Sashe 149
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta ƙyar da suɗin goshi ta yarda amma da tuburewa tayi ita ɗakinta zata koma, don gaba ɗaya a tsorace take da shi, yay ta begging ɗinta, yana lallashi da ban haƙuri tukunna ta yarda tayi bacci ajikinsa.
washe gari da safe kafin ta farka har ya haɗa ma ta kayan da zata tafi da su acikin trolly, sannan ya dawo ya tasheta, ko da ta farka ƙin yarda tayi ta kalle shi, ta sauko akan gadon kawai ta wuce toilet kamar dai tana fushi da shi.
da ta fito yana zaune a bakin gado, ta fita daga ɗakin ba tare da ta kalli in da yake ba. shi ma ɗin kuma bai bi ta ba balle ya takura ma ta, kuma yanda kowa ke da zuciya za su iya yin faɗa, sai ya miƙe ya shiga toilet yay wanka yazo yana shiryawa, dan Mum tuni ta kirasa ta faɗa masa sun ɗauki hanya.
yana zaune yana saka takalmi Fillo ta dawo ɗakin, tunaninsa duk shiryawa ta tafi yi sai ganinta yay ta dawo ɗauke da tray, ta wuce ta dire akan table sannan ta ƙara fita.
ɗaki ta koma don shiryawa, tuni ya fiddo ma ta kayan da zata saka, su na ajiye akan gadon, yau ma abaya ya ƙara ɗaukota ma ta blue colour kalar boyel ɗin da taga ya saka, da murmushi a fuskarta ta ɗauka ta saka sannan ta zauna duba iyakar kayan da ya haɗa ma ta, sai kace mace babu abin da bai saka ma ta acikin trolly ɗin ba, which he knows she will need.
sai da ta gama shiryawa tsaf sannan ta fita ta koma ɗakin nasa sai zuba ƙamshi take yi, samu tayi har ya zuba tea a cup, yau ƙin yarda tayi yay feeding ɗinta, ƙarshe ma bata zauna kusa da shi ba, ta ɗauki soyayyan bread da ƙwai ta koma ɗaya kujerar, shi ko yaƙi bi ta kanta.
ba su jima wajen yin breakfast ɗin ba saboda lokaci da ke neman ƙurewa, sannan ya kira Bello a waya ya sanar masa zai biyo ta office sai ya wuce ya kai su airpot, haka suka fito dai a gidan babu wanda ya kula wani.
cikin lokacin da bai kai awa É—aya ba suka sauka a airpot na Taraba state, su na sauka Drivern gidan su Hajiya Ramla yazo ya É—auke su.
gidan na su babban family house ne, parlon Granny cike maƙil da ƴaƴanta da jikokinta, kuma kamar zaman anyi shi ne domin tarbar su, su na shigowa aka yi kansu ana yi musu oyoyo kowa sai murnar ganinsu yake, Granny na faɗin a matsa a bawa kishiyarta hanya ta iso, Fillo sai so take yi ta ƙwace hannunta daga riƙon da yay ma ta amma yaƙi har sai da suka shigo tsakiyar parlon tukunna.
Kowa sai zuwa yake yana rungumeta, da ma kowa ita ke ta so ya gani musamman waÉ—anda ba su sami zuwa dinner É—in su ba, kuma kowa sai yaba kyanta yake yi kamar za su cinyeta, ana faÉ—in Turaki yay dace da tsaleliyar mata, ita dai sai murmushi kawai take yi, musamman yacca taga kowa na farin cikin ganinta, tamkar ita ma da ma can a family É—in take.
a kusa da Granny ta zauna wacca ta kama hannunta ta riƙe, tana yiwa wata tsohuwa bayanin ai yana da wata matar amma sun rabu, da alama tsohuwar ƙanwarta ce don sun ɗan yanayi.
Tsohuwar tace,"yo wannan Tuzurun ma ai mata huɗu ya kamata a haɗa masa, sa'anninsa su na nan kowanne da yara amma shi sai yanzu yake aure, al'adar bature duk ta ɓata mana yara suyi ta zama suƙi aure".
Fillo ta ɗaga ido yanda ba za'a lura da ita ba, ta sauke su akan Turaki da ke can cousin sisters ɗinsa sun baibaye shi, tayi dariya tana kallon yanda ya riƙe wata ƴar Baby yana cewa da Mamanta ta karɓi kayarta kar tayi masa fitsari ko kashi, ta karɓeta tana faɗin taga yacca zai yi ranar da aka haifa masa tasa, ba kashi ko fitsari ba tumbuɗi kaɗai ya ishe shi, Allah na tuba kwana nawa suka rage.
kuma kamar ya san Fillo na kallonsa a lokacin, sai ya ɗago karaf suka haɗa ido, ya langwaɓar da kai ta sakar masa murmushi, shi ma yay murmushin yana kanne ma ta ido ɗaya, yau duk sai yanzu tayi masa murmushi, dan tun tashinta take faman cin magani, shi kuma bai takura ma ta ba dan ya san abin da yay ma ta ne jiya.
gida dai sai ya koma kamar gidan biki, don har wata walima suka haɗa wai ta murnar zuwan Mum, wacca tun bayan dawowarta bata sami zuwa ba, Fillo kam sosai taji daɗin zuwanta, kuma nan da nan duk sai ta sake sosai, irin Family ɗin nan ne masu saurin sabo, kuma masu sauƙin kai da mutunta wanda ya shigo cikin su.
da yamma su na zaune a bedroom ɗin Granny wata me suna Nilfat ta shigo, ta kalli Granny tace,"duk kinga balarabiya kin maƙale mata".
Granny tayi ma ta daƙuwa tana cewa,"ungo nan".
Nilfat ta ce,"na gode, ai ba zan bari muyi faɗa ba, dan lallaɓaki nake na bi ki europe nima naje na samo irin wannan sulɓin fatar taki da bata tsufa".
ta wuce wajen Fillo tana cewa,"ki je inji mijinki".
Hajjah Yayar Granny ta ce,"kije kice masa ba zata zo ba, ashe shi ma irin Ahmad ne bai da kunya".
"yaran yanzu ne fa, ai sai adu'a kawai, amma kunya ina suka ganta". cewar Granny.
"to Hajjah tafiya fa zai yi, ai sallama za su yi ba wani abu yace zai yi mata ba". Nilfat ɗin ta ƙara faɗa.
Hajjah ta ce,"kije kice masa yay tafiyarsa, dole ne sai sunyi sallamar, kaji min mara kunyar yaro, ko wani abu zai bata".
Nilfat tayi ƙofa tana faɗin,"ni dai ban taɓa ganin inda akayi irin haka ba gaskiya, ya zai tafi ba tare da yay sallama da matarsa ba, wallah idan ni ce sai ince ta fasa zama, in ɗau kayata mu tafi, yo in ma ba sallamar zai yi ba ina laifi anan dan miji ya nemi matarsa".
Fillo dai na kusa da Granny kanta a ƙasa, har ga Allah so take taje ta gan shi, tun ɗa zu rabonta da shi wai sun fita shi da wani Baffayo ɗan gidan Anty Hajar.
Mum ta shigo a lokacin, ta zauna tana cewa,"wai Babana zai tafi, jirgin ƙarfe bakwai zai bi, daga masallaci zai wuce".
sai ta kalli Fillo tace,"je kuyi sallama". sai ta kasa sakkowa, duk kunya ta kamata, ga shi ita ba waya ba balle tayi masa text tace ya tafi kawai, sai da Mum ta ƙara yi ma ta magana sannan ta sauko akan gadon ta ɗauki mayafinta ta fita.
a compound ta tsaya tana kalle kallen inda zata gansa, Fareeda na zance daga can wajen flowers ta ƙwala ma ta kira,"Antee".
Fillo ta É—aga kai da murmushi tana kallonta.
ta ƙarasa wajen na su, Farida tace,"ga wanda zan aura".
"masha'Allah". Fillo ta faÉ—a kafin su shiga gaisawa da Modi.
Farida ta ce,"mijinki ba?".
Fillo ta É—aga ma ta kai.
"yana É—akin Baffayo".
"ina ne É—akin?".
"ki zagaya ta wurin shukokin nan, É—aki na tsakiya me bishiyar ayaba a gabansa".
Fillo tabi hanyar da Farida ta nuna ma ta, tun daga ƙofar ɗakin ta san Turaki na ciki saboda ƙamshin turarensa da duk ya cika wajen, ta shiga ɗakin bakinta ɗauke da sallama.
Baffayo ne ya amsa sallamar, Turaki kuma ya É—aga kai yana kallonta, Baffayo ya fita a É—akin, ita kuma ta zagaya ta zauna akan kujerar da Turaki yake, ta shige jikinsa kamar yanda ya buÉ—e ma ta hannu.
"yau ni kike gudu ko?".
ta É—ago kai tana kallonsa ta ce,"kaima ai mantawa kayi da ni ka tafi wani wajen".
yaja hancinta,"munje gidan wani Kakanmu ne, ƙanin me sunana, da naje suna ta tambayarki nace za ku zo ke da Mum".
"to me ka siyo min?".
"É—a zu ba gani nayi kin saka fura agaba kina sha ba, ko irin ma ki tuna da mijinki a kusa".
"to a gaban su Mum É—in zance kazo ka sha?".
"ni ma shiyasa ai da naje Alhaji ya ban abin daÉ—i ban iya cewa zan ragewa Matata ba".
tai murmushi da kiran sunansa,"Turaki".
ya ce,"na'am Halima".
ta É—an bugi kafaÉ—arsa,"sunan fa Ummi ne".
yasa hannu ya rufe bakinsa,"Allah na tuba ka yafe ni".
sai kuma ya kama kumatunta yana cewa,"to ni ma ai sunan Abba ne kike faÉ—a".
"to ai dai ba ainihin sunansa na faÉ—a ba, Turaki na ce".
"ehh haka ne afiruwa".
ta turo baki gaba,"mene afiruwa?".
"É—an siririn mutum da za ki gansa kamar lamba É—aya, kin san one bata da kauri kwatakwata".
ta shiga kai masa dukan wasa, shi kuma yasa hannu yana karewa yana dariya har sai da ya kama hannayenta ya riƙe.
"ai indai ƙiba ce zan yi".
yace,"ni ma na san da wannan, aikina kawai zanyi".
sai kuma ya kalli agogon hannunsa ya ce,"za ki sa nayi late, jirgi ya tashi babu ni, tun ɗazu na aika ki zo kika ƙi, da nayi tafiyata ai".
"da ni kuma yau banyi bacci ba nayi ta kuka, saboda duk yau nayi kewarka ban ganka sosai ba".
"ehh ba ke bace naga yau duk kina ta shareni, kawai saboda na saka kinji daÉ—i jiya".
ba shiri tasa hannu ta rufe fuska, ya É—auke hannun yana faÉ—in,"idan kika tashi dawowa ki dawo da babban shiri".
"shirin me?".
ya goga hancinsa da nata yana jan haɓarta,"sai kin dawo ɗin dai, ke dai kawai kici tuwon dawar Innah kiyi ƙarfi".
ta cuno baki tana faÉ—in,"ni dai sai ka faÉ—a min shirin me?".
"shirin karatu".
"wanne karatu?".
"karatun manya".
"wanne karatun manya kuma?, ni ban sansa ba ai".
ya ɗora hannunsa saman cinyarsa ya tallabi haɓarsa yana kallonta ya ce,"karatun da zai mayar da ke cikakkiyar matar aure".
ta É—an murguÉ—a baki bata ce komai ba.
ya lanƙwasa yatsanta ya ce,"ni dai kici tuwon dawa da yawa kiyi ƙarfi, don karatun ba na wasa ba ne, Mum tace 7days za kuyi, ni kuma 7days yay min yawa, dan haka ki dame ta ku taho jibi".