← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 176

Sashe 161

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kwantar da murya ya soma magana yana faɗin,"na san ban kyauta miki ba akan canjawar da nayi miki, tsawon kwanaki tara kenan ina ƙuntata miki, ba zan hana ki jin haushina ba, amma ki yi haƙuri don Allah, ni ma nawa ranne babbu daɗi, tilasta min da aka yi akan mayar da auren nan duk shi ya dagula min lissafi ".

tsabar tuƙuƙi da ɗacin dake tasowa a ƙarƙashin zuciyarta, tun da ya fara magana har ya kai ƙarshe bata ko kulasa ba, haka bata ɗago kai ta kalle shi ba, sai ma zame hannunta da tayi a nasa.

Turaki ya gyara zamansa, ya matsa kusa da ita ta yadda numfashinsu yake gauraya da na juna, ya riƙo hannayenta duka acikin nasa yana murza lallausan tafin hannun nata, ya kifa goshinsa saman kanta yana sauke numfashi.

baya jin a duniya akwai wata mace da zata kama zuciyarsa kamar ƙaramar yarinyar nan, kullum cikin adu'a yake yi Allah kar yasa sai ya rigata mutuwa.
cikin hikima da iya tsara zance na miji ya shiga bata baki, yayi amfani da duk wasu kalamai da za su kwantar mata da hankali da shigar da nutsuwa cikin zuciyarta, har sai da yaga alamar hucewa a saman fuskarta.

but hakan duk bai sa Fillo ta samu sauƙin zafin kishin da take ji ba, abu ɗaya kawai ta sani mijinta yana mata tsananin so, kuma yana sonta fiye da ɗayar matarsa.

da kansa ya sauƙa ƙasa ya dafo mata indomie, ya zo ya sakata a gaba taci da ƙyar saboda lallamar da yake yi mata.
tamkar ɗacin magani haka ta dinƙa cin indomie ɗin, but babu yanda ta iya sosai take buƙatar abinci, dan zata iya cewa rabonta da wani abu a ciki tun kunun gyaɗar da ta sha a gidan Yusuf.

sai da ta kwanta sannan Turaki ya bar ɗakin, tana jin fitarsa ta ƙara fashewa da kuka, ba wai don tana so ba sai dan bata ma san lokacin da yake zuwar mata ba ɗin.

washe gari da sassafe kuwa sai ga text ɗinsa akan ta shirya ta tafi gidan na su. 
tsabar farin ciki da jin daÉ—i bata san lokacin data tura masa da reply É—in thank you ba.
lokacin da ta fito zata tafi yana hangota ta balcony, fuskarta ta gaza ɓoye jin daɗin da take ji, yay murmushi kawai tare da juyawa ya koma ciki domin ya sanarwa da Ilham ita ma ta shirya ta tafi, tun da kusan yaune yinin bikin gidan.

da rana taro yay taro, cikin taron mutanen da ake ta É—aukar hoto Fillo ta yanke jiki ta faÉ—i.
cikin tsananin tashin hankali Hajiya Madina da Hajiya Ramla suka sureta aka yi asibiti.
zuwan su babu jimawa sai ga Turaki shi ma ya ƙaraso, cikin matsananciyar damuwar da ta kasa ɓoye kanta ba.

ya zauna kusa da Maama, ta dafa kafaÉ—arsa tace,"ka kwantar da hankalinka insha'Allahu ba wata matsala ba ce babba".

Mum ta kalle shi rai a ɓace tace,"na jima da fahimtar kana ƙuntatawa yarinyar nan. to wallahi kaji na rantse maka muddin silar ɓacin ranka take kwance anan sai ranka yayi mugun ɓaci".

wucewar mintuna ashirin su na zaune jungum jugum sai ga likita nan ya fito, ya buƙaci cewar wani acikin su ya biyo shi.
Hajiya Madina tace da Turaki ya tashi yaje, ya shiga office ɗin Dr jikinsa a matuƙar sanyaye, duba da yayin da yake gani akan fuskar likitan.

"Bismillah zauna".
ya faÉ—a yana yi masa nuni da kan kujera.

Dr ya É—auko file ya buÉ—e, ya dubi Turaki ta cikin glass É—insa sannan ya ce,"Halima BorkinÉ—o right".

Turaki yay saurin jijjiga masa kai,"yes".

Dr ya sauke numfashi, ya furzar da iska daga bakinsa sannan ya ce,"kun san cewa ta kamu da heart failure?".

"mun sa ni Dr".
"to amma ya akayi ku ka yi sakacin da har damuwa tayi mata yawa haka?, tana fa ƙoƙarin barin matakin farko da take ciki ne ta shiga na gaba".

Turaki ya sauke doguwar ajiyar zuciya bai iya cewa komai ba. haushin kansa yayi matuƙar kama shi.

"anyway ga wannan drugs ayi gaggawar siya mata, gudun samun matsala babba. and a kiyaye sosai da duk abin da zai haifar mata da damuwa kar a kai stage É—in da Babynta zai cutu".

idanuwan Turaki suka ƙanƙance yace,"Baby?".
ya tambaya da mamaki sosai.

Dr ya jinjina masa kai,"ƙwarai Baby, ko ba ku san tana da ciki ba ne?".

bakin Turaki ya buɗe, duka haƙoransa suka yo waje,"i din't get you clearly Dr, wanne irin ciki wai?".

Dr ya faÉ—aÉ—a murmushin sa, yana kallon Turaki yace,"zauna da kyau kar ka faÉ—i".

sai ya É—ebo sauran takardun da ke cikin file É—insa ya zubewa Turaki a gabansa ya ce,"ashe kamata yayi in fara yi maka congratulations, so you are expecting a baby in the next five months Insha'Allah, a test É—in da aka yi mata ya nuna mana cikinta yana cikin wata na huÉ—u ne, but how comes duk baku yi noticing ba?"

Turaki ya kasa amsa tambayar Dr, sai É—aga hannu sama da yay yana godewa ubangiji.
ya daÉ—e a hakan kafin ya mayar da hankalinsa kan doctor É—in yace,"thank you very much, ga wannan kasa mai a mota".

ya ajiye masa kuÉ—i saman table É—insa, hakan kuma yayi wa Dr daÉ—i sosai, nan da nan ya shiga bawa Turaki shawarwari akan yacca za su kula da cikin.
Turaki duk ya ƙosa ya miƙe akan kujerar, hannu ya miƙawa Dr ɗin su kai shaking, tukunna ya fita a office ɗin bakinsa sam yaƙi rufuwa saboda tsabar farin ciki.

kai tsaye room É—in da Fillo ke kwance ya wuce, a ciki ya sami Maama da Mum, lokacin ta farka tana zaune, sun sakata da tambayar me take son ci, ita kuma duk ta narke tana faÉ—awa Mum wai Mangoro take so me warin gawasa.
kallo É—aya Mum ta yiwa Turaki ta zunguri Maama suka fita suka bar É—akin, su na fita ya rungume Fillo da farin cikin da ba zai iya misaltuwa ba.

ta ture shi daga jikinta tana turo baki gaba tare da ɓata fuska.
"ni ka matsa daga kusa da ni".

yay murmushi me sauti yana zura hannunsa cikin rigarta, cikinta ya shiga shafawa yana faÉ—in,"ta ya zan barki alhalin akwai ajiyata anan?. congratulations very soon za ki zama Mother".

ta yi masa wani kallon mamaki, ya É—aga mata gira duka biyu,"am serious Angel".
sai ta kulle idonta tana jin wani daÉ—i na tsarga mata, ta kai hannayenta duka biyu ta dafa cikin tare da hannunsa da yake kai.

"Allah ka azurta ni da zuri'a É—ayyiba".
ta faÉ—a hawayen farin ciki na sakko mata, Turaki yay kissing É—inta a goshi tare da faÉ—in,"amin summa amin uwar Æ´aÆ´ana, i love you so much".

lokacin da suka fito su Maama har sun wuce, duk kunyar da yake ji, bai iya haƙuri ba sai da ya ɗaga waya ya kira su Maama ya sanar musu.
bayan sun gama wayar ya kira Bello, yana É—agawa yace da shi,"Bello ai na zan sami Mangoro me warin gawasa?".

Bello ya ce,"yanzu na mayar da farantin tallan gida, ya ƙare tass da yake yau anyi ciniki".

Turaki yay tsaki,"kai dai kana da matsala".

"to MT haka kawai sai ka kama wani kirana kana tambayana in da zaka samu mangoro, hanyar kasuwa ne baka sa ni ba ko me?. ni don Allah kace a bani matata yau wallahi duk na gaji a matse nake".

Turaki yaja dogon tsaki ya kashe wayar, ya kamo hannu Fillo dake dafe da ciki yace,"sorry Angel, duk in da mangoro yake zamu samo shi yanzun nan, ki tayani bawa Baby haƙuri".

sai ya kuma ya fara ce mata,"yanzu idan namiji ne wanna suna zamu saka masa?".

"ai kai kake da wannan alhakin".

"to in dai namiji ne sunan Abba zamu saka, idan kuma macece zamu sa sunan Maama, in kuma twins ne duka maza zamu sa sunan Abba da Baffa, idan twins ne duka mata sai mu sa Maama da Ummi".

"Mum kuma fa?".
"ita ma zamu saka nata idan kin ƙara haifar wasu twins ɗin".

"wai haka Doctor É—in yace maka twins ne?".
"hakan nake fata Angel".

sai ta marairaice fuska, idonta ya ciko da ruwan hawaye, ta damƙe hannunsa ta ce,"Jannaty ina tsoron haihuwa, an ce akwai wahala".

tausayinta ya kama shi,"kar ki damu Angel insha'Allah ke kalar taki haihuwar zata banbanta da ta su, cikin sauƙi zata zo miki".

"Allah yasa. amma Jannaty ka dinƙa yi min adu'a kullum na haihu da raina da lafiyata, ina so na raini yarana da kaina domin in ba su ilimi ingatacce tare da ba su kyakykyawar tarbiyya, ba na so na mutu a lokacin dana san ƴaƴana za su buƙace ni".

sai kawai ya gangara motar gefe yay parking, yacca jikinta yay sanyi haka ma nasa, ya juyo ya kalleta yaga tana zubar da hawaye, ya janyota ya rungumeta.
ta fashe da kuka sosai tana faÉ—in,"Jannaty bana so su tashi acikin maraicina, ina so su ma suji wannan daÉ—in na uwa".

lokaci É—aya Turaki yaji idonsa ya ciko da ruwan hawaye, yana shafa bayanta yace,"mene kuma na zancen mutuwa Angel?, don Allah ki daina, da izinin ubangiji da ranki da lafiyarki za ki haihu, kuma insha'Allahu ubangiji zai ba ki aron tsawon ran da har auran Æ´aÆ´anki za ki gani".

ita dai bata iya cewa komai ba, kuma har suka ƙarasa gida jikinsu duk yay sanyi.
Fillo kuwa tana shiga bedroom É—in Mum ta rufe fuskar ta, saboda haÉ—a ido da su da tayi, don samun su tayi zaune su ma duk cikin farin ciki, kuma ganinta kowa ya shiga mata adu'ar Allah ya raba lafiya.

Zaytuna da Samha sai tsokanarta suke yi wai ta zama uwar biyu.
tun daga wannan ranar kuma Fillo sai ta koma rayuwar gidan su Turaki, don ƙememe Maama taƙi barinta ta koma can gidanta tace sai cikin yayi ƙwari, duk ranar kwananta nan Turaki yake zuwa sai su tare a ɗakinsa na gidan.
Chapter 161 · 0% Book details