Sashe 81
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ana idar da sallar juma'a a masallacin aka ɗaura auren Muhammad Habib Lateef da Rumana Hashim Lateef akan sadaki dubu ɗari uku. ɗaurin auren da ya samu halarta manya manyan ƙusoshin ƙasar nan, dan duk wanda yake da faɗa aji a ƙasar nigeria da wajenta sai da Mai Martaba ya gayyace shi ɗaurin auren, kuma cikinsu babu wanda ya turo wakilinsa duk da kansu suka zo.
duk girman masallacin fada sai da mutane suka cika shi taf, ciki da wajensa babu masaka tsinke, ango dai yana tare da mahaifinsa dan babu abokinsa ko É—aya, Bello ma da yace zai biyo jirgin safe Maama ce tayi sai taci ubansa matsawar yazo. ango dai kamar ba ango ba dan fuskarsa babu walwala, ga shi dai acikin mutane kuma inda ake É—aura aurensa, amma hankalinsa gaba É—aya na can kan Fillo, ina take? da kuma halin da take ciki.
bayan gama ɗaurin aure aka tafi reception, inda ɗumbin jama'a suka ci sukai hani'an, dan babu wanda zai ce bai goge haƙori da naman kaza ba. ana dawowa daga reception kuma aka koma can gidan mai martaba, cikin masarauta kenan, duk ta yanda Turaki yaso ya zame ya zille ya tafi gida abin yaci tura, dan Baffa na riƙe da hannunsa sai nunawa jama'arsa shi yake cike da tsantsar farin cikin da ba zai misaltu ba, shi kansa Turakin sai da yaji tausayin mahaifinsa, bakin Baffa sam yaƙi rufuwa, da zarar sun gaisa da mutum zai nuna masa Turaki yace,"shine babban ɗan nawa, asa masa albarka". haka ya dinƙa yawo da shi yana nunawa jama'arsa da jama'ar mai martaba.
Turaki kam ya koma kamar yaro, bai sami salama ba sai da suka dawo fada, dan iyakar wanda suka dawo fadan duk Æ´an'uwa ne, yana jin wayarsa na ta buga ringing daga Maama sai dai babu ta yanda za'ai ya É—auka.
acikin fadar Mai Martaba ne zaune daga tsakiya akan royal chair, sai Hakimi a kusa da shi ta hannun dama, sai Baffa a kusa da shi ta hannun hagu, sannan Falmata a kusa da shi sai Boɗejo daga kusa da hakimi ta wani hakimci ƙafa ɗaya kan ɗaya cikin alkyabba me ƙallin bala'i, sai ɗaukar idon jama'a take, bakinta yaƙi rufe haƙwaran makka ɗinta guda huɗu duk a waje.
Mai Martaba ne ya fara doguwar nasiha ga amarya da ango akan zaman aure, bayan ya gama ya damƙa amanarta a hannun mijinta, ya kuma yi musu addu'ar samun zaman lafiya da samun zuri'a ɗayyiba. bayan ya gama Hajiya Boɗejo ta ɗora da nata, tayi doguwar nasihar aure da babu wanda jikinsa bai amsa ba a wajen hatta Turaki, daga ƙarshe kuma sai ta fashe da kuka tana zuba musu adu'oi iri-iri.
bayan ta gama Hakimi ma yay nasa, bayan ya gama Baffa yay musu tasa, sai a sanda yake yi musu nasihar ne kawai Turaki sai jin hawaye yayi ya sauko masa ba tare da sani ba, daga ƙarshe Inna Falmata ma tayi nata.
bayannan kuma aka rarrabawa ƙur'ani da littafan adu'oi. daga nan kuma aka ɗauki amarya akayi cikin gida da ita ana batun gobe idan Allah ya kaimu za'a shiga sauran hidiman taron biki.
Turaki na fitowa daga fada ya fice bai bari sun haÉ—u da Baffa ba, iyakar kyau dai yayi kyau kowa ya gansa yaga sabon ango amma sam babu wannan annurin na farin ciki a fuskarsa.
Gimbiya Ilham kam tun sanda tai ƙoƙarin kama hannun Turaki taji yanda ya make hannunta taji jikinta yyi sanyi, musamman da ta kalla fuskarsa taga ya murtuke kamar wanda aka yowa aiken mutuwa, kace bai taɓa dariya ba a duniyarsa.
Turaki na isa gida Hajiya Madina tasa key ta kulle side É—inta dan bata ma so wasu Æ´an bani ka iya É—in suzo mata, ko kuma Baffa ya dawo yace zai shigo.
hakan ko sai data faru, mutane suka dinga zuwa gidan suna juyawa, Mai Gadi na faÉ—a musu abinda Hajiya Madina tace masa na cewar basa nan, a same su acan masarautar.
to haka dai ranar Hajiya Madina da yaranta suka yini cikin ɓacin rai, iyakar yin Baffa ya gana da matarsa da yaransa Hajiya ta toshe duk wannan ƙofar, sai haƙura yayi dole, dan ko a washe gari sai gidan Hakimi ya tafi yay breakfast dan shima irin Turaki ne bai iya cin abincin restaurant ba.
kuma a ranar da daddare BoÉ—ejo tazo ta tayar da wuta a gidan, kamar zata cinyesu saboda masifa akan Turaki sai yaje Dinner, har da cewa,"aini Madina ban san ke fitinanniya bace sai yanzu, ashe kin ma fi Fulani Azima haÉ—ari, to wallahi dai akan auren jikana da jikata aniyarki ta koma miki".
Maama dai ɗaga kai bata yi ta kalla Boɗejo ba balle ta tanka mata, har ta gama zazzaga masifarta da yaɓa magangunta.
Boɗejo ta tasa ƙeyar Turaki a gaba tace,"wuce motar Nasiruddeen na waje suyi maka rakiya, in an hana ƙawayenka zuwa ai kana da ƴan'uwa".
sannan ta juya kan su Zaytuna tace,"ku kuma ku wuce muje, haka kawai za'a tusa muku baƙin hali a zuciyarku, tsakani da Allah mene abin baƙin ciki a wannan aure banda ma dai zuciyar mutum ba ta da ƙashi. to kuyi gaba muje ba sai kunyi wata kwalliya ba, idan ban isa da wasu ba ku ai na isa da ku. ƙulla auren zumunci kuma yanzu na fara, kuma inga uban da zai sa Turaki ƙaro aure dan naji ana ƙishin ɗin haka, in ban ba'asa naje na bankawa ƴar mutane wuta ba".
haka ta saka su a gaba har Khalil da su Samha da suka dawo a yau suka wuce suka tafi. wajen dinner dai iyakar haɗuwa ya haɗu, amarya da ango sun haska guri, amma ko kaɗan fuskar ango bata murmusa ba, MC ma da yay batun liƙi sai Khalil ne ya fito ya wakilce shi ya watsa bandir ɗin ƴan 500 har guda biyu.
kuma fuskar ango kaɗai zaka kalla ka hasko tsantsar rashin son auren a tare da shi, Gimbiya Ilham kam da ƙyar ta iya controlling hawayenta ta dinƙa yaƙen ƙarya, saboda gaba ɗaya ta fahimci Turaki ba auren ne baya so kaɗai ba ita kanta ba sonta yake ba.
bata tabbatr da hakan ba sai after an tashi daga dinner sunzo shigo mota yace,"ki bar cusa kanki gare ni, domin ni ba sonki nake ba, cusa min ke akayi. idan kuma wancan son kike tunani har kika iya amfani da shi kika sa aka ƙulla wannan auren to kinyi babban kuskure, domin ni son ƙanwa nake miki ba shirmen so irin naki ba. and again ki san da cewar baki da matsuguni a zuciyar Turaki dan already wata da ta fiki komai ta cike wannan gurbin".
wannan maganganun nasa yasa tayi kuka ta gode Allah a wannan daren, kuma sai ta dasa zarginta akan Gimbiya Aisha.
washe gari ma kamar ba zata je Cocktail party ba amma haka dole taje, shima kuma taga abinda yafi na jiya a wurin Turaki, don opalli ya nuna kowa ba auren so suka yi ba.
ranar lahadi da za'a kaita tamkar ta shiÉ—e haka taji, tunanin ta inda zata fara zama da shi kawai take yi, Mai Martaba da Fulani Azima su suka kaita gidan anan Estate É—in su Turaki, daga gidansa zuwa nasu babu nisa, gidan ya gaji da haÉ—uwa kamar a turai, bai san sanda Baffa ma ya gina gidan ba.
shima Turaki Baffa da Maama ne suka masa rakiya, kuma banda cewar É—anta za'a kai babu abinda zaisa taje. ko kula Baffa bata yi ba har suka je, yana ta janta da hira tai banza da shi sai Turaki da take kulawa, tana faÉ—a masa ya cire damuwa saboda yanda duk ya rame.
acan gidan Amarya da Ango ma Hajiya Madina kallon inda Mai Martaba yake bata yi ba balle wata Fulani Azima, bata san ita Fulanin ba so take ba. haka suka gama yiwa ma'auratan nasiha da adu'a sannan suka baro su.
kamar yanda sunnah ta koyar Turaki suka yi nafila tare da matarsa, bayan sun idar ya kama kanta yayi adu'a, sannan ya gabatar mata da abinci.
ita taci dan shi bai iya cin komai ba, sai bayan da ta kammala ya tashi ya bar ɗakin ya wuce parlo ya zauna, tunda ya fito kuma yake ta tunanin Fillo, Allah kaɗai yasan me yake ji a zuciyarsa. ya jima zaune anan daga baya ya tuna fa cewar aure aka yi masa and amayar tana ɗaki, ko kaɗan baya ƙaunar ganin Ilham, kuma baya jin zai iya haɗa jiki da ita su kwana a shimfiɗa ɗaya, amma kuma ba shi da yanda zai yi, ba shi da wani hope, dole ne zai bi koyarwar addini, zai yi amfani da ilimin da yake da shi dan ganin bai kaucewa addininsa ba kuma bai ƙi yin koyi da sunnar ma'aiki ba a daren farko.
babu zancen ya ƙauracewa shimfiɗarta a yau dan zai iya jefata a halaka, tunda addini ma ce yay ka ƙauracewa shimfiɗar mace a sanda tai maka laifi in har kayi wa'azi taƙi dainawa, Maganar kauracewa a shimfida sai idan har ta yi wani laifi ne , kuma kayi wa'azi taƙi dainawa, abinda musulunci yace kenan game da ƙauracewa shimfiɗar mace.
dan haka a wannan dare dai Turaki ya mayar da Ilham cikakkiyar mace, ba dan ya so ba, kuma ba dan yana farin ciki ba, kuma ba dan yayi farin ciki ba da samun budurcinta ba. haka kuma rashin sonta bai sa ya zalunceta ba wajen kusantarta, ya tafiyar da ita a hankali ta yanda yasan ba zai ƙuntata mata ba, sai dai hakan ba shi ya hana Ilham kuka sosai ba a wannan daren.
*Vote, Comment & Share.*
[8/31, 00:32] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
_Shafin gaba É—ayansa sadaukarwa ne ga duk wani makarancin littafin *LULLUÆIN BIRI*, ina jin daÉ—in yanda kuke bibiyar littafin nan, alkhairin Allah ya isa gare ku._
*34*
da asuba Turaki na dawowa daga sallan asuba kira na shigowa wayarsa, babu suna ajikin lambar dan haka ya tsaya yana kallonta da son ya fahimceta, ganin ba lambar da ya taɓa sani bace ya ɗaga.
yana karawa a kunnensa Gimbiya Aisha ta kwaÉ—a sallama cikin dodon kunnensa da irin muryar da kana jinta kasan tasha uban kuka.