← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 176

Sashe 43

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nihal tace,"ku tashi muje let me escort you". ta faÉ—a tana gyara zaman glasses É—inta, da gyara dogon wandon dake jikinta.
"je ki ɗauko littafan naku". ta faɗa tana nuna Ɗausiyya ɗaya ƴar aikin. da ganinta tana da hanzari akan yin abu, dan cikin sauri ta ɗauko ta dawo, kuma kallo ɗaya zaka mata zaka san she is typical ƴar ƙauye, balle kuma ka kai ka ga kallon the way take abubuwanta, maganarta duka hi da ha ne, jiya ana kawota Hajiya Madina tasa Baba Jummai dake kawo mata ƴan aiki ta kaita saloon aka wanko dattin kanta, kuma suna dawowa tasa tai wanka me kyau da dettol da turaren ƙamshi. haka Hajiya Madina take, bata nuna ƙyama ko ƙyanƙyami ga duk yaran da ake kawo mata, karɓarsu take ta nuna musu hanyar gyara kawai.

Nihal na gaba suna biye da ita a baya, zasu fita daga falon Zaytuna ta kira sunan Fillo, ta waigo tana kallonta bayan ta amsa kiran. ta mayarwa da Zaytuna murmushin da take yi mata. "i wish you all the best in your studies dear". abinda Zaytuna tace mata kenan, kuma kamar yanda bata fahimci me tace ba haka itama Zaytunan ta fahimci bata san abinda tace mata ba.

Zaytuna ta ƙara mata wani murmushin tace,"ina yi miki fatan alkhairi a karatunki, Allah ya bada sa'a". kan Fillo na ƙasa tace,"amin ya Allah, na gode Adda". da haka tabi bayan su Nihal da suka riga suka fice.

awa biyu suka ɗauka suna karatun kafin su gama, kuma sosai Fillo ta gane duk abinda aka koya musu ɗin, karatun ya mata daɗi fiye da yanda ta tsammata, ashe shima karatun boko haka yake da daɗi?, shi kansa teacher ɗin nasu sai da ya mata kyautar biro, har yana tambayarta ko ba yanzu ta fara ɗaukar darasi ba, dan ko da ya basu class work guda biyu ta faɗi a examples ɗin da ya ce su bayar, rubutun ta kuwa baka ce wacce ke koyo ba, Ɗausiyya ce yay ta fama da ita, to itama kuma da yake tana da kishi sai da tai ƙoƙarin iyawar. teacher ɗin nasu ba bahaushe bane, amma yana jin hausa sai dai bata kama bakinsa sosai ba. yay da hausa ya haɗe da turanci, su gane hausar da yake yi su bagarar da turancin nasa, idan ya faɗi wani abin da hausa Fillo har gimtse dariyar dake taho mata take yi. dan da ace ita da Maijidda ne ma sai sun saki kayarsu.

suna komawa sallah kawai sukai sannan suka fito suka shiga kitchen, suna aikin Fillo na bitar karatunta, É—an gutun turancin da brain É—inta ta haddace sai maimaita shi take a zuciyarta, idan ta faÉ—esa a fili kuma sai taji maganarta wani banbarakwai sai tayi dariya, haka kawai Amir ya faÉ—o mata a lokacin, idan yay mata turanci sai yace ta faÉ—i abinda yace sai ta kasa, yace zata iya tace ita kunya take ji tasan ba zai yi daÉ—i a bakinta ba irin yanda yake daÉ—i a nasa bakin, sai kuma ta tuna abinda ya faru tsakaninsu a É—azu, tai saurin watsi da tunaninsa tana jin zuciyarta na zafi.

Zaytuna ce ta taya su Fried rice É—in da basu iya ba, sun maida hankali sosai wajen ganin yanda ake yi, duk abinda ta É—auko na vegetable zata faÉ—a musu sunansa da amfaninsa da kuma yacca ake sawa, babu jimawa suka kammala Fried rice É—in. suna aikin ÆŠausiyya ke tambayarta,"Anty kuma sai ku iya cin abinda muka saka hannu?".

Zaytuna tai murmushi tace,"Hammah ne kawai baya cin abinda Æ´an aiki suka dafa, amma mu kam muna cin duk abinda Æ´ar aiki ta dafa muddin ta kula da irin tsaftar da muke so, kema baki ga yau fes dake kika fito ba, kuma ina kallonki duk abinda kike yi cikin tsabta kike yinsa...yanzu ma kalle ki tsab, to tsabta ita ke sawa aci girkin mutum, duk daÉ—in girkin mutum idan baida tsabta sai dai yaci kayansa shi É—aya".

Zaytuna da Ɗausiyya suka ɗauka tray suka fita da shi, suka bar Fillo da ƙarasa haɗa kunun shinkafar da Samha tace tana so tasha. ta fasa madarar gwangwani ta ruwa kenan sai taji kamar mutum a bayanta, ta waigo ta ga Turaki ne tsaye hannayensa a aljihu yana kallon abinda take preparing, da alama ma ba shigowarsa kenan ba.
sai ta nemi ta dirirce, ta durƙusa a gabansa da sauri tana gaishe shi, ita bata san me yasa ba amma duk sanda ta gansa sai ta tsorata. bai amsa mata ba ya wuce ya ɗauki cup ya dawo, tana nan durƙushen har lokacin, da wani irin voice tace da shi.

"kana buƙatar wani abu ne?". ya kalleta amma ba ita yake kallo ba hannayenta yake kallo, yace. "tashi". ta miƙe tana ɗan matsawa daga kusa da shi. fuskarsa a ɗaure yace,"what is this?". ta so fahimtar abinda yace, amma hakan bai samu ba, jin tai shiru ya waigo ya dubeta, tana tsaye kamar gunki duk ta cika da tsoronsa, hannun nan sai karkarwa yake, shi kuma abin na basa takaici.

yaja guntun tsaki ya ƙara cewa,"i am asking you, what is this that you are making?". yanda yay maganar murya a sama yasa ta fara ƙoƙarin hargitsewa, ta ƙanƙame hannayenta a jikinta tare da kulle idonta, shin har sai yaushe zai fara fahimtar wannan yaren ita kam bata jinsa, ita kuwa ko ba dan komai ba ai dole ta tsaya ta mayar da hankali akan wannan gatan da Hajiya Madina tai musu ta koyi turanci. ji take kamar tayi kuka, bata ko ƙaunar tana aiki a kitchen ya shigo, ko ba'a kitchen ba bata so tana aiki taga giftawarsa, ita haɗuwa ma da shi totally bata so.

Turaki ya tsaya yana kallon ikon Allah, shi kam ba dan ba dan ba, da sai yace yarinyar nan bata sahun mutane sai dai wata halittar. karkawarwa take kamar wadda ruwan sanyi yaywa mugun duka, ko kuma wacce iskar fanka ke kaɗawa. sai ya ajiye cup ɗin hannunsa kawai ya rungume hannunsa a ƙirji, ya jingina da jikin drower ɗin yana ta kallon sarautar Allah, ba zai ƙara magana ba balle motsi har sai ta gaji dan kanta ta dawo cikin hayyacinta, sannan zai buɗi baki ya faɗa mata karta ƙara ganinsa ta tsorata tunda shi ba dodo ba ne.

lokacin da ya tsareta da tambaya a asibiti ya haska acikin kansa da cikin idonsa, wannan lokacin da ya riƙe hannayenta dan hana su rawar da suke yi, amma still basu daina ba sai ma rawar hannun nata ya haɗe har da nasa, tambayarta yay kawai me ya kaita wannan wajen, amma yanda tabi ta ruɗe ta nemi ta firgice har sai da yasa ɗaya hannunsa ya riƙeta da kyau, dan kamar zata faɗo ne daga kan gadon.

_"me ya kai ki wannan wurin a wancan ranar?"_ tambayar da yay mata kenan amma kamar ya tuhumeta ne akan me yasa tai kisan kai. sai da ya matse hannunta da ƙarfi sannan ta buɗe ido ta kalle shi hawaye na sakko mata tace masa,_"ina?"_ harara kawai ya galla mata a lokacin, kafin yace,_"wurin da kika je za ki kashe kanki"._ sai kawai ta shiga girgiza masa kai, cikin rawar murya tace,_"Allah ba kashe kaina naje yi ba, ai babu kyau mutum ya kashe kansa"._ taji yay shiru bai yi magana ba, sai ta buɗe idonta dake rufe ta sauke a kansa, ƙwayar idonta ta shiga nasa, taji wani abu da bata taɓa jinsa ba, taga ya ɗaga mata gira duka biyun yana cewa,_"ummm ina jinki, to wa kika je kashewa?"._, saura kaɗan yay dariya saboda yacca ta ƙara ruɗewa da tambayar tasa, har tana ja da baya wanda inda ba'a kan gadon take ba tsab zata arta da gudu.

ƙoƙari take ta zare hannunta a cikin nasa tana girgiza kanta cikin tashin hankalin da ya rufeta farat ɗaya. hawaye ne sosai yake sakko mata a sanda take ce masa,_"Allah babu wanda naje kashewa, me yasa zan kashe wani, akan me?, ko cinnaka bana iya kashewa ka tambayi Kaka kaji, dan Allah kayi haƙuri kar ƴan sanda suji su kamani"._ tai shiru tana fashewa da kuka, har sannan bai ɗauke idonsa daga kanta ba, ganin kallon da yake mata yasa tace,_"na rantse da Allah babu wanda naje kashewa, nima gani na kawai nayi a wajen, ban san ya akayi naje ba, kuma ina ta neman hanyar gida na rasa"._

ya ƙara damƙe hannunta sannan yace,_"har lokacin da ya kaɗeki baki sani ba?"._ ba tare da ta kallesa ba tace,_"na sani, ina ta ɗaga masa hannu bai ganni ba kawai sai ya bige ni"._ numfashi ya sauke yace,_"to kin yafe masa ko kin barsa da Allah?"._ sai da ta ɗago ta ɗan kallesa tukunna tace,_"na yafe masa"._ ya ƙara sauke numfashi sannan yace,_"to aljanun naki da suka kai ki su nawa ne?, dama suna yawo dake ko ranar su ka fara?"_ a wannan lokacin kawai tsaida idonta tayi akan kafaɗunsa, ta girgiza masa kai tace,_"banda aljanu ai, ni banda aljanu, ko Malami za'a kira a tambaya"._ yace,_"wanne Malamin?"._ tace,_"Malamin Ruƙiyya"_.

yana kallon yanda take kallon ƙirjinsa kamar me karantar wani abu a wajen, sai da ya kalli wajen yaga babu komai kawai dai ba zata iya kallonsa ba shine take kallon wajen. sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya saki hannayenta ya miƙe ya fita daga ɗakin ba tare da yayi musu sallama ba.

a yanzu da yake kallonta sai yake ganin kamar a wancan lokacin, har yanzu yana mamakin me ya kaita wajen, me taje yi?, abu ɗaya kawai zai yarda da shi tana da aljannu kuma su suka kaita, abunda kowa ya faɗa kenan. to ya yarda da wannan, amma wannan tsoron nata fa?, shi jininsa babu tsoro a cikinsa, saboda haka ya kamata wannan tsoron nata ya ragu tunda har jininsa na yawo a jikinta yanzu. ya rumtse ido yana tuna the first abunda likitoci suka faɗa sanda suka isa hospital, _"ta zubar da jini da yawa, jini take buƙata a halin yanzu, cikin gaggawa ba da ƙurewar lokaci ba"._
Chapter 43 · 0% Book details