanzu tunaninta na jikinta, to ai ba zata manta ba tsawon shekara guda da akai abun har yau mai aikin tana cikin kurku a kulle akan laifin da ba'a da tabbacin ta aikata shi._

_Saboda haka bata san lokacin da siraran ƙafafunta masu kama da sillan kara suka bar wajen ba cikin sauri kamin daga bisani kuma ta haɗa da gudu, sai dai a lokacin da ta ke shirin barin harabar wajen gaba ɗaya taji tayi tuntuɓe da dutse, ta tsuguna domin ɗaukewa kawai sai tayi tozali da laya da kuma wata leda baƙa ɗaure a wurin, cikin kanta bata kawo tunanin komai ba tasa hannu ta ɗauki layar da ledar sannan ta janye dutsen daga wurin._

_A wannan lokacin kai tsaye ɓangarensu ta koma, ta zauna ita ɗaya dan kowa yana can masarauta anata hidimar bikin naɗi, ita kuma duk tsoron kar ta fito a ganta ita ɗaya a cikin gidan a fara yi mata tambayar tuhuma. A ranar ma haka dole ta kashe haɗuwarsu da Amir._

"wai tunanin me kike?". Maganar Maijidda ta dawo da ita cikin duniyar zahirin da ta bari tsawon daƙiƙu masu yawa. Kallonta kawai tayi ba tare da tace da ita komai ba.

"Fullo kin san fa wurin nan ba wajen zuwanmu bane, ɓangaren masu gida ne. Amma kin kawo mu kin ajiye salon azo aganmu ace wani abun muke ƙullawa".

"Maijidda wuta zamu cinnawa wajen nan".
Maganar ta Fullo tasa Maijidda zaro ido waje tare da hanzarin miƙewa tsaye. Da yake ita sarkin tsoro ce tuni jikinta ya hau makyartata.

Kuma bata kai ga ƙara magana ba, Fullo ta kai hannu ta ɗau ƙaramar galan ɗin petir ɗin da suka sato a cikin gida ta shiga yaryaɗawa a wurin. Sai da ta juye shi tas sannan muryarta ta fito a hankali da cewar,"Maijidda matsa baya".

Cikin tsoro ba tare da mamakin abunda Fillo zata iya aikatawa ba tace,"ke wai me yasa ba kya iya kallo matsalar da zata faru a gaba, ke kawai abunda yazo cikin kanki shi kike yi. Yanzu mene amfaninki na cinnawa wajen nan wuta? salon kija mana barin gida".

"ai kin san dai ni ba mahaukaciya ba ce ko, duk abunda kika ga nayi ina da dalili...dan haka matsa da baya".

"wai na matsa da baya kike cewa, ke kuma fa?, kina kallo fa petir É—in da kika zuba yana da yawa, kina kunna wutar nan fa tasowa sama zata yi".

"ni dai kija da baya kawai nace".

Sautin muryarta ya fito cikin amo na ɓacin rai. babu shiri Maijidda taja da baya tayi nesa da ita. Fullo kuwa tasa hannu a gefen zanin da bata iya ɗaurinsa ba har yanzu ta kunto layar da take ajiye da ita. tasa a tsakiyar tafin hannunta na dama tana ƙare ma ta kallo, kamin daga bisani ta shiga warware baƙi da jan zaren da aka naɗeta da su.

Sau uku tana duba sunan da ke jikin layar, ranar farko da ta fara warwareta ta kasa karanta rubutun da ke jiki tun lokacin bata iya karatu ba, da rana ta biyu da karatun da Amir ke mata ya fara zama akanta ta É—auko ta duba dan haddace yanda harufan jiki suke, da kuma rana ta uku da ta rubuta harufan a wata takarda ta daban tayi compairing rubutunta da na jikin layar dan tabbatar da tayi daidai, kuma a ranar ne ta iya karanta hurufan da ke jiki, harufan sunan MUHAMMAD TURAKI.

To amma ga mamakinta sau ukun nan da ta buɗe bata taɓa cin karo da wani rubutun na daban ba bayan sunan Muhammad Turaki da yake jiki, sai yanzu da take ganin wani rubutun sunan na daban da akayi shi a ƙasan na turakin shi kuma da baƙar tawada amma ya fara disashewa hakan yasa ta kasa fahimtar kome aka rubuta.

Kawai sai taji wani dunƙulallan yawu ya wuce ta maƙogwaronta, tun a ranar farko da layar nan taje hannunta wani ɓari na zuciyarta ke gaya mata Halimatu kar ki jawa kanki bala'i, irin wannan abun mutum idan ya gani kauda idonsa yake akansa, amma yau kece da ɗaukar takardar da babu makawa anyi ne dan asirin wani.

Amma yau sam zuciyarta bata yi mata wannan gargaɗin ba, illama ƙwarin gwiwar da take bata akan tayi iya duk ƙoƙarin da zata yi kan ganin ta karya wannan asirin, dan zata iya rantsewa wanda ake abun akansa ba shi da alhakin kowa, don haka ta shirya yin jihadi akansa.

Saboda haka kawai sai ta cure takardar wuri guda ta jefar, ta ɗauki baƙar ledar da ta bawa Maijidda ajiya gudun kar Kaka ta gani, itama ta jefar a wurin.

Muryarta ta fito a fili tana faɗin,"har yanzu banda tabbacin asiri ne ku ka yi ko ba shi ne ba, to koma dai menene sai dai yaci ku ku ɗaya, ga abinku nan ya koma kanku". Tana faɗar hakan ta ƙyasta ashana ta jefa, nan da nan ko wuta ta kama da wajen.

Garin tayi baya ta bige ƙafarta a jikin kujerar wurin har taji ciwo a babban yatsan ƙafarta. Amma ko tsayawa tabi ta kan ciwon ba tayi ba.

Maijidda ko banda ambaton, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Babu abinda ta ke. Har sanda Fullo ta risko wajenta ta kama hannunta dan su bar wajen. "ni kam na shiga uku da ke Fullo, yanzu kin san iyakar inda wutar nan zata tsaya ne?, ba kya gudun abinda zai faru damu?".

"idan an tambaya sai kice mune muka kunna kinji".
Fullo ta faɗa tana ƙara jan hannunta dan su bar wajen. Duk rashin iya gudu na Maijidda sai gashi har tana kusan kerewa Fullo saboda ita numfashinta ya fara ƙoƙarin tsayawa.

Kuma kan kace kobo hayaƙin wutar ya fallasu a cikin gidan, saboda wuta ce ta tashi ba kaɗan ba sakamakon fulawoyin da ke wajen, cikin mintunan daba za su haura biyar ba sai ga fire service sun zo.

Irin tashin hankalin da wutar ta haddasa a zuƙatan al'umma Allah ɗaya yasan yawansa, an kewaye wajen anata salati, saboda irin tashin ƙarni da ke fita ta cikin wutar yana shiga cikin hanci ya haura saman ka, ya haddasa faɗuwar mutane da dama a wurin.

wani irin wari ne da ba shi da daÉ—i, dan asthmatic ma bai iya tsayawa. Haka ambulance tayi ta shige da ficen É—aukar mutane. A yayinda a wannan lokacin Fullo da Maijidda na can cikin uwar É—akin Yami, hankalin Fullo kwance kamar ba ita tayi ba, Maijidda kuwa tayi tsilli-tsilli da idanu kamar ta fashe da kuka.

Tana ta yiwa Fullo maganar amma kamar da dutse ta ke. Dan ita a wannan lokacin ma tunaninta na kan wani lamari na daban da take haskowa wanda take tunanin yafi wannan hatsari. Ƙarshe dai da Maijidda ta isheta da maganar da ba zata iya zaman jinta ta miƙe ta bar mata ɗakin.

Ta wuce É—akinsu ta É—auki littafinta ta hau assignment É—in da Amir ya bata, wanda kusan kwana huÉ—u kenan da bata amma batayi ba saboda shiririta.

Don Allah share to other groups🙏

Youtube Channel-NishaÉ—i Media.

[8/12, 08:00] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*©️Halima h.z*

*11*
"Mommi dan Allah kiyi shiru". Nuratu ta faÉ—a idanuwanta na kawo ruwa, zuciyarta cike da tsananin tausayin matar.
Chapter 18 · 0% Book details